← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 127

Sashe 66

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yoseef dan Allah Kadena kukan nan, zaka É—agamin hankali, ya isa haka please kar kanka yayi ciwo kaji"

"Hmm, my wife tsawon shekaru talatin da biyu, abu yana damuna a zuciya, ban samu nayi kuka yadda nake so ba, dan haka dan Allah ki barni inyi, kin ƙyaleni nika ɗai nasan what i go through, na shiga damuwa da baƙin ciki daban daban a rayuwata, i suppose to cry ko zan rage "

"No Yoseef, kace Alhamdilillah daya barka da ranka da lafiyarka, kuma insha Allah daÉ—i yana tafe, dan bayan duk wata wuya se daÉ—i da yardar Allah, ka dena kuka kaji ÆŠan uwana, we are now family ai ko?"

Ajiyar zuciya ya dinga saukewa, yace  "Widad dagaske zaki cigaba da zama dani, koda mun koma gida?"

Widad tace  "dagaske nake, Insha Allah mutu ka raba nida kai, kaine dai dai da rayuwata Yoseef, a yanzu kasanni fiye da yadda kowa ya sanni, ciki harda mahaifina, kasan abunda nake so kasan wanda bana so, you are such an amazing guy, kuma ni labarinka da naji, bazan iya rabuwa da kai ba, ƙaddarorinmu suna kamanceceniya da juna, dan haka zamanmu zeyi dai dai da yanayin rayuwar mu, zan zauna da kai Yoseef, ba ruwana da a inda aka samo ka ko makamancin haka, kuma insha Allah bazaka sake zubda hawaye saboda haka ba, ka dena kuka kaji Mijina "

Tai maganar tana share masa hawaye, itakuma tana zubda hawayen, Yusuf ya ɗago kansa yana share mata hawayen fuskarta itama yace " Am sorry Baby, na saki kuka ko? Yi haƙuri yau nayi ragwanci a gaban matata, zata rainani"

Ya ƙarasa maganar yana murmushin yaƙe, "kwanta muyi bacci, dare yayi kar gobe in Allah ya kaimu a barni da yunwa"

Yai murmushi tare da kwanciya a jikin ta, tasa hannayenta ta zagaye bayansa dashi, tana shafa sumar kansa da hannunta É—aya, Yusuf yana ta jan ajiyar zuciya, ta shiga É—an duddukan bayansa alamar rarrashi.

Wani irin kallo Hajiya Halima ta shiga yiwa mutumin, Mutumin yace "kina mamakin ganinane? Ai bekamata kiyi mamaki ba, butulu mara Alƙawari"

Ramlah ce ta fito ita da Amal, Ramlah tace  "Mummy ya har yanzun baki tafi ba? What are you still doing their?"

Suka ƙaraso inda take tsaye ita da mutumin nan, Amal ta buɗe baki tare da dafe ƙirji, Ramlah tace "Mummy wannan kuma wanene? Barar ce baza'a bari kifi ta ayimiki ba, se an biyoki har nan, mutane sun fiye zalama kamar zasuyi ƙwace dan azabar son kuɗi"

Amal tace  "kai Ramlah, babanmu ne fa, baki gane shi bane?"

Ramlah tace "What? Wannan É—in kalle shi wani buguzun buguzun dashi kamar korarre"

Hajiya Halima tace  "rufemin baki dan ubanki, Babanku ne"

Ramlah tace "Taɓɗijan, God forbid in nuna wannan ince shine ubana, alhalin ina bearing da Sunan Nasir Daula, sannan wannan yazo yace wai shi ne babanmu, Allah ya kiyaye wallahi wannan ko riƙon jakata bazan ɗauke shi ba, ni ubana ya mutu da daɗewa, sedai babansu Anwar"

Ta juya ta shige gidan tana ci gaba da maganganu, mutumin ya kalleta yace  "Halima haka mukayi dake? Saboda son zuciya irin naki haka kika mayar min da 'ya' ya, yarinyata ta kalleni tana gayamin wannan maganganun, dama haka mukayi dake?"

Hajiya Halima tace  "kaga, dan Allah karka ɗagamin murya a gaban ma'aikatana, kazo mu shiga daga ciki ayi duk wacce za'ayi mana"

Ya bita suka shiga cikin falo, Amal ta tafi gurin Ramlah ta buɗe ƙofar ɗakin nata ta shiga, ta sameta tana zaune tana danna waya, Amal tace 

"Ramlah bekamata kiyiwa mahaifinmu haka ba, ai duk lalacewarsa  shine ya haifemu"

Ramlah tace  "wait, wai dan Allah dagaske wannan bagidajen shine mahaifinmu?"

"Ramlah ki gyara maganarki fa, wallahi babanmu ne ya zaki manta fuskarsa, wallahi babanmu ne"

"gaskiya sedai Babanku, kalli mutum a koÉ—e kamar baya cin Abinci, kalli suturar jikinsa yazo yace shi babanmu ne, gaskiya niba ubana bane, ai abun kunyane mu nuna wannan muce ubanmu ne, bayan duniya tasan da sunan Daula muke amfani, ai kawai babanmu ya mutu, amma wannan ai be kai mutum ba balle ace masa uba"

Amal tace  "ikon Allah, wallahi Ramlah kina sane, babu yadda za'ayi kice kin manta kamanin mahaifinmu, dukda tunda muka bar gurinsa bamu kuma zuwa ba"

Ramlah tace  "ke ina sane wallahi, na gane shi sarai, amma ni karan kaina kunya nakeji in kalle shi ince mahaifina ne, haba mutum a tsiyace kamar matafiyin da guzuri ya ƙare masa, kuma ya tsaya ze fara kora bayani a gaban wannan gidadawan, salon su raina mutane"

Amal tace "lallai Ramlah, ke abun naki babbane ma"

"Haba shu'aibu, ya zakazo a wannan lokacin da ake tsakiyar tarzoma da tashin hankali? Kazo babu aike bau Sanarwa haka akeyi, kuma ka tsaya kana neman ka tona min Asiri a gaban mutane, kai har yanzu bazaka waye ba?"

Shu'aibu ya kalleta yace  "dama ina zan waye, mara mutunci dama haka mukayi dake? Nace haka mukayi dake? Akan yarjejeniya mukayi komai, amma da yake ke butulu ce, kinzo kin samu jin daɗi kin watsar dani, kinyi watsi da Yarjejeniyar da mukayi, shine nazo in miki tuni, ki cika Alƙawari sannan ki bani 'ya' yana"

"wane 'ya' yan naka, malam karma ka É—akko wannan maganar, dan ba zata yuwu ba, me ka sani na 'ya' yan naka, seda na gama wahalar? Lokacin mora yayi sannan kace in baka no, baze yuwu ba"

Shu'aibu yace   "kin san Allah Halima, sekin bani 'ya' yana gaba ɗayansu bazan bar ko guda ba, kuma sekin cika Alƙawarin da mukayi daku"

Tsaki tayi tace "bani account number É—inka, zan baka dubu É—ari biyar, ka tafi ka bani guri dan Allah"

"Ni zaki kalla ki bawa dubu ɗari biyar, ki riƙe kayarki amma ki saurari abunda ze biyo baya"

"Kaga dan Allah karmuje ga haka, ka zauna muyi magana, Alƙawari da mukayi fa har yanzu wannan kuɗi basu samu ba, ya kake so inyi ne"

Shu'aibu yace  "ƙarya kike, shakrar ki nawa a gidan nan, kima nufin duk zamanki a gidan nan baki samu komai ba, aiko duk jikina kunne ne bazan yadda ba Wallahi"

"Wai kai baka san 'yarsa itace ta hana ruwa gudu ba,? dan Allah karka É—agamin hankali ka bani account number, zan samaka million É—aya"

Shu' aibu yace  "ashema bani da hankali, kusan shekara goma sha, ko ficika bata shiga hannuna ba kice zaki ban million ɗaya, baki nemi sulhu ba tabbas, kuma abunda ze biyo baya baze miki daɗi ba na gaya miki"

Hajiya Halima tace "kaga shua'aibu bazaka zo ka ɗagamin hankali ba Wallahi, yanzu ma daka zo a wani zullumin bala'in nake, ko dai ka haƙura da abunda zan baka kokuma ka haƙura, dan ban san ya kake so inyi ba, yarinyar daza'a karɓi dukiyar a hannuta ba'a san inda take ba, shi kansa me gidan ba'asan a inda yake ba, komai yana nema ya jagwalgwale min, kuma kazo kana gayamin maganar banza, dan Allah ka sauraramin"

"Naji zan saurara miki, amma nima ki saurari abunda ze biyo baya, kin sanni kin sam abunda zan iya aikatawa, wallahi nima zan baki mamaki, zan ƙara miki matsala akan wadda kike ciki, sannan ki gayawa 'ya' yana ina nan zuwa in ɗauke abuna"

"ka ɗauki wa? Can kaje ka nemi 'ya' yanka, karka ƙara ce mana 'ya' yanka, can ka nemi 'ya' yanka malam"  Ramlah da ta fito daga part ɗinta take faɗa.

Shu'aibu yai murmushi yace "Allah sarki yaro yarone, Halima na fuskanci wannan yarinyar halina ta É—akko, Rawar kanta da zafin kanta kamarni, amma ki gargaÉ—eta in ba haka ba, abunda ze biyo baya ke dasu baze muku daÉ—i ba Wallahi"

Mummy tace "ke Ramalh, wannan fa mahaifinku ne, kidena gayamasa maganar da kika ga dama kinji ko?"

"wallahi karki ƙara haɗani dashi, can ya nemi yaransa ba dai niba, uwar meya maganta  mana a rayuwar daze zo yana wani mu 'ya' yansa ne, dan Allah mu yayi ya wuce ya bamu guri, kidena ssaurarensa ki fita a samo mafita akan ɓatan Anwar, idan ba hakaba kika biyewa wannan koɗaɗɗen mutumin, komai ze iya faruwa, Anwar ze iya tona miki asiri idan wannan be tona miki ba"

Zaro ido shu'aibu yayi yace  "Anwar ɗin ne ya ɓata? Halima dagaske ne abunda nakeji?"

A fhaace tace "Eh gaske ne shu'aibu, duk akan a samu kuÉ—in nan, Anwar ya gudu ya bar gidan nan, se me ina nikaÉ—ai naita É—awainiya dasu ina ruwanka dasu, dan Allah ka barni inji da kaina"

"zan barki kiji da kanki, zan tafi a yanzu bazan kuma dawowa ba se a lokacin daya dace, ko kuma in cigaba dayi miki aike, zan baki account number na, ina buƙata kuɗi naira million hamsin, nan da kwana bakwai idan baki turamin wallahi, wallahi abunda ze biyo baya baze miki daɗi ba"

Ramlah tace "ai se kazo ka ƙwata ai, tunda kai ka tara mata"

Aikuwa ya shammaci Ramlah ya wanketa da mari, jikinsa na rawa kamar wanda aka kaɗawa gangi yace  "da uwarki nake magana, ba dake ba ko ita lokacin da tana hannuna idan ina magana tana magana, tasan me yake biyo baya, idan kin manta dan lokacin kina ƙarama gara in tuna miki, Halima ki gargaɗeta ki gaya mata abunda zan iya, idan na kuma zuwa gidan nan, taimin tsinin baki sena yagalgalata a gurin nan, kuma nan ba gidana bane, zanzo in ɗauke ku, lokaci yayi da zan mori abunda na haifa nima"

Ramlah ta zabura zata yi magana, amma Hajiya Halima ta dakatar da ita, ta hanata, shi kuma ya juya ya fice yana huci yana sauke numfashi.

Tunda garin Allah ya waye, Widad take nan nan da Yusuf, se wani lallaɓashi take tana tarairayarsa, daya tashi da safe, idanunsa sunyi ja sosai sun ɗan kumbura, saboda kukan da yayi jiya, da ta kalli Yusuf se taji kamar ta fashe da kuka, idan ta tuna labarin daya bata, da irin wahalar da ya sha shida mariƙiyarsa, sun sha wahalar rayuwa sosai.

Ta ɗakko kunu, ta dinga ɗebowa tana bashi a baki, Yusuf yace "yau kuma nina koma jaririn? Se wani lallaɓani kike?"

"ba dole in lallaɓaka ba, nima kana lallaɓani ai, ko baka sone?"

Yace "ina so mana, ai gara kiyita lallaɓanin"
Chapter 66 · 0% Book details