Sashe 47
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙura masa ido tayi tana kallonsa, sam Yusuf bashi da makusa gashi da ƙira me kyau, gashi shikansa me kyau ne, ga kuma uwa uba zuciya me kyau.
Tasowa tayi tazo inda yake ta zauna, ta kwanta a jikinsa hannunta kuma tana shafa gadon bayansa.
Yace "Kin tashi kenan? Fatan kin tashi lafiya?"
Maimakon tayi magana sema wani sake lafewa da tayi a jikinsa, tana sake shafa bayansa.
Yusuf yayi murmushi ya cigaba da abunda yake, can yace "in kin gama shafanin seki É—agani zanci Abinci, tunda naga kamar ke bakya jin yunwa"
Yanzunma shirun ta kuma yi, ta cigaba da abunda take, janyota yayi gaba ɗaya ya ɗorata akan cinyarsa, yana ƙaremata kallo yace "ƙalau kuwa? Ko yau da son jiki kika farkane?"
Murmushi tayi masa, ta kwanta sosai a jikin nasa, tana ƙare masa kallo tun daga fuskarsa har ƙirjinsa, ta kai hannu tana wasa da gashin nasa.
Buge hannunta yayi yace  "mara kunya nan kika gama cewa abun ƙyamane, amma indai kika gani sekin taɓa"
MurguÉ—a baki tayi tace "ai idan baka yi wasa ba, da fork zan maka shaving, duk in cire shi"
Yai dariya yace "Kin fasa tsigeshi É—aya bayan É—ayan?"
"Duk wanda ya samu zanyi ai"
Yai murmushi yana cigaba da cin Abincin sa, still kallon Yusuf take yadda yake komai a nutse, Yusuf yace "Malama karfa ki cijeni"
Bata san lokacin da dariya ta ƙwace mata ba, tace "aikuwa dan kasan na saba ba, da an takurani idan naga bani da mafita, se cizo kuma haƙorana dafi garesu, duk abunda na kama sena fasa shi, shiyasa Fahad ɗin Bulama yake cemin Mayya, tunda na huda shi da haƙorana"
Jiki a sanyaye Yusuf yace "yanzu idan muka rabu, muka koma gida Fahad zaki aura ko?"
Da sauri tace "Allah ya kiyaye, wallahi ko maza sun ƙare bazan auri wannan ba, mashayin giyane fa, ga neman mata kai zaka so in Auri wannan?"
Yusuf ya girgiza mata kai, ya ɗan tsura mata ido yace  "I can't imagine my life without you Widad, ko mu koma idan zaki Auri wani bazan iya jurewa ba, ban san ya zanyi ba"
"waye yace maka zanyi Aureni? Ni ba zanyi Aure ba, bani Abincin nima inci, amma a baki zaka bani yau" tai maganar cike da son da basar da wancan zancen da suke yi.
Haka ya dinga bata Abincin tana karɓa, kamar 'yar yaye suka gama sannan yayi shirin fita, yau da kanta har soro ta raka shi, ta tsaya ta kalle shi tace "bana son ka fita Yoseef, kamar kazo mu koma ɗaki"
"Yau kuma? To idan ma dawo me zaki ban?"
"Kawai inta kallonka, kana bani nishaÉ—i, da jokes É—inka da halayenka masu kyau"
Yai murmushi yace "nima idan na fita, duk damuwa nake in dawo, saboda inzo inga abar sona, am missing you fa idan na fita".
Tace "nima haka, keep missing me harkaje ka dawo kaji"
Yusuf yace "yanzu abunda za'ayi shine, Yimin wani abu da in na fita har in dawo bazan manta ba"
Tace "kamar me kenan?"
Yusuf yace "just kiss me here 'yai maganar yana nuna mata kumatunsa na dama.
Ganin tsakar gidan ba kowa yasa Widad, ta rungume Yusuf ta fara kissing É—insa a baki, he was so much surprise da abunda Widad É—in tayi, dan haka yasa hannu biyu ya rungumeta yana murmushi.
Hari ta bankaɗo labule zata fito daga ɗaki, hannunta da kofin da' aka karya, kawai tai gamo da Yusuf da Widad a bakin zaure, Yusuf ya bawa Hari baya dan haka be ganta ba sam, Widad kuwa ta ganta, amma tana sane ta basar ta ƙara maƙalƙale Yusuf ta cigaba da abunda take.
Da gudu Hari ta koma ɗaki, ta bankaɗo labule ta rufo ƙofa, Widad ta zame bakinta ta hau dariya, Yusuf yace "ya dai?"
Tace "bakomai, muje hanyar waje in raka ka"
Yusuf yace "rana me matuƙar tarihi a gurina, ba iya yau zan cigaba da tunanin ki ba har abada zanyi tunanin ki My Queen"
Murmushinta me ƙayatarwa ta cigaba dayi masa, da sukaje soronma soyayyarsu suka cigaba dayi, dukda Yusuf ne kawai ke furta mata yadda yake sonta, Widad kam ta kasa ce masa uffan.
Ya riƙo ƙugunta yana kallon ƙwayar idonta, Widad tace "Idan ma makara baka fita da wuri baf ba ruwana"
"Aiko ke kike da ruwa, dan ke kika hanani fita, ɗan ƙara min kiss ɗin mana kona 10 seconda ne"
Tureshi ta shiga yi tana dariya, tim suka ji an saki kwano, Hanne ta taho da fantekarta cike da Albasa, tayi karo dasu Yusuf, take taji ganinta ya É—auke ta saki fantekar albasar, Yusuf yace "Subhanallah garin yaya kika zubar? '
Yai maganar yana sakin Widad, ya yunƙura da nufin ya durƙusa ya tayata tsince albasar, amma Widad ta riƙe shi ta tsatstsare shi da ido tace " meye naka a ciki? Ko kai ka zubar mata? "
Yusuf yace "A' a amma kinga mu muka tsoratata ta zubar da albasar, yakamata a tayata kwashewa"
Wani mugun kallo tayi wa Yusuf, taja tsaki ta koma cikin gida, Yusuf ya durƙusa ya taya Hanne suka tsince Albasar, yace "ki dinga kula sosai, ki dena yawan tsorata kinji?"
Hanne ta jinjina kai tace "to nagode"
Ta É—au fantekarta tai waje, tana kuka tana tunanin me zata yiwa Widad yadda zata É—an É—ana mata taji abunda take ji.
Alhaji Musane yace "Nifa gaba ɗaya na fara gajiya da wannan wahalar, daga wannan se wannan abu sekace jaraba? Abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, shi ya ɓace ɓat kamar kuɗi an neme shi an rasa, shima wannan ɓangaren yarinyar har yanzu babu wanda ya ganosu, suma lawyoyin nasa sun kawowa mutane wasu surutansu na banza "
Alhaji Haruna yace "haba Alhaji Musa, ni ban taɓa ganin ka karaya ba akan abu se yau, duk abunda aka fiye shan wuya akansa za'a samu ne, yanzu mafita yakamata mu nema amma dole mu kassara Daula, mu kassara wannan dukiyar dayake taƙama da ita"
Alhaji Musa yace "to meye mafitar, nagaji wallahi haba, ni zuwa zanyi in maida hankali akan harkar takarata kawai"
Alhaji Munir yace "kaga dan Allah Kadena mana zancen wata takara please, zancen takararka kai kaÉ—ai ta shafa, mu muyi abunda ya dame mu kawai, Alhaji Haruna meye mafita"
"na saka a duba mana, wanda ze iya kwafar mana saka hannun Daula, sannan kafin a samu me saka hannun ayi fafutuka a bincika mana bankin nan, shima mu gwada muji ta ina zamu dace"
Alhaji Musa yace "to ai shikenan, Allah yasa mu dace, amma ni na fara gajiya wallahi, gashi shima wancan banzan yaron har yanzu ba'a gano shi ba, nifa sonake a kamashi kafin su shigo garin nan"
Haruna yace "karka damu, ai matakan da muka saka baze tsallake tarkonmu ba, ka kwantar da hankalinka komai ze tafi dai dai"
Alhaji Musa yace "shikenan Allah yasa hakan, ynzu a duba mana me iya kwafar signing É—in nan"
Gidan Alhaji Daula kuwa, Hajiya Halima se shagalinsu suke da dukiya suna facaka, A ɓoye Ramlah take satar wasu abubuwan ba tare da mahaifiyarta ta sani ba ta kaiwa Fahad ya sayar ya kawo mata abunda yaga dama, sannan kuma su raba abunda ya kawo mata ɗin, Amal kam gaba ɗaya a cikin damuwa taje, dukda irin romon bakan da Mahaifiyar su take mata, akan cewar ai bakomai dan an kama Yusuf, amma hankalinta yaƙi kwanciya, sam bata da nutsuwa sosai take jin Yusuf a ranta, take tausayin halin da ze shiga idan aka kamashi da laifin ya sace Widad.
Anwar kam kasuwarsa ya koma zuwa, sam baya zaman gidan nan saboda irin takaicin da yake ƙunsa a cikin gidan, a kan idonsa yana ji yana gani haka Fahad yake zuwa ya ɗauki Ramlah a mota su fita, kuma mahaifiyarsu na gani bazata ce komai ba, shikansa ya fara lura da sauyin ɗabi'a na Ramlah, ya fara zargin ko ta fara shaye shayey, amma yasan da yayi magana mahaifiyarsu zata ƙarhata shi ƙarshe ma su ƙareta babu daɗi dan haka ya zuba musu ido.
Ma'aikatan gidan kuwa, su Isa se yanzu suka gane zaman Widad a gidan nan Rahama ne a garesu, saboda tsagwaron wulaƙanci da cin mutunci da suke fuskanta daga gurin Hajiya Halima da 'ya' yanta, zagi da cin zarafi gami da wulaƙanci ba irin wanda ba'a musu, Albashinsu kuma duk Hajiya Halima tabi zaftare musu, shima se sufi wata ba'a basu ba, zaman haƙuri kawai sukeyi a gidan nan, duk inda suka zauna banda tsinewa Hajiya Halima da 'ya' yanta babu abunda sukeyi, suna shiwa Widad da Alhaji Nasir Albarka, saboda kaɓakin arzikin da suke basu shida 'yarsa se yanzu suke ganin duk izzar Widad a cikin gata suke, dan gashi a yanzu an maidasu kamar bayi a gidan haka suke zaune.
Saleh ma yana ji yana gani, a gidan gonar nan haka Hajiya Halima ke zuwa ta ɗau abunda takeso ta fito dashi daga gidan ta siyar, ba yadda ya iya dan idan ya zaƙe su Alhaji Musa zasu iya gano shi, balli ya tashi dan haka se dai ya zura ido.
Hanne bayan ta dawo daga kai albasarta kuwa, ɓangaren Jamila ta wuce taje tayi jifa da fantekar albasar, Jamila tace "ke lafiya kuwa, ke da yayanki yana nan kikazo kika mana jifa da kwanon nan da yaci ƙaniyarki ai"
Hanne tayi tsaki tace "wallahi Jamila na tsani wannan koÉ—aÉ—iyyar bayahudiyar, na rasa me zan mata in huce"
Jamila tace "wace bayahudiyar?"
"wannan farar banzar ta gidanmu mana"
Jamila tace "dama ba musulma bace?"
"Musulma ce mana, sedai shegiya ce, bata da mutunci"
Jamila tace "wai meye tsakanin kune? Me tayi miki haka kuke takun saƙa"
"Wai ba damar magana ta haÉ—ani da mijin ta, seta hau gayan magana, kokuma seta ganni se ta hau wani rungumeshi"
Jamila tace "ikon Allah, toke meye naki a ciki, ba mijin ta bane ba?"
"to dan mijin ta ne seta dinga min haka? Naga dai namiji na maya huÉ—une, shikenan kuma baza'a kula shi ba?"