Sashe 43
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yusuf yace "kije ki kwanta kawai, ni bana jin bacci"
Tace "Shikenan nima bana ji, bari mu zauna kawai"
"A'a, kije ki kwanta kinji nasan zaki bacci idan kika kwanta"
Tace "shikenan, kwanta se in kwanta a jikinka"
Yusuf yace "No jikinki ze ciwo, ki kwanta akan katifarki"
Tai murmushin ƙarfin hali tace "baka san jikinka yafi katifar nan daɗin bacci ba, kwanta se in kwanta"
Haka Yusuf ya kwanta, ita kuma ta kwanta a jikinsa, tasa hannu ta zare ribbon É—in kanta, ta kamo hannunsa ta É—ora a kan gashin ta, a hankali ya rungumeta da hannu É—aya, yasa hannu É—aya yana wasa da gashin nata.
Tana jin yadda zuciyarsa ke lugude da ƙarfin gaske, ya zamana ma taji kamar baya numfashi daidai, dukda a duhu ne amma Widad ta gane har yanzu Yusuf kuka yake, yana da matuƙar dauriya da juriya, amma wannan karon ya kasa jurewar, saboda jin Widad yake tamkar wani sashine na tsoka a zuciyarsa, haka kurum yake jin kamar shi akayiwa laifin ma ba ita ba.
Ƙanƙame Yusuf tayi ta fashe da kuka, Cikin jan numfashi Yusuf yace "Widad lafiya, kukan me kike kuma?"
"Dan Allah Yoseef kamanta da labarin nan da na gaya maka, karkasa shi a ranka dan Allah, kar wani abu ya same ka ji yadda kake numfashi fa"
Sosai ya sake rungumeta yace "Never mind dear, ba abunda ze sameni insha Allah, ina tunanin meye mafita ne kawai, a shirye nake da in baki gudunmuwa kota wani ɓangare dan tina Asirin wanda suke aikata muku wannan zalunci haka, amma kafin nan nasan koba duka ba kin san wasu daga cikin mutanen nan, meyasa kika ƙyalesu baki tona musu Asiri ba? "
" Yossef yadda nake shiri akansu haka suke yi a kaina, sun fini iya mugunta da zalunci, na haskawa mahaifina wasu daga cikin su, hakan yasa ya yanke hulÉ—ar kasuwanci da wasunsu, sannan wace hujja nake dashi daze tabattar da abunda nake zarginsu? Bani da sheda se Allah"
Cikin raɗa Yusuf yaje dai dai kunnenta yace "meyasa kika ƙyale Bulama, bayan ko a binciken da nake, ina sanya babbar alamar tambaya a gareshi, dan sam ban yadda da shiba, amma naga kina masa kallon uba, kuma ni shine babban suspect ɗina"
Widad tace "saboda ko yana ciki ni ba ta tashi nake ba"
"Meyasa?" Yusuf ya tambaye ta.
"Saboda bashi nake hari ba, Bukar nake hari, na barwa zuciyata insha Allah koni ko shi, ko kuma muyi mutuwar kasko dashi, Insha Allah se Bukar yaje ƙiyama da tabon da zan masa, ya azabtar da rayuwata, yaso kassarani da mahaifina yamin zalunci mafi muni, wannan abunda akayi mana nasan da sa hannunsa, da Bukar da Baban Nurat sesun wulaƙanta a rayuwa, sun cutar dani Yoseef " tai maganar tana fashewa da kuka, rarrashinta ya dingayi sannan yace
"Waye kuma Bukar? Banji kin faÉ—e shi a labarin da kika bani ba"
Ta gyara kwanciyarta sannan tace "Bukar! Bukar! Alhaji Bukar! Tabbas ban faɗeshi a labarin da na baka ba, saboda labarin ma wani sashe na baka, na ɓoye maka wani, na kuma canza inda faɗa maka bashi da amfani, saboda jin wani sashin na labarina a gareka tamkar tarwatsa shirin sa nake ne, amma ina fatan ubangiji, Allah ya maida mu gida lafiya, zan baka sauran ɓangaren dana cire maka a labarin, dan se mun koma gida jin ɓangaren zeyi amfani, har in cika dukkan burikana, sannan a lokacin zan baka labarin waye Bukar "
Yusuf yace " Shikenan, ubangiji Allah ya kawo lokacin da zamu koma, Insha Allah se inda ƙarfina ya ƙare Widad, zan baki goyon baya ɗari bisa ɗari mu shiga kowane irin ƙalubale dan cikar burinki"
"Thank you Yoseef, Allah ya jiƙan magabatanka, nagode sosai"
Tai maganar tana Ƙanƙame shi sosai.
Haka suka kwana a ƙasa shida ita, a gurin nan ga sanyi cikin dare amma basu iya tashi daga gurin ba, saboda damuwar da zukatansu suke ciki.
Umman Yusuf se fama take da hawan jini saboda damuwa da tunani, ga rashin cin Abinci da bata iya ci balle bacci, gaba ɗaya ta rame tayi wani iri saboda tunanin halin da ɗanta Yusuf ke ciki, ga kuma wannan labari daya cika gari, ita dai tasan ɗanta ba mutumin banza bane, dan tasan tabbas wannan zance ƙaryace akayi masa.
Tana nan kwance bayan la'asar a inda tayi salla, tana jan carbi tana ta kai kukanta ga Allah akan Allah ya kuɓutar mata da ɗanta, yasa yana cikin ƙoshin lafiya.
Sallama Suleiman yayi, taja jiki da ƙyar ta tashi zaune da ƙyar ta amsa masa, ya tsorata ganin halin da take ciki, a ɗan firgice Suleiman yace "Umma meyasameki haka?"
Take ta fashe da kuka tace "baka ga Sanarwar da akayi a kafafen yaɗa labarai bane? Wai Yusufana ake nema ido rufe wai ya sace 'ya, haɗuwar Ɗana da wannan alhali ba alheri bane, tunda ya fara aiki da yarinyar nan walwalarsa ta ragu kullum cikin tunani yake, kullum cikin damuwa yake banda sintirin fita da wuri baze dawo ba se dare amma ƙarshe abunda za'a sakamana da shi kenan, bakomai akwai Allah, Allah ya bimana haƙƙinmu"
Suleiman yace "Umma kiyi haƙuri, yanzun ma abunda ya kawoni kenan, amma yanzu zan fara kaiki Asibiti tukuna, a duba ki kamar baki da lafiya"
Umman Yusuf tace "Ni ba inda zani, lafiya ta ƙalau ɗana nake tunani kawai, shiyasa ake ganin kamar bani da lafiya"
Da ƙyar Suleiman ya lallaɓata ta yadda ya kaita Asibiti, sukaje akayi mata gwaje gwaje, akace hawan jinine ga ulcer, aka rubuta mata magunguna sannan ya ɗauketa zuwa gida.
Suna tafe tana share hawaye, bayan ya kaita gida yace "Umma ki kula da magungunanki, kidinga shansu akan lokaci, sannan shi lamari irin wannan Addu'ar ku muke nema, idan harda Addu'ar ku, babu wani abu daze same mu insha Allah, Yusuf Addu'ar ki yake nema kiyi haƙuri, komai ze daidaita insha Allah"
"Amma Suleiman, kana ganin yau watanni huÉ—u kenan, ban saka Yusuf a idona ba, baya nan ban san idan yake ba katsam kuma inga wannan al'amari haka, kuma naji labarin Abokinsa Abbas yazo, amma ko jaje bezo yamin ba"
Suleiman yace "ki kwantar hankalinki Umma, Abbas baze dawo miki da Yusuf ba, ki manta dashi, Insha Allah muna nan muna ƙoƙari akai, sannan insha Allah zan kawo miki kayan Abinci dana buƙata, amma kisa haƙuri a ranki"
Umma tace "shikenan, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, Allah yayi maka albarka ya raba ka da duniya lafiya"
Suleiman yace "Ameen" sannan ya tafi.
Aka cigaba da yamaɗiɗi da zancen Yusuf, akan ya sace Widad ya gudu da ita, fastocinsa suka cigaba da yawo, dayake in Allah yasa kana zaman lafiya da kowa, baka rasa masoya, wanda suka san Yusuf suka san halinsa suka dinga ƙaryatawa, suna taya shi da Addu'a.
Ramlah na kwance akan gadon ɗakin Hotel, Fahad yana tsaye yana taje kansa a gaban mudubi, Ramlah tace "Fahad, lokaci fa yana ƙurewa, zuwa yanzu yakamata ace an fara maganar aurenmu, amma naga kamar baka damu ba ko zancem baka yi"
Fahad cikin salonsa na yaudara yace "Beb kin fiye garaje fa, mubi komai a hankali mana, nida nake so ayi classic wedding, so nake bikinmu ya zama the expensive wedding of the year, wasu kuɗi nake jira a hannun Dad, shiyasa amma kiyi haƙuri, soon za'ayi komai insha Allah"
Ta ɗan kwaɓe baki tace "Allah yasa, danni ina ma tantama akanka, kar inje Widad ta dawo kaƙi Aurena kace se ita, dan haka kayi min wancan karon"
"No karki damu, ai abunda yaaa nace zan Aureta, saboda in karɓo mana kuɗaɗen hannunta ne, in rabata da komai im azabtar da ita, sannan in sake ta, that's my plan, but unfortunately it's fails, ni yanzu wannan jakin daya gudu da ita, Allah yasa karya karɓe abun ya barmu "
Ramlah tace 'kamar kuwa ka sani, dan wallahi zata iya bashi, can you imagine ATM ɗinta yayi over 1 week a gurinsa, naje masa mu haɗa kai a samu wani abu amma fafur yaƙi, munafuki se gashi yayi awon gaba da ita"
Fahad yace "suje su ƙarata, ai tunda ba' a san inda Dad ɗinta yake ba, zan cigaba da kawo masu siyan kadarorim nan, a rage wani abun"
Ramlah tace "hakane kam, nidai so nake ayi muyi Auren nan, kaga sau biyu ina abortion fa"
"Ai kece, nace miki kije kiyi planning, amma kinƙi"
"Aini kasan abun planning É—in nan, suna da nasu matsalolin, É—an bani tablet biyu in saka a coc, i want doze up"
Ya miƙo mata magani, ta zuba a lemo ta girgiza tasha, sannan ta kwanta bacci.
Ya kalleta a ransa yace "baki da hankali, uban waye ze Aureki ashe ma bani da hankali, zanta lallaɓaki ina morewa, gefe guda kuma in cigaba da damfararku"
Yauma Yusuf se a É—aki sukayi salla, dan bacci be É—auke shi ba, se daf da Asuba.
Bayan sunyi salla, suka koma suka kwanta bacci, sedai shi Yusuf baccin ya gagareshi sam, a cikin tunanin ma ya raaa wanne zeyi, se kusa ƙarfe goma sannan ya kwantar da Widad ya tashi ya shiga gyaran ɗaki, ya shaee ɗakin ya haɗo kwanukan wanke wanke ya fito tsakar gida.
Da Hanne yayi karo tana shara, tana ganinsa ta zuba masa ido tana murmushi, Yusuf yace mata "Ina kwana"
Cikin yashe baki tace "ina kwana"
Yusuf yace "lafiya ƙalau kina lafiya"
"Lafiya ƙalau, kawo in wanke maka kwanukan"
Yusuf yace "A'a, yi shararki kawai"
"bakomai kiyi aikinki kawai"
"A'a dan Allah ka kawao"
Tasa hannu ta karɓa, Yusuf ya koma ɗaki ya dafawa Widad ruwan wanka, sannan yaje ze tasheta.
Zama yayi ya zuba mata ido, yana jin ƙaunarta da wani irin tausayinta yana ratsa ko ina na jikinsa
Numfashin da yake mata a fuskane yasa ta buɗe ido tana kallonsa, har yanzu idon Yusuf ja, ga alamun damuwa nan ƙarara a fuskarsa.
Yusuf yace "tashi ga ruwan wanka nan, kiyi wanka ki karya"
Miƙa tayi tana ɗan lumshe ido, Yusuf se binta da kallo yake.
"To ka matsa in tashi mana, ka danne ni kuma kana ina tashi"
"Widad bana gajiya da kallon ki, nidai ina sonki Widad"
Ajiyar zuciya tayi, ta shafi sajensa a hankali tace "naji É—agani in cire kaya inje inyi wanka"