Sashe 62
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Umma, idan baki amince ba shikenan, amma Umma bakya tunanin da akwai wani tsayayyen ɗan sanda me gaskiya a gurin da an tsaya mana gurin karɓo haƙƙinki, Umma kin san mutane nawane ke shiga garari sakamakon rashin aiki yadda yakamata da wasu maciya amana sukeyi a ƙasar nan? Umma in dai zamu dinga ƙyamar aikin mu dingawa 'yan sanda kuɗin goro to tabbas za' aita cutar mutane, duk abu ba'a rasa na Allah, sedai idan suka yi ƙaranci zalunci ne yake yawaita, Umma idan kika bibiya akwai mata irin irinki wanda aka zalunta, kuma za'a cigaba da yi idan har ba'a ɗau mataki me kyau ba, ina son yin aikin ɗan sanda ne saboda in temaki al'umma, ima son zama ɗan sanda dan in ɗora daga inda mahaifina ya tsaya, dan Allah Umma ki amince, amma in bakya so na haƙura "
Jikinta ne yayi sanyi, ta ɗanyi shiru taga tabbas maganganun Yusuf haka suke, kuma tana da yaƙinin cewa Yusuf mutum ne nagari, abune mawuyaci a haɗa kai dashi a cuci wani.
Ta numfasa sannan tace " Shikenan Yusuf, na amince ubangiji Allah yayi maka jagora, ya goyi bayanka ya kareka a duk inda kake, Allah ya wuce maka gaba a al'amuranka, ina fatan zaka zama mutum nagari me gaskiya da riƙon Amana, Allah yasa a sanadiyar ƙudirinka ya zamana an share hawayen wanda aka zalunta, kayi gaskiya da adalci Yusuf "
Yusuf yayi murmushin jin daɗi da farinciki, yace " Insha Allah Ummana, in Allah ya yadda ba zanyi wani abu wanda ya saɓawa Alƙawarin da mukayi dake ba, Addu'ar ki nake buƙata, Allah ya kauda zuciyata daga aikata duk wani abu da ze saɓawa Allah "
Umma tace "Addu'a ai kullum cikinta nake Yusuf, ina fatan Allah ya tsare, amma bana son ka sha wahala, training É—in nan nasufa da wuya, karka je su baka wanda bazaka iya ba, Abbanka yana bani labarin wahalar abun nan"
"Haba Umma, sekace wani ragon maza, kin ganina santalelen ƙato dani, se in goya maza goma in gudu dasu a bayan nan nawa"
Umma tai dariya tace "eh lallai, ba shakka naga alama kam"
Nanma Allah ya temake shi ya samu makarantar horar da 'yan sanda, Yusuf yasha wahala ya fuskanci ƙalubale daban daban, a haka harya kammala makarantar nan, sukayi passing out, Allah ya temake shi ya fita da babban rank, sakamakon yayi karatu yana da degree.
Yusuf ya kama aiki, sedai Umma kullum cikin nasiha take, na akan yaji tsoron Allah akan wannan aiki daya fara, cikin ikon Allah yana fara samun salary yazo ya zubewa Umma kuɗin yace "Umman Yusuf, Insha Allah inaji a jikina lokacin da zamu samu sassauci yazo, ga wahalarmu ta wannan watan, na karɓo salary"
Umma tace "Alhamdilillah, dama komai yayi farko zeyi ƙarshe ai, Allah yayi albarka amma ka ɗau kuɗinka, ni duk abunda ka sanmun karɓa zanyi ince Allah yayi albarka"
"Haba Umman Yusuf, wannan nakine halak malak, na bar miki, ba abunda zanyi dasu ni duk abunda kika sanmun a ciki shikenan nagode, ki fara more wahalar da muka sha Umma"
Kawai seta fashe da kuka, Yusuf ya rikice gaba ɗaya yace "subhanallah, Umma laifi nayi mikine? Yi haƙuri dan Allah, ban san zan ɓata miki rai ba"
Ta girgiza kai cikin kuka tace "Tun kana ƙarami Yusuf, naso inyi duk me yuwuwa dan ganin baka gane bamu muka haifeka ba, amma hakan ya gagara, duk yadda muka kai ga ɓoyewa nida Abbanka abu ya gagara, bakin mutane yakasa yin shiru, suka dinga wulaƙantamin kai da maganganu marasa daɗin gaske masu muni, har seda suka saka kasan bani na haifeka ba, amma haka kake min biyayya kamarni na haifeka, A baya nayi kukan Gorin rashin haihuwa, an goran tamin nayi kuka nayi kuka, amma tunda Allah ya bani kai, na dena wannan kukan, nasan ba lallai ɗan dana haifa yayi min biyayyar da kake mun ba Yusuf " ta ƙarasa maganar cikin kuka, Yusuf yaji ta fama masa ciwon dake raɗaɗi a cikin zuciyar sa, yaji kamar ya fashe da kuka, sedai be taɓa gangancin zubda hawayen rashin sanin suwaye iyayensa a gaban Jidda ba, dan idan yayi haka ya zama butulu abun Allah wadai, ya tattara nutsuwarsa ya dake, ya riƙe hannunta yace "wayema yace ba Yusuf ba ɗan Ummansa bane, samun uwa kamar Umman Yusuf me sadaukarwa da juriya a wannan lokacin se anyi tonawar gaske, Wa Yusuf zeso in be so Ummansa ba, waze wa Biyayya idan bebi Ummansa ba, Ummana ina neman Aljannata, duk me neman Aljannarsa Annabi salallahu alaihi wassalam yace yabi Allah da ma'aiki sannan yabi uwa, shiyasa nake bin tawa mahaifiyar domin neman albarka da samun wannan Aljannah, shiyasa nake bin Ummana nasan babi da abun biyanta ladan shayarwarta da ɗawainiyarta, Allah ya haɗamu a Aljanna gaba ɗaya, amma wannan kuɗin na Umman Yusuf ne halak malak, da Yusuf da abunda Yusuf ya mallaka duk na Ummane"
Ta rungume Yusuf ta fashe da kuka, a hankali Yusuf ya lumshe ido yana zubar da nasa hawayen ƙasa ƙasa, dan karta ji yana kuka, ta goge hawayenta tace "Yusuf indai nice, nagode sosai Allah yayi Albarka, amma ka ɗauki kuɗinka, kaje kayi buƙatunka gabanka, sedai ka ɗan sai mana Abinci"
Yusuf yace "Umma, nifa kuÉ—in nan bazan ciba, ki sanmun na mota zuwa gurin aiki kawai"
"A'a Yusuf, bana son jayayya fa"
Yusuf yace "ni na isa inyi Jayayya dake, tunda kin rasa abunyi dasu bari in baki shawarar yadda za'a kashe, ki rabasu biyu, rabi ki ban abunda zakimin, ki riƙe sauran, rabin idan mun samu kuɗi mudinga ƙarawa a kai, mu nemi fili a wata unguwar, mu fara gini, gara mu koma gidan kanmu "
Umma tace " na daɗe ina wannan tunanin Yusuf, yana da kyau ko fili mu siya, sedai bazan karɓe maka kuɗi duka ba, nasan kana da buƙatu kaima "
Yusuf ya haɗe rai, tace " ya dai naga ɓata rai"
"Umma ni zan baki abu kiƙi karɓa ko? Allah ya jiƙan masoyina, nasan da shine baze min haka ba"
Umma tace "shikenan, naji Allah yayi albarka, Allah ya kareka daga sharrin maƙiya"
Shigar Yusuf aikin ɗan sanda na farin kaya, nan da nan sunansa aka fara saninsa, musamman jin laƙabin sunan mahaifinsa, Yusuf Bashir Maitama, Yusuf akwai ƙwazo akan harkar aiki, baya wasa ba ruwansa da cin hanci ko rashawa shidai aikinsa kawai.
Bayan ya fara aikine ya gano irin cakwakiya da maguɗin dake cikin aikin, da irin tuggu da maƙrƙashiya dake aikin, ga me laifi ƙiri ƙiri kana gani amma saboda yana da wane ko yasan wane, se ace a ƙyaleshi, amma idan aka kamo ɗan malam wane ƙarshe 'yan sanda suna iya ajalinsa, ko ka samu case ka fara aiki a kai, daga sama se a turaka wani gurin a karɓe aikin, ko a ƙirƙiri laifi a ɗorawa wani dan a samu wani abu a hannun sa, da ire iren wannan ha' incin, A haka Yusuf yai tunanin yadda rasuwar mahaifinsa ta kasance, a nan ya gane tabbas set up ne mutuwar mahaifinsa da ubangidansa, sedai bashi da evidence dan in be manta ba, suna kan wani case ne, aka kira shi shida ubangidansa can Lagos, daga tafiyarsu se gawarsu, Yusuf baya son ɗagawa ummansa hankali dan haka be gayamata bata ba, ya bar zancen.
Yusuf ya dage da aikin ginin gidansu, dukda muguntar da'ake masa a gurin koyon aiki, a haka ya iya aikin kafinta, ya kama shago ya zuba yara suke masa aikin yana biyansu.
Duk yadda aka so asa Yusuf a harkar cin hanci amma yaƙi, aka dinga cewa shima tsinannen kafiya da taurin kaine dashi kamar ubansa marigayi, ko talauci ze kasheshi baya karɓar kuɗin rashawa.
Yusuf ya kammal ginin gidansu, da kansa yayi furnitures ya zuba a gidan, kamar gidan wata amarya, gidan yayi kyau hatta kayan sawa seda ya canzawa ummansa kafin su koma gida, ya zuba kayan Abinci rana ɗaya yaje ya ɗakkota ya kawo ta gidan nan, umma sarkin kuka seda tayi kukan nata data saba, yaita rarrashinta, suka kwaso sauran kayan buƙatunsu suka dawo sabon gida, Yusuf ya sai Babur lifan me kyau.
Alhamdilillah rayuwa ta fara yi musu sauƙi, Daidai gwargwado suna hutawa, ga salary ɗinsa ga gurin furnitures, ya hana Umma sana'ar komai, data motsa se yace "Umman Yusuf me kike so, Ummana me za'ayi miki?"
Sam bata da damuwar komai, dama gata ba wani girma tayi ba dan lokacin da Suka tsinci Yusuf ba tafi sha bakwai ba, dan da ƙuruciyarta sosai akayi mata Aure, bayan mutuwar Bashir wasu sun nuna suna sha'awar Auren ta, amma taƙi Aure saboda rayuwar Yusuf, tasan ba lallai a riƙe mata ba.
Babban abunda yake damun Umma da Yusuf shine ko abokan kirki bashi dasu, gashi kamar mace wani lokacin kullum yana naniƙe da ita, da girmansa da komai amma idan zata unguwa, seya bita, ya jirata a waje itakuma ta shiga, ko zata wuni yana gurin a zaune, idan kasuwa ce haka zasu tafi tare, haka idan Asibiti ne, idan ya dawo daga makaranta, idan ba masallaci ba baze je waje ya ɗanyi hira da abokai ba, tayi faɗan harta gaji amma yaƙi denawa, abun da Ummansa bata gane ba shine, shi hana gudun magana ne, ko ace anyi rigima yana gurin ko kuma wani abu ya haɗashi da wani ayi masa gori.
Yanzu gashi ya kammala karatu, ga aikin yi gashi ya zama cikakken namiji amma ko budurwa bata taɓa jin Yusuf yayi ba, to mutumin da bashi da abokai mazama balle wata budurwa, ko a gurin aiki abokinsa ɗaya da yake biyo shi gida shine Abbas, banda wannan Yusuf bashi da wasu Abokai.
Rannan yayi musu Abincin dare, ya zubi suna ci Umma tace "Wai nikam Yusuf, kai ko budurwa baka da ita ne, sa'aninka sun fara Aure, amma kai ko zancen budurwa baka yi, ko dai nice ake ɓoyewa"
Ya ɗan tura baki yace "Umma ni me zanyi da wata budurwa kuma, ni bani da wata budurwa"
"Saboda me baka da budurwa? Se kace ba namiji ba, haka zancigaba da zama da kai gunsumeme ba Aure, sedai duk inda zani kana biye dani? Ai lokaci yayi da zaka nemi iyali kaima"
"Nidai umma bana so, ki ƙyaleni a hakana kawai"