← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 127

Sashe 88

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"dole ka tambayeni lafiya mana, munafuki macuci, to bari kaji in gaya maka, barin gidanka zanyi bazan zauna ba da kai ba Wallahi, dama can ba sonka nake ba aka ƙaƙabamin kai"

"Ni se wasu maganganu kike wanda ban gane inda kika dosa ba, kimin bayani yadda zan gane mana"

Jefo masa wayarta tayi, ya ɗauka ya duba, message ne aka turo mata da wata baƙuwar lamba  "Ki saka ido akan mijinki, in bahaka ba watarn ze shafa muku ciwo, dan yana ta'amalli da mata a guest house ɗinsa, idan kin musa ina da sheda, zan iya turomiki idan kina da buƙata"

Wani gumine ya fara tstatsafo masa, ya dake yace "wannan wane irin shirme ne za'a turomiki ki yadda, kawai a turomiki magana ki yadda, wataƙila ma bake za'a turowa ba"

"ɗan saurara karka rainamin hankali mana, idan ƙarya ake maka saƙon ya rasa wayar waze faɗo se tawa? Kuma yawan fitar cikin dare da kake wataran bako sallama ina kake zuwa?"

"wannan kuma harkar aikine ke fitar dani"

"harkar banza dai, wans irin aiakine baza'ayi shi da rana ido na ganin ido ba se a takatainin dare, wallahi kaji tsoron Allah, kome kake aikatawa Allah yana kallonka, kuma wallahi idan na tabattar da abunda naake zargi seka sakeni wallahi, kuma sena tona maka Asiri a idon duniya, bani wayata ni"
Ta saka hannu ta ɗauke wayarta, tai waje ranta a matuƙar ɓace, ya dafe jansa kallai wanna kafon ya ɗebo ruwan dafa kansa, ga ya haɗu da mskira 'yar damfara.

Kiran Bukar ne ya shigo wayarasa, jiki na rawa ya ɗaga suka gaisa  yace "Haruna na gaji da wannan zagaye zagaye da raini hankamin da kakemin, ka fito ka gayamin gaskiya mske faruwa, ina takaddar nan take? Idan kuma wata manufar ce da kai kuma seka ajiye agurinka"

Alhaji Haruna yace "Babu yadda za'ayi takaddar nana tana gurina inƙi kawowa, wata 'yara matsala aka samune, kuma ba da daɗewa ba zan warwarwta a ɗan ƙara ɗagamin ƙafa"

"Bana alfarma a karo biyu, daga ta farko bana ta biyu, Amma ka sani daga wannan shikenan, idan wani ya samu takaddar nan Asirinmu ya tonu, ze zama hujja akanmu, gara idan ɓataraa kayi ka nemota tun wuri, idan kuma ɓoyewa kayi kaje ka cigaba da ajiyar ta karka fito da ita "

Ya kashe wayar, Alhaji Haruna ya rasa abunda zeyi, aka kuma kiransa da ovt number, kamar kar ya ɗaga amma ya ɗaga," ɗan duba what's app ɗinka akwai saƙo"

Be É—auki muryara waye ba, amma dai muraya mr mace ce, ya kunna data ya shiga what's app É—insa, messages suka gama shigowa sannan ya shiga dubawa.

Video ɗin tsiraicinsa ne da wata wadda besan kowacce ba a guest house ɗinsa, daga ƙasa aka rubuta  "dukda wannan abubuwan da na maka banji na fanshi mutuncina daka keta ba, wallahi idan baka biniba sannu ba sena yaɗawa duniya, kuma yanzu a haka akwai video ɗin nan a wayar mutum huɗu, isan har wani abu ya faru dani zasu watsa a duniya"

Ko ba'a gayamasa ba yasan message ɗin Amal ne, yace  "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, be taɓa gamuwa da masifa a rayuwar sa irin wannan ba, ya ɗebo ruwan dafa kansa over.

Widad kam seda gari ya waye yayi haske sannan tai alwala ta fito tayi sallar Asuba, ta dinga kai kukanta ga Allah, kuka kama dama ya zame mata jiki, dan inda sabo ta riga ta gama sabawa.

Tana cikin kukan ne Sabuwa ta shigo mata da abun karyawa, Widad ta kalleta tace "yanzu dan Allah jiya baki ji ihuna ba cikin dare?"

Sabuwa tace "idan nace vamji ba nayi ƙarya, sedai kona fito ba abunda zan iya yi miki, saboda Kinsan nima aiki aka ɗaukeni inyi, idan na shiga hurumin da ba nawa ba, zasu kasheni ne, seda akamin wannan sharaɗin sannan na fara aikin kula dake ɗin nan"

Widad ta jinjina kai tace "É—auke wannan Abincin bana ci"

"Saboda me?"

Widad tace "kawai bana ci"

Haka Sabuwa ta kwashe kayan Abincin nan ta fita dasu.

Widad tana nan zaune sega Bulama ya shigo ɗakinta, shida wasu ƙarti su biyu, aka kawo masa kujera aka ajiye, ya hau kai ya zauna ya kalli Widad yace  "karo na ƙarshe, ki gayamin inda takaddun nan suke"

Widad ta kalle shi tace  "gargaɗi na farko kuma na ƙarshe, ka jawa ɗanka kunne, idan ya sake zuwa inda nake, wallahi sena kasheshi har lahira"

"ina miki magana kina gayamin wani shirme daban? Ki kasheshi É—in karki fasa, ina takaddu suke su nake tambayar ki"

"Na miƙasu ga masu shi"

Bulama yace "zan azabtar dake, azaba irin wadda ba'a taɓa yi miki ba, ina suke?"

"Duk Azabarka a duniya ne kawai, kuma babu wanda yake da ikon yin azaba se Allah, na gaya maka na bawa masu dukiyar nan dukiyarsu, ka ƙyaleni ka rabu da rayuwata haka"

Bece mata uffan ba, taga na jona wani abu a jikin socket, an miƙawa Bulama ya karɓi abun yayo kanta gadan gadan, bata motsaba ta tsaya tana kallonsa, kawai ya jona mata abun a hannunta, ji tayi kamar ba a duniya take ba, ta rasa meke mata daɗi gaba ɗaya ta fita hayyacinta.

"zaki faÉ—a ko bzaki faÉ—a ba?"

Girgiza kai ta dingayi tana kuka, amma taƙi magana, yasa ƙafa ya take yatsunta yana murzawa ciki mugunta, amma dayake Indai taurin kaine Widad ta iya shi taƙi magana.

Ba azabtarwar da basu mata ba amma taƙi faɗa, haka suka gaji Bulama ji yake kamar yasa wuƙa ya yanka ta, amma yaga idan ya kashe ta beyi Achieving komai ba, haka suka tashi suka fita, suka barta  a galabaice.

sedai fitar sa babu daɗewa wani irin ciwon kai ya kama Widad, ko iya gani ba tayi sosai,  ga ƙirjinfa daya riƙe gam, nan ta kwanta tun tana kwnace, harta fara juyi ya zamana bata iya ganin komai, se dishi dishi daga baya kuma ta dena gani gaba ɗaya.

Daga nana bata sake farkawa ba se a gadon Asibiti, taji anayiwa Bulama bayanin zuciyartace ta kumbura kuma ga jininta ya hau, Ba tausayi ba imani Bualama yayiwa doctor Hamisu umarnin ya cire É—an cikin Widad koda tsiya ne.

Ta buÉ—e idonta fes a kansu, amma hakan besa Bulama yai shiru ba, ya bada umarnin a cire cikin.

Haka doctor Hamisu yaje ya É—akko allurai, yazo ya haÉ—asu yayi mata duk tana kallonsa, sedai ta kasa motsa koda É—an yatsanta ne, gaba É—aya tama rasa inane yake mata ciwo, haka ya kwance cannula yai mata wata allura, sannan yasa wata a ruwa, ya gama ya fice tana kallonsa.

Sosai Yusuf yake jinsa a damuwa, hankalinsa yaƙi kwanciya sam, yake jin jikinsa ba daɗi, tunanin Widad ya cika masa zuciya.

"To wai kai Haruna ya akayi ka bari haka ta farune? Ta yaya yarinya ƙarama zata dinga wasa da hankalinka haka?"

Alhaji Haruna yace "kai dai bari kawai Alhaji Musa, wallahi nikaina ban san abun ze kai haka ba, ganin irin kuÉ—aÉ—en dana bata, ni nama rasa abunyi wallahi, babban abun tsorona shine video na data É—auka, karta saki a duniya mutuncina ya zube"

Alhaji Musa yace "rabu da ita, duka barazanar banzace ba zata saki ba ƙarya take"

"Ya zakace ƙarya take? Bayan har Salma ta turawa message a kaina?"

"ni nace maka ka ƙyaleta ai, to ka ƙyaleta ba zata iya yaɗawa ba, sannan batun takadda ka gayawa Bulama gaskiya kawai, ai da tun farko ka faɗa masa ma da tuni an wuce gurin, ƙilma yai maka maganinta"

Alhaji Haruna dai yai ajiyar zuciya yai shiru kawai.

Bacci ne ya ɗauki Widad me nauyi, sedai wani irin gigitaccen ciwon mara yasa ta farka babu shiri, ji tayi wani irin ciwo yana ratsata, tun daga mararta zuwa bayanta da ƙafafuwanta, wani irin ƙarfine yazo mata, ta zabura ta fizge cannula, aikuwa take jini ya shiga zuba daga inda ta cire cannulan.

Ta faɗo daga kan gadon, Nurses ne suka shigo da sauri, suka ga yadda Widad ta faɗo ƙasa, ta riƙe mararta hawaye na zuba daga idonta, alamar tana jin jiki, ɗayar ta kalli ɗaya tace  "Sister, ki kira likita da sauri yazo ya dubata"
Tace "shikenan bari inje"

Tana zuwa ta sami doctor Hamisu a Office tace "doctor, patient É—in Alhaji Bulama ta Amenity she's unconscious fa, harta faÉ—o daga kan gadon"

"Ku kaita labor room kuyi mata abunda yakamata, Abortion ne cikin jikintane ze faÉ—i"

"doctor, amma naga kaman ba case É—in Abotion aka kawota ba, cardiac failure ne, da hypertension kawai, ya za'ayi within a minutes ace kuma Abotion yai occurring"

"Are you going to teach me my job? Wace makarantar kika yi ne, baki san cardiac failure na uwar ze iya shafar abunda ke cikinta bane? Get out from here kije kuyi abunda nace"

Jiki a saluɓe Nurse ɗin ta fita daga Office ɗin ta koma ɗakin Widad, ta tarar da ɗaya Nurse ɗin rungume da Widad tana mata sannu.

"Sister ina doctor É—in?"

"naje yamin wulaƙanci, wai mukai ta labor room abortion ne, muyi mata abunda yakamata, shikenan babu wani taimako da za'a bata se a bari cikin ya fita?"

'haka yace miki? "

" Gashi kuwa ina gayamiki, zan masa ƙaryane? "

Widad kam banda aikin gumi babu abunda take yi, fuskar nan tayi jawur saboda azabar wahala, haka taita wannan wahalar tana addu'a tana ambaton Allah, tana roƙon Allah ya bar mata cikin nan.

ÆŠayar taje ta samo wata allura a pharmacy tayi wa Widad, cikin ikon Allah se bacci ya É—auketa, can sega doctor Hamisu ya shigo yana cewa "Yaya? Cikin ya fita dai ko?"

ÆŠayar tace "ta samu relief bacci take yi"

"Ya faÉ—in dai ko?"

Nurse É—in tace "Eh ya faÉ—i, mun gyarata ne ta samu hutu, amma babu wani wanda suka zo tare da ita ne?"

"Ba ruwan ku da wannan, tunda mun samu ya faÉ—i Alhamdilillah, a bata medication É—inta na dare"

"To insha Allah, za'a bata"

Bayan fitarsa ɗaya ta kalli ɗayar tace  "Sister Habiba, kijimin ikon Allah, ni anya ba doctor ne yai mata wani abuba akan cikin nan ba kuwa?"
Chapter 88 · 0% Book details