Sashe 25
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Likitoci suka rufu akansa, suna monitoring ɗin bugun zuciyarsa, salati kawai yake yana faɗin " Yayana, ɗan uwana, shi kaɗai ne ya ragemin, Anty Nadiya da ɗansu duk babu, innalillahi wa inna ialaihi raji'un "
Wani liktane yace " haba ɗan uwa kamar ba musulmi ba, kayi haƙuri kayi tawwakali, idan kaji ƙaddarar wani seka rufe baki, kayi haƙuri mu samu mu ceci rayuwar ka, an san mutuwa da ciwo amma kayi haƙuri "
Nasir yace " likita, É—an uwana ya mutu, da zan tafi umara ya muka dinga hira, ashe wasiyya ce, nayi rashi likita, banji rasuwar iyayena kamar yadda naji mutuwar Yusuf da Nadiya ba, har É—an namu ma na rasa, innalillahi wa inna ialaihi raji'un wayyo Allah yayana"
Yai maganar yana fashewa da kuka, kamar ƙaramin yaro.
Likitan ya dafa kafaɗarsa yace "Allah yasan da kai, kayi haƙuri, Allah shike da rayuwar kowane bawa, ka kwantar da hankalinka, matarka mafa tana can munata ƙoƙari akanta, karta rasa hankalin ta, idan taganka a mawiyacin hali to jikinta ze rikice"
Jinina kai Nasir ya shigayi yana "Allah sarki Hudana, Huda munyi rashi, mun rasa 'yan uwa dagani harke, Allah ka zama gatan mu, Allah kayiwa bayinka Rahama"
Likitan ya amsa da Ameen, yana cigaba da kwantarwa da Nasir hankali.
Nasir yace "likita, ku kaini inga matata"
Likitan yace "A' a ka bari za'a kawo ta, har nan inda kake bama son ka dinga wahalar da jikinka"
A wannan kwanaki biyar ɗin Huda tayi ɓari, amma saboda halin da suke ciki ba'a sanar musu ba, dukda alhini da Ahmad ke ciki, amma a haka yake ta sintiri a Asibitin, wata ƙawar mahaifiyar su Nasir ce take sintirin jinyar Huda, yayin da Ahmad ke kula da Nasir, 'yan unguwa nata zuwa yi musu jaje da kuma duba su.
Duk Wanda yaga halin da suke ciki, sya tausaya musu, gaba ɗaya sun rame mussman Huda abun yafi mata yawa, yanzu ta rasa kowa da komai nata, se Allah da kuma mijinta Nasir, shima gashi a kwance se yadda Allah yayi dashi, ga ɗan uwan mahaifinsu ya sallamasu, dan bezo Nigeria gurin ta'aziyya ba, kuma labarin gobarar ya iskeshi, yace suje can su ƙarata ba abunda yayi masa zafi.
Nasir ya takura akan yana son ganin Huda, a haka aka turo Huda a wheel chair tazo duba Nasir.
Tana ganinsa a zaune ta ɗanji sanyi a ranta, ganin nasa jikin da sauƙi, ana ƙarasawa da ita suka rungume juna suna kuka, Kuka me tsuma zuciya, a hankali Huda tace "zaujee, mun rasasu gaba ɗaya babu wanda yayi rai a cikin su '
Nasir yace " Na sani Huda, babu yadda muka iya se mu rungumi ƙaddararmu, sukuma mu cigaba da yi musu Addu'a "
Nan suka dinga kuka, aka rasa me rarrashin wani, Ahmad ne ya shigo ya tarar dasu a wannan yanayi, suna ta kuka.
Ahmad yaja kujera ya zauna, ya dubi su Nasir cike da rauni da karaya shima ya fara magana yace " Nasir, dama itafa duniya munzone tamkar matafiya, dole wataran mu barta, sannan dukkan ɗan Adam dole ne Allah ya jarrabe shi, Allah baya barin mumini babu jarrabawa, dan haka nida ku mu rungumi ƙaddrara mu, mu yi tawwakali mu barwa Allah komai, shi ze bamu mafita, su kuma da muka rasa muyi musu Addu'a "
Ahmad ya ƙarasa maganar, ƙwalla na zuba daga idanunsa, amma ya cigaba da tausarsu yanayi musu Nasiha.
Seda suka shafe sati biyu a Asibiti, saboda jikin Nasir, dan zuciyarsa ta taɓu saboda damuwa, haka likitoci suka gindaya masa sharuɗa da magunguna, sannan aka sanar dashi ɓarin da Huda tayi, sam da gashi har ita basu san da cikin ba, dan koda zasu tafi umara da aka yi gwaji babu, yanzu kuma an tabattar masa da cikin watansa uku ma, Ba laifi Bulama ma yayi zaryar Asibitin nan sosai, saboda Nasir, dan dukda rashin jituwar da yake da Yayan Nasir ya tausaya masa wannan rashin da suka yi lokaci ɗaya, shima ya dinga rarrashin Nasir, akan ya kwantar da hankalinsa ya rungumi ƙaddara.
A haka aka sallamesu suka koma gida, sedai babu me iya rarrashin wani a cikinsu, idan abun ya taɓosu se su wuni kuka ita dashi, dama ga Nasir da raguwar zuciya, su wuni cikin damuwa babu me ko iya cin Abincin, saboda dukkaninsu mutuwar tana dukan su.
Kusan watanni Uku, da mutuwar har ɗan gara Nasir ya fara jarumta yanzu, amma Huda kam babu wannan batun, musamman gari ya waye da ta saba ta tafi gidan Nadiya, ko Yayarta Islam taje taita musu rainon 'ya' ya kasancewar tana matuƙar som yara, amma lokaci ɗaya Allah ya karɓe su gaba ɗaya.
Yanzu Nasir na iya zaman rarrashin ta, yaita bata baki yana tausarata, yace "Huda, ni dake Allah ne gatanmu, shiya haliccemu gaba ɗaya, kuma yafi mu sonsu daya karɓesu, ni dake dole muyi kukan maraici, nasan zakiyi tunanin ya rayuwarki zata kasance a nan gaba? Huda a duniya bayan iyayena ina jin maganar Yayana fiye da tunaninki, kuma nima nasam abunda ya dace, nasan gwagwarmayar da akayi kafin in Aureki, dan haka ko sau ɗaya karki sawa zuciyarki Nasir ze juya miki baya, nida ke yanzu gaba ɗaya muna cikin maraici gaba da baya, dan haka mu rungumi ƙaddararmu mu rayu tare, mu jure duk wani ƙalubale mu kasance a tare har zuwa namu wa'adin, in dai ta ɓangare nane, Insha Allah bazaki zubda hawaye ba"
Huda tayi ajiyar zuciya tace "Zaujee, nima nasan abune mawuyaci in fuskanci ƙalubale ko juya baya daga gareka, ina da kyakkyawan yaƙini akanka, amma dole in koka, munyi rashin da ba zamu mayar da wannan gurbin ba, kamar yadda ka faɗa insha Allah, duk tsanani zan jure duk wata ƙaddara in rayu da kai, bani da kowa se Allah sekuma kai"
Nasir yace "Insha Allah, bazan baki kunya ba Huda, nasan halaccin da kikamin a rayuwa, dan haka insha Allah zan kasance dake, zan kasance me baki kariya, kuma zan zame miki mijin marainiya insha Allah"
Haka su dinga kwantarwa da junansu hankali, suna bawa junansu haƙuri.
Amma duk da haka, Huda ta kasa sakin jiki ta haƙura gaba ɗaya, ƙarshe seda Nasir ya bar unguwar gaba ɗaya ko hankalinta ya kwanta, dan ko fita tayi tazo wucewa ta layin gidajen ƙarshenta idan ta fara kuka hadda suma.
A haka Nasir ya daddafa ya cigaba da kasuwancinsa, kuÉ—i ko ta ina shigomasa suke, a haka har Ahmad yayi Aure, Bulama ma ya tattago maganar Aure, kusan Nasir ne yayiwa Bulama komai na Auren, dan har gidan daze zauna shiya bashi.
Shikuma Nasir likkafa se ƙara cigaba take, gaba ɗaya ya zama busy man, yawo ƙasa ƙasa kasuwanci kala kala, duk ba wanda ba yayi.
Shine saida kayan sarƙoƙi, motoci, kayan masarufi, ga shaguna da yake dasu a kasuwa, na siye da siyarwa, hannun jari dayake siya a manyan kamfanunnuka.
Nan da nan ya zama kamar bashi ba, gashi dai matashi amma ya tara kuÉ—i.
Nasir ya ɗauki Huda sukaje ƙasarsu can Maroco, amma baffanta yayi musu wulaƙanci, Kasancewar besan Nasir ya fara arziki ba, yayi musu fata fata yace yadda aka cinye 'yar uwatta itama haka za' a cinyeta, haka suka dawo Nigeria da ɓacin rai.
Ganin Huda ta kasa samun nutsuwa har yanzu, ga tarin damuwa data sa a ranta, hakan yasa ya ɗauketa ya tafi da ita ƙasashen waje, can Dubai inda yafi harkokinsa, ya koma makaranta a can, sedai tun bayan ɓarin nan Huda bata sake samun ciki ba, kullum cikin addu'a take ubangiji Allah ya bata rabo itama.
Ya zamana Huda tana Dubai, kowani abun zezo yi Nigeria, ita tana can duk dan ya samu ta rage damuwa.
Seda suka shekara takwas da Aure bata sake yin ko ɓari ba, abun duniya duk ya addabeta, shikam ko a jikinsa, dukda yana addu'a sosai a ransa a bun yana damunsa, amma sam baya nuna mata, ta takura masa sukaje Asibiti akayi musu gwaje gwaje, amma akace lafiyarsu ƙalau.
Se a shekara ta tara Allah yasa Huda ta samu ciki, aikuwa Nasir yayi murna babu adadi, nan suka shiga rainon cikin nan da tattalinsa, gefe guda kuma ya zama matashin ɗan kasuwa na farko, wanda sunansa yake zagawa a cikin Nigeria, a hankali yasan manyan 'yan siyasa da attajirai, saboda har harkar kwangila yake yi, nan dangin mahifinsa suka shiga ƙoƙarin nuna ai ɗansu ne, amma fafur yaƙi yadda su raɓe shi, a cikin dangi can suka haɗu da wani Musa, sun ɗan haɗa alaƙa amma ba irin ta sosai ɗin nan ba, ɗan unguwarsu ne dai, ya dinga shisshigewa Nasir, tun Nasir na basar dashi, har ya fara sakewa dashi.
Musa ya nuna sha'awarsa ga harkar siyasa, Nasir ya haɗashi da manyan 'yan siyasa, ya goyi bayansa akan harkar siyasar, nan da nan mutane suka karɓi Musa, a dalilin Nasir, kasancewar Nasir mutum ne na mutane, mutane na ƙaunarshi saboda hannunsa a sake yake, ga shaharar da yayi ganin Nasir ne ya talatta Musa da kansa, hakan yasa mutane suka karɓe shi hannu biyu biyu.
Bulama kam basa jituwa da Ahmad, dan haka ya dinga shiga yana fita danya raba Ahmad da Daula, gashi kusan duk wani harkar kasuwanci Ahmad ne yake jan Daula, dan tun yana ƙarami Mahaifinsa ɗan kasuwane, dan haka yasan sirrin kasuwanci sosai, Ahmad yana yawan ankarar da Daula akan ya kiyayi Bulama, amma se Nasir yace ai Bulama ya zamani na zama shi, rabuwarmu abune me wahalar gaske.
Bulama ya kunno musu wata rigima akan harkar kasuwancin da suke, ya shiga ya fita seda yasa Daula da Ahmad sukayi baran baran suka rabu, ya zamana shine ma gaban Nasir.
Watan cikin Huda tara cif ta haifo sankaceciyar jariryarta mace, Daula ya rasa inda zesa ransa dan murna, sedai haihuwar ta fama musu mutuwar mutanen da suka taka mahimmiyar rawa a rayuwar su, yau gashi kamar yadda Nadiya ke fata, Nasir ya amsa sunan Daula, ga rabo sun samu, amma babu ɗaya a mutanen nan daze taya su farinciki.
Haihuwar jaririyar nan tasa sun zubda hawaye, har damuwa taso ta maye gurbin farincikin da suke ciki, wani abun mamaki jaririyar nan ta É—akko kamanin Islam Yayar Huda, dukda Huda da Islam suna kama sosai, amma kamanin Jaririyar nan sunfi karkata ga Islam.