Sashe 119
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
160_161
Umma ta bi mutumin da kallo kamar taga baƙuwar halitta, mutumin yace "Madam a bamu guri mu zauna mana, an tsaya ana bina da ido"
Jin yace a basu gurin zamane yasa Umma leƙa bayansa, taga mutumin tare da Widad a bayansa, take Umma ta ɗan tsuke rai.
Mutumin yace "Jidda wannan kallon fa? Ki bamu gurin zama mana"
Umma tai musu jagora zuwa falonta, taje fridge ta kawo musu ruwa da lemo, Widad tace "Umma ina wuni"
Umma ta amsa sama sama, Mutumin yace "Jidda dama rai kanga rai? Rabona dake tun kina budurwa, ban sake sanin inda kike ba, se kwanan nan naji ashe Bashir Maitama ne mijinki, Allah ya jiƙansa da Rahama"
Umma tace "Ameen ya Allah, kwana ba adadi Alhaji Ahmad, dan yanzu sedai ince Alhaji ka ƙara ƙiba, kamar ba kaiba kamaninka sun canza saboda kuɗi sun zauna"
Alhaji Ahmad yace "bari Jidda, abubuwa duk se godiyar Allah kawai"
Ya juya ya kalli Widad yace "daughter na, wannan ce sirikar taki"
Widad ta jinjina kai, Ya kalli Umma yace  "dama kece sirikar tamu kike wahalar min da 'ya?"
Umma tace "kamar yaya kenan?"
Alhaji Ahmad yace "to a al' adar Hausawa dai, namiji ke zuwa biko, to hula taja ɗankwali, munzo muyi bikone, dan Allah a temake mu a bamu mijin mu mana, ayi mana afuwa"
Umma tace "wai ya akayi ta zama 'yarka kuma? Kuma ni gaskiya ina tsoron abunda ze biyo bayane, ni inajin tsoron ɗana ya sake shiga matsala gaskiya"
Alhaji Ahmad yace "labarin dogone, amma dan Allah ayi haƙuri a bamu mijinmu, zamuyi miki bayanin komai, amma waini ina sirikin nawa yake nema? A nunamin shi in ganshi, inga ya yake a yanƙwanamu akansa haka?"
Umma tace "A'a ba wani na musamman bane, kawai ni bana son ɗana ya sake shiga matsala saboda itane, ya wahala fiye da tunaninka, duk saboda ita, wahalar da akayi a baya Allah ya amfana"
Yusuf ne yayi sallama, hannunsa É—auke da ledar aiken da Umma tayi masa, ya shigo falon cikin nutsuwa da sallama, sedai yana ganin Widad a zaune gabansa ya faÉ—i, ya É—an tsaya yana kallonta, ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta.
Yusuf ya durƙusa ya gaida Alhaji Ahmad, Alhaji Ahmad ya amsa yana ƙarewa Yusuf kallo, yace "iko se Allah, lallai dole a mana jan aji akan wannan zuƙeƙen matashin, Widad banga laifinki ba da kikabi kika ɗaga hankalinki akan mijinki, dan an ganshi kyakkyawa shine ake wani jamana Aji"
Yusuf ya É—anyi murmushi, yana son sanin waye wannan mutumin da suka zo tare da Widad?
Yusuf ya maida kallonsa ga Widad, ya ɗan kashe mata ido, amma ta haɗe rai tana ƙoƙarin maida ƙwallar idonta, girgiza mata kai Yusuf yayi, ya ɗakko handkerchief ɗinsa, ya faki idon Umma, ya miƙawa Widad, Alhaji Ahmad suna magana da Umma, amma hankalinsa yana kansu Yusuf.
Yusuf ya miƙe ze bar falon, Widad tabi Yusuf da kallo, kamar zata cinye shi.
Alhaji Ahmad ya kalleta yace "Widad ɗan bamu guri, maza tashi ki bishi, ai tunda Allah yasa munzo se Jidda ta bamu mijinmu, an dena wahalar min da 'ya dan anga yana da kyau, nasan dai' yata tafi shi kyau"
Umma tayi murmushi, Widad kam cikin hanzari ba kara ba kunya, ta miƙe yabi bayan Yusuf, yayin da Umma ta jinjina rashin ta ido irin na Widad "
Suna fita Yusuf ya janyota gefe yace " sweetheart, waye wannan mutumin ne? "
" Nima ban sanshi ba"
"Are you serious?"
"dagaske nake" ta bashi amsa
"Amma ya akayi kuka zo tare?"
"Nifa ban sanshi ba, ya cemin yasan Ummane, nazo mu bada haƙuri"
Yai murmushi yace "shikenan naji, zomuje ɗakina muyi hira kafin su gama maganar"
Widad ta zaro ido tace "haka kurum, Umma tace bani da kunya, ni a nan zan zauna"
Ya shimfiÉ—a musu dadduma, suka zauna hirarsu suke kawai kamar babu abunda yake damunsu, Umma ta fito ita da Alhaji Ahmad, Alhaji Ahmad yace "Widad taso mutafi, se Allah ya kaimu weekends É—in"
Widad ta tsaya tana kallonsa, kamar bata gane me yake faÉ—a ba.
Ya sake maimaita masa maganar, amma Widad taƙi motsawa.
Yusuf yace "ki tashi ku tafi mana"
Aiba kunya Widad ta noƙe kafaɗa, alamar ba inda zata je.
Alhaji Ahmad yace "iko se Allah, kiyi haƙuri kizo mutafi, idan Allah ya kaimu Weekend zamuyi tafiyar nan, kuma ina lallaɓa sirikata mu, dan haka kiyi haƙuri za'a baki mijinki"
Widad tace "dan Allah ni ka ƙyaleni a nan, wallahi bana son zaman gidan nan nika ɗai, damuwa damuna take, dan Allah ka barni a nan zuwa weekends ɗin mu tafi ta nan gaba ɗaya"
Alhaji Ahmad yace "Ikon Allah to sirkarmu kinji abunda tace, bakomai ta zauna É—in a nan, zuwa Allah ya kaimu weekends É—in?"
Umma tace "toni me zance, in dai gidane gashi nan ta zauna, sedai mu bamu da Arziki ba lallai muna da abubuwan da take buƙata ba"
Yusuf a ransa yace "Umma da kin san a ƙungurmin ƙauyen da muka zauna, da baki faɗi haka ba"
Widad kam cewa tayi "Ni dai zan zauna a nan"
Alhaji Ahmad yace "toke yanzu gashi baki ɗakko kayanki ba, a haka zaki zauna ɗin?"
Widad tace "zamuje da Yoseef in ɗakko"
Alhaji Ahmad yace "ina ganin ƙauna, ikon Allah dan Allah Jidda ayi haƙuri idan muka dawo daga tafiya Yusuf ya koma ɗakinsa"
Seda Umma tayi dariya, jin abunda Alhaji Ahmad ya faÉ—a, gaba É—aya suka raka shi har bakin mota ya tafi, sedai tafiyarsa babu wuya aka girke 'yan sanda a bakin layin su Yusuf dan basu tsaro.
Mutanen layin sunata gulma dan sunga an kawo' yan sanda layin, wataƙila Yusuf aka kuma zuwa kamawa, tunda yai wannan laifin unguwarsu bata rabo da 'yan sanda.
Yusuf yana son ya keɓe da Widad suyi hira sosai, amma kunyar Umma yake ji sosai, Umma kam basar dasu tayi kamar bata san da zamansu ba, sabgogin gabanta kawai take yi.
Bayan sallar magariba Yusuf ya dawo daga masallaci, Widad tace "Yoseef nayi waya gida, Nura zezo da mota muje farm House mu ɗakko kayan.
Yusuf ya kalli Umma, amma yaga basu take kallo ba.
Ba daɗewa sega Nura direban Daddy ya ƙaraso, Yusuf yaje ya samu Umma yace " Umma zan raka Widad ta ɗakko kayan ta "
Umma tace "sekun dawo"
Sam Yusuf baya jin daÉ—in yadda Umman keyi, duk se yaji ya damu ya tsargu sosai, baya jin daÉ—in hakan sam.
Widad ta saka takalmanta tayi waje, Yusuf yabi bayan ta, suna zuwa Nura ya buɗe mota ya fito yana, jinjinawa Yusuf hadda duƙawa yana  "Allah ya temaki me gida, Allah ya tsare gabanka da bayanka mijin Hajiya Widad, siriki ga Alhaji Nasir Daula"
Yusuf yai murmushi yace "Nura karka bani kunya mana dan Allah, ni nayi laifi ma, tunda aka sakeni, ban samu nazo mun gaisa na muku godiya ba, saboda bana son sake zuwa gidan nan ne, amma ina godiya Nura"
Yai maganar yana miƙawa Nura hannu su gaisa, Nura ya zare ido yace "wane talaka haɗa hannu da kai yanzu? Ai sedai ai muku gaisuwa irin taku ta manya"
Yusuf yace "dan Allah Nura ka bari, bazanji daɗin haka ba, ka barni a Yusuf direba na kawai"
Widad tace "aikuwa naga wanda ze kiramin miji da direba, yaga yadda zanyi dashi, koda yake ni kaɗai zan dinga ce masa direbana"
Sukayi dariya gaba ɗaya, Widad ta ɗakko ƙaramar jakarta, ta ɗebo kuɗi ta miƙawa Nura tace "gashi nan, ka hau mota ka koma gida, bawa Direbana mukullin, zamuje yawo tare"
Yusuf yai murmushi yace "Yarinya ki cigaba da cemin direba, idan na kaiki bazan dawo dake ba"
"kai ka isa"? Tai maganar tana kaimasa dukan wasa a ƙirjinsa, Yusuf ya karɓi mukullin motar suka shiga suka tafi.
Nura kuma yai ram da kuɗin da Widad ta bashi, dan kuɗin yafi ƙarfin dubu Ashirin, yana tafe yana mamakin yadda Widad ta canza gaba ɗaya, ga kuma ga dukkan alamu ba ƙaramin so takewa Yusuf ba.
Haka ya isa gida yana wannan mamakin da tunani, Isa yace "ha na ganka kao kaɗai? Ina motar da kuma gimbiyar Daula?"
Nura yace "barni inyi mamaki Isa, gaskiya gimbiyar Daula ta canza, kaga wasa da dariya?"
Isa yace "na gani ranar data zo nan kam"
Nura yace "mhmmm, na yadda dare ɗaya Allah kanyi bature, nikam dama can Gimbiya bata son Yusuf kuwa, tunani nake yadda ko a baya da yana direbanta, tana masa wulaƙanci son ranta amma bata yadda wani ya taɓashi ba, kai kaga soyayya, motar suka karɓa wai zasu unguwa, Allah sarki dafa a cikinmu yake, amma Allah ya tsame shi ya auri 'yar masu gida, shikenan Allah ya masa sitirar arziki, dan ynzu yayi hannun riga shida talauci, da Daula yana da wata' yar nima se ince inama inama"
Isa yace "Inama me? Kana ganin baƙar azabar da ya sha, kafin ya kuɓuta, ni mamakin da nake ya akayi sukayi auren ne?"
Nura yace "kanaji ana gayamaka, Saleh ne ya kuɓutara dasu, ya kaisu wani ƙauye aka ɓoyesu, kasan ta bata da yadda sam, taƙi yadda da kowa seshi, kuma ance lokacin bata da lafiya sosai, tace bame kula da ita seshi, shine fa sukayi Aure a can, daga nan kuma abu ya zame masa silar Arziki, dan nasan yanzu ita da abunda ta mallaka yana da iko dasu, dama ka santa ga kyauta, gaskiya ze warwasa, inama inama nima ace in samu dama haka ko bata kai kamar tasa ba"