← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 127

Sashe 109

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salma tace  "kai ko kunya bakaji ba kake cewa ifa ga kawo maka kanta? Allah wadaran halinka nayi dana sanin Aurenk, Wallahi da in Auenka gara ace Yusuf ɗina na Aura dukda rashin asalinsa, dan nasan baze taɓa wannan akuyancin ba"

Hajiya Halima tace  "Haruna ka bani kunya, ka bani mamaki ka cutar min da yarinya, gaba ɗaya kun kassaramin rayuwata data yarana, wancan ya ɓata kunce a kasheshi, wannan kai ka lalata ta, waccan kuma Bulama ya lalata ta ɗansa ma yayi, sun saka mata HIV, na rasa dame ma zan kiraku, kun cuceni kai da Bulama dukda kasancewarsa ɗan uwana Allah ya isa wallahi "

Tai maganar tana kuka, Alhaji Haruna ya saki tumbi yana kallonta, duk damfara da satar da 'yarta tayi masa bata gani ba se shi zata kalli abunda yayi mata.

Ya kalleta sama da ƙasa yace "Malama ki fita ki barmin gidana, kije can ku ƙarata, ita bata gayamiki abunda tayimin ba, se wanda nai mata, kije kiyi duk abunda zakiyi, kinzo kin ɗagamin hankali a cikin iyalina"

Hajiya Sarah ta kalleshi tace "ni kakewa haka? Ni kake kora daga gidanka? Kamin wannan mummunan abu sannan ka Kalleni kace in bar maka gida?"

fice daga gidan, zuciyarta na ƙuna gaba ɗaya yaranta sun lalace gaba ɗaya.

Salma taje gabansa ta tsaya tace "wallahi banga amfanin zama da fasiƙin mutum irinka ba, dan haka ka sakeni malam"

Alhaji Haruna yace "Ai Aurena dake har abada tunda iyayenki kwaÉ—ayayyune, sunga kuÉ—i sun auramin ke wallahi bazan sakeki ba dan ina sonki"

"karka sake ka zagarmin iyaye, kuma wallahi seka sakeni tunda ba tare aka haifemu ba, macuci me abun kunya kawai"

Ya tureta yai wucewarsa yace "kanki ake ji, wadda taga zata zauna shikenan, wadda bzata iya ba ta ƙara gaba, amma saki kam babu shi"

Cikin kuka Salma tace "wallahi ƙarya kake seka sakeni, wallahi bazan cigaba da zama sa fasiƙi ba"

Uwargidan kam bata iya magana, sedai kuka dayake irin ta da ɗin nan ce, tun auren ƙuruciya gashi babu wani isashen ilimi a tare da ita.

Lamarin mahaifiyar Nurat fa sam babu sauƙi a lamarin, dan sati guda kenan babu wani cigaba, gaba ɗaya Nurat ta ɗaga hankalinta akan halinda mahaifiyarta ke ciki, jin mahaifintane yai sanadiyar faɗowar mahaifiyarta daga bene yasa taji gaba ɗaya ya fita daga ranta, ko san ganinsa ma batayi, gashi idan yazo Asibiti dubata 'yan uwanta suyi ta haɗe masa rai, ko sabgarsa basa shiga, Nurat kam an sallameta tuni amma taƙi barin Asibitin, idan tana buƙatar wani abuma gidan su Khalil take tafiya, gidan yayar mahaifiyarata kenan.

Ramadan kam Asibiti ya kai mahaifiyarsu, ya kira Iman dake makaranta suka zauna a gurinta dan kula da ita, dan ta samu shock ne a wannan lokacin.

Bulama kuwa bayan tafiyar Ramlah ya bita har gida, yana zuwa lokacin Hajiya Halima ta dawo da baƙincikin gidan Alhaji Haruna, yazo yana wani muzurai yace  "Ina Ramlah take?"

Hajiya Halima ta kalleshi tace  'ban sani na, azzalumi ma cuci burinka ya cika, gaba ɗaya yaran sun watse Bukar saboda muguntarka da rashin imani"

Bukar yace "saboda son zuciyarki dai, da son Abun duniya"

"Ni kake gayawa haka?"

"Na gayamiki ɗin, ai ba ƙarya nayi miki ba, mugun son Abun duniyarkine ya janyo miki da kwaɗayi"

"Lallai Bulama ka cika butulu azzalumi, to wallahi zan taka bakin faranti komai ya watse"

"kar Allah yasa ki fasa takawar, kije kiyi duk abunda zakiyi, ai idan ta tashi watsewa tare zata watse mana, kuma ki sani idona idon Ramlah sena saka an kashe ta"

"ka daÉ—e baka sa an kasheta ba, kayi maza karka fasa"

Ramlah ta fito daga sashensu tana tauna cingan, kallo ɗaya za kamata kasan 'yar wisi ce, ta kalli Bulama tace  "kai ka isa kasa a kasheni, ai base kunyi barazanar taka bakim faranti ba, kuji da abunda ke tunakaroku, Asirinku na daf da tonuwa a kotu, a nan yakamata ku maida kai mussman ma kai, ba wai zaka kasheni ba, dan ni na diha na kasheka da ranka tuni"
Ta ƙarasa maganar tana ɗura ruwan roba a cikinta, ta juya ta wuce dining dan cin Abinci, Hajiya Halima ji take tamkar tayi hauka, komai ya dagule mata, ta rasa meke mata daɗi.
Bulama ya fita da sacacciyar gwiwa jiki ba ƙwari, yanzu duk wannan barazanar da kwarinin dayake ana tsoronsa duk babu.

Tunda Ramadan ya ɗau mahaifiyarsa daga gidan basu sake komawa ba, har Allah yasa ta farfaɗo, aka ɗibi jininta aka gwada amma ba'aga ƙwayar cutar ba, akace bayan watanni uku zasu dawo sake yi, se kuka take tana tunanin wans irin lamarine wannan, ɗa ya nemi mace ta bashi kanta, kuma ta koma tabi mahaifinsa saboda Taɓarɓarewar ƙarshen zamani.

Daga Asibiti kai tsaye, Adamawa Ramadan ya tafi da Mummyn, saboda can ne ainihin garinsu.

Bulama yaje Asibiti aka É—ibi jininsa, da niyyar yasan a wani mataki yake, yana da cutar ko babu? Amma yakasa tsayawa a gaya masa sakamakon saboda fargaba ya gudu.

Haka abubuwa suka cigaba da damalmalewa azzalumai, basu fargaba lokacin komawa kotu yayi, ga kawunansu a rarrabe, kowa yana kallon kowa a banza, ga yadda suka dinga zaluntar  junansu.

Yau kuma Barrister Hafiz ne ya fito ya gabatar da kansa, tunda Bulama ya ga Barrister Hafiz cikinsa ya É—uri ruwa ya zuba ido yaga meze faru.

Barrister Hafiz ya fito ya gabatar da kansa, yace  "Sunana Barrister Hafiz, lawyer me zaman kansa, ina ɗaya daga cikin lawyoyi gidan Alhaji Nasir Daula, kuma ina ɗaya daga cikin lawyoyin da zasu bawa wanda ake ƙara kariya, kimanin shekaru goma sha biyu baya, tun bayan da ayyana cewar kaso bakwai na dukiyarsa akwai me ita, yasa aka dinga bibiyarsa da 'yarsa akan lallai a karɓi wannan dukiya, har kawo ga kashe matarsa da akayi, wanda ba' a ƙarabi ta kan case ɗinba tsawon shekaru, a tare dani akwai shedu da hujjoji da zasu tabattarwa da kotu wanda ake ƙara bashi da hannu gurin yin garkuwa da 'yar gidan Alhaji Nasir Daula, ko kuma shi Daula kansa "

Ya ƙarasa inda Yusuf yake tsaye, ya kalli Yusuf yace " Malam Yusuf, ko zaka iya gayamana yadda akayi ka fara aiki a gidan Alhaji Nasir Daula? "

Yusuf ya ɗanyi shiru yana kallon Barrister Hafiz, Barrister Hafiz ya jinjina masa kai alamar ƙwarin gwiwa.

Yusuf yace  "Abokin aikina Abbas, shine yazo ya sameni da maganar ga aikin da ake so inyi, shugabanmu yace a bani umarnin yin wannan bincike, da farko naƙi amsawa, daga baya naga tunda aikinane bazan iya cewa a'a ba, tunda ni na ɗau alƙawarin aiki, Abbas shine ya kaini gidan Alhaji Nasir Daula da kansa, yana zuwar musu gidan a matsayin Sani me yankan farce, kuma yana mutunci dame gadin gidan "

" waye me gadin gidan? " cewar Barrister Hafiz.

Yusuf yace " Isa ne"

"muje kotu na saurarenka"

"Bayan an kaini gurin 'yar gidan Daula, tace min sena saka hannu akan wata takadda kafin in fara aiki da ita, na karɓa na saka, tace min saka hannun da nayi tamkar na saka hannu a contract ɗin mutuwana ne, da farko naji tsoro se ban nuna ba saboda tunda aiki najeyi, bazan janye ba saboda abunda ta faɗa "

Barrister Hafiz ya jinjina kai yace " ko Isa megadi yana gurin nan? "

Isa megadi ya miƙe, aka masa umarni daya fito, ai kuwa ya fito yazo ya tsaya.

Barrister ya kalle shi yace " me zaki iya cewa akan abunda Yusuf ya faÉ—a "

Isa megadi yace" tabbas lokacin da ake neman direban da ze dinga jan 'yar Alhaji Daula a mota, Sani me yankan farce, wanda se da aka fara shari'a naji sunansa Abbas kuma ɗan sandane, shine ya kawo Yusuf gidan nan, kuma daya kawo shi me gidan yana matuƙar ƙaunarsa saboda haƙurinsa, kuma duk rashin yaddarta ita uwarɗakin nasa tana yadda dashi sosai"

Barrister Hafiz yace  "Isa megadi zaka iya komawa"

Kafin Barrister Hafiz ya kuma gabatar da sheda, Barrister Sadik yace yana da tambayoyin da zewa Yusuf, Alƙali ya bashi dama, yaje gaban Yusuf ya tsaya yace  "Kamar yadda ka bayyanawa kotu cewa, 'yar gidan Nasir Daula tace maka aiki da ita tamkar signing ne akan contract ɗin mutuwarka, meyasa ka amince kayi aiki da ita, ko duk cikin shirinka ne na saceta"?

"Objection ya megirma me shari'a, Barrister yana ƙoƙarin saka wanda ake zargi yayi confessing ne ko kuma tambayarsa yake?"

Alƙali ya buga guduma yace "Order, Barrister Sadik cigaba da tambayoyinka"

Yusuf yace "Ni É—an sanda ne, kuma dama rayuwar É—an sanda na tsakanin rayuwa da mutuwane dan kare rayuwa da dukiyar wasu, shiyasa ban razana na janye ba, saboda aiki nake"

Barrister Sadik yace "kace bincike kaje yi gidan Alhaji Nasir da kuma bawa 'yarsa kariya, wane irin bincike?"

"Kamar yadda Barrister ya faÉ—a É—azu, ana kai musu farmaki, saboda dukiyar da yace batasa bace, an bani aikinne dan gano suwaye da kuma bawa Widad kariya"

Barrister Sadik yaga idan ya cigaba da tambayoyin nan, tabbas Yusuf ze ɓallo ruwa, dan haka ya koma ya zauna.

Barrister Khalil ne ya shigo cikin kotun da hanzari, fuskarsa babu annuri idonsa jajawur, ya tsaya yace  "ina me neman afuwar kotu, na gaza halartar kotu da wuri, hakan ya biyo bayan neman wata sheda da bata zo hannunmu akan lokaci ba, sunana Barrister Ibrahim Khalil, lawyer me zaman kansa ina cikin tawagar lawyoyi dake bawa wanda ake tuhuma kariya, idan kotu ta bani dama, zan fara gabatar da shedu da hujjoji, amma kafin nan ina son yiwa wanda ake ƙara tambayoyi"

Aka bawa Khalil dama, Khalil yaje gaban Yusuf ya kalleshi, dukda Yusuf a wahale yake amma hakan be hana Khalil ganin kyau da Yusuf yake dashi ba, yace  "Malam Yusuf, kamar yadda kayi iƙrarin bincike kaje yi gidan Alhaji Nasir Daula, kotu zata so ta san wane sakamako ka samu na binciken? Sannan ina kudin binciken da kayi?"

Yusuf ya ɗaga ido yai ido huɗu da Hajiya Halima, ya kalli inda Bulama ke zaune, ya ɗauke kai yace "An karɓi kundin binciken, lokacin da aka kamoni ina hannun 'yan sanda, sannan a bincikema na farko, akwai yunƙuri da akayi na sace' yar gidan Daula, a gidan wani tsohon ɗan majalisa da taje taya 'yarsa murnar zagayowar haihuwarta"
Chapter 109 · 0% Book details