← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 127

Sashe 33

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yazo ze É—auki kayan shimfiÉ—arsa, yaji ta kira sunansa "Yoseef"

Ya amsa da "Na'am"

Widad ta tashi zaune tace  "meyafaru ne?"

"Me kika gani?"

"Naga kamar kana da damuwa ne, wani abu yana damunka"

Murmushi yayi yace  "bakomai, yi kwanciyarki kawai"

"Yoseef" ta kuma kiran sunansa

Ya sake amsa mata kamar É—azu.

"Dan Allah ka gayamin abunda yake damunka, zaka sani a damuwa fa"

Yaji daɗi a ransa, da yaga ta damu da damuwarsa, "kece kike ganin wani abu yana damuna, ni lafiya ƙalau nake"

Harya juya ze tafi inda yake kwanciya, yaji ta riƙe rigarsa, tsayawa yayi ya juyo yaga ta zuba masa ido.

Zama yayi akan katifar yace  "ya akayi kuma?"

"Yoseef, ba yau nafara ganinka ba, ina gane fushinka ko damuwa, just recently kake walawala, suddenly kuma mood É—inka ya canza, me nayi maka?"

"Ni ba abunda kikamin banda bani joy da happiness i ever expected to get"

Yai maganar yana jan hancinta, "kana son ka koma gida ko? Nima na damu mu koma dukda ina jin daÉ—in zaman gurin yanzu, amma ina kewar Daddy sosai"

Gyara zamansa yayi yace  "Dole ne muyi kewar iyayenmu da masoya Widad, kasancewar ƙaddararki na kamanceceniya da tawa, sedai sun sha banban, Akwai dalilin da yasa Allah ya haɗamu a nan, se mucigaba da haƙuri muga hukuncin da Allah zeyi, amma ni ba abunda kika yi min kinji masoyiyya, ni farinciki kika bani ma, wanda baze taɓa gogewa a zuciyata ba, I love you so much Baby "

Yai maganar yana rungumeta, ba tace komai ba se murmushi da tayi, Yusuf yana daga cikin mutanen da bazata manta dasu ba a rayuwarta, dan Ya canza mata gurɓataccen tunaninta, yayi sadaukarwar da bata taɓa tunanin wani zeyi akanta ba, yana haƙuri da dukkan halinta me kyau ko akasin haka.

Ya nisa yace  "bari in baki guri ki kwanta, nasan lokacin baccinki yayi"

Dukda a cikin duhu ne, amma ta niƙe kafaɗa tace  "mu kwana anan tare mana"

Murmushi yayi yai ƙasa da muryarsa dai dai kunnenta yace  "haka kawai inje wani abu yafaru, kiyi ta haɗemin rai kina hararata, yanzu ma ban san yadda akayi ba naga an ƙyaleni, dukda haka ban fidda ran da safe inga an ɗauremin fuska ba"

"Kai kuma abunda ke ranka kenan, nidai mu kwana tare kawai"

Yusuf ya gyara kwanciyarsa yace  "as you wish your majesty, ni dama haka nakeso, saboda hakan yana ƙara danƙon soyayya a tsakanin ma'aurata"

Bata kula shi ba, sedai sake shigewa da tayi jikinsa sosai tana lumshe ido.

Yusuf yace "Babyna, baki ƙarasamun labarin nan bafa"

"shhh, lokacin bacci yayi kayi bacci kawai, bana son in ƙara maka damuwa"

"wai waye yace miki ina cikin damuwa ne?"

"Hmm Yoseef kenan, tunda kaƙi yadda ai shikenan"

Haka suka wanzu a haka, bacci ya ɗauke Widad yayin da Yusuf ya kasa samun nutsuwa, yana sake ji a jikinsa akwai wani abu mara daɗi dake  faruwa a wani guri, wanda hakan ya shafeshi ko kuma ya shafi Widad.

LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏

74_75

Yadda Uman Yusuf taga rana haka taga dare, gaba ɗaya ta rasa wanda zata kira ta gayawa halin da take ciki, unguwarsu kuwa tuni labari ya cikata, akan ga abunda Yusuf ya aikata, beji ba be gani ba an ɗaura masa mugun sharri, wasu suna ƙaryene, wasu suna ba'a shedar mutum.

Mata suka dinga shiga da nufin suyi mata jaje, hadda wanda tun ɓatan Yusuf basu yi mata jaje ba, se yanzu da wannan labarin ya fasu.

Saleh ne a office ɗin Suleiman, ya kai gwauro ya kai mari, ya kalli Suleiman yace "ni gaba ɗaya kaina ya rufe ruf, na rasa me yakamata inyi, gaba ɗaya mutanen nan sun shammaceni, banyi zaton ta nan zasu ɓullo ba, duk yadda nake tunanin zaluncinsu sun wuce nan, na rasa mema zanyi ko me zance"

Suleiman dake zaune akan kujera yai shiru, ya nisa ya ɗago daga jinginar da yayi yace  "ni kaina bansan me zan iyayi ba, naje na samu Sp amma yaƙi saurarata, wai sakamakon da aka bashi shiya sanar, nabi duk nayi ƙoƙarin da zan iya, na tuntuɓi masu ruwa da tsaki akan abun, amma kowa ya nunamin ba ruwansa, ma'aikatan gidan nan gaba ɗaya hankalin mu a tashe yake, kuma nasan muddin mukayi wani yunƙuri, to muma baza'a barmu ba, zasu ɗau mataki akanmu ne, amma yanzu meye abunyi? "

Saleh yace " Abunyi be wuce inje in ƙara tabattar da na toshe duk wata kafa, wadda zata sa a gane inda suke ba, sannan in ja masa kunne da wannan uwar taurin kan yarinyar, akan duk tsanani karsu sake su bar gurin nan, idan har bani ne naje nace su baro gurin ba"

Suleiman yace "gaskiya, ka gaggauta zuwa ka same su kam, sannan ni gaba ɗaya kunyar mahaifiyar Yusuf nake ji, ban san me zance mata akan wannan al'amarin ba, ni nake bata ƙwarin gwiwa akan ɓatan nan nasa, akazo kazo da labarin sun kuɓuta, amma still hankakinta a tashe yake, ban san ya zata yi ba idan ta samu wannan Mummunan labarin "

Saleh yace " dole zata damu sosai, Amma haka nan za'ayi ƙoƙari a kwantar mata da hankali, dan barinta haka babu me rareshinta shima wata babbar matsala ne"

Suleiman yace  "hakane, ubangiji Allah ya shiga lamarin bayinsa, bari in tashi insha Allah zanje in gaisheta, a sake bata haƙuri da kwantar mata da hankali"

Daren Yau kusan kwana su Alhaji Haruna sukayi suna meeting, sunyi farincikin da jin mafitar da Bukar ya samo musu, dan ba suyi zaton irin wannan mafitar ze kawo musu ba, dan haka yanzu kallo ze koma ga sauraren  'yan sanda aga ta inda zasu fara kamo Yusuf.

Alhaji Musa yace  "yanzu idan aka gano su, yaya zamuyi da wannan shu' umar yarinyar me jarababben taurin kan bala'i"

Alhaji Munir yace  "kai dai bari, yau shekaru kusan goma muna bibiyar abun nan, amma 'yar masu baƙin halin yarinyar nan ta hana, ba abun mu kashe ta ba kuma muzo muyi biyu babu"

Alhaji Haruna yace  "idan muka kashe ta ai kuma zamu tashi a tutar babu ne gaba ɗaya, ya zamana duk wannan wahalar ta tashi a banza, ai yadda naji Bukar yace, shi wannan ɗan sandan yaron da an kamosu shi zamu fara kawarwa, saboda Kasancewar sa tare da ita matsala ne a gare mu, idan aka kauda shi, itakuma tunda babu wanda yasan inda ubanta yake, zamuyi poisoning ɗinta ne, a fita da ita waje neman lafiya, idan yaso kodai ta faɗi inda suke kokuma a aikata"

Alhaji Munir yace  "Amma fa kun san rashin sanin inda Daula yake, itama wata babbar barazana ce me zaman kanta, muna ruwa fa idan Daula ya bayyana bamu samu abun nan ba, yakamata ace mun san inda yake a hallaka shi tunda wuri"

Alhaji Musa yace  "Ai ana nan kan bincike, an duƙufa sosai gurin gano inda yake, kuma akwai alamun nasara, sannan idan aka gano shi kasheshi kawai za'ayi, karma a ɓata lokaci, tunda dama an bada sanarwar duk wannan yaron shine yayi garkuwa dasu"

Alhaji Haruna yace "nifa a gurin nan kamar anyi wauta, in ba hakaba ta yaya za'ace waishi ne ya sace Daula, duk tsaron dake Asibitin nan"

Alhaji Musa yace  "nima da nayi wannan tunanin, amma Bukar yace ya san abunda yasa yayi hakan, ni wai ya maganar wannan yaron da muka yi magana, Barrister Hafiz, har yanzu bece mana komai game da abunda suka yanke ba"

Alhaji Munir yace  "Aishine, yau kusan sati biyu amma babu wani feedback, idan ba zasuyi ba kawai muje mu haɗo kai da banki, mu kunno wata wutar"

Alhaji Haruna yace "kamar yaya kenan?"

"Ahh ayi takkaddun boge mana, ace ana bin kasuwancinsa wasu mahaukatan kuÉ—i mana, idan yaso se muyi agreement da bankin, mu basu wani percentage"

Alhaji Musa yace  "amma fa kasan Daula baya cin bashin banki?"

Munir yace "Nida kai muka san wannan, sauran mutane basu sani ba, dan haka muyi tunani akai, idan can baze samu ba se mubi nan, kasan na san Ambassador Auwal Inuwa, kuma kunsan suna da banki, komai zezo da sauƙi"

Haka suka cigaba da ƙulla tsiyatakunsu, kala kala babu ko tsoron Allah a ransu.

Nurat a wuni ɗaya amma gaba ɗaya ta zube ta rame saboda zunzurutun damuwa da tunani, tana tunanin irin hukuncin da za'ayiwa Yusuf idan har aka gabatar da shi a gaban kotu, tana tunanin wannan zalunci ace an sace mutum, kuma a koma da baya a ɗora masa laifin da hukuncunsa daze iya sanadiyyar ɓata feature ɗinsa, tunani ta shiga yi, me za tayi wanda zesa ta samu abunda zata taimaki Yusuf dashi idan buƙatar hakan ta taso?

Ta ɗakko wayarta ta kira Anwar, sedai wayarsa bata shiga sam, ta kuma jarraba layin Khalil amma shima se ace mata busy, ƙarshe dai se haƙura tayi ta ajiye wayar ta maida kai ta kwanta.

Yanzu ɗaliban Widad in sunzo, suke mata wanke wanke da shara, dukda ta nuna bata so amma sesu dage se sunyi, suna matuƙar sonta, dukda bata da fuska amma tana jansu a jiki tana koya musu abubuwa da dama.

Yau Habi ce ta taho mata da soyayyiyar gyɗa me ɓawo, kusan kwano guda tace babarta ce ta kawo mata, Widad tace  "Aini dan Allah nake koyar daku, ba dan ku bani wani abuba, ina dai roƙonku ku dingamin addu'a, amma ni base kun biyani ba, kuma duk wanda yake sha'awar koyar wani abu, ko abunda nake koya muku ƙofata a buɗe yake yazo ya koya"
Chapter 33 · 0% Book details