← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 127

Sashe 74

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mummy tace "eh Bulama ya cemin idan aka gama bincike kotu za' a kaishi, dan haka ni yanzu ba ta tashi nake ba, ta Anwar nakeyi har yanzu shiru, tunda Amal ta kai musu takaddar basu sake cemin komai ba"

Ramlah tace "zasuyi miki magana ne, bari mu kunna TV mu sake ganin idon munafukin nan, dan ban manta lokacin da ake wulaƙantamu ana cin zarafin mu saboda shi ba"

Ajiyar zuciya Amal tayi, wanda yasa suka juya gaba É—aya suka kalleta, wucewa tayi kitchen dan Samarwa kanta abunda zata ci.

Mummy tace  "Auta ya jiki?"

Ta kalli Mummy ta É—auke kai, ta wuce kitchen, ta fito daga kitchen tazo ta zauna tace "Mummy, hira naji kuna yi kamar an kama Yusuf ko?"

Ramlah tai farat tace  "Eh an kama shi, seme ne kuma? Ko zaki fara wa mutane shirmen naki ne?"

Amal ta girgiza kai tace  "No akanme? Ina Ita Widad ɗin take?"

"Tana gidan Bulama, dan shi ze iya wannan haukan nata"

Amal ta jinjina kai, ta tashi ta tafi ɗakimta, tana jinjina kai, da sauri ta ɗauki wayarta ta shiga social media, aikuwa taga yadda labarin ya cika social media, yadda aka haɗa ƙarya da gaskiya.

Ta ajiye wayar tayi shiru tana tunani, kasa shan tea É—in nan tayi, se tunani daya dabai baye zuciyarta, gaba É—aya tausayin Yusuf ya mamaye zuciyarta, tama jin tsohuwar soyayyar sa na taso mata.

"Nurat" Alhaji Musa ya kira sunanta, ta amsa masa da "Na'am Daddy"

"ya maganar shirye shiryen tafiyarki ne, you should preparing for it fa, lokaci yana gabatowa"

"but Daddy, i thought we have discussed this issue since"

Ya kalleta yace "muka ce mene?"

"Daddy na gaya maka ni bana son tafiyar nan, ni ba inda zanje a gida Nigeria zanyi karatun"

"ba zakiyi a nan ɗin ba, ƙasar nan zaki bari, waike yaushe muka fara sainsa dake ne? Ni zance ga yadda za'ayi amma ki bijiremin? To baki isa ba nina haifeki bake kika haifeni ba"

Ya dinga banbamin bala'insa, yayi ya gama tsaf bata sake cewa komai ba, seda ya gama tukuna sannan ta miƙe ta bar masa ɗakinsa, tana zuwa ɗakinta tace 'wallahi ba inda zanje, bazan bar ƙasar nan ana wannan halin ba, se naga abunda ya turewa buzu naɗi"

Yusuf kam ya daku a gurin jami' an tsaro, akan lallai seya amsa shine ya sace Widad, amma Yusuf ƙemem yaƙi magana, dama shi Saleh ba'a maganarsa saboda ya galabaita fiye da Yusuf ko magana baya iyayi, bama shi da lafiya.
Juyin duniya Yusuf ya amsa shine ya sace Widad yaƙi, yaƙi ko ɗaga kansa ma balle yayi magana.

Mutumin da yake jibgarsa yace "ga 'yan jarida cam suka cika harabar gidan nan, zamu basu lokaci suyi magana da kai, ka furta kaine ka sace yarinyar nan koka samj sassauci, idan kuma kaƙi to haka zamu ci gaba da casaka a gurin nan, gara ka nemawa kanka mafita, ka amsa kai ka sace ta"

Yusuf dai beyi magana ba, aka taso ƙeyarsa a gaba aka saka masa handcuffs hannu da ƙafa, aka fito da shi harabar headquarter na 'yan sanda, fuskarsa duk ta kumbur saboda duka.

' yan jarida sun cika gurin nan, suka kewaye Yusuf da abun magana, kowa yana yanko masa tambaya, wasu ta gaske wasu ta cin mutunci, amma Yusuf yai shiru, sukayi sukayi har suka gaji, har ya juya za'a maida shi ya tsaya ya waigo, ya kalli' yan jaridar nan yace "Bani na sace ta ba"

Kawai ya juya, ds ƙyar 'yan sanda suka dakatar da' yan jaridar nan aka mayar da Yusuf inda aka ɗakko shi.

Nurat gaba ɗaya ta tayarwa da Khalil hankali akan maganar Yusuf, ga koke koken da take akan batun komawarta karatu, tana ta saƙawa da warwar akan ta gudu ta bar gidan gaba ɗaya, amma sedai tasan idan tayi hakan ba zata sake daraja a idon mutane ba.

Alhaji Haruna duk ya shiga damuwa da tashin hankali, akan takaddar nan da Amal keta rainamasa hankali akan ta, ya shiga part ɗin Amaryarsa ya tarar da ita ta ƙurawa TV ido cike da damuwa, ya zauna kusa da ita yace "Baby kallo ake ne?"

Ta ɗan ɓata fuska tace "ina kallon wani abune daya tsayamin a zuciya, wannan bawan Allah da aka kama akan 'yar gidan Daula ya tsayemin, i can't imagine ze aikata wani abu makamancin haka, ƙarya ce kawai akayi masa"

Yace "ke ya akayi kika san ƙarya akayi masa? Wannan shine abunda ya dace dashi, kuma zamu tsaya kai da fata se an hukunta shi anyi maganin irinsa a cikin al'umma"

Ta kalle shi tace "Nasan Yusuf, fiye da yadda kake tunani, inaga mahaufiyarsa ce kawai zata fini sanin waye shi, wallahi wannan maganar ƙarya ake masa, mutumin da yake kamar waliyyi dan haƙuri, wannan maganar ƙaryane wallahi"

Alhaji Haruna yace "Salma meye haɗinki dashi da kike wannan zaƙewar, meye haka kike yi akansa, kuma a gabana?"

Ta Harare shi tace "Yusuf unguwar mu ɗaya, kuma tsohon saurayi nane, wanda aka hanani Aurensa aka ƙaƙabamin kai"

Kawai ya kwashe da dariya yace "lallai baki da hankali, aikuwa kina ji kina gani ze tafi prison Salmata, sedai haƙuri"

Ya tashi ya barta a gurin, tausayin Yusuf ya kamata, tasan Yusuf baze taɓa aikata abunda akace yayi ba.

Widad tana zaune kamad wata mahaukaciya, tun jiya da safe rabonta da Abinci, tana jin yadda zuciyarta take bugawa ba daidai ba, tai shiru tunani da tausayin Yusuf ne yake ta ratsa zuciyarta.

Iman ta shigowa da Widad da Abinci tace "ga Abinci, ki daure kici dan Allah"

Widad tace "kiramin Bulama, zamuyi magana"

Iman tace to, befi mintuna biyar da fitarta ba sega Bulama ya shigo É—akin, yana shigowa ya kalleta yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Widad har yanzu bakya cin Abincin, subhanallah ko mota za'a É—akko mu tafi Asibiti ne?"

Tace "wani hali Mijina yake ciki?"

Bulama yace "waye mijinki kuma?"

"Yoseef" ta bashi amsa

"yaushe kikayi Aure bamu sani ba?"

Cikin tsawa tace "ka dena amsamin tambayata da tambaya, ina Yoseef yake?"

Bulama yace "yana hannun hukuma har yanzun"

Ta miƙe tsaye tace "har yanzu baka yi komai a kai ba ko? Ni ka maidani gidan mu gurin Daddy na, shiyasan ranar da Yusuf yayi masa, baze bari ya cutu ba akan laifin da beyi ba"

Bulama yace "kinga ki kwantar da hankalinki".

"Karka ƙara cewa in kwantar da hankalina, ina Alhaji Nasir Daula yake? Ina babana Daddyna nake maka magana, yana ina? Ta yaya za'ace tun jiya har yanzu babu shi babu dalilinsa bezo inda nake ba"?
Tai maganar a jere bako haÉ—iyar yawu, tare da É—aga murya sosai.

Bulama yace "kinga zauna kici Abinci tukuna"

Ai be rufe baki ba tasa ƙafa tai ball da kayan breakfast ɗin, ta riƙe gaban rigar Bulama tace "ka gayamin gaskiya, ina Daula yake? Idan an kashemin shine ka gayamin, yana ina? Ina yake ina Daddyna?!"

Jin Hayaniya yasa tuni mutan gidan suka fara taruwa a ɗakin, Hajiya Sarah tace "babanki Nasir Daula, tun bayan ɓatanki ya kwanta rashin lafiya, aka bishi har gadon Asibiti aka sace shi, har yau babu wanda yasan inda yake"

A hankali Widad ta saki rigar Bulama, tana kallon Hajiya Sarah "Annn. An sace Daddyn Widad a gadon Asibiti, this serious, Daddyn how comes? Ta yaya za'a sace shi ba wanda ya sani, shikenan na rasa Yoseef É—ina, Daddyna ma ace ba'a ganshi ba, Noooooo! This impossible!!!

Tana maganar ta silale ta faÉ—i ta ruf da ciki, ko numfashi ba tayi.

Ayi haƙuri ba editing

Ayi subscribing YouTube channel É—ina dan Allah, me suna Cool Arewa TV
11/21/21, 7:45 AM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

110_111

Me Adda ya kawowa mutumin kujera ya zauna, ya kalli Saleh yace "ka dena mamaki mana, ai bekamata kayi mamaki ba, a zatonka kai kaÉ—aine me wayo, ko kuma kafi kowa wayo? Kifi na ganinka me jar koma, kallonka kawai nakeyi"

Saleh yace  "hmm Bukar kenan, kaima kuka karya Alƙawari balle ni, haka mukayi daku? Ashe kun kashe min ɗan uwana, banma sani ba balle kua bamu gawar muyi masa sitira, dama haka akeyi, kunyi amfani dani ne dan cinma burinku?"

"ƙwarai kuwa, muna amfani da kaine dan cinma burinmu, kai bari in gayamaka wani abu, ku duka wanda nake aikin harƙallar nam daku, ina amfani da kune dan cinma burina nikaɗai, na ɗaukeku karnukan farauta tane kawai "

" Amma wallahi Bukar baka da imani, baka da adalci "

Me Adda ya yunƙura ze kaiwa Saleh duka amma Bukar ya hana shi yace "ƙyaleshi, ai baaka ga komai a cikin ƙudrina da AƘIDATA ba, kuma dama tuntuni kowannen ku nayi masa tanadin makomarsa idan deal ɗinmu ya kammala, sedai kai kayi gaggawa gurin riskar taka makomar, tunda ka yaudareni kaci amanata zaka riski makomarka a nan kusa, ina Widad take? "

Saleh yai masa wani irin mugun kallo yace "ni ka bawa ajiyarsu kokuwa? Kaje ka tambayi wanda aka sa su sacesu gasu nan a gabanka"
Chapter 74 · 0% Book details