← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 127

Sashe 36

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nanma bata samu amsa ba, dan haka ta ɗakko bargo ta lulluɓeta, itama ta shiga bargon ta rungume Ammin nata, daga nan bacci yayi awon gaba da ita.

Dukda Kasancewarta yarinya ƙarama, amma da Asuba Amminta ke tashinta salla, Asuba tayi Widad ta tashi taje tayi salla, Amma Amminta bata motsa ba, ta sake zuwa ta kwanta a jikin gawar ta koma bacci, har kusan ƙarfe tara na safe Widad ta farka, ta shiga girgiza gawar Ammin tana  "Ammi ki tashi bakiyi salla ba, kuma yunwa nake ji, Ammina ki tashi ina jin yunwa, Ammi Abinci"  haka Widad ta cigaba da hayyata irin tasu ta yara, ba tare da tasan Ammin mutuwa tayi ba.

Tana nan zaune, ta gaji ta shiga wasa da gashin kan Ammin nata, tana mata surutu ba tare da tasan mutuwa tayi ba.

Tana nan zaune Bala ya buÉ—e É—akin ya shigo, ya kalli Widad yace "ke a ina kika kwana?"

Kallonsa Widad tayi ta É—auke kai, ya kalli Gawar Huda dake kwance a gurin, ya juya ya fita.

Wajen ƙarfe sha ɗaya sega Bulama da wasu abokan kasuwancin Daula, suka shigo har ɗakin, Bulama ya kalli Huda ya shiga rangaɗa salati, ya kalli Bala yace " kuma ba rashin lafiya ce ta kamata cikin dare ba?"

Bala yace  "nima ban sani ba, gani nai shiru banji motsinsu ba, shine na shiga dubawa, nazo na tarar da gawa da yarinya"

Bulama yayi ajiyar zuciya yace "Allah me iko, Allah yayi mata rahama amma abun da mamaki, munyi waya da Daula, lafiya ya tafi ya barsu, amma a wayi gari ta rasu, Allah kenan, yanzu dai a kira motar Asibiti aje da gawar a dubata a Asibiti, ita kuma daughter a tafi da ita gidana, zuwa muga yadda hali zeyi"

Widad ta dinga bin Bala da ido, tamkar bata taɓa ganinsa ba, duk inda ya motsa seta bishi da ido.

Aka É—auketa aka tafi da ita gidan Bulama, aka tafi da gawar Huda Asibiti.

Tunda aka kai Widad gidan Bulama, ba tace uffan ba se kallonsu da take kamar baƙin halitta, aka bata Abinci harta fara ci, ta ture ta shiga kuka tana kiran Ammina.

Gaba ɗaya tausayinta, ya kama Hajiya Sarah, ta dinga rarrashin Widad amma fafur Widad taƙi yin shiru, Fahad yace "kai wannan wace irin jarabbabiyar yarinya ce, banza kawai ana ta magana ana rarrashin ta se wani iskanci take yi, shegiya kai me kama da Aljanu"

Fahad be rufe baki ba, Widad ta ɗauki wani kofin glass ta jefa masa, gaba ɗaya ta basu mamaki, suka juyo suna kallonta, kofin ya sameshi a ƙafa ya faɗi ya fashe, sannan kuma ta koma gefe tana kallonsa tana huci, kanta yayo ze maketa a zuciye, Hajiya Sarah ta tareshi tace

"yi haƙuri, marainiyar Allah ce, meyasa zaka zageta"

Fizgewa yayi ze daketa, amma Widad ta shammaceshi, ta kafa masa haƙora a hannu, da ƙyar aka ɓanɓareta dan seda gurin ya fashe.

Fahad ya dinga ihu yana "na shiga uku Mayya, 'yar gidan mayu zata shanye min jini"

Tun daga lokacin, ko hanya basa haɗawa da Widad, dan tunda ya zageta ta tsane shi, a wunin ranar nan gaba ɗaya suka rasa yadda za suyi da Widad, suka kasa gane kanta dan bata jin rarrashi, bata sanshi ba ga kafirin taurin kan masifa, taƙi cin Abinci taƙi saurarar kowa, da Hajiya Sarah ta gaji ta kira Bulama ta gaya masa, shi kuma yace ayiwa direbansa magana Fahad ya rako su Asibitin, dan Daula ya iso.

Fahad yace "Allah ya kiyaye in raka Mayya, wannan a binciki danginsu mayune, shegiya kawai"

Ƙarshe direba ne ya kai Widad Asibiti,  bata tsaya jiran direban ba, ta shiga cikin Asibitin tana leƙe leƙe, ta buɗa wannan ƙofar ta buɗe waccan.

A saman bene ta buɗe wani ɗaki, taga su Bulama da Bala a ciki da wasu mutane, se Mahaifinta durƙushe a gaban gado an rufe gawa, yana rusar uban kuka kamar ƙaramin yaro, Widad ta tsaya tayi sak tana binsu da kallo, Daula na ɗaga ido yaga Widad ya sake fashewa da kuka, ya miƙowa Widad hannu, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta faɗa jikinsa, cikin kuka Daula yace  "Lovely daughter, mun rasa Amminki, ta tafi ta barmu"

"Daddy ina Ammina"

Daula ya buɗe mata fuskar Huda, kamar kace mata tashi ta miƙe zaune.

"Your Mum is dead Daughter" yai maganar cikin kuka.

Zumbur Widad ta miƙe tsaye, tana kallon mahaifinta, idan bata manta ba ko a film da take kallo, when someone is dead, you won't see him again, that's mean her Ammi has gone, she won't see her again.

"Noooo Daddy, she's alive, she's not death!"

Wata irin ƙara tayi tana tirje tirje, ƙarshe se ɗaukarta akayi aka kaita pediatric, aka mata allurai, se bayan an kai Huda nakwancinta sannan Widad ta farka.

Amma tunda ta farka ba ummm ba umm, idonta a buɗe amma sam bata magana, bayan an dawo daga kai Huda, Daula se kuka yake yana sharɓe hawaye, Asibiti ya wuce gurin Widad ya tarar ta farka, su Bulama dai yana biye dashi dasu Bala, ya zauna ya rungume Widad a jikinsa, yana kuka yayin da Widad ta tsaida idonta akan Bala megadi, bata ko ƙyaftawa.

"Daddy, what exactly kills Ammi?" Tayi tambayar a bazata.

Daula yace "i don't actually know daughter, likitoci sunce ta samu cardiac failure ne"

"is a lie Daddy"

"How?"

"someone sponsored her murder, she was killed Daddy"

Daula yace "what are you trying to say?"

Mamaki ya cika su yadda take magana, sekace wata babba, kuma she's very serious about what she says "

Alhaji Munir yace  " ranka ya daɗe, yakamata fa muje gida, mutane na jiranka.

Haka suka tafi da gida, Daula na cigaba da kuka wiwi, Bulama da sauran mutane suka raka shi gida, har an kafa manyan rumfuna, manyan mutane gaba ɗaya sun hallara, anata miƙo gaisuwa.

Daula na rungume da Widad a jikinsa, Widad gani take kamar ƙaryane wai Ammi ta mutu.

Seda ta kwana biyu cirr ko gyangyaÉ—i ba tayi ba, hakan ya firgita Daula kar wani abu ya sameta, ya fara tunanin ko Asibiti ze maida ita, dan seta wuni ba tace uffan ba, sedai lokaci lokaci ta fashe da kuka.

Ranar uku, gidan nan ya cika da É—an Adam, babu masaka tsinke Kasancewar ita kanta Huda mutuniyar kirki ce ga kyauta.

Ana zauna a nayiwa Daula gaisuwa, ta dubi wani babban ɗan sanda, ta tashi daga jikin Daula ta tafi gaban ɗan sandan ta zauna, ta kalle shi tace  "Are you a police?"

Ya amsa mata da 'yes my dear "

" Can i ask you a question? "

" Yes of course "

Widad tace  " idan na tambayeka, will you do your best to help me? "

Yace" insha Allah "

Widad tace" karka saɓa Alƙawari fa"

Mamaki ya kama mutanen gurin, yadda take zaro magana haka, daki daki kamar babbar mace.

Yace "insha Allah, i promise you, bazan saɓa ba"

Daula yace "lovely, dawo na kusa dani, karki dameshi"

Widad ta ɗagawa mahaifinta hannu, alamar ya ƙyaleta, ta kalli cikin idon ɗan sandan tace   "you promise to help me, tambayar da zan maka itace, idan aka rufe fuskar mutum da pillow ze mutu?"

Yace "kamar yaya?"

"misali, Daddy ya doramin pillow fuskata, inta motsi amma yaƙi ɗagani, kawai se misali Bala megadi ya dawo ya riƙemin ƙafa, in dena motsi, to zan iya mutuwa"

Yace "yes of course dear, it's a murder attack, kisan kai kenan a ina kikaga anyi?"

"Yanzu misali, idan na gaya maka a inda na gani, wani mataki zaka É—auka?"

Gaba ɗaya rumfar tayi shiru, ana sauraren Widad, Ɗan sandan yace  "zamuyi abunda doka tace akai, idan har muka kama mutum da laifi, zamu kashi kotu a yanke masa hukunci"

"Arrest Bala! And the doctor that confirms that my Mum is dead, as a result of cardiac attack" ta faÉ—a kai tsaye

"Why" ya tambaye ta

Cikin ƙara tace  "Bala yasan suwaye suka kashe Ammina, kasheta akayi fa, i use to watch in movies, she was killed not dead as a result of cardiac attack, Ka kama Bala ko in kasheshi, he's responsible for the murder, na ganshi shine ya buɗe wa wasu ƙofa, suka rufe ammina da pillow, Arrest him i said "!

Gaba É—aya Widad ta hargitsa gurin, ihu take sosai tana nema ta fita daga hayyacinta, se kurma ihu take tana akama Bala.

Alhaji Haruna yace" ya za'a biyewa yarinya ƙarama tana wa mutane shirme, watakila alhinin mutuwane ko mafarki tayi "

Daula ya fashe da kuka yace " Widad mutum ce, kuma yarinya ƙarama, amma idan kaga tayi maka ƙarya ajizanci ne irin na ɗan Adam, dan haka Arrest him, ayi bincike akai "

Yai maganar yana kuka, aikuwa Bala yana ihu haka aka buga masa ankwa akayi gaba dashi, nan wasu suka dinga jinjinawa kaifin basira irin na Widad da ƙarfin hali, yayin da wasubsuke ganin be kamata a kama Bala ba, tunda shirmen yarane.

Nan fa 'yan sanda kuma suka shiga bincike akan Bala, Widad ta fayyace musu yadda abun ya faru, Alhaji Haruna yace "Nasir, bekamata a biyewa yarinya ƙarama ba, ta faɗi magana sannan a yadda"

Daula yace "Tunda Widad ta faɗi haka ba ƙarya take ba, bata taɓa haka ba, kuma akwai ƙamshin gaskiya a lamarin nan, dan haka se abunda hukuma tace, dan nikaina bana ja da ikon Allah, amma tabbas mutuwar Huda, abar a bincika ce, lafiya muka rabu da ita, ba ta da wani ciwo, ace in dawo in tarar ta rasu, Allah na tuba "

Kawai ya fashe da kuka, Bulama yace " Nasir, kayi haƙuri nasan irin mahimmancin Huda a rayuwarka, amma karkayi abunda zaka dawo kana dana sani, kar azo aji kunya "

Widad na kan kujera, tana wasa da yatsunta, tunda suke maganar su bata saka baki ba, se yanzu tace "Daddy, ko nima na mutu kar ka bari a ƙyale Bala, seya faɗi wanda suka kashe Ammina, idan ba hakaba zan faɗa maka ko suwaye"

Zaro ido sukayi, suka juyo da kallonsu kanta, Daula yace "Baby na, dagaske kin san suwaye? Ya akayi kika sani? Gayamin suwaye, meyafaru?"
Chapter 36 · 0% Book details