Sashe 83
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hari ta tashi ta shiga ɗakinta ta samo mukulli, tana ƙoƙarin rufewa taga bokitinsu a tsakar gida, ta tafi ta ɗakko bokitin, kawai ta fashe da kuka tace " Allah sarki Wudas, da yanzu muna faɗa akan ruwan zafin da zata yi wanka, tace sena bata na bawa mijin ta, ban taɓa ganin abun tausayi kamar yau ba, yadda ta rikice tana kuka, Allah sarki Allah ya fitar dasu"
A kaita bata haƙuri, aka kulle ɗakinsu aka bawa Megari mukullin, ya kai ɗakinsa ya ɓoye.
Yusuf yana kwance a cikin cell, an raba masa cell shida Saleh, sauro yana ta masa buduri a ka, yai rigingine yana tunanin ya Umma zataji idan wannan mummunan labari ya isheta?.
Aka buɗe ƙofar cell ɗin, wasu 'yan sanda suka shigo su biyu, ya tashi zaune yana kallon su.
Ɗaya ya kalleshi yace "munafuki, kalleshi kamar na Allah, amma ƙasurgumin Azzalumi ne, kai garkuwa da' ya ka koma kayi da Ubanta, saboda kai Azzalumi ne, kuma a haka wai kai ɗansanda ne"
Yusuf yai shiru be ko É—aga kai ba, É—ayan yace "rabu dashi corporal Sani, zuwa gobe in Allah ya kaimu semun sauya halittun fuskarsa, kafin 'yan jarida suzo, a buga shi a nunawa duniya shi, azzalumin banza dana wofi kawai"
Yusuf dai yai shiru bece komai ba, suka gama zage zagensu suka fita, suka sake rufe shi, tun Abincin safe Yusuf be kuma cin komai ba, ga doguwar tafiyar da suka yi, amma sam baya jin yunwa tunanin makaomarsa kawai yake a wannan hali da yake ciki.
Nurat na kwance cikin dare, taji Mahaifinta yana waya ƙasa ƙasa, ya fito daga ɗakinsa da alama dai fita zeyi, ta kalli agogo ƙarfe biyu da rabi na dare, ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito falo, aikuwa yana fitowa ya ganta a falo, ya ɗan haɗe rai yace "ke me kike yi a falo a wannan tsohon daren haka?"
Tace "ruwa na fito sha"
"ina ma fridge É—in dakinki?"
"yayi sanyi da yawa, duk ya zama ƙanƙara shiyasa na fito"
Yace "to kin sha É—in ne kokuwa?"
Tace "A'a yanzu dai zan sha"
"maza jeki sha, kizo ki wuce ki kwanta"
Ta nufi hanyar kitchen, tana tunanin ina zashi a wannan tsohon daren, ta fito ta tarar da shi a falon a tsaye, yace "kinsha ruwan?"
Tace "eh na sha"
"to maza ki wuce, ki tafi É—akinki ki kwanta"
Harta juya ta tafi, ta waigo taga yana tsaye yana kallon ta, tace "Amma naga kamar fita zakayi, ina zaka yanzu dare yayi sosai"
"Yaushe na fara wasa dake? Ko kuma kika zama uwata da zaki dinga tuhuma ta haka?"
"hmm Daddy kenan, ai kaine kake abun tuhumar, wani irin abune wannan da ba'ayi ido ma ganin ido ba se yanzu a tsakiyar dare haka hmmm Allah dai ya kyauta?"
Ta buÉ—e É—akinta ta shige, ta barshi tsaye yana binta da kallo, yarinyar da idan ta ganshi jikinta ke rawa, itace take gaya masa magama haka, tabbas uwarta ce ke zigata kuma zeyi maganinsu gaba É—aya.
Kamar yadda suka saba haÉ—uwa yauma sun hallara gabaÉ—ayansu, suna zazzaune a É—akin Hotel É—in da ya zamana babu ma me kama shi sesu.
Bukar yace "kyakkyawan labari"
Alhaji Musa yace "muna jinka"
Alhaji Bukar yace "yaron nan yazo hannu"
Sukace wane yaron?
Alhaji Bukar yace "ku duk baku sani ba, dukda yadda da labarin ya yaÉ—u a daren nan? To ina nufin Yaron nan Yusuf, direbanta wanda aka yi garkuwa dasu tare"
Sukace "Alhamdilillah, abu yayi kyau"
Alhaji Bukar yace "An kamosu a wani ƙauye a Bauchi, inda Saleh ya basu mafaka, yanzu haka yana hannun 'yan sanda, za' a tattare duk wata sheda da ta kamata daga nam za'a kaishi kotu, zamu saki kuɗi ayi masa shari'a da hukuncin daya dace da shi, saboda babu wanda ya ta:a kawo mana cikas da tangarɗa a harkar nan kamar shi, kunga daga nan babu wanda ya isa yace mune muka sa akayi garkuwa dasu"
Alhaji Munir yace "good, wannan abu yayi kyawuuu sosai, kuma ya tafi yadda ake so, dan haka semu hanzarta, mu kuma samu hanyar da zamu ɓalli namu kason tun kan Daula ya bayyana, dan shi har yanzu bamu san fa inda yake ba, kar muje wasu su rigamu karɓa abun nan fa"
Bukar yace "na toshe duk wata hanya da zata saka wani ya mallaki abun nan bamu ba, sannan dole nasa a matsa yaron nan, idan ma abun yana hannunsa ya faÉ—i inda suke"
Alhaji Musa yace "kai amma abu yayi kyau wallahi, komai ya tafi yadda yakamata"
Alhaji Bukar yace "Haruna ina takaddar da wancan yaron ya bari, É—an gurin Halima? Shima nasa a nemo shi, duk inda aka ganshi kawai a kawar dashi, bama san duk wani abu da zesa a samu sheda a kanmu"
Alhaji Haruna yai tsilli tsilli da ido yace "Amm.. Mm.. Wallahi an ɗan samu akasine, na rasa inda takaddar ta faɗa amma ina ta ƙoƙarin dubawa"
Alhaji Bukar yace "Amma kasan bana son akasi ko?"
Yace "Ayimin afuwa dan Allah, Insha Allah za'a nemota in kawo"
Alhaji Bukar yace "shikenan, nan da kwana bakwai, na baka isashen lokaci, nan kusa nake so a fara shari'ar yaron nan, ba da nisa ba, kuma ina son a rufe duk wata hujja da zata bayyana mu"
Alhaji Haruna yace "insha Allah, zan kawo takaddar nan ba da jimawa ba"
Haka suka gama tattaunawa sannan suka watse.
Widad ce ke ƙoƙarin farkawa, se jujjuya wuyanta take tana kuka cikin bacci, "Wayyo Allah na, yuzarsef yunwa nake ji, zuciya ta ciwo take, Yoseef dan Allah, dan Allah ka dawo please! Ta farka a gigice tana kiran Yoseef! Yoseef kana inane?"
Bulama ne da Matarsa Hajiya Sarah a gigice suka yi kanta gaba ɗaya, Bulama yace "Sannu daughter, sannu ki kwantar da hankalinki, kin ganni a tare da ke, ga Maman Iman ma, an kuɓutar dake ki kwantar da hankalinki"
"Ni bazan kwantar da hankalina ba, ina mijina yake? Ina Yoseef kace su sakarmin shi, ni ba saceni yayi ba, wallahi idan basu sake shi ba mutuwa zanyi, laifina ne, duk saboda ya ceceni haka ta faru dashi, beyi laifi ba, tun farko seda na gaya masa death contract ne amma ya amince, kaga abunda nake nufi Yoseef, dan Allah ku ƙyaleshi idan wani abu ya sameshi bazan yafewa kaina ba, dan Allah ka cewa Bukar na dawo, ni yazo ya kamani yasa a sakarmin mijina dan Allah "
Tai maganar wasu irin hawaye na ambaliya daga idonta, idanun da suka rine zuwa kalar ja jawur suka kumbure.
Bulama yace "toni ina na san wani Bukar, balle in nemo miki shi? Ke kaÉ—ai kika sanshi, ni ban san a inda yake ba"
Kafin ya rufe baki...
Ayi subscribing YouTube channel É—ina please 🙠🙠🙠ðŸ™
Ayshercool
11/23/21, 8:06 AM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
118_119
Alhaji Haruna kam juyi yayi ya farka ya ganshi kwance a gurin daya sha lemon nan, shi dai yasan da magariba Amal tazo, amma yanzu yaga kamar yammace, nan da nan ya tashi da sauri yana dube dube, ya kalli agogo yaga ƙarfe biyar na yamma, ya duba yaga wayarsa a gefensa a kashe, me yarinyar nan tayi masa haka? Ko kuma meye ya faru da shine?
Yai yai ya tuna wani abu amma ya kasa, ya gagara tuna komai daga inda ya sha lemon nan baya iya tuna komai, ya tashi ya fito falonsa amma komai yana nan yadda yake, babu abunda ya canza.
Duk ya lalleƙa babu wani canji daya gani, amma ya akayi yayi wannan baccin haka?
Ya tambayi kansa, tabbas wannan yarinyar ce tayi masa wani abu, sedai ya kasa gane meyafaru dashi.
Sunusi duk yadda yake tunanin lamarin ya wuce nan, dan daya zo Kano ya samu labarin inda su Saleh suke tsare, sedai tun daga bakin gate wani yace masa tun wuri yayi takansa, karma a san daga imda yazo ko kuma shi wanene a gurin Saleh, idan ba haka ba tabbas shima kamshi zasuyi su rufe har dashi.
Haka Sale ya koma babu wani daddaÉ—an labari, su kuma su megari suna can suna jiran sa yazo ya gaya musu yabake ciki, sedai yanayin fuskarsa kawai ya nuna musu babu nasara.
Me gari yace "Sunusi, kayi mana bayani, da kaje kanon menene ya faru? Ya kukayi dasu?kaga su Yusuf É—in da Saleh fatan suna lafiya?" megari ya jero masa tambayoyin.
Sunusi yace "Baffa, lamarin nan fa ya wuce inda kake tunani fa, duk abun ba yadda muke tunani bane, ita wannan yarinyar daka gani, matar wannan Yusuf ɗin Wato Widad, 'yar gidan Alhaji Nasir Daula ce, wai ance Yusuf ɗin ne suka haɗa kai da Saleh sukayi garkuwa da ita, dan su karɓi kuɗin fansa, shine sukazo suka ɓoyeta a garin nan"
Hansai tace " wai Daula dai shahararren attajirin nan da ake labarinsa? Wanda ake yawan faÉ—ansa É—in nan"
Sunusi yace" to da daulan guda nawane? Shi dai 'yarsa ce"
Gwaggo tace 'biri yayi kama da mutum, kwata kwata yarinyar nan ba kalar wahala bace, yanayin yadda take rayuwarta da yadda bata iya wasu abubuwan ba ze tabattar maka da bata tashi cikin wahala ba, sedai gaskiya bazan taɓa yadda wai satota sukayi ba, nan fa suka zo da ita babu lafiya Yusuf ne ya goyota a bayan sa, bata yadda da kowa seshi farkon zuwa su, kuma da satota yayi da tabbas tayi yunƙurin guduwa wataran "
Hari tace " Akwai dai wani abu a ƙasa, amma yadda take ji da Yusuf ɗin nan ƙaryane a ce satota yayi, komai shi, kullum tana liƙe dashi, sannan ace satota yayi gaskiya ban yadda ba sam "
Sunusi yace " to kai Baffa da baka san daga inda suke ba, ka karɓe su?"