← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 127

Sashe 89

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sister Habiba tace "ya za'ayi in sani, amma nima ina zargin hakan wallahi, Allah sarki tana murƙusus amma fatanta Allah ya bar mata cikin ta, Insha Allah be zube ba, ko akanme ze damu cikinta ya zube oho"

"Hmm kedai bari, shida wannan Bulaman dama basu fiye ƙulla abun Arziki ba, naga shiya kawota kika bibiya karuwarsa ce, ko kuma dai cutarta sukayi suke so su rabata da cikin, kin san ɗan Bulaman Fahad ya saba kawo mata nan a cire musu ciki"

Sister Safiyya tace  "ai kedai bar masu kuɗin nan kawai, Allah dai ya shirya naga ta samu bacci, gashi babu kowa a gurinta, balle idan ta farka a bata Abinci"

Sister Habiba tace "ai kamar yadda kika faɗa ɗinne, kika bibiya dai ba ta hanyar Allah aka samu cikin ba, shine suke son su zubar mata ta ƙarfin tsiya"

Baiwar Allah, ita Widad sam bata san meke faruwa ba, wani galabaitaccen baccine ya ɗauketa, wanda fal yake da mafarkin Yusuf cike da bege da shauƙin son ganinsa, se kuma mafarkin daddy da take yi.

Ɓangaren Ramlah kuwa, taga kwata kwata kusan Fahad yayi dumping ɗinta aside, kwata kwata baya ta tata yanzu, dan haka ta shirya da kanta ta tafi Hotel ɗin da yake zuwa, tana zuwa kuwa ta sameshi da wata mace a ɗakin, Ranta ya ɓaci matuƙa ta dube shi tace  "Lallai Fahad, ka cika tantirin butulalle, a wani postion ka ajiyeni ma tukuna?"

Fahad yai murmushi yace "postion É—inki dai na farko, a nan ns ajiye ki, me kike tunani"

"dalla saurara, karka gayamin maganar banza mana, ban gane postion É—ina na farko ba, ina maganar Auren mu da kai?"

Fahad ya kwashe da dariya yace "haba tawan, meye muma na É—aga jijiyoyin wuya haka? Maganar Aure tana nan mana, ki bari idan na Auri Widad kema se inzo daga baya in Aure ki"

Ta kalle shi tace  "Fahad, yau wace irin giya ka Shane haka? Data gaya maka ƙarya wadda harta saka ka kalli idona kake gayamin maganar banza da iska?"

"irin wadda na saba sha ce dai, sedai ban sani ba ko nasha expired ne"

"Lallai Fahad kana wasa, baka san abunda ka aikata me ze haifar ba ko? Ds kyau wallahi ka É—ebo ruwan dafa janka in dai Ramlah ce, zakaga tsiya"

Ta juya buguzun buguzun tai waje, bata zame ko 'ina ba se ofishin Bulama, tana zuwa ta tarar yana aiki a Office, sedai tayi mamaki ganin É—inki haka a fuskarsa, koda yake ba wannan yakawo ta ba.

Ya É—ago ya dubeta yace "Ramlah lafiya kuwa? Ya kika shigomin Office haka?"

"Kamawa tayi na shigo a haka, ina maganar ds mukayi da kai?"

"wace maganar kenan?"

"Maganar da mukayi akan wannan mutumin, da yake iƙrarim shi mahaifin mu ne, kace zaka ɗau mataki akansa, amma har yanzu bani da tabbas na ka ɗauka kokuwa?"

"Banda abunki Ramlah, nima fa ban san takamaimai inda yake zaune ba, ta yaya zan É—aukar miki matakin? Nasa aje inda nasan shi, amma baya nan baya zama a guri É—aya sam"

Tai tsaki sannan tace  "waima ni wane irin hatsari ne dashi haka, wanda yasa Mummy ke tsoronsa?"

Bulama yace "wannan tambayar ai ita zakiyiwa bani ba, kije ki tambaye ta zata gayamiki komai"

Tai ajiyar zuciya, tare da jinjina kai tace "idan kai baka É—au mataki ba, nika gayamin inda yake in É—au matakin daya dace dashi mana"

"Haba Ramlah, kema kin san da nasan inda mutumin man yake aida da kaina zam É—auksr miki mataki akansa"

Kallon Bulama kawai take, ba wai dan ta gamsu da abunda yake faɗa ba, ta suri jakarta tai waje tana ƙwafa.

Fafur Nurat ta dena fitowa ko falo, saboda karma su haɗu da mahaifinata yai mata zancen komawa ƙasar waje.
Dayake yau Weekend ne sam be fita ba, yana gida amma still bega gilmawar Nurat ba, ya tafi ɗakin matarsa ya tarar tana kwance tana chatting, yace  "wai ina yarinyar nan ne? Wunin yau banga gilamawarta ba"

Ta tashi zaune tace "tana ɗakinta mana, kasan halimta wasu lokutan bata san shiga mutane, tafi son zaman kaɗaici a ɗakinta, balle kuma ka ƙwace wayoyin ta"

"Ina fatan dai tana nan tana shirin tafiya?"

"tafiya ina? Ai wannan maganar kuce kai da ita"

"kamar yaya kenan?"

"kamar yadda nake gayamaka mana, kai ds ita kukayi magana, dan haka babu ruwana ka tambaye ta idan tana shirin da kanka"

Ya jinina kai, kwanan nan yaga zam iyalin nasa sun dena tsoronsa kamar yadda suke tskronsa a baya, ya rasa dalili.

Yana shiga É—akin Nurat, ya tarar tana tilawar Al'qur'ani mai girma, ya jira ta kai aya ta É—ago ta kalle shi, dan taga magana yake son suyi.

Yace "dama zuwa nayi in ji ko kina shirin tafiyar nan kuwa? Jirginku ze tashi jibi in Allah ya kaimu fa"

Nurat ta miƙe taje ta ajiye Al'qur'anin ta sannan tace "nifa ba inda zanje Daddy, tsawon shekaru ina maka biyayya, dukda yi maka biyayya umarnin Allah ne, amma nima kayimin adalci mana, wallahi idan na tafi karatun nan bashi zanyi ba, rayuwata kawai zanyi"

A fusace  yace "ni kike gayawa haka?"

"wallahi Daddy kace sena tafi guduwa zanyi daga gidan nan, ni bana son tafiyar"

Ya ƙura mata ido na wasu mintuna, sannan yai ƙwafa ya tashi ya fita.

Widad tana gadon Asibitin nan, ko iya miƙesa ba tayi, amma a haka aka sakata a wheel chair, Aka kaita mota aka maida ita wannan gidan da ake ɓoye ta.

Haka aka maida Ita, yau s bsta wannan maganin gobe a ɗurma mata wannan Allurar, haka take ta fama ga ciwo yaƙici yaƙi cinyewa, banda izayar da Bulama ke mata akan ta bada takaddun nan.

Kwanci tashi asarar rai, Yusuf ya cika sati uku cif a gidan yari, rana ta zagayo aka koma dashi kotu domin ci gaban shari'arsa.....

IDAN KIN SAI LITTAFIN NAN KE KAÆŠAI KIKA SIYA, KUMA AMANACE TSAKANINA DAKU, IDAN KUKA FITAR BAKUMIN ADALCI BA, TUNDA BAMUYI DAKU ZAKU FITARMIN BA.

AYSHERCOOL
07063065680
11/23/21, 10:26 PM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

134_135

Yauma kotun a cike take maƙil da ɗan Adam, 'yan jarida kota ko' ina, ga 'yan sanda da sauran mutane domin sauraren cigaban ƙararar, seda akayi kusan shari'a uku sannan aka gabatar da ƙarar Yusuf, Barrister Sadik ya fito ya sake gabatar da kansa a gaban kotu, sannan yace ze fara gabatar da shedun su akan Yusuf.

Barrister Sadik yace  "zan fara gabatarwa da kotu shedarmu ta farko akan cewar Yusuf shine yayi garkuwa da 'yar gidan Alhaji Nasir Daula"

Nan Barrister ya kira wani mutum, mutumin ya fito ya tsaya ya fuskanci kotu, Barrister ya taka gaban sa yace  "ko zaka iya faɗawa kotu sunanka?"

Mutumin yace  "Sunana Sada"

"Kasan wannan" yai mavanar yana nuna masa Yusuf.

Sada yace "eh nasan shi"

"Meye a tsakaninka dashi?"

Sada yace  "Eh nasan shi, sunanshi Yusuf, yana kawomin gyaran motoci"

Barrister Sadik yace  "yaushene ganinka na ƙarshe dashi?"

"Eh ganina dashi na ƙarshe shine, ranar daya kawomin wata mota yace in siya, nace masa gaskiya ni bana siyan mota sedai zan haɗashi da masu saida mota, bayan na haɗashi dasu se aka kawon lambar motar da na kawo maka, wadda ta kasance lambar motocin gidan Daula ne "

Aikuwa aka kawo lambar mota aka nuna a kotu, wannan lambar ita ce lambar dake jikin motar da Yusuf suka fita aka sace su a cikinta, tunda Yusuf yake be taɓa ganin wannan mutumin ba me suna Sada, amma yau an samoshi an masa sharri.

Yusuf yai shiru ya dafe kai, ya kasa cewa komai.

Barrister Khalil yace  "Sheda na gaba da zan gabatarwa da wannan kotu shine wanda ake zargin tare suka haɗa kai da Yusuf suka sace 'yar gidan Nasir Daula wato Saleh"

Aka shigo da Saleh, yana takawa da kyar wanda gaba É—aya ya fita a hayyacinsa, kallo É—aya zakayi masa kasan bashi da lafiya aka rakitoshi.

Akaje aka tsaida Saleh, Barrister Sadik yace  "Malam Saleh, ko zaka iya gayamana waye kai a gidan Daula?"

Cikin murya ƙasa ƙasa yace  "Ni tsohon sojane, kuma hadimi a katafaren gidan Daula"

"Waye wannan?" ya nuna masa Yusuf.

"Shine direban 'yar gidan Daula, shi yake kaita duk inda zata je"

Barrister Sadik yace  "ya akayi kuka haɗa baki kuka sace ta, harka basu mafaka?"

Saleh ya kalli Yusuf, ya sunkuyar da kai yace  "Bayan Yusuf yayi duk shirin daze, ya nemi da ina nema masa inda ze zauna ya ɓuya, ba tare da an gano inda suke ba, yayi Alƙawarin ze bani kuɗi, ni kuma na yadda na amince, daya sato ta na gaya masa inda zamu haɗu, shine na kaisu wannan ƙauyen daga baya ya je ya saida motar, muka raba kuɗin "

Yusuf ya ƙurawa Saleh ido, amma Saleh ya kasa ɗaga kai ya kalli Yusuf, ya sunkuyar da kai yai shiru, yakasa kallon Yusuf, shima Yusuf bashi da zaɓin daya wuce ya sunkuyar da nasa kan, Umma se kuka take tana mamakin, ya za'ayi ace ɗantane yai wannan abubuwan haka? "

Barrister Khalil yace 'idan kotu ta bani dama, zan gayyato Malam Audi, wanda shine Saleh ya nemo ya ɗauki Yusuf da' yar gidan Daula, a ƙurƙurarsa zuwa cikin ƙauyen da akayi garkuwa da ita"

Malam Audi ya fito shima, Barrister Khalil yai masa tambayoyin duk daya dace yai masa, shima ya bada amsa, kamar yadda aka buƙata.

Barrister Khalil, ya kira doctor Mustapha wanda shine Likitan daya duba Widad lokacin da aka harbeta, shima ya fito ya tsaya ya bayyana sunansa a gaban kotu.

Barrister Sadik yace  "Doctor Almustapha, kaine Likitan daya karɓi 'yar gidan Daula, lokacin da Wannan bayin Allah suka kaita Asibitinka ha akayi?"
Chapter 89 · 0% Book details