← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 127

Sashe 110

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khalil yace "ko kana da sheda?"

Yusuf ya girgiza kai, alamar a' a.

Khalil yace "cigaba ina jinka"

"Matar Alhaji Nasir, tana da wani ɓoyayyen nufi akan Widad, suna bata maganin gusar da hankali, sannan suna da wani nufi akan dukiyar Alhaji Nasir, dan akwai babbar 'yarta data taɓa cemin in bata password ɗin Banki na' yar Alhaji Nasir"

"ya akayi kasan password É—in nata kai?"

"Saboda tana aikena, Na kanyi kwanaki da ATM É—inta a hannuna"

Barrister Saminu ya mike yace "Objections sir, wannan tambayoyin da Barrister kewa wanda ake ƙara, basu da tushe balle makama kame kame ne kawai sukeyi, dan haka ina Roƙon wannan kotu me Alfarma, da tayi watsi da wannan magana da wanda ake ƙara yake faɗa"

Cikin zafi Khalil yace  "ina da tabacci da ƙwararan shedu akan abunda wanda ake ƙara gaskiya yake faɗa, idan kotu ta bani dama ina son ganin Hajiya Halima, matar Alhaji Nasir Daula, don gabatar mata da wasu tambayoyi"

Aka bashi dama, Hajiya Halima ta fito, gaba É—aya ta tsoste tsufanta ya fito jikinta se rawa take yi, bayan ta tsaya Barrister Khalil ya nemi ta gabatar da kanta, ta gabatar da kanta a gaban kotu, Khalil yaje gabanta ya É—akko wata takadda a aljihunsa, ya ajiye a gabanta yace "kin san rubutun waye wannan?"

Jikinta ne ya hau rawa, wasiƙar da Anwar ya bari ce, ta kalli Khalil a razane ta girgiza kai tace  "A'a ban sani ba"

Yace  "waye Anwar a gurinki? '

Tace " É—ana ne"

"kina nufin bashi ya rubuta wannan takaddar ba?"

Ta jinjina kai alamar eh, Khalil ya juya ya kira Murtalah, Murtalah ya fito ya tsaya, Khalil yace   "kotu na buƙatar ka gabatar da kanka, sannan ka faɗi abunda ka sani"

Murtalah yace  "Sunana Murtalah, kuma ɗaya daga masu aiki a gidan Alhaji Nasir Daula, wata ɗaya zuwa biyu baya, naje ɗakin Anwar zan gyara masa, na ga ya bar wannan takaddar, na ɗauka na karanta na kaiwa mahaifiyarsa ba tare da na nuna mata na karanta ba, bayan na kai mata da yamma 'yarta Amal tazo zata fita tana ga sauri, bata sani ba seta yarda takaddar, nikuma na tsinta, kamar yadda ya rubuta a takaddar, tun daga wannan lokacin ba' a ƙara ganin inda yake ba ya bar gidan gaba ɗaya "

Barrister Khalil yace "zaka iya komawa ka zauna"

Yaje ya dudduba cikin takaddunsa ya ɗakko wani littafi, ya dawo gaban Hajiya Halima ya miƙa mata littafin yace  "wannan kamar littafin ɗanki me Anwar, na Jami'a ko?"

Ta karɓa ta duba, ta jinjina kai, Khalil yace  "ki dubamin ko akwai bambanci tsakanin rubutun cikin wannan littafin dana takaddar gabanki?"

Take ƙafafunta suka hau rawa, taji tana numfashi sama sama, ta tsaya tana rarraba ido.

Khalil ya ɗau takaddar da littafin da takaddar, ya miƙawa Alƙali.

Alƙali ya karɓi takadda da littafi, Khalil ya kalli Hajiya Halima yace " wane irin rashin gaskiya ne haka ɗanki yake tuhumarki dashi? Wanda yasa har ya bar gida?"

Hajiya Halima tace
"Ni babu wani rashin gaskiya da nake aikatawa fa, kawai maganace tsakaninsa da 'yar uwarsa akan abunda take aikatawa, da kuma zargin nafi fifita' yan uwansa akansa"

Barrister Khalil ya jinjina kai yace  "shikenan zamu gani"

Akace taje ta zauna, ta koma inda ta taso tana godewa Allah.

Barrister Khalil yace  "ina neman wannan kotu ta bani dama, domin yiwa Babban Amini ga Alhaji Nasir wasu tambayoyi wato Alhaji Bukar Bulama!!!"

Ayshercool
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

152_153

Suleiman yace "Yusuf ka kwantar da hankalinka, dama Allah ya ƙaddara hakan seta faru, ta wannan dalili naka, mudai fatanmu Allah ya baka lafiya ka warware"

Yusuf yace "Ameen, nagode sosai Yallaɓai"

Suleiman yace "bakomai Yusuf, Allah dai ya baka lafiya ya ƙara wanke mana kai daga sharrin maƙiya"

Yusuf yace "Ameen ya Allah, to su lawyoyin da suka tsayamin sun sanni ne? Meyasa suka tsaya min, kuma meyasa basu taimakeni da farko ba?"

"Yusuf, lokacin da ake maka shari'a ta farko, su Bulama sunyi mamaya ga wannan shari'a fiye da tunaninka, ta ƙarƙashin ƙasa aka bi aka dinga samo shedun nan fa, a yadda Khalil yake gayamin, Nurat ce ta takurashi akan lallai ya tsaya a fitar da kai, saboda tasan wasu daga abubuwan da mahaifinta ke aikatawa, to yazo dai ya kawomin ziyara, muka tattauna na gaya masa abunda nasani daga abunda Saleh yake zuwa yana gayamin, yayi duk binciken su daya dace na tallafa masa da abunda nasani, to su dai sauran lawyoyin bansan yadda akai ya samosu ba, nidai ya sanarmin zasu ɗaukaka ƙara, shikenan se ranar shari'a nima na gansu "

Yusuf ya jinjina kai  yace " Alhamdilillah, Allah nagode maka "

Suleiman yace" An gode Allah kam, ka kwantar da hankalinka, komai ze wuce insha Allah "

Umma tace " dan Allah ka kwantar da hankalinka, sannan kai shiru da wannan surutun ka samu isashen bacci "

Yusuf yace " to Umma "

Har Yusuf yayi shiru, ya kuma cewa " Yallaɓai ya Widad fa? A wani hali take ciki? "

Umma tace " Meka ce? "

Yusuf yace   " cewa nayi a wani hali Widad take ciki? "

A fusace Umma tace " waya san mata, baka da zuciya Yusuf, yarinyar tazo ta bada sheda akanka, bayan a dalilinta ka shiga halin da kake ciki, amma kana wani maganar tana ina, in sake jin kayi maganarta sena saɓa maka"

Yusuf yai shiru, Amma yana tunanin shiya kuɓuta, to matarsa fa?.

Widad kuwa tuni 'yan sanda sukaje suka ɗakko ta a gidan nan bayan an kama Bulama yaji matsa ya faɗi inda take, tana zaune a ɗakin da take, taji ana guje guje, ba inda ta iya motsawa daga inda take zaune, Sega' yan sanda sun shigo, suka ɗakko ta suka tafi da ita Asibiti, tayi baƙi duk ta kukkumbura, haka suka ɗakkota a gakabaice ga babu isashen Abinci da kulawa.
'yan sanda suka kama har wannan Sabuwar, wadda take kuka da Widad a gidan.

Da aka kaita Asibiti ma, a emergency aka ajiye ta, saboda ciwon zuciya da jininta daya hau fiye da kima, ga dislocation data samu a hannunta saboda ball da Bulama yake da ita.

Likitoci sun fara tunanin ko a cire mata cikin, saboda kar yai sanadiyyar rasa ranta, Amma Widad a wahal ce tace  "likita, dan Allah ka barmin cikina, gara in mutu dashi a jikina, dan Allah a bawa Yoseef haƙuri, na bada sheda ne dan in ceci rayuwarsa, amma nasan ya bani gudunmuwa, dan Allah ya yafemin, nagode Allah tunda ya kuɓuta"

Haka taita surutai, seda aka mata Allura sannan bacci ya É—auketa, ta É—au tsawon lokaci tana wannan baccin, kafin ta farka sedai ga mamakin su, bayan ta farko jininta ya sauka ba kamar da ba, suna yi suna monitoring É—in yanayin jikinta, da kuma probability na surviving É—inta da wannan cikin.
   Sedai babu kowa a gurin Widad, musamman mace wadda zata dinga kula da ita, Nurses ne suke mata komai, nan ta sake kukan rashin dangi, da tana da dangi da an samu me kula da ita.
    Ramlah gaba ɗaya itama a zabure take, mutuwar Anwar ta da keta, bata taɓa zaton dagaske Bulama yasaka a kashe Anwar ba, gashi 'yan sanda suna kama mahaifiyarsu, ga Amal ita bame hankali ba ita ba mara hankali ba, haka suke zaune gaba ɗaya rayuwa ta juya musu baya.

Seda Yusuf ya kwan tara a Asibiti, ana masa screening daban daban dan tabattar da ingancin lafiyarsa, Yusuf ya É—an murmure sakamakon Abinci da kulawa da yake samu, kullum se an dafo Abinci daga gidan Suleiman an kawowa Yusuf, ya É—an farfaÉ—o sedai uwar rama da yayi.
Aka sallameshi daga Asibiti, tare da magunguna zuwa gida, tunda suka koma gida 'yan jaje ke sintirin zuwa gidan nan, wasu dan suyi jaje wasu dan suyi kallo, sedai Yusuf ko tsakar gida baya fitowa saboda baya san Hayaniya.
Abokan Aikinsa suka yi tawaga guda sukazo duba Yusuf, seda wasu suka yi kukan farinciki, dukda miskilancin Yusuf, amma akwai kirki da girmama mutane, duk wanda ya ganshi se yayi mamakin ramar da yayi.

Ɓangare guda kuma, hankalin Yusuf yana kan ta ina zega Widad, a wani hali take ciki?

Seda Widad tai sati biyu a Asibiti, cikin ikon Allah ta murmure, jininta ya sauka amma an kafa mata sharaÉ—in idan ta tashi haihuwa ta taho Asibiti, saboda tana cikin hatsari karta ce zata haihu a gida, dama tunda aka kai Widad Asibitin kullum 'yan sanda cikin patrol suke a Asibitin, har zuwa sallamarta da akayi.

Da aka sallameta ma headquarter na' yan sanda aka tafi da ita, domin amsa wasu tambayoyi da za'a mata, gaba ɗaya saboda yadda akayi shari'ar Yusuf da yadda abubuwa suka wakana, an sauya manyan shugabbani dake riƙe da manyan muƙamai a hukumar, duk an canza wanda Bulama ya siye da wasu.

Widad ta faɗi yadda komai ya faru, tun daga kan kisan mahaifiyarta, da irin Abubuwan da Bulama ya dingayi, ba tare da yasan tasan shine Bukar ba, har sace ta da akayi tare da Yusuf, ta nuna musu inda aka harbeta a hannu, da yadda Yusuf ya dinga wahala da ita, ƙarshe seda aka kamo doctor Hamisu wanda yake mata allurar hauka, da sauran wanda suke da hannu a miyagun laifukan ta'addanci da aka dinga aikatawa Daula da iyslinsa, Shima Saleh can aka samoshi a wani Asibitin gwamnati babu kulawa, saboda garin dukan daya dinga sha ya samu rauni a hantarsa.
Chapter 110 · 0% Book details