← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 127

Sashe 30

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace  "Hindu ce ta bani, ina son wannan abubuwan da Aya, da wata baƙar aba mulmulmulalliya, da yama sunanta wani abu baƙa cikinsa ja ƙanana me ɗan tsami tsami"

Yusuf ya jinjina kai yace  sannu bagwariya, ɗinya da tsamiyar biri dai ko? "

Widad tai murmushi tace " what ever dai "

Haka ya kammala shafa mata mai, se sheƙi fatar take saboda man zaitun daya shafa mata, yaje ya buɗe Akwatinta ya ɗakko mata kaya, Ya kalleta yace  " bari in samiki "

Tura baki tayi tace "A'a bana so"

Yusuf yace "Meyasa ba kyaso? Ai tunda na shafa miki mai saura sa kaya kuma"

Tace "A'a ni gaskiya bana so, ka ƙyaleni kawai in saka abuna"

Kokawa suka shigayi ita da Yusuf, aikuwa ta buɗe baki ta shiga kiran sunan Gwaggo da ƙarfi, ba shiri ya cikata ya  ƙyaleta, dan a wautar Widad ba taƙi azo a tarar dasu a haka ba in be ƙyaleta ba, ta koma gefe tana harararsa hadda murguɗa baki.

Yusuf yace "Ni kikewa wannan ihun Masoyiyya?"

"An maka É—in, waye yace kamin abunda zanyi ihun?"

Murmushi yayi yace  "Shikenan Allah ya baki haƙuri"

Zumɓura masa baki tayi, ba tare da tace komai ba.

Labari ya game gari a game da Yusuf, Nurat tana kwance tana kallon labaran dare a TV aka nuno zancen Yusuf, ta kaɗu matuƙa da ganin labarin da gudu ta tafi ɗakin mahaifiyarta tana ƙwala mata kira.

"Ke lafiya kike ƙwalamin kira hak?"

"Mummy kinga abunda na gani kuwa?"

"Ta yaya zanga abunda kika gani? Ina nan kina can"

"Mummy an buga fastocin Yusuf, wai he is wanted shine yayi garkuwa da Widad sannan yayi da mahaifinta"

Tace  "wai waye Yusuf ne?"

Nurat tace "Mummy direban Widad ne fa"

Tace "Allah sarki, dama duk abun nan shine ya sacesu aketeta nemansu?"

Nurat kamar ta fashe da kuka tace "Mummy, ki gane me nake nufi mana, wannan abun duk shirin su Daddy ne, Daddy ne suke ƙulla wannan abubuwan, Yusuf bashi da laifin komai fa"

Da sauri Mahaifiyarta ta riƙota, ta rufe mata baki tana waige waige, a fusace ta kalli Nurat tace  "waike yaushe zakiyi hankali ne? Kina kallo kwanan nan ya kusa halakaki, shine kike wannan maganar, maza ki bari ya jiki idan ya ƙarasaki shikenan"

Cire hannun Mahaifiyarta tayi daga bakin ta ta kalle ta tace "haba Mummy, yanzu shikenan mu zuba ido babu wani abu da zamuyi, wallahi Umma Yusuf baze sace Widad ba, ina yaga yadda ze iya sace Daula a gadon Asibiti, shikenan idan baka da kuÉ—i baka da gata a garin nan?"

"to dan ubanki kije kiyi tayi, ina gargaɗinkibakan shiga wannan sabgar tasa, akan ya hana ki fita kawai ya kusa aikaki lahira, amma se sake cusa kanki kike kina bin diddiginsa, ki cigaba karki fasa, inya kasheki ya kashe banza dukda shiya haifeki, kinfi kowa sanin takun saƙar dake tsakaninsa da Daula, kuma kin san alwashin da yayi, ki cigaba da sa kanki a lamuransa, inkin ƙiji ba zaki ƙi gani ba"

"Amma Mummy......"

A fusace tace "Amma me? Kije kiyi dan ubanki karki fasa, fita ki barmin É—aki"

Jiki a sanyaye ta fito daga É—akin, tana jin wani irin jiri yana kwasarta, tana fitowa falo taci karo da mahaifinta, yana shirin fita, suka haÉ—a ido ya ganta kamar wata mara gaskiya, tana tafiya a hankali, ya kalle ta yace "ke lafiya kuwa?"

Ba tace masa komai ba, se binsa da tayi da ido.
Yace  "jeki ki kiramin mahaifiyar ki" ko kallon inda yake ba tayi ba, ta shige ɗakinta ta kulle ƙofa, ta faɗa kan gadonta ta fashe da kuka.

Mamaki ne ya kama Alhaji Musa, ya nufi ɗakin Maman Nurat, yaje ya tarar da ita tana gyara kan mudubinta, ya kalleta yace  "to uwar masifa, hala wani abun kikayiwa yarinyar nan, na ganta a waje na mata magana taƙi kulani"

Wata uwar harara maman Nurat tayi masa tace  "masifa harna kaika, daka kusa hallakata saboda tsabar masifarka da son zuciya, niba wani abun nayi mata ba, halayenka ne suke baƙanta mata zuciya"

"Halayena kamar yaya?"

Tace "Ahh gaba ɗaya ka canza mana, kana treating ɗinta kamar ba kai ka haifeta ba, dole ranta ya dinga ɓaci"

A fusace yace  "ƙarya kike munafuka, kece kike zigata, idan ba haka ba ya za'ai in haifi 'ya sannan kikama kawomin ƙabali da ba' adi, babu yadda za'ayi 'yata ta dinga min wannan halin na taurin kai, in bake kike zigata ba"

Ta Harare shi tace  "au har kamanta tantama kakeyi akan ko kai ka haifeta? Ai baka da tabbacin kaika haifeta ko ba kai ka haifeta ba"

"Malama karki gayamin maganar banza, Nurat' ya tace nina haifeta, kuma ina son abata"

Tsaki tayi ta miƙe tace  "ƙaryar banza kawai, ji wata fuffuka kake 'yarka ce, bayan da hannunka ka kusa kasheta"

"Muka kusa kasheta dai, waye sila?"

Banza tayi masa ta shige banɗakinta, ta rufe ƙofa ta barshi a gurin a tsaye.

Juyawa yayi ya fito daga ɗakin, ya kuma kallon ƙofar Nurat, still a rufe take bata buɗe ba, girgiza kai kawai yayi ya fice abunsa.

Ita kuwa Nurat tana cikin É—akin, se rusa uban kuka take, tana jinjina zalunci irin na Mahaifinta, sun haÉ—a kai sun sace 'yar Daula tare da Yusuf, kuma ya koma sunsa ace shine yayi garkuwa da mahaifinta, tuna tana iya kukan hawaye na zuba, har tayi shiru se ajiyar zuciya da take yi.

Da Yamma Widad suna zaune dasu Hindu, kowacce da littafinta tana koya musu karatu, cikin ikon Allah da yake sunsa kansu, suna fahimtar karatun sosai, duk me tambaya ta bashi damar ya tambaye ta, dukda idan tare da su Indo take koyawa Hindu karatu bata wani sakar musu fuska, amma a hakan girmamata sukeyi sosai, saboda bata hantararsu sam, bayan sun kammala karatun ne kuma ta shiga yi musu bayani akan tsafta da mahimmancinta, ta shiga ɗakinta ta ɗakko musu pad a cikin wadda Yusuf ya siyo mata, ta bawa kowa ɗaya, tayi musu bayanin yadda ake amfani da ita, da kuma yadda zasu dinga kula da kansu lokacin al'ada, kunya suka dingaji suna wani sinne kai, hakan seda ya kusa bawa Widad dariya, dan sam ba taga abun jin kunya a bayanin nata ba, suka karɓa suka dinga yi mata godiya, suna nan zaune suna bitar karatun da tayi musu, ita kuma tana ta faman saƙar mafici da Hindu ta koya mata.

Yusuf ne yayi Sallama, suka amsa gaba ɗaya suna gaishe shi, hannunsa ɗauke da ledoji, Widad ta kalle shi ta basar tana zumɓura baki, Gwaggo ta harareta, ta gane kallon da Gwaggon take mata, taje ta karɓi kayan hannun Yusuf ne, aikuwa ta tura baki tace  "mhmm Mama kayanfa da nauyi, kuma ze iya kaiwa ɗakin"

Dariya ta bawa su Indo, dan yadda take haɗe rai tana koya musu karatu, bazaka ce tana dariya ba, Gwaggo tace  "haba yarinyar kirki, aikin ladane fa duk abunda kika masa yaji daɗi lada zaki samu, ko ba kyason ladan ne?"

"Ina so mana"

Gwaggo tace  "Yawwa 'yar Albarka, aje a karɓi kayan hannunsa"

Widad ta miƙe ta ƙarasa inda Yusuf yake yana kallonta, tana zuwa ta karɓi leda ɗaya tana harararsa, Yusuf yace  "to mara kunya, ni kike harara ko?"

"Mama kinga yana cemin mara kunya ko?"

Gwaggo tace  "Allah ya huci zuciyarki, tuba muke, kai kuma haka akeyi, ka samu za'a karɓi kayan naka shine za kace mata mara kunya?"

Yusuf yayi dariya suka wuce ɗaki, Hari tace  "wallahi Wudas ɗin nan ba ƙaramar taɓararriya bace, gaba ɗayanta gaɓuwa ce"

Hansai tace  "Allah yasa ta jiki, ta ƙare miki tatas ai"

Me gari kam yana ɗaki yana jin dramarsu, koda ya fito ya kalli Gwaggo yace  "Allah ya saka miki da Alkhairi Hasana, kina ƙoƙari da wannan 'yar taki"

Sukayi dariya, ya koma kan É—aliban Widad yana cewa "masha Allah, kuna gane karatun dai ko?"

Hindu tace "muna ganewa sosai"

Ya kalli inda Hanne take zaune, yace  "ke ina naki littafin?"

Hindu tace  "ai banda ita ake koyamana"

Me gari yace "saboda me banda ita? Ke meyasa ba zaki koya ba? '

" Baffa ni bana so" Hanne ta bashi amsa.

"ba kyason ƙaniyarki, kije ki samu Ila, ki gaya masa nace idan yaje kasuwa ya taho miki da kayan rubutu kema, idan na kuma zuwa na tarar ana karatu bake senaci mutuncinki"

Kallon me gari tayi, ta yaya ma zata fara zama wannan mara mutuncin, 'yar wulaƙancin ta koyar da ita? Shiru tayi masa taƙi kula shi, dan ba zata taɓa zama wannan banzar ta koya mata karatu ba.

Gaba É—aya Anwar a rikice ya shigo babban falon gidan, ya tarar da Amal da Hajiya Halima na shirin fita, yayin da Ramlah ke zaune tana zuba Coca-Cola a kofi tana sha a hankali.

"kai lafiya kuwa na gankaba haka? Kamar wani korarre?"

"Mummy, kin saurari labarai ne yau? Ko kuma kin kalla?"

"A'a ni kasan ba wani shiri nake da radio ba, dama da Daula yana nan ne, shine sarkin labarai da radio saboda kasuwanci"

Anwar ya girgiza kai yace  "Mummy, na rasa mema zance miki, yanzun nan naji a labarai, wai hukumar 'yan sanda sun fitar da sakamakon binciken ɓatan Widad"

Cikin Hajiya Halima yayi wata ƙara, ta dake tace  "me sukace, ni sam banji labarai ba, am ganta ne?"

"Mummy wai ana zargin Yusuf ne yayi garkuwa da ita, ya nemi maƙudan kuɗaɗe da aka hana shi, shine yayi garkuwa da Daddy"

Wani sanyi ne ya ratsa Hajiya Halima, dan ba ƙaramin daɗi labarin yayi mata ba, amma ta nuna kaɗuwarta a fili tace  "to yanzu ya ake ciki? An kama shi ne?"

"Mummy ba'a kama shi ba, amma ance duk inda aka ganshi ko a mace ko a raye a kamo shi, Amma ni sam banji na yadda da wannan labarin ba Mummy, ya za'ayi Yusuf ya iya aikata haka? Yusuf baze wannan abunba, dukda ban daÉ—e tare da shiba, amma beyi siffar miyagu ba, ni ban yadda da wannan labarin ba"
Chapter 30 · 0% Book details