← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 127

Sashe 19

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan mun rabu shine zaka ce bazaka dawo gidanmu ba, sannan idan na koma gida dole ta bar mana gida"

Yusuf yace "meyasa?"

"Saboda wani dalili me girman gaske, amma yanzu ba wannan maganar muke ba, dan Allah idan mun koma gida ka dawo gidanmu da zama,"

"Nida bakya sona, me zan zo gidanku inyi? Idan dai har ina ganinki zan cigaba da sonki ne, kuma ni bakya sona"

"Nifa ba tsanarka nayi ba, kawai ni bana son soyayya ne, ban santa ba kuma ban iya ba, dan bata birgeni, ƙarya ce da tarin damuwa a cikinta, amma ni bana son ko mun koma gida kayi nesa dani, na saba da kai sosai, kana iya haƙuri da dukkanin halayena, kuma kai garkuwa ne a gareni, dan Allah Yoseef ka yadda kaji ɗan uwa"

Yusuf kam murmushi yayi, a ransa yace  'sarkin taurin kai, kina sona amma kina garani'

A fili ya maze yace "Idan muka koma gidanku ace munje kwaÉ—ayi, ni nafison in zauna a gidanmu nida Ummana"

"dan Allah, ba wanda zece muku haka, Dan Allah Yoseef kaji"

Juyowa yayi yana kallonta, har cikin ranta take maganar.

Wani abune ya dinga fizgar Yusuf game da Widad, yana jin wani irin farinciki a tare da shi, abunda bata son dai yayi mata, sedai wannan karon bata hana shi ba, sema biye masa da tayi.

A hankali ya cire bakinsa daga nata ya riƙe hannunta  yace  "ina sonki Habibty"

Ajiyar zuciya tayi ba tace masa komai ba.

Kawai ya tsaya ya zuba mata ido, a hankali tace "yakamata muje muci Abinci"

Yusuf ya cikata, suka miƙe ya shimfiɗa musu abu suka zauna, ya buɗe shinkafa da wake, da manja ya ɗakko tumatir da gurji ya yayyanka, ya juya suka fara ci.

Suna ci yana kallon Widad, ta kwantar da hankalinta, ta rugumi ƙaddarar rayuwarta, da farkom zuwansu ne se yayi fama kafin taci Abincin, amma yanzu hankali kwance ta dinga cin Abincinta.

"Wai meye kake kallona haka?"

"Gani nayi kina loma fiye da tawa, zaki cinye Abincin ki barni"

"Cigaba da kallona, cinyewa zan in barka"

Ya dinga jin farinciki, ganin yadda Widad ɗinsa ke nishaɗi tana fara'a, saɓanin Widad ɗin daya sani a baya, me shegen haɗe ran tsiya da koke koke, mara afuwa da tausayi.

Juyawa yayi gefensa ya tsinko wata 'yar ciwa, ya miƙo mata yana cewa

"If you ask me to be your king, i will turn around and said, you mean to tell me that I can have you when ever I want, i can tell you that I love you when you love me too, no more waiting for ever our love...

Kwashewa da dariya Widad tayi tace " Ai ba haka ake waƙar ba, kuma flower ake bayarwa, amma ni ka bani ciyawa sekace wata Akuya"

Yusuf yayi murmushi yace  "A yanzu bani da wani abu da zan baki ai, shiyasa na baki wannan instead of flower"

Hannu tasa ta karɓa, ta kalli Yusuf tana murmushi.

Saleh ne a gigice ya shiga babban Ofishin dake cikin harabar gurin, Suleiman ne zaune yana danna system É—insa, Saleh ya shigo da sallama.

Suleiman ya ɗago tare da yin murmushi yace  "Masha Allah, yau kaine a ofishin nawa? Kwana biyu"

Saleh ya miƙa masa hannu suka gaisa, yace  "Suleiman ya aikin naku?"

"Alhamdilillah, ya Yusuf fatan yana lafiya?"

Saleh yace  "lafiya ƙalau, yana gaisheku ina sa ran zuwa gurin mahaifiyarsa, im sake kwantar mata da hankali tare da tabattar mata yana cikin ƙoshin lafiya"

Suleiman ya gyara zama yace  "hakane, hakam abune me kyau nima da week ends ɗin nan, naje gidan sedai har yanzu ta kasa kwantar da hankali ta, akwai buƙatar ka ɗakko mata muryarsa, kokuma ka haɗasu a waya su gaisa"

Saleh yace  "No baze yuwu ba, ai bama zuwa garin nan da waya, kai mutanen nan fa sun shallake tunanin ka, nima ina lura da duka abunda nake yi, bana shiga da waya, haka nake zuwa in fito"

"to ubangiji Allah ya kuɓutar dasu, ina mamakin yadda abubuwan suke tafiya, kullum sake taɓarɓarewa sukeyi"

Saleh yayi ajiyar zuciya yace  "yanzun ma matsala ce gagaruma ta taso"

Suleiman ya tattara hankalinsa yace 
"wace irin matsala kuma?"

"mutanen nan sun gano waye Yusuf, kuma suna shirin É—aukar mataki akan hakan?"

Suleiman yace "ya akayi suka sani?"

Saleh yace "niba wannan ba, babban abunda ya dameni shine, rashin sanin wani irin mataki zasu ɗauka akansa, gashi kuma yana can yana cikin zulumi akan ta yaya ze sanar da Widad gaskiyar waye shi, kasanta bata afuwa bata yafiya ga duka wanda yayi mata ƙarya, muddin suka dawo garin nan sannan ta gane waye shi akwai matsala "

Suleiman yace " ai tasan waye shi? "

" kamar yaya? Sannan ta yaya?"

Suleiman yace '" dukda gargaÉ—ina da tayimin, amma bari in gaya maka yadda akayi tasan waye shi, wataran da yamma na kammala abunda nake zan bar office É—in nan, kawai sega wata mota ta shigo gurin nan a guje, kamar zata tashi sama,
ma' aikatanmu sukayi kanta don son ganin wane mara ɗa'ar ne haka? Ko a jikin me tuƙin, Ta buɗe motar ta fito, wata matashiyar budurwa ce jikinta sanye da abaya, ta saka face mask, sannan ta rufe fuskarta da glass.

Kai tsaye inda nake ta shiga tunkarowa, da ma'aikatanmu sunyi kanta zasu hanata ƙarasowa, nace su barta ta ƙaraso.

Ko kallonsu batayi ba tazo inda nake ta tsaya ta kalleni tace "kaine Suleiman?"

Nace mata "Eh nine"

Tace   "ina son muyi maganane"
Nace mata shikenan, nai mata jagora har office ɗina, muka shiga muka zauna, ta kalleni ta cire glashin fuskarta da face mask tace  "kasanni?"

"Nace mata a'a"

Tace "Amma kasan Nasir Daula?"

Nace "ai duk Nigeria babu wanda be sanshi ba"

tace "sunana Widad Nasir Daula, nazo me zan maka wasu tambayoyi, kuma idan ka amsamin ba dai dai ba, ka shirya karɓar abunda ze biyo baya, bana sassauci ga mutane maƙaryata, waye Yusuf?"

Suleiman yayi ajiyar zuciya yace "wane Yusuf É—in?"

"Direbana" ta bashi amsa

Suleiman yace "Yusuf jami'inmun ne, É—an sanda ne na farin kaya" Suleiman ya bata amsa

"danme zaku turoshi? Me yasa kuka turoshi,? wato an haÉ—a kai daku a cuceni"

Suleiman yace  "Yusuf bashi da laifi, jajirtaccen ma'aikacine me kishin ƙasa, umarni aka bamu daga sama akan cewar, a baki kariya sannan kuma ayi bincike akan wanda suke bibiyar rayuwar ki, amma bayan haka Yusuf be san komai ba"

Cikin isa da izza tace  "akan me? Sannan kuma waye ya bada umarnin hakan? Ko kuma ni nace ina buƙatar hakanne? An haɗa kai daku za'a cutar dani, in ba hakaba meyasa Yusuf yasa hannu akan takardar zeyi aiki dani, dukda na gaya masa hakan tamkar saka hannu akan kwangilar mutuwarsane? Na kama Yusuf da bindiga"

Tun anan Suleiman ya jinjinawa Yusuf, ya yabawa ƙoƙarin sa na jure zama tare da yin aiki da Widad, saboda yadda take magana cike da izza da isa.

Suleiman yace " kamar yadda na gaya miki, Yusuf jajirtaccen ɗan sandane, kuma ba abun mamaki bane samun ɗan sanda da bindiga, sannan Yusuf baza'a taɓa bashi aiki ya dawo dashi yace ya karaya ko baze iyaba, amma sam bashi da laifi, kuma da farko bashi mukayi niyyar bawa aikinba, abokin aikinsane yace a bashi saboda jajircewarsa da haƙurinsa"

Ajiyar zuciya Widad tayi tana huci, inda Allah ya temaki Sulaiman gaskiyar data buƙata ita yake gaya mata, ta kalle shi tace  "Ina buƙatar sanin waye yasa a dinga bin diddigi na?"

Suleiman yace  "kamar yadda na gaya miki ne, ban saniba nima umarni aka bani daga sama, ban san komai akai ba"

Widad tace "shikenan, ni zanje in bincika da kaina, amma zan maka gargaÉ—i da jan kunne, Yusuf be san na ganshi da bindiga ba, kada ka kuskura Yusuf yasan nasan waye shi, idan har ka gaya masa nasan waye shi zan gane, and you know what am capable of doing"

Suleiman yace "karki damu, Insha Allah baze sani ba, bazan gaya masa ba"

Tace "and Mark you, bana son kowa yasan da nice nazo gurin nan, and zan cigaba da bibiyarka, duk lokacin da Yusuf yayi misbehaving ko wani abu na yunƙurin cin amana ta, to dasa hannunka a ciki"

Suleiman yace "ina me tabattar miki da babu abunda zeyi na cin amanarki"

Ta miƙe a gadarance, ta maida face mask ɗinta, ta saka glass ɗinta ta fito, sedai tana fitowa Abbas ya kawo kai yana shigowa, ta tsaya ta ƙura masa ido, harya shige wani office, sam Abbas be lura da kallon da take masa ba, ba tace komai ba tayi gaba da sauri ta hau motarta ta bar gurin.

Bayan wasu 'yan kwanaki da yin hakan, Widad ta kira Suleiman tace tana son ya gayamata full name na Abbas da rank ɗinsa, amma Suleiman yace  hakan ya saɓa da ƙa' idar aikinsu, sedai ta gaya masa meyasa take neman hakan, bata kuma bi takansa ba bayan kwana uku, aka kawo transfer later na Abbas aka maye gurbinsa da Yusuf.

Saleh ya jinjina kai yace "wato duk inda mutum yake tunanin hatsabibancin yarinyar nan ta wuce haka, yana cam yana ta zullumi akan yadda ze gayamata, ashe tuni ta sani"

Sulaiman yace "tabbas tasan waye Yusuf, kallonsa kawai take sannan kamar yadda naimata Alƙawari ban gaya masa ba"

Saleh yace "Allah sarki, ni gaba ɗaya tausayi yake bani wallahi, bejiba be gani ba yana ta ɗawainiya da yarinyar ta bata san kimar mutane ba, duk naga ta rage wannan zafin kan nata, ta kwantar da mai tana rayuwa a ƙauyen da babu wuta, babu ruwa babu abubuwan more rayuwa, abun gaanin ban tausayi"

Suleiman yace  "Allah sarki Yusuf, samun mutum me irin zuciyarsa se an tona, ina masa fatan ubangiji Allah ya kuɓutaf dashi, daga sharrin Azzaluman nan"

Saleh yace "Ameen ya Allah, amma tabbas Yusuf yana cikin jarrabawa, dan ina tunanin matakin da zasu É—auka akansa, basu da imani sam"

Suleiman yace "Allah ya fisu kam, amma indai batun sadaukarwa ne, to tabbas Yusuf yayita"

Haka suka cigaba da tattaunawa a tsakanin su.
Chapter 19 · 0% Book details