Sashe 86
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Justice Abdullah yai murmushi yace "Bukar Bulama, ai komai akan doka akeyinsa, dukda munawa dokar karen tsaye wasu lokutan, saboda irinku da mukewa alfarma, amma karka damu insha Allah zanyi duk yadda zanyi in ƙarƙare shari'ar nan, ba da daɗewa ba yanzu se Allah ya kaimu bayan sati uku zamu sake zama "
"Gara dai ayi a sake zaman, dan Allah karka zake jan lokaci dayawa, bazan iya jira ba, sonake a ƙare komai"
"Shikenan, kaje ka kwantar da hankalinka, nan kusa zan ƙarƙare shari'ar hankalinka ya kwanta"
Bulama yace "da dai yafi ai"
A dutse yace "Amma, wai ya akayi kaji wannan raunin haka? Gaba ɗaya kamaninka sun sauya kayi wani iri, fuskarka ko ina ɗinki"
Bulama ya miƙe yace "karka damu da wannan, ƙyaleni kawai daga nan wani guri zanje, ina nan ina sauraren yadda zata kaya"
A dutse yace "shikenan, nagode sosai ka gaida gida"
Sukayi musabaha sannan Bulama ya tafi.
Nurat! Nurat!! Alhaji Musa ya shigo yana ƙwalawa Nurat kira, ta fito falo tace "Gani"
"Ubanwaye yace ki aika wai aje a duba miki Widad?"
Ta kalle shi tai shiru, ba tace komai ba.
"Ba magana nake miki ba? Ubanwaye yace ki aika wai a dubo miki ita babarkice ita meye haÉ—inki da ita?"
Yai maganar yana zazzaro ido kamar ze daketa.
Nurat ta girgiza kai tace "A'a Daddy nifa ba da wani abu na aika ba, kawai naga ƙawata ce kuma ga abunda ya sameta, ni kuma ka hanani figa, shine nace aje a dubamin"
"Ƙawarki ɗin banza da ta wofi, kuma wallahi ki kiyayeni da wannan yaron Khalil, idan kika bari na sake ganinsa a gidan nan sena ci mutumcinsa, sannan kije ki kwaso min wayoyinki ki kawomin su nan, kuma ko kina so ko bakya so sati me zuwa zaki bar ƙasar nan "
Mahaifiyar Nurta ta fito tana cewa," Kwanan nsm bam san meyasa kake wannan abubuwan haka ba, meye laifi dan kawai tace aje a duba mata ya take? "
" Idan ina magana kika ƙara sakamin baki wallahi sena ci mutuncinki, na gayamiki kin sani sarai abunda ke tsakanina da uban yarinyar, amma take shisshige mata"
"Amma larura ai tafi ƙarfim wasa, abun jaje ya samu mutum kace baza'a jajanta masa ba?"
Yace "eh baza'a jajanta ɗin ba, wuce kije ki kawomin wayoyinki, daga yau har ranar da zaki bar ƙasar nan, bake ba fita ko ina, kuma kar wani ya sake yazomin gida, ɗakkomin wayoyinki gabaɗaya, har System ɗinki"
Nurat ta shiga ɗakinta, ta ɗauki wayarta ta ɓoye, ta ɗakko sauran ya kai masa, ya karɓi wayoyin da system ɗin yace "ina ɗaya wayar taki take"?
Yai maganar yana kallon ta, Nurat tace "Na bawa Khalil ya kaimin gurin gyara"
"to ki gaya masa maza maza ya kawota, ki aika direba maza ya karɓomin wayar nan, maza fice daga nan ki bani guri"
Nurat ta wuce ɗakinta, tana tunanin meye abunyi, koda tsiya koda tsiya tsiya dai bazata bar ƙasar nan ba, se taga abunda ya turewa buzu naɗi"
Wasa wasa fa fiye da wata guda babu Anwar babu labarinsa, duk neman dazaa'yi anyi amma ba'a samu Anwar ba, hankalin Hajiya Halima gaba É—aya a tashe yake, da tana iya basarwa amma yanzu ta kasa jurewa, ga Shu'aibu ya sata gaba yana ta tatsarta kota ko ina, ta zauna tayi shiru a falo ta rasa abunda yake mata daÉ—i.
Sallamar Alhaji Haruna ce tasa ta ɗaga kai ta kalle shi, mamakine yakamata ganinsa da tai kamar korarre, tace "lafiya kuwa?"
"Ina fa lafiya, ina' yarki take?"
"wace 'yar tawa kake nufi?"
"Yarinyar da kika aiko ta kawon takadda"
"Wai Amal kake nufi?"
"Eh ita, wadda ta karye"
Hajiya Halima tace "to meye yasa kake nemanta? Wani abun tayi makane ko kuwa?"
"Eh nemanta nake"
Amal tace "gani nan, lafiya kake nemana haka? Ko kuma naci ban biys bane?"
Suka juya, suka bita da kallo, tace "meye kake nemana?"
Sekuma ya diririce, ya rasa me zece ganin ga Hajiya Halima ta tsatstsare shi da ido.
Amal tace "faɗi mana, ina jinka"
Hajiya Halima tace "nifa gaba É—aya kaina ya kulle, kumin bayanin abunda yake faruwa"
Amal tace "Mummy, ki kwantar da hankalinki babu wani abu fa, Alhaji muje farfajiya muyi magana"
Amal ta janye shi zuwa farfajiyar gidan ta kalle shi tace "lallai kaci ksi, baka da hankali da nasani nz tona maka Asirin abunda kayimin a gabanta, tunda kanka baya js yadda yakamata"
"wace maganar banza kikeyi hakane? Me kika aikatamin?"
"ba wani abu na aikata maka ba, illa na saka maye na ɗauki wayarka na bayar anyi abunda yakamata na turi kuɗi daga Account ɗinka, na raba kuɗin gida biyu na ɗau rabi, shine fansar budurcina daka ɗauka, kuma bari in gaya maka wani abu, akwai mahimmin saƙo da na ajiye na rarrabawa mutane, wallahi duk abunda ya sameni kaine, seka ƙara wannan akan kaidim mata da kace mim ba wanda baka sani ba, wawa kawai kuma wallahi ka kuma zuwa gidan nan duk abunda nayi maka kaika siya da kuɗinka ba wani ya sai maka ba, kuma a taƙaice takadda dai babu ita dan nima ban san inda take ba"
Ta ƙarasa maganar tana masa wani irin mugun kallo, ta shigevta barshi a gurin kaman gunkin mutanen farko.
Har ta shiga zata wuce ɗakinta, Hajiya Halima ta kira sunanta  "Amal"
Ba tare da ta juyo ba ta tsaya cak , "meye haÉ—inki da wannan mutumin?"
"Babu komai"
"Karkimin ƙarya, meye haɗinki dashi?"
Yace "yana so nane, nikuma nace bana sonshi, ya takuramin nikuma na zage shi, shine zezo ya É—agamin hankali"
"to dan ba kya sonsa meye na zagin masa kuma? Ai bekamata ki zage shi ba"
"to Mummy ni kalarsa ce? Ko da ƙuriciyata zan Auri wannan dattijon mutumin ne? Ai uba na ɗauke shi, amma tunda bega hakan ba shine nai masa abunda ya dace dashi"
"koma dai meye karki kuma zaginsa, dan ya haifeki kuma koba komaiakwai mutunci, da alaƙa tsakanina dashi"
"karki ji komai Mummy, hakan bazata sake faruwa ba"Â ta wuce É—akinta.
Bulama ya fito ze fita, yaga motar Fahad a harabar gidan, dan haka ya fasa fitar ya nufi BQ inda suke, a falo ya tarar da Fahad, yana ƙoƙarin kunna TV, ya kalli Fahad yace "kai daga ina kake? Na samu labarin seka kwanaki baka gidan nan, gidan ubanwa kake zuwa haka?"
Fahad ya sosa kai yace "Daddy gurin abokaina nake zuwa, shiyasa"
"wasu irin abokaine zakaje ka kwana huÉ—u a gurin su? Kai baku da gidane?"
"muna dashi"
"to ya akayi kake zuwa kwana wani guri?"
Fahad yai shiru, Bulama yace "Shikenan ka kiyaye idan na sake ji sena hukunta ka na gaya maka"
Fahad yace 'to, amma Dad what's wrong with you in your face, naga É—inki a fuskarka"
"Da ka damu dani ai da baka fita ba, kaje kayi kwanaki haka ba, ban sani ba"
"Sweet heart, wai har yanzu me kake a falon ne?"
Wata yarinya ce ta fito da Towel ɗaure a ƙirjinta daga bedroom ɗin Fahad, Fahad ya shiga zazzare ido, Bulama yace what, mezam gani haka? Fahad wacece wannan? "
Fahad ya sunkuyara da kai yana sosa kai," ba magana nake maka ba? Wacece wannan É—in me take a nan ".
" Daddy dan Allah kayi haƙuri "
" Sallameta tazo ta barmin gida maza maza "
" wallahi ka bani kunya Fahad, neman mata? Akanme kuma a cikin gida na dan asara"
Fahad yace "wallahi Daddy ni Aure nakeso, kuma har yanzu kaƙi ka auramin Widad shiyasa, ni gaskiya shiyasa kawai nake bi ta ɓarauniyar hanya"
Bulama ya dinga masa bala'i, ya kori karuwar nan, ya taho cikin gida yana zazzaga bala'i, "Sarah, kina gidan nan amma yaron nan yake neman mata, kai Ramadan ga ɗakinka ga nasa, amma yake kawo mata gidan nan baka taɓa faɗa ba?"
Ramadan yace "ai Daddy kafi sonsa, kuma kona faÉ—a ba yadda zakayi ba Shiyasa"
"Nika ke gayawa haka Ramadan?ke Sarah kina kallo amma baki É—au mataki ba, ko ki gayamin ba?"
"Barewa bata gudu, É—anta yai rarrafe"Â shine amsar kawai data bashi, ya tsaya sororo yana kallonta.
Nurat taje ta ɗauki wayarta, ta ɓoye ta shiga tunanin yadda zata bawa Khalil wayar nan, ba tare da mahaifinta ya sani ba, tunda an hanata fita, kuma Mahaifiyarta na ja maata kunne sosai akan shisshigi akan lamarin mahaifinta.
A hankali ta lallaɓa ta sato wayar Mum ɗinta, ta dawo ɗakinta ta kira Khalil, yana ɗagawa tace "Brother a gurguje, dan Allah karka sake zuwa gidan Bulama neman Widad, akwai wata ƙulallaiya a ƙasa, akwai wani abu ds suke ƙullawa shi da Daddy na, ya gaya masa kaje gidansa neman Widad, amma Daddy yazo yana ta faman min faɗa, ya ksrɓs wayoyina saura ɗaya kawai, ya za'ayi kazo ka karɓa? "
" Nima na fuskanci akwai wani abu a ƙasa a tsakanin mahaifinki da Bulaman nan, ina da wani plan ne a ƙasa, amma karki damu zanzo in karɓi wayar "
" karka soma zuwa Brother, akwai matsala, zan san yadda zanyi idan ina so muyi magana zan kiraka a wayar Mum, se anjima "
Tai sauri ta kashe wayar, ta lallaɓa ta mayar mata da wayar.
Bulama ya kalli Fahad dake zaune ya sunkuyar da kai yace " kai dama Aure kake so amma ka tsaya kana bin wannan sakarkarun matan? Bayan zan aura maka cikakkiyar mace "
" Daddy wane cikakkiyar mace, bayan har ciki gareta?"
"ina ruwanka da cikinta? Nayi wani planning akanta, yanzu haka tama gidana na can hanyar ƙuyukan nan ma bayan gari, in da nake noman albasa, wannan gidan can na kaita na ajiye, kuma ko tana so ko bata so, za'a zubar da cikin nan ka Aureta, amma wannan da kake kawowa aiba mata bsne, idan aka kamanta su da ita "
Fahad ya washe baki yace " to Daddy nagode sosai, wallahi idan na Aureta sema rama dukan da tayi min, bazan manta marin nan ba"
Bulama yace "kai dai ka bari, aure kamar anyi an gama ne ai"
Fahad ya dinga washe baki, kamar wani sakarai.