Sashe 57
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idan ciwonta ya tashi, shine yake ayyukan gidan, ko kuma yayi zaman jinyarta a gida ko a Asibiti, duk wata kulawa daya dace ya bata yana bata, katsam Allah ya bata ciki ba zato ba tsammani, ya dinga murna shida ita, sedai cikin beje ko ina ba ya zube saboda yawan rashin lafiya.
Bashir mutum ne me tawakkali dan haka be taɓa gazawa ba, baya nuna mata ya ƙosa da rashin lafiyar da take yawan yi, ya kance a tausayi irin na mata da son da matarsa Jidda ke masa, idan shine yake a halin yawan larurar nan bazata guje shi ba, to shi meze sa ya gujeta, bayan ba ita tayi wa kanta ba, Allah ne ya jarabceta.
Bashir Ya zama abun kwatance a dangi, mijin tace nusari da ire iren wannan miyagun sunayen haka suke kiransa, wai ya ƙare a gindin mace seta talautashi tukuna ta tsiyata shi, kullum cikin ciwo gashi bata da wata mamora tunda ba haihuwa take yi ba, ya zamana saboda irin wannan cin mutunci da ake mata ko shiga tarurrukan biki ko suna ko makamancin haka ya hanata, saboda muddin zasu haɗu da 'yan uwansa gorin nan ne se anyi shi.
Idan suka fuskanci baya gari, haka zasuje har gida su zazzaga mata rashin mutunci iri iri, su ɗauki abunda suka ga dama, suce ai kayan ɗan uwansune, banda tayi Asiri ta mallake shi, ta yaya ze dinga bata abubuwa bayan juyace ba haihuwa take ba, se aikin larura dasa ɗanuwansu zaryar Asibiti, duk ta tsiya tashi saboda yawan rashin lafiyar da take yi, yayi da lafiyarsa yayi da aljihunsa, dan hatta jini idan ta buƙata shike bata.
Ita kuma ba sawa ba fitarwa, haka zasuyi abunda suka ga dama idan sun tafi ta sha kukanta, kamar yadda suka saba baya gari sukaje suka mata cin kashi yadda suke so, ya dawo ya tarar da ita tasha kuka, ya tambaye ta meyasa meta? Tace masa ai bakomai, seda taga ze ɗau zafi sannan ta gaya masa, shi yayi mamaki, be taɓa sanin har gida suke biyota suyi mata ba, aikuwa yaje yayi musu tatas, kuma yace musu mutu ka raba shi da matarsa, tana da matsayi me girman gaske a zuciyar sa, dan haka komai tayi bata laifi a gurinsa, yace larura da lafiya duk na Allah ne, me lafiya na ina komawa mara ita, mara ita ya samu, babu wanda yake sa kuɗinsa dan ya sai cuta, sedai Allah yana jarrabar komai, dan haka ya yadda rashin haihuwar Jidda, da rashin lafiyar ta jarabtace Allah ya jarrabesu dan ya gwada imaninsu.
Nan ma dangi suka kuma kwaroroto, suna yamaɗiɗi dashi, waiya fifita matarsa akan danginsa, abun takaicin hadda maza ake wannan sakarcin, ba abunda yake ƙona masa rai irin hadda ƙannensa da suke uwa ɗaya uba ɗaya suke ƙin abunda yake so, ya tabattar a zuciyar tausayi da imani na mahaifiyarsu, da tana da rai duk bazata bari ayi masa haka ba, shikam Bashir ya musu banza dasu da surutun da suke yi, yayi kamar besan sunayi ba.
Daga baya ma ya koma, indai zeyi tafiya ta 'yan kwanaki wani garin harkar aiki, da ita yake tafiya suje su dawo, dan karma wani daga danginsa su bita gida su ɗaga mata hankali Wataran tafiya ta kama shi, yace ta shirya su tafi Tare, haka kuwa akayi suka tafi tare, seda sukayi wata guda sannan suka shirya dawowa Kano, sedai dare yafa yi musu a hanya, Bashir yace 'Jidda, dole idan muka shiga gari mu samu Hotel mu kwana, kin san ƙasar nan ba security "
Jidda tace " dama abunda nake son in gaya maka kenan, dan a tsorace nake "
" to sarkin tsoro, karki damu muna samun guri zamu tsagaita da tafiyar "
Da yake daga kudu suke, wani dajin idan sukabi, sesu shafe tafiyar awa guda basu ga ko giftawar me keke ba, balle abun hawa.
Daga nesa suka dinga hango hayaƙi, gaba ɗaya Jidda ta tsurw tace "Anya bazamu juya ba? Nifa tsoro nakeji hayaƙin meye wancan?" '
"idan mun juya mu koma ina? Aiba inda zamu se naga meke faruwa a gurin"
Jidda ta cigaba da salati, dan tunda yasa kansa seya ƙarasa, saboda Bashir Jarumi ne sosai, bashi da tsoro.
Suna suka ga wata motace tayi hatsari a gurin, sun daki bishiya motar ta kama da wuta, ma'aurata ne a ciki sun kasa buɗe murfin motar su fita, se matar ta daki glass ɗin motar da yayi saura be ƙarasa rugurgujewa ba, ya fashe, tana ta ihu Wuta na cin jikinta tana Yusuf ɗana, ɗana Yusuf ta jefo jariri daga Widow, hannun ta duk ya ƙone se salati take, da alama shi mijin nata dama tuni ya mutu.
Ta wurgo jaririm ta wannan tagar, sedai jikinsa lafiya ƙalau beji ciwo ba, amma gefen wuyansa ya yanke, saboda glass ɗin motar daya fashe, yaron yasha hayaƙin gobara, baya numfashi sosai ga jini na zuba a wuyansa, Jidda tai Wuf ta ɗauki kyakkyawan jaririn a towel, se ƙamshim turare da ƙaurin hayaƙi yake yi, suna ji suna gani haka Wuta ta ƙone motar da iyayen wannan jariri yake.
Jidda tai kuka tai kuka, tunda take bata taɓa ganin bala'i da tashin hankali irin wannan ba, Bashir ya rarrasheta, suka shiga mota ya dinga tsala gudu, har suka fita gari suka sami Asibiti suka shiga, kasancewarsa ɗan sanda id card kawai ya nuna akayi admiting ɗin jaririn.
Bashir ya ɗakko waya daga aljihunsa, Jidda tace "wa zaka kira?"
Bashir yace "zanyi wayane, in gayawa abokan aikina incident É—in É—aya faru, azo a san yadda za'ayi muyi mus handing ove jaririn mutafi gida"
Girgiza kai ta shigayi tace "dan Allah Yaya Bashir ina son yarom nan ka barmin shi, karma ka gayawa 'yan sanda mun samu yaro, kabarmin ina so tunda ban taɓa haihuwa ba"
"to yanzu ai danginsu zasuji daɗi idan suka ga yaron ya kuɓuta"
"Yaya Bashir, komai nasu fa ya ƙone, ta ina za' a fara neman dangin nasa, dan Allah ka barmin inajin ƙauna da tausayin Yaron nan a raina, dan Allah ka bsr maganar nan, zan raini yaron nan in dai kamin izinin hakan, dan Allah"
Bashir yayi shiru, ganin yadda take kuka, bilhaƙƙi son ɗan nan take dagaske, yasa yace "shikenan is ok, Allah ya tayaki riƙo maman Yusuf, Allah ya raya mana Yusuf bisa tafarki madaidaici, ya bashi haƙuri da juriya irin na me sunan"
Nan ta dinga murna, ta rungume Bashir tana zuba masa godiya da Addu'a, ita da Bashir sukaje yayo siyayyar kayan jarirai kala kala, da duk abunda zasu buƙata, seda suka kwana uku a Asibitin daba'a garinsu ba, dan jaririn ya samu sauƙi.
Bashir kuma yayi waya, akaje aka kwashe gawarwakin nan a inda aka yi hatsarin.
A kwana ukun nan madara take haɗawa ta bashi, Jaririn sam bashi da rigima, harta ɗan fara damuwa ko jikin nasa ne be gama warwarewa ba, daga baya kuma ta fuskanci haka halinsa yake, bashi da rigima sam, bayan an sallamosu suka kamo hanyar gida, amma tun a hanya ta fara tunanin me zata cewa dangin mijinta idan suka ganta da ɗa? Bashir ya lura da yadda tayi shiru, yace "Maman Yusuf, ya kuma naga damuwa a fuskarki?"
Ta ɗan yi ajiyar zuciya tace "Yaya Bashir, ina fargabar amsar da zamu bawa mutane, idan suka ganni da jariri, mussman su Yaya Asma'u"
Bashir yace "ba dai kina son É—anki ba?" ta jinjina masa kai alamar eh.
"to karka damu da abunda mutane zasu faɗa, kisa a ranki ba rainon kariri kawai zakiyi ba, harda na ƙalubale ki manta da wani ƙalubake da abunda mutane zasu faɗa, mu rungumi jaririnmu, Allah ne ya bamu"
Ta kallesh tace "dagasake kaima kana son jaririn nan?"
Yace "meze hana, muda muke nema Allah ya bamu, ai ina son duk abunda kike so, ina son Yusuf nima bari kiga mu koma gida, hakika zan kuma yanka masa, muyi shagalin suna dan Jaririn naki befi watanni biyu ba, gashi me kyau masha Allah kamar ke"
Jidda tayi murmushi tace 'mijina ɗan Aljanna, Allah ya baka abunda kake nema duniya da lahira "
" Ameen tare da ke matata"
Se fargabar da take ta É—an ragu, suka nufi gida.
Bayan la' asar suka isa gida, bayan sun yi salla sun huta, ta dafa ruwa ta yiwa jaririnta wanka, ta canza masa kaya, ta goya abunta tana jin ƙaunarsa a ranta.
Bashir da kansa ya sai cingam, ya dinga aikawa mutane cewar za suyi taron sunan jariri, mutane suka dinga mamaki dan su dai basu san tana da ciki ba.
Nan 'yan uwansa sukazo domin ganin ba' asi, aikuwa suka tarar da ita da Jariri.
Wani Yayansa ya sashi a gaba da tambayoyi, akan sun san matarsa ba haihuwa take ba, ina suka samo ɗa Bashir yaƙi gayamusu, suka haɗashi da wani ƙanin babarsu, ya kira shi ya tambayeshi,
Bashir yace "gidan marayu sukaje suka ɗakko yaro, jaririn iyayensa ne suka yi hatsari suka mutu, kuma ba'a san daga inda suke ba, shine sukaje gidan suka karɓo shi.
Nan ma 'yan uwa suka samu nayi, wai ya biyewa matarsa sunje gidan marayu sun É—akko shege, babu wani iyayen yaron sun mutu, duk yaran dake gidan shegune.
Jidda ta dinga kuka tana É—anta ba shege bane, Bashir yaita rarrashinta, ya gayyaci mutane akayi sunan Yusuf, akayi shagali sosai aka watse.
Jidda ta rungumi jaririmta da mijinta, sedai wani abun mamaki da iko na ubangiji, tunda Allah yasa suka fara rainon ɗan nan, Jidda ta dena wannan rashin lafiyar da take yawan yi, ta warke sarai ta dena kwanciyar Asibiti, idan ba an faɗa maka ba bazaka ce tayi fama da jinya ba a baya, sosai suke rainon Yusuf, bazaka taɓa cewa ba ɗansu bane, idan har kana son farincikin Jidda da Bashir to kaso ɗansu Yusuf.
Sedai fa dangin mijinta suka kuma sata a gaba, suka tsani yaron nan ƙarara suke nuna masa ƙyama, suke ce masa shege, Sedai Jidda tayi kuka, ita dai tasan Yusuf ba shege bane da iyayensa, amma haka take sharesu ta cigaba da kulawa da shi ita da mijinta Bashir.