← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 127

Sashe 51

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf ya ɗanyi murmushi yace  "Anƙi a faɗa ɗin, kema ai jamin rai kika dingayi, kika ƙi gayamin tarihinki"

Cikin Shagwaɓa tace "please"

Yusuf yace "to shagwaɓaɓiya karkimin kuka dai, bincike daga cikin gidanku na fara yi, sedai nayi mamakin ƙiyayyar da matar mahaifin ki ke miki, da farko nayi zaton tana yi ne saboda halayenki, da abunda kikeyi na wulaƙanta ta da 'ya' yanta, sedai daga baya na gane son zuciyarta ne abunda take, akwai ranar da kika rufe ƙofa kika ƙi buɗewa, nasa Amal ta kawo miki tea, sedai kika zubar da tea ɗin, nayi mamakin ganin ƙwaya a ƙasan kofin shayin"

Widad tace "Kasan meyafaru a wannan daren, da na birkice?"

Ya girgiza mata kai alamar a'a.

Tace  "samunsu nayi a falo, suna tattauna yadda zata damfari Daddy kuɗi, kasan na kanyi kwanaki a part ɗina ban fito ba, shine suka sakankance suna hirarsu, basu yi tsammani ba kawai suka ganni a ƙofar falo, shine suka shiga kame kame, bance musu komai ba, na fita dama fita zamuyi da kai ranar, bayan mun dawo cikin dare ina bacci, da yake ban rufe ƙofar ɗakina ba, kawai seji nayi cikin bacci ana lalabun hannuna, nayi yinƙuri zan ƙwaci hannuna kawai akayi min Allura, irin Allurar da'ake min a baya a birkita ni, take na fara dena gane abubuwa sosai, ban san wanda yayi min allurar ba, amma a haka bayan ya fita na tashi ina tangaɗi na rufe ƙofata, tun daga nan ban sake sanin abunda ke faruwa ba, se bayan dawowar Daddy, shiyasa a rayuwa na tsani matar nan Yoseef, na tsaneta fiye da yadda kake tunani, ji nake kamar in shaƙeta seta mutu"

"a'a karki kuma cewa zaki kashe mutum, sannan kika sani ko Daddy yana son matarsa? Ki barwa Allah zakiga sakayyar daze miki, amma banda ambaton kisa"

"Rabu dani bazaka gane ba Wallahi, dama muna komawa Seta barmana gida, sannan Aure zan nemawa Daddy da kaina, sannan ko banyi kisa ba idona idon Bukar a zahiri seya tafi lahira da tabom da zanyi masa"

"Kibi komai a hankali Widad, Insha Allah komai zamu bishi a hankali, kuma zamuyi nasara da yardar Allah, Amma karki yinƙurim ɗaukar doka a hannu, dukda bansan waye Bukar ɗinba, kuma bansan meya yi miki ba, amma karkiyi ganganci, muyi komai a dokance"

Ta girgiza kai tace "bazaka gane me nake jiba a Yoseef, idan ban kashe mutumin nan ba kona masa illar da zan nakasta shi ba, to zan mutu ne" tai maganar tana kwanciya a jikinsa.
Yasa hannu ya rungumeta a jikinsa, shiru ya wanzu a tsakanin su.

Yusuf idan suka gaji da zaman ɗaki sesu dawo tsakar gida, suyi shimfiɗa suyi zaman su, sannan gaba ɗaya Yusuf ya shiga kiyaye abunda yasan zai ɓata mata rai.

Lokaci lokaci takan shiga ɓangaren Jamila, dan ta ɗau jaririyarta, dan har goya mata ita take yanzu, idan ta goyamata ita ta zauna guri ɗaya ta nutsu sosai kamar am goyawa yaro, Jamila tace  "Widad waike bakya saka Atamfa ne,? Kullum se ƙananan kaya, baki san yawan saka abu ɗaya yana gundurar mijinki ba?zeso yaga kin canza ai"

Widad tace  "nifa ban iya saka wata atmfa ba, tun taso wata ni bana saka wata Atamfa fa ko makamancin haka"

Jamila tace "Eh naga alama nima, amma Aikuwa yakamata mu bawa mijinki mamaki, ina da sabuwar atamfa na haihuwar Yusra da aka bani na barka, zan kai a É—inka miki"

Widad tace "A'a karfa Yoseef yaji haushi, ko yace ban gaya masa ba"

Jamila tace "baze ce komai ba, zeyi mamaki ya ganki acikin Atamfa, karki damu ba abunda zece zeyi murna shima, kim san maza nason a basu mamaki, amma ina fatan kun shirya da shi"?

Widad tace "eh mun shirya, tun jiya amma da ƙyar yayi fushi dani sosai"

Jamila tayi murmushi tace  "Yawwa tawan, karki ƙara bari ya kwana yana fushi dake kinji ko, sannan ke zakiyi dabarun daze dena daɗewa yana fushi dake"

Widad tace  "to ni ya zanyi?, yana daɗewa beyi ba, amma idan yayi fushi da ƙyar yake sauka fa"

Tace "to kidena yin abunda ze sashi fushin mana, kuma Kinga yadda kike da kyan nan masha Allah, gaki da manyan idanu masu ɗaukar hankali masha Allah, ki dena kallonsa kamar yadda kike kallon sauran mutane, ki nuna masa Wata kissar sai mata (wanda be karanta littafin wata kissar sai mata ba na Ammar da Mufeeda, ya garzaya ya nemi nashi, akwai darasi a ciki 😍 da Nishaɗantarwa)

Idan zaki masa magana, ki dinga kashe masa ido, ko ɗan shanye idanunki kamar kina maye, dama na ganki masha Allah, shagwaɓaɓiya ce duk kidinga masa, ko yayi fushinma da kansa ze sakko, saboda karya yi missing wannan kallon"

Widad kawai ta kwashe da dariya, "Au dariya ma na baki? Aiko ki gwada zaki bani labari, ki dinga zuwar masa da abubuwan da bakya masa a baya, hakan zesa ya ƙara sonki, kin san mazan ne seda lallaɓawa, amma dukda haka suna mana ƙoƙari kuma suna haƙuri damu, sedai duk Allah ya bamu haƙurin zama da juna"

Hanne ce ta shigo, ta dinga jiyo dariyar Widad da Jamila, ta ƙaraso ta ɗaga labule, taga Widad a zaune da goyon 'ya suna hira da Jamila, ai shigowar da ba tayi ba kenan ta koma, tana tsaki.

Sunusi ne mijin Jamila ya dawo, dan haka Widad ta bawa Jamila' yarta ta fice, dama ba gaisawa suke ba da Widad, dan haka ne kulata ba bata kula shi ba ta fito ta tafi ɓangarensu, ta tarar Yusuf ya shimfiɗa tabarma a tsakar gida yayi ruf da ciki, yana karanta azkar.

Tana zuwa ta cire hijjabinta, ta hau kan bayansa.

Yace "ya hakane? sekin karyamin baya ne? So kike ki maidani gurgu?"

"Idan na maida kai gurgu ai dai mijinane bana wata ba ko?"

Yusuf yace "Allah? waye mijin naki, gayamin"

Tace "Yoseef ne mana"

Yace "to naji ɗagani, dan kin ƙara nauyi, matar ƙauye kawai kina ƙauye amma ƙiba kike"

"kaima Mijin ƙauye, kuma bazan tashi ba, idan ka takuramin kuma ka sha cizo ba"

Yusuf yace "hmm aikin taɓa cizona fa, akwai tabon a jikina"

Ta zare ido tace "yaushe na cijeka?"

"Ranar da aka yi ruwan sama mana da daddare"

Tace  "wane ruwan saman akayi?"

Yasa hannu ya janyota daga bayansa, ya kwantar da ita a jikin bango yana kallonta, sannan yace 

"Ranar da kika kusa taramin jama'ar garin nan, kalli inda kika cijeni, banda duka dana sha a gurinki"

Tura baki tayi tace  "Eh anyi ɗin ba kaine ka... Se tai shiru

Yace " ƙarasa mana"

"Anƙi a ƙarasa ɗin" tai maganar tana dariya.

Yusuf ma dariya yayi ya juya yayi rigingine, ta kwanta a ƙirjinsa tace  "Yayan Daddy, a rayuwa yadda da farinciki sune gaba gurin sada mutum da walwala, kalleni a garin da babu wauti, ba ruwa, ba waya, ba system, ba motoci babu duk wani abu na more rayuwa, amma gashi kai kaɗai kana bani farincikin da duk wannan abubuwan dana rayu dasu basu bani ba, dukda na sha wahala kafin sabawa da wasu abubuwan a garin nan, amma bayan na saba sena gane ita rayuwa a bace me sauƙi, yadda ka ɗauketa haka take zuwar maka Nagode sosai Ɗan uwana, kayi rawar gani a rayuwar Yarinyar da baka haɗa komai da ita ba"

Rungumeta yayi yace "ina fatan kasancewa dake har ƙarshen rayuwa ta Widad, dukda bani da tabaccin ina da mahalli a zuciyarki, kuma ban san yadda al'umma zasu karɓi Auren nan namu ba, amma nidai nasan ina sonki Widad, ban san yadda hali zeyi ba a nan gaba, ko dai mu kasance tare, kokuma mu rabu, amma ni dai nasan ina sonki, Dukda soyayya ta ta baya, banji naso wata kamarki ba, I love you Widad "

Ƙanƙame Yusuf tayi, tana jin wani irin shauƙi yana ɗibarta, a koda yaushe ta kanji farinciki idan yana tare da ita, koda suna gida yana a matsayin direbanta, ko tana cikin ɓacin rai idan taga yazo se taji damuwarta ta ragu, tana jinsa sosai a ranta amma ta kasa danganta hakan da Soyayya, a duk lokacin da taji damuwa ta mata yawa, tana haɗa ƙirjinta da nasa zataji bugun zuciyarta na daidaituwa, da zarar ya fara rarrashinta  ta kan manta ɗinbin damuwarta, tayi wani irin sabo na bazata da Yusuf, wanda har take jin ya zata kasance idan ta koma gida, Yusuf ya nesanta ida?.

"Yayana, zaka dawo gidanmu da zama dan Allah"

"meyasa kika dage sena koma gidanku da zama?"

"Saboda Halima zata bar mana gida, da kaina zan samowa Daddy mata ya aura, zaka dawo gidanmu ko?"

"Meyasa kika damu sena dawo gidanku bayan bakya sona?"

"Nima ban san dalili ba, sedai ina jin a jikina, rasa ka a rayuwata babban giɓine, kuma tamkar rasa garkuwa ne a gareni"

"Nima rashinki a gareni babban giɓine, saboda na kamu da makauniyar soyayya cikin bazata, amma ban saniba ko zaki iya cigaba da zama dani idan kika san wani abu game da rayuwata"

"Ni dai koma meye, dan Allah ka zauna a gidanmu idan mun koma kaji"

Ta maganar cikin Shagwaɓa tana kallonsa,  "Babyna wannan wane irin kallone haka kikemin? You look so cute da kika juya idonki"

Kamar ƙaramar yarinya ta kuma cewa "dan Allah kec zaka dawo mana"

Yace "sedai in dawo im cigaba da kaiki unguwa, ni nafi son aikina"

"Aikuwa demotion zan maka, ka koma gadin É—akina"

"Bakomai in dai hakan zesa in dinga ganinki"

Yai maganar yana saka hancinsa a wuyanta.

Ji suke tamkar suka ɗaine a duniyar, Kasancewar gidan ba kowa dan haka hankali  kwance suke soyayyarsu a tsakar gida, basu san Hanne tana ɗaki tana jiyo dariyarsu ba, dan har leƙsensu take ta taga tana share hawaye.

Anwar yayi tunanin bari ya tsaya a gidansu Nurat su gaisa, kwana biyu kota waya basa haɗuwa dan bama hawa yake social media ba sosai balle su gaisa, sannan su jajantawa juna abubuwan da suke wakana, sedai a bakin gate megadi ya tareshi yace  "wa kake nema ne?"

Anwar yace  "gurin Nurat nazo"
Chapter 51 · 0% Book details