Sashe 28
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yace "dare yayi sosai yanzu, ma cigaba wani lokacin, ki kwanta ki huta"
Ta jinjina masa kai, ya gyara mata pillow ya kwantar da ita ze miƙe, ta riƙe hannunsa, ya kalleta yace "ya dai?"
"Akwai hadari a garin, akwai yuwuwar ayi ruwan sama, ka kwanta anan kawai".
Yusuf yace "to ai ba'a fara ruwan ba"
"Eh bakomai ka kwanta, i need a shoulder to cry on, ka kwana a kusa dani"
Har yanzun dai kuka Widad take yi, ya kwanta ya ɗora kanta a Ƙirjinsa, ya dinga sauke ajiyar zuciya, tana cigaba da zubar da hawaye.
Yusuf yaja wata doguwar ajiyar zuciya yace "Gimbiya kina son ki karyamin zuciya ne in cigaba da kukan nima?"
Girgiza masa kai tayi, yace "kinga har shaƙuwa kikeyi, kin kusa shiɗewa ɗazu saboda kuka, kiyi haƙuri dan Allah ki dena haka ya isa, yi shiru muyi musu addu'a"
Widad tace "karka damu da shiɗewar da nayi, bayan ciwon hauka inada ciwon zuciya kamar Daddy na, dan haka ba wani abu bane, nasan idan kwana na ya ƙare zanbi Ammi na ne"
"Widad bakya tausayina ko? Baki damu da ki dinga gayamin zaki mutu ki barni ba ko? Babu ruwanki da halin da zan shiga idan kika mutu kika barni bako?"
ÆŠago kanta tayi tana kallon Yusuf, dukda a cikin duhu suke amma ta kai hannunta fuskarsa taji É—umin hawaye a fuskarsa.
Murmushi tayi tace " Ragon maza kawai, É—an sanda yana kuka, se kace ba jarumi ba, ni meyasa ka damu dani haka baka son in mutu in barka? Dukda tarin rashin kirki na a gareka"
Tai maganar cike da son bagarar da wancan zancen da suke.
Mirginata yayi ya koma kanta, a hankali ya kai fuskarsa kunnenta yana mata numfashi a kunne sannan yace "saboda ni bana ganin laifinki, kuma ni bana riƙo ina sonki sosai, kuma ba kince ni ɗan uwanki bane?, kuma seki tafi ki bar ɗanuwa haka akeyi? Bakya tunanin halin da ɗan uwa ze shiga? Anya kina 'yan uwantakar dani kuwa?"
Murmushi tayi tace "wani lokacin inayi, wani lokacin kuma ba nayi"
Tai maganar tana dariya, ta rungume Yusuf tace "dare yayi sosai, muyi shiru haka mu kwanta"
Yusuf ya sake gyara kwanciyarsa a jikinta, yayi shiru wani irin matsanancin tausayin ta yana ratsa ransa, daga ita har mahaifinta kowannen su yaga ƙaddarar rayuwa daban daban.
A haka har bacci yayi awon gaba da dukkaninsu.
Alhaji Musa yana zaune yana karyawa da safe a falonsa, wayarsa ta fara ringing, É—aukar wayarsa yayi ya tafi bedroom, ya rufe É—akin ya saka key sannan ya É—aga wayar.
"Ka kasa kunne yau, zakaji matakin dana É—auka akan Yaron nan, dan haka ka kwantar da hankalinka babu abunda ze faru"
Ajiyar zuciya Musa yayi yace "Alhamdilillah, Insha Allah zan saurara inji wani irin mataki ka ɗauka akan lamarin, amma to batun Daula fa? Har yanzu fa babu wani labari a game da shi, ya muke ciki a wannan ɓangaren?"
"Karka damu, shima ina nan ina tunanin mafita, sannan wannan Likitan shima masa a kau dashi, dan amfaninsa ya ƙare"
Musa yace "doctor Sufyan kake nufi wai?"
Bukar yace "Eh shi, na bada umarnin da ya dace akansa shima, dan haka kowa ya kwantar da hankalinsa"
Alhaji Musa yace "to shikenan, babu laifi godiya muke"
Daga nan ya kashe wayarsa, yana jin wani sanyi a ransa, dan da ba ƙaramin ɗurar ruwa cikinsa yayi ba.
Nura direba ne a cikin lambun Widad yana ta gyarawa, yana cire ciyayin ciki yana gyara flowers ɗin tare da sharewa, yace "Allah sarki, lambun nan kansa yayi babban rashi, da meshi tana nan babu yadda za'ayi a barshi a haka, kai rayuwa ba tabbas"
Kukan mage ya dingaji a tsakanin flowers, har ya tsorata ze ruga da gudu, sekuma yayi ta maza ya dake, leƙawa ya shigayi a hankali, yana duba ciyayin.
Roux ce magen Widad a kwance, gaba ɗaya tayi wani iri abun tsoro, da ƙatuwace magen nan, gata da kyau gwanin ban sha'awa da yake bata Nigeria bace, amma yanzu kamar an jiƙata a ruwan zafi, gaba ɗaya gashin jikinta yayi wani iri, gashi duk ya zube ta koma wata iri abun tsoro.
Nura yasa hannu ya É—akkota, ya nufi bakin gate da ita, yana zuwa ya ajiye ta, Isa ya kalleshi ya yamutsa fuska yace "meye wannan haka?"
Nura yace "Magem 'yar masu gidace"
Murtalah yace "itace ta koma haka?"
Nura yace "kaima dai ka faÉ—a, ai maraici yakama magen nan, abun tausayi"
Isa yace "wannan matsiyatan basu kula da mutum bama balle wata mage, duk halin nan da ake ciki na rashin me gidan nan da' yarsa ko a jikin su, sabgarsu kawai suke har gara ma Anwar ɗin nan, shikam akwai kirki sosai"
Nura yace "bari Isa, Allah abun tsoro duniya abun tsoro, kalli da yadda gidan nan kullum cikin shige da ficen mutane ake, amma yanzu tsit kake ji"
Murtalah yace "kai dai bari, bari in jarraba bawa magem nan Abinci ko zata ci"
Isa yace "kaga fa baka da abunda zaka bata, dan Wani Abincin da fake ci kai kanka baka taɓa ciba, ka ƙyaleta kawai ta ƙarasa ta hutawa rayuwarta"
Murtalah yace "A'a ba'ayi haka ba, Yanzu a dalilin taimakon dabbar nan se kaga Allah nima yaji ƙaina, kuma dame ita tana nan kasan bata yarda abar wani da yunwa a gidan nan ba, dan haka zan jarraba bata Abinci ko zata ci"
Isa yace "ai se kai tayi É—an wahala, ga hanyoyin neman lada nan ba adadi, amma ka tsaya wahalar da kanka akan abar data kusa mutuwa"
Murtalah be kuma kula shi ba, yaje ya siyo biscuit katako, da madara 'yar talatin yazo ya haɗa ya bata, ai nan da nan magen nam ta lamushe, saboda azabar Yunwa da take ji, abunka da dabba da sabo, tana jin ƙwarin jikinta ta koma ɗakin Widad, tana kuka ta hau kan gadonta ta sauka, ta fito falonta zuwa babban falo.
Ramlah tace "wai dama wannan shegiyar halittar tana raye bata mutu ba?"
Amal tace "ni kaina na zata ta mutu fa"
Ramlah tace "aikuwa ƙarasata zanyi, sena kasheta"
Amal tace "ke Ramlah, ina ruwanki da ita? Me tayi miki?"
"ke nifa duk wani abu daya shafi waccan banzar ba sonsa nake ba, tunda Allah yasa ta bar gidan nan mukayi 'yanci, muke warwasawa son ranmu, babu tsawa balle hantara, shiyasa bana son ganin duk wani abu daya shafeta balle raina ya ɓaci"
Amal tace "dukda haka dai karki huce akan magen nan danni tausayinta nake ji, itama magen wata kinibabbiya kamar uwarÉ—akinta, bata zuwa ko ina se tare da ita, ai gashi yanzu tana wahala"
Ramlah tace "tunda uwaɗakin nata bata nan, ai itama seta ƙara mai"
Da ƙyar Yusuf ya iya tashi sallar Asuba saboda daɗewar da suka yi basu yi bacci ba jiya, hadari yana ta cida, da akama ruwan sama za'ayi.
Ya tashi Widad sannan yaje yayi alwala ya fita salla, sedai harya dawo bata tashi ba, hannunsa yaje ya wanke yazo yana shafa mata ruwan a fuskarta.
A hankali tayi miƙa, ta koma ta kuma lumshe idonta, ɗagota yayi daga kwanciyar gaba ɗaya ya ɗan ƙura mata ido sannan yace "wai wani darem za'a kuma yi miki ne?"
Kasa buÉ—e idon tayi saboda baccin da take ji, hannayenta ya shiga matsawa yace "kalli gari ya wayefa, buÉ—e idonki ki gani"
. A hankali ta buɗe idonta, tabbas gari ya fara hasks duhun Asuba ya yaye, ta kalle shi tace "meyasa baka tasheni ba"?
"na tasheki baki tashi bane" a hankali ta zauna sosai, sannan ta miƙe taje tayi alwala tazo ta tada salla, Yusuf yana gefe yana cigaba da lazumi, ya kwaɗaitu da son jin ƙarshen labarin Widad, sedai yasan halinta da rikicin tsiya, idan bata ga dama ba haka zatai ta ja masa rai ba zata gaya masa ba, idan ya takura ta se yaji kuma suyi faɗa.
Data idar da sallar ta fara lazimi ta kife a gurin, yana kallonta da alama bacci ne sosai a kanta, ya tashi a hankali ya É—agata ya maida ita kan katifar, still yana jin tausayinta yana ratsa ruhinsa da ganganr jikinsa.
Ya kwanta a bayanta cike da fargabar kar ta tashi ta kama masifa, tunda ba ita tace ya kwanta ba, sedai ta É—anyi juyi taji shi a bayanta, a hankali ta juyo tana fuskantarsa, ba tare da ta buÉ—e idonta ba, ta zura hannunta ta rungumeshi, ta kwantar da kanta a jikinsa, a haka bacci ya sake yin awon gaba dasu.
Har shaɗaya da rabi na Safe basu farka ba, Hari sunata aikace aikacen su a tsakar gida, ta kalli Gwaggo tace "Yaya, har yanzu fa Wudas basu fito ba, lafiya kuwa?"
Gwaggo tace "lafiya ƙalau insha Allah, ai da Asuba shi yaja salla, dan haka lafiya ƙalau"
"Yaya sha É—aya da rabi fa"
Hansai tace "A'a haba Yaya Hari, abu na mata da miji ina ruwanki? Ba suyi niyyar fitowa yanzu bane"
Hanne ji tayi kamar ta faɗi ƙasa dan haushi da takaici.
Widad ce ta fara farkawa, ta buɗe idonta taga yadda rana tayi, a hankali ta bar jikin Yusuf ta tashi zaune, garin ta tashin ne shima ya farka, ya kalli garin yadda rana ta buɗe, yace "Subhanallah, rana tayi ma"
Widad tace "Aikam dai, kasan bamuyi bacci da wuri ba, shiyasa"
Yusuf yace "hakane, gashi ko breakfast bakiyi ba, bari in tashi idan akwai Abinci a gurin Gwaggo shikenan, in babu se inzo in dafa"
Widad tace "karka damu ni bana jin Yunwa, wanka nake son inyi amma ina son Ka temakamin in wanke kaina, gani nake kamar baha fita yana damuna sosai saboda babu gyara"
Yusuf yace "to aini ban san yadda ake yi ba, ban san yadda ake wanke gashi ba"
Widad ta kalleshi tace "eh amma ka iya taɓawa ai"
Yusuf yayi murmushi yace "wannan ai me sauƙi ne, dan bana gajiya da taɓawa, amma wankewa ni ban san yadda ake yi ba"
"Yau zaka koya kuwa, zan karɓo ruwa a gurin Gwaggo seka tayani mu wanke"
Yusuf yace "wait, waima a ina zamu wanke kan? Ba dai banÉ—aki ba"
"Koma a inane" ta bashi amsa