Sashe 55
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haɗe rai tayi sosai tace "nice ma kake gayawa haka? Dole kace ganina ba alkhairi bane, kuma ai ganin naku ba alkhairi bane ba, malam ɗana ya ɓata Anwar, tun jiya ban san inda yake ba, idan wata ƙulla ƙullar kuka haɗa, kowani makircin to kufito min da ɗana, dan babu ruwansa a harƙallar da mukeyi "
Alhaji Munir yace " to akama É—anki ayi masa me? Har akwai abunda za'ayi aji tsoron gayamiki ne? Kije can kineme shi, idanma a cikin namu ne toni dai bada yawuna ba, dan ban san anyi ba, sedai ko Musa kowani amma ni ban san komai ba kam"
"to bari kaji in gaya maka, idan ma ka sani ka rainamin hankali wallahi duk abunda nayi maka kai ka ja, dan wallahi sena saka mutum dana sani da cizon yatsa"
Alhaji Munir ya taɓe baki yace "a banza ƙiba a kunne, ƙarewa 'yar gidan Daulama duk zare idonta da hura hanci shekaru kusan Goma sha biyu ta kasa gano mu balle ta ɗau mataki, se wata ke zakizo min da wannan ƙaramar barazanar taki dan ki firgitani, kije kiyi duk abunda zakiyi karki fasa, tunda naga alama daga ke har Musa kun fara hauka"
"Shikenan, zakaga hauka ganin idonka, wallahi idan da saka hannunku kika sacemin yaro wallahi se kunyi danasani, zan nuna muku masifa da kaidin mace, shima Musan zanje in kasa masa warning, tun wuri ka kiyaye ni, ku fita daga idona kallon ku kawai nake yi"
Ta juya a fusace ta koma inda motarta take, Alhaji Munir ya bita da ido, yayi tsaki ya koma ciki yana jinjina hauka da rashin hankali na mata.
Daga nan gurin Alhaji Musa taje a Office ɗinsa na neman zaɓe, nan ma suka fafata, sukayiwa juna kaca kaca shi da ita, sannan ta bar gurin rai a ɓace.
Murtalane yake gyarawa Anwar ɗakinsa wasu lokutan, wani lokacin kuma da kansa yake gyara abunsa dan shi babu ruwansa, be ɗau duniyar da zafi ba sam kamar yadda mahaifiyarsa da' yan uwansa suka ɗauka, Nura ya shiga yana gyara ɗakin Anwar, yaga takadda a ƙarƙashin fulon Anwar ya ɗakko tajadar ya buɗe yakaranta ta tsaf sannan ya ɗauka ya nufi cikin gidan.
Suna zazzaune a falo sunyi jugum jugum, suna jimami da tunanin inda za'a ga Anwar Murtalah yayi sallama.
Suna kallonsa amma ba wanda ya amsa masa, a fusace Hajiya Halima tace "dalla malami meyene, kamar baka san a halin da muke ciki ba, kazo ka samu a gaba da sallama, meyene jarababbu kawai?"
Murtalah yaji haushin abunda Hajiya Halima tayi masa, koda yake imda sabo sun saba, hantara da Wulakan da cin mutunci, sun saba ganinsa dan abunda wanda ya ɗaukesu aikin baya musuma yanzu yi musu ake sedai haƙuri, amma ya dake yace "Dama ba wani abu bane, ina gyara ɗakin Anwar ne na tsinci takadda a ƙarƙashin fulonsa, shine nace bari in kawo miki"
Tasa hannu ta karɓi takaddar sannan tace "to ai seka tafi ko? Ko a gabanka zan duba kaga reaction ɗina, aji daɗin gulma, munafukai kawai 'yan sa ido"
Sum sum Murtalah ya fice yana ƙunƙuni, a ransa yace "Ubangiji Allah ya kawo mana ƙarshenku, jarababbiya dake da wannan matsiyatan' ya'yan naki masu kama da jakuna, da bakinsu kaman na yaran hankaka'
Nurane yaji Murtala na zage zage da tsine tsine, yace  " kai kuma kai dawa? "
Murtalah yace "nida wannan balamar matar mana, daga zuwa na tsinci takadda a ɗakin ɗanta naje kaimata, ta kama zagina tana cemin munafuki, ni dana san hakane ma da wallahi ban kai mata takaddar ba, inga ta tsiya"
Nura yace "kaima meya kaika? Jiya Daga Isa ya ɗanyi mata tunanin albashi, ta zage shi tsaf taci masa mutunci, hadda wai tunda ba gidan ubanmu bane, wanda ya gaji yaga baze iya ba ƙofa a bude take ya ƙara gaba, kajifa se kace ita nata gidan ubanne, ko daga gidansu tayi gammo tazo dashi, aimu tsakanin mu da wannan matar sedai Allah ya isa wallahi "
Murtalah yace " Allah ya isa me 'yanci makuwa wallahi, dan koni na mata ba adadi banza tana tafiya a karkace, ita ba É—a' a 'ya' ya babu tarbiyya, se kayan É—uwawu kamar zata kai kayan tusa birni"
Sosai Nura ya dinga dariya yace "Wallahi idan ta jika seka bar gidan nan, kaima ka sani yaseen, amma fa ka iya ba'a da cin mutunci"
Murtalah yace "to takorenin mana, ai yanzu gidan Daula sunan ne kawai, amma babu komai a ciki duk a bushe muke, saboda wannan iblishiyar matar, kana gani yanzu duk tarin jama'ar dake zuwa gidan nan yanzu babu kowa saboda baƙin halinta, wannan da a aljanu tazo ba shakka se ace itace babar sheɗan"
Nura yai dariya kamar cikinsa zs ciwo, ganin yadda Murtalah ya harzuƙa sosai se bala'i yake yana zage zage da rashin mutunci da gani kasan an kai shi maƙurar bangone.
Nura yace "malam kar dai kayi saɓo, a gidan ubanwa ka taɓa jin ance sheɗam yana da uwa, hattara dai"
"Bari Nura rainane ya ɓaci wallahi, Allah yasaka mana wallahi, Allah ya nuna mana ranar da dubunta zata cika a tarkatata a koreta da wannan iblisan 'ya' yan nata"
Nura yace "Ameen dai, manyan iblisai makuwa, dan wannan babbar me soyayyen ido shaye2 take yanzu, saura ƙiris shekaranjiya tabi ta kan ƙafar Isa da tayoyin mota, Allah ya temake shi yai saurin matsawa kuma ta fito daga motar, ta zage iyayi da kakaninsa tsaf sannan tabar gurin nan tana maye "
Murtalah yace " haka zasu ƙare, saura kuma hauka da tamɓele, tunda haƙƙin mutane suka san susa a gaba suci babu imani babu tausayi "
Hajiya Halima kuwa tana buÉ—e takaddar, taci karo da rubutun Anwar kamar haka
 " *_Asslam Alaikum warahmatullah zuwa ga mahaifiyata, nasan lokacin da zaki riski saƙona nayi nisa da gida, nisam da bana tunanin zan iya waiwayar gida a kwanan nan, na bar gidane saboda faɗar ma'aiki salallahu alaihi wassalam, babu biyayya ga abun halitta gurin saɓawa Mahalicci, dan haka bazan iya jure cigaba da zama daku ba ana aiakta abunda be kamata ba, nasan idan nayi Yunƙurin yi miki nasiha ba zaki saurareni ba, kin zaɓi lalacewar 'yarki saboda tana miki hanya gurin tara dukiyar Haram, kin fifita akanmu wanda kema kin san hakan ba dai dai bane, kuma kina ɗauki ɗai ɗai ga kayan mutumin daya yayi sanadiyar fitarmu daga masifar talauci zuwa arziki, kin haɗa kai da maƙiyansa ana cutar dashi, nayi dana sani nayi kuka da bincike na ya tabattar min da dake aka haɗa baki komai yake gudana tsakaninsa da maƙiyansa, kaicon wannan butulci naki Mummy, ni bazan iya cigaba da zama daku ba dan haka na bar muku gidan, dama bana ubana bane ba, ina miki fatan Alkhairi dake da ƙannena a duk inda kuke, Allah ya sadamu da alkhairi, ɗanki me ƙaunarki har kullum ANWAR *_
Jikintane ya hau tsuma tana rarraba ido, yayin da wani irin gumi from no where ya shiga tsatsafo mata, ta dinga rarraba ido kamar shege a rabon gado.
Ramlah tace "Mummy lafiya kuwa, wetin inside that later?"
Miƙo mata tayi, domin idinta ya gane mata, Ramlah ta karɓa ta shiga karantowa a fili, tana zuwa ƙarshe ta yarda takaddar tace "shikenan munshiga uku Mummy, wallahi tonon asirinmu yazo, dan abune me sauƙi a gurin Anwar ya tona mana Asiri, kin san halinsa Mummy, yau munshiga uku, wayyo wallahi har cikina ya fara ciwo"
Amal tace "wannan shi ake kira tashin hankali wanda ba'a samasa rana, ina muka kama tunda wannan me iƙrarin ustazancin ya san abunda ake ciki"
Hajiya Halima ta goge fuskarta tace "ni tunanina a gidan ubanwa yasan wannan maganar? Waye ya gaya masa? Tsawon shekaru goma sha É—aya ana abun nan a sirrance cikin rufin Asiri, waye ya tina min wannan Asirin haka ni Halima?"
Ramlah tace "Mummy ba wannan tunanin ya kamata kiyi ba, tunanin meye mafita yakamata ayai, tunda sanin inda ya samu labarin bashi da amfani"
Hajiya Halima tace "toni ta ina zan fara ne? Ta ina yakamata infara neman mafitar? Na farko ban san inda ya tafi ba, kuma tabbas abune mawuyaci ya iya ɓoye abun nan yakasa gayawa wani, ke ni gaba ɗaya na rasa abunyi wallahi, kuma ɗazun nan naje mukayi kaca kaca dasu Alhaji Munir, da Alhaji Musa na zata su suka sace shi, ni wallahi da iya tafiyar yayi da sauƙi, amma sanin wannan abubuwan yafi komai masifar ɗagamin hankali, kar Anwar ya tona min Asiri in lalace a bakin duniya"
Ramlah tace "aida iya lalacewa a bakin duniya ne da sauƙi Mummy, idan Asiri ya tonufa se komai ya watse ya lalace manya manya abubuwa ne zasu tonu, wanda baki isa kici bulus ba"
Cikin tashin hankali Hajiya Halima tace "Au nikaÉ—ai ma banda ku?"
Ramlah tace "Mummy koda mu koba mu, ai laifinki yafi namu yawa, duk abunda mukayi kece kika samu a hanya, yanzu mafita É—aya ce, kije ki samu su su Alhaji Harunan, ku sake sasantawa dama kun saba faÉ—a ku shirya ai, kuje ku sasanta kunemi mafita, dan wallahi Asirin ki ya tonu nasu ya tonu dan se mun faÉ—i komai "
" Kai Amma wannan yaro akwai shege me baƙin hali, kamar duk fafatukar nan ba danku nakeyi ba? "
Amal tace " Mummy amma kin san halinsa, dama da kuÉ—in nan sun samu ban san yadda za'ayi dashi ba, dan kema kanki kin san baze cisu ba"
Halima ta zauna kawai murza goshi take yi, saboda tashin hankali da damuwa.
Widad fafur taƙi Yusuf, zaman ɗakinma ta ƙiyi, ya dafa Abinci da safe amma taƙici, ƙarshe ma ta koma ɗakin Gwaggo, ta hau gadon Gwaggo tayi kwanciyar ta, Yusuf ya rasa ta ina ze fara yiwa Widad bayani, ta ina ze fara nuna mata yana mata son da baze taɓa juya mata baya akan wani abu da takeso ba muddin be saɓawa ubangiji ba? Yana da dalilinsa me ƙarfi ya zeyi tagane gaba ɗaya ta fututtuke taƙi saurarensa.
Haka ya shirya ya fita, se bayan ya fita ta koma ɗakin ta gyara, ta barmasa Abincinsa taƙi ci, da yamma ɗalibai suka shigo karatu gurinta, sukayi karatunsu har kusan magariba sannan ta sallamesu.