← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 127

Sashe 64

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Usman yace  " ke abun da haushi fa, mutum be fika da uban komai ba amma ya dinga hura maka hanci, baze dingawa mutane magana ba, ai dole ayi dashi"

Salma tace "to ka sani ko haka nature É—insa take, maybe jan ajinsa yake yi".

Habu yace  "Nature ɗin banza da wofi, kuma jan ajin me sekace mace, jan aji ai se mata, kana namiji ubanwa zaka jawa wani aji, yana gaddi ina gaddi za'a jamin aji, wallahi mutum be isa ba"

"Nikam nafison irin haka, inga mutum gentle, yafi ma wata macen jan aji amma ace duk inda mutum ya zauna dan yana namiji ya dinga sakin baki haba, ai abun ba tsari"

Habu yace "wannan yarinyar kinci kai tabbas baki da hankali, namiji in ba É—an daudu ba meye na wani jan aji"

Haka suka cigaba da wannan jayayya a tsakaninsu, ya zamana kusan kullum se anyi zancen Yusuf, saboda ko minti biyar liman ya ƙara bezo ba, se kaji ana Malam Yusuf a jamu salla, saboda kawai suji ƙira'arsa me daɗin sauraro.

Zuciyar Salma ta kwaɗaitu da san ganin Yusuf, saboda yadda take jin ana maganar sa, wataran da yamma taje karɓar kuɗi a chemist ɗin Usman, Yusuf yaje siyawa Umma Inhaler, tunda ya shiga daga tafiyarsa ma taga yadda yake taku cikin nutsuwa, yayi sallama suka amsa sannan ya gaishesu, ƙamshin turarensa ya gauraye shagon, Salma ta shagala da kallonsa, wanda shi sam be san ta nayi ba, ya karɓi abunda ze siya yai waje.

Yana fita Salma tace  "Masha Allah, Yaya wannan ma a unguwar nan yakene? Kaga mutum nutsatse, ga ƙamshin turare, wanda seka gifta maza goma ba kaji ba, se warin hamnata mussman irinsu Yaya Habu"

Usman yace "Allah yasa yaji abunda kikace ya casaki san ransa, shegiya uwar leƙe leƙe, duk tarin samarinki amma kuma kina yaba wani"

Tace "kai Yayana, wallahi ko kai da kake namiji kasan gayen nan ya haÉ—u, kaga da yai murmushi, wasu dimples suka lotsa wayyo Allah na, gaskiya me kyau ne, kuma me ajine"

Usman yace  "dalla wuce can, haka zaki ƙare ƙarshe mummuna zaki aura"

Tace "Allah ya kiyaye, aini naga miji"

"A ina?"

"wannan wanda ya fita É—in mana, in dai a unguwar nan yake, ina ciki"

. Usman yace "aikuwa zakiyo waje daga cikin da kika shiga, dan girman kaine dashi kamar ƙaruna"

Salma tace "kamar yaya kenan?"

"Shine fa Yusuf É—in da muke magana, wanda Habu yake zagi"

Salma tace  "haba dai? Wayyo Allah na gaskiya ya haɗu, bashi da makusa, ga kyau ga ilimi ga nutsuwa ga tsafta, gaskiya yamin"

"to 'yar wahala, wata wahalar ta ganki kenan, dan wannan banga ta inda ze kulaki ba, dukda wannan koÉ—aÉ—iyar fatar taki"

"to fatar tawa ma hassada ake mata, to Allah ya shiryeka, ni na tafi ka tayani addu'a kawai"

Ta juya ta fita da sauri, tun daga ranar ta gano gidansu Yusuf, take daidaitar lokacin fitarsa da dawowarsa, idan ta ganshi se tayi masa magana, farko da yake ƙin amsa gaisuwarta tayi zaton zancensu Habu haka yaje yana da girman kai, seda taje gidansu sawa Ummansa Ruwa taga yadda yake aikin gida, ga shagwaɓa kamar mace, ga tsananin biyayya ga mahaifiyarsa, anan ta gane mutane da yawa basu fahimce shi ba, bashi da son shiga mutane ne, amma mutum ne simple.

Tun daga nan Salma ta liƙe masa, idan ta ganshi seta masa magana kota tsikane shi, wataran sedai ya harareta yai tafiyarsa, ta maida gidansu Yusuf gidan zuwanta, ko tayo girki ta kawowa Umma, ko tazo nan gidan ta tayata aiki.

Sabo ne ƙarfi ya shiga tsakanin Umma da Salma, tana jin daɗin yadda take girmamata take tayata wasu ayyukan, dukda Yusuf haushin Salma yake ji amma a hankali, saboda soyayyar da take nunawa Ummansa da mutuntawa yasa, yake ɗan saurara mata kuma har cikin ransa yake jin daɗin kulawar da take nunawa mahaifiyarsa.

Wataran Salma taje gidansu Yusuf wajen ƙarfe sha ɗaya na Safe, ta tarar da babur ɗinsa be fita ba, ta shiga cikin gidan ta tarar da Umma a tsakar gida hannunta da mayafi, Salma tace  "Umma ina zuwa haka? Kuma Yaya Yusuf be fita bane? naga babur ɗinsa"

Umma tace "dama chemist ɗin yayanki zanje, kwanan sa kusan biyar yana zazzaɓi sama sama, nayi nayi yaje Asibiti yaƙi yau jikin nasa rau da zazzaɓi ko gurin aiki ya kasa fita, shine nace bari in kira yayanki, ya duba shi idan akwai abunda ze iyayi masa to, in kuma babu mutafi Asibiti, yana jin jiki, kin san shi da dauriya da taurin kai, yauma dan yaji uwar barine ya kasa fita gurin aiki"

Salma tace "Ina Yaya Yusuf É—in yake? Nima zan iya duba shi ai"

Umma tace "muje yana É—akinsa"

Umma na maganar aka kirata a waya, ta tsaya ɗagawa Salma ta shiga ɗakin nasa da Sallama, ɗakin tas dashi kama r na mace, komai fes fes se ƙamshin turaren wuta da drumer ke tashi, gwanin ban sha'awa.

Ta hango Yusuf kwance akan gado, ya lulluɓa da bargo, a hankali ta ƙarasa gaban gadon nasa, tasa hannu ta janye bargon tace  "to shagwaɓaɓɓe, kazo ka kwanta kaƙi zuwa Asibiti, ka tayarwa da Umma hankali"

A hankali ya buɗe idonsa ya kalli Salma, cikin ƙarfin hali yace  "malama fitarmin daga ɗaki"

"bazan fita ba É—in, meke damunka ummance tace inzo in duba inga me ya kamata ayi maka"

Lumshe ido yayi yaƙi magana, Umma tazo tace "Salma yaya? Za'a iya duba shi a gida"

Salma tace "eh, za'a iya, zanje in karɓo ruwa da allurai in masa, amma ya rage kayan jikinsa, ki shashshafa masa ruwa ina zuwa"

Haka akayi Salma ta sassaka masa ruwa, da allurai sannan Yusuf ya samu kansa.

Washegari da safe da ta dawo, ta tarar da abokan aikinsa sunzo duba shi, babu wanda yasan Yusuf É—an sanda ne a unguwar dan haka Salma tayi zaton 'yan uwansa ne suka zo duba shi, ta taho masa da Abinci daga gida.

Abbas yace  "Yusuf ka samu kaci Abincin mana"

Yusuf yace "bani da appetite ne, amma zanci"

Sakina tace "ko in zuba naka, ka É—anci ko kaÉ—anne?"

Salma tace "No karki damu, zeci in kun tafi da kaina zan bashi ko Yayana"

Sunkuyar da kai yayi yai mata shiru, yayin da Abbas suka shiga tsokanarsa, Sakina kuwa ta dinga harar Salma, ta dinga cika tana batsewa, saboda gaba É—aya Haushi Salma ta bata.

Bayan ya warke ya koma gurin aiki, sedai Sakina ma ta fito da manufarta na soyayyar ta ga Yusuf, sedai Yusuf ya nuna mata sam shi babu wannan, babu maganar soyayya a tsakaninsa da ita.

Salma kuma ya maida ita kamar Ƙanwarsa, dan wataran shike ɗakkota ma daga inda take attachment, kusan duk ta kori samarinta saboda Yusuf, se sukai sha ɗayan dare suna waya, amma sam shi Yusuf ba wai dan yana sonta ba, dan ya ɗauketa ƙanwa ne kuma takan bashi shawarwari masu kyau.

Ita kanta Umma ita duk a zatonta soyayya ce tsakanin su, tana ta jin daÉ—i tana murna Yusuf zeyi dacen mata, dan Salma akwai kirki sosai.

Wataran Umma ta sai wata doguwar riga me kyau, ta saiwa Salma ta bawa Yusuf tace shi ze kai mata rigar.

Haka Yusuf ya karɓi riga ya kai a matsayin shine ya siya, Salma ta dinga murna tana masa godiya, har ze tafi tace  "Yayana nawa nikaɗai"

Yusuf yace "meye kuma? Dare fa yayi ki bari in tafi gida"

Salma tace "Yusuf yaushe zamuyi Aure ne?"

Yusuf yace "what? Aure kuma Salma? Ai babu batun aure a tsakanin mu, ni ƙanwa na ɗaukeki fa"

"Yusuf, ƙanwa kuma? Yanzu duk abunda ke tsakaninmu ba soyayya bace? Yusuf na kori kowa a samarina, babanmu ya tambayeni, nace ni kai na tsayar yace in sallami masoyana, amma ka cemin babu soyayya a tsakanin mu?"

Yusuf yace "Salma, banyi hakan da cutar dake ba, amma dan Allah kiyi haƙuri, ni gaskiya ban shirya yin aure ba"

Ai bata jira me zece ba ta shige gida da gudu tana kuka, Yusuf ya dinga mamakin son da take masa.

Kwana biyu Umma taga kwana biyu ba taga Salma ba, tacewa Yusuf   "kaga kwana biyu banga 'yata ba, ko zaka je anjima ka jimin ko lafiya?"

Nan Yusuf ya warwarewa Umma komai, aikuwa ta sameshi ta inda ta shiga bata nan take fita ba,  "haba Yusuf, dan wulaƙanci yanzu duk sintiri da ɗawainiyar da yarinyar nan take damu, kace kai bakama san sonka take ba? Ni ina nan na saki baki zan samu Kayi Aure amma ka cemin kai bakama son sonka take ba? Idan ba sonka take ba ubanka take yi? Wani irin mutum ne kai Yusuf? Haba Yusuf haka rayuwa zata yi? Ba zakayi Aure ba haka zamuyi ta zama a cikin gidan nan, kamalar mutum ai aure, amma kai in anyi gabas seka yi yamma, duk abunda mutane ke gani daidai kai Ba haka yake a gurinka ba? Haka rayuwa zata tafi a haka? Wallahi in baka yi wasa ba haƙƙinta ze kama ka "

Ganin ran Ummansa ya ɓaci, yasa ya shiga damuwa ya dinga bata haƙuri, tace idan yana son ta haƙura yaje ya rarrashi Salma sannan ya amince zw Aure ta, tunanin Farko daya fara zuwa zuciyarsa shine waye ze tsaya masa yayi Auren? Amma gudun ɓacin ranta yai shiru.

Yaje gidansu Salma ya tarar bata da lafiya duk tayi wani iri saboda damuwa, Yusuf ya dinga rarrashinta, ya tabattar mata da ya amince da batun Auren, Salma ta dinga murna, take taji tama warke daga ciwon.

Suka shiga soyayya shida Salma, shi dai tausayinta da yake ji yafi yawa, dan baze ce ga takamaimai feelings É—in da yake dashi akan Salma ba, Sone da tausayi, ko kuma tausayin ne kawai.

Nan aka shiga gulma a unguwa, wai Yusuf daga zuwansa yasa Salma ta kori kowa yana juyata yadda yaga dama, ya maida ita 'yar aikin babarsa, kullum cikin sintiri take  a gidansu, saboda Salma yasa ya fara kula yayyenta a hankali sukuma suke jansa cikin jama' ar unguwa dan seka zauna dashi zaka gane bashi da wani girman kai.
Chapter 64 · 0% Book details