← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 127

Sashe 114

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kalli Nura tace ya kawo mata ruwa, ya kawo ruwa aka dinga shafawa Amal ɗin, can taja ajiyar zuciya ta buɗe ido, Ramlah tace  "Amal meyasa zaki yunƙurin kashe kanki? Komai yai zafi maganinsa Allah"

Cikin kuka Amal tace   "Mummy, Mummy na, Yaya Anwar, dan a kainin inga Mummy i love hery, she's my Mum, dan Allah kice ayi haƙuri bazata sake ba, ina son in ganta"

Ramlah ta rungumeta tana rarrashinta, tace  "kiyi haƙy, za'a kaiki ki ganta insha Allah, amma karki ƙara yunƙurin kashe kanki, kinji ko?"

Amal ta jinjina mata, ta kama hannunta zuwa cikin gidan, yayin da masu aikknysuka shiga gulmarsu.

Gabaɗaya walwalar Yusuf ta ɗauke, ko Abinci baya iya ci, idan ya kwanta tunanin Widad kawai yake yi, yana son ya ganta sosai, Amma Umma taƙi.

Ya zauna yai shiru a tsakar gida, Umma ta fito da gyalenta a hannu tace  "Yusuf bari zan ɗan shiga kasuwa, ba daɗeaayzan ba yanzu zan dawo"

Yusuf yace "to A dawo lafiya"

Tace  "Allah yasa" ta sa kai ta fice.

Widad tana zaune ta tasa 'ya' yan itatuwa a gabanta, ta kasa ci ta zuba musu ido, tana kallonsu kamar ranar ta fara ganinsu, kamar an tsunkuleta ta tashi da hanzari, tai waje ta samu É—aya daga 'yan sanda dake bata tsaro, ta tambayeshi ina wannan É—an sandan da suka fita tare, yace mata "Ai ya tafi aikin da kika sashi ranki ya daÉ—e"

Tace "maza kiramin shi a waya"

Ba musu, ya kira shi a waya, aikuwa ya ɗaga ya miƙa mata wayar, Widad tace  "ka gano min gidan nasu?"

Yace "eh na gano, naje na tambayi abokan aikina da suka kaishi Asibiti"

"a cikin ƙasa da mintuna uku, ka hanzarta ka turomin Adress ɗin"

Yace an gama ranki ya daɗe, aikuwa ya tura mata, ta karɓa ta duba ta shiga cikin gidan da sauri, taje ta shirya tsaf ta fito, bata sairari kowa ba, ta buɗe wata mota ta shiga, 'yan sandan suka taho kanta suna tambayar ina zata?

Babu wanda ta saurara a cikin su, ta fafari motar tana wani irin mahaukacin horn, wanda ya tilastawa masu gadin buɗe mata, saboda gudun ɓacin ranta, tai waje da motar a guje.

Nan da nan' yan sandan suka É—au mota suka rufa mata baya.

Yusuf yana nan zaune, ya gaji da zaman tsakar gidan, ya tashi ya koma ɗaki, Sallama yaji a tsakar gida, ya amsa Sallamar daga ɗaki yace  "Umman bata nan"

Me Sallamar tace  "dan Allah zan sha ruwa"

Haushine ya kama Yusuf, shi ga abunda ya dameshi amma baƙuwa zata addabeshi, ya fito ransa a ɓace kawai yaci karo da Nurat, tai masa murmushi, gaba ɗaya ya ɗan ruɗe yace "dama kece?"

Nurat tace  "Nice ko in koma ne?"

"Ni na isa ince ki koma, É—azu Umma ta fita nasan zuwa yanzu tana hanya, shigo bismillah"

Nurat tace  "Yaya Khalil yana waje, tare muka zo"

Yace "bari inje mu gaisa da shi"

Yusuf ya bata gurin zama a falo, shikuma ya fita waje, yana fita suka gaisa da Khalil, Yusuf yace "shigo daga ciki mana, ka tsaya a waje"

Khalil yace   "A'a bazan shiga ba, Naga ta gaji da zaman kaɗaicine damuwa tana damunta, nace bari mu fito tazo ta dubaka ta gaida Umman kota samu relief"

Jiki a sanyaye Yusuf yace  "Barrister ina matuƙar jin tausayin Nurat, ga kunyarta nakeji gani nake duk nine sanadin shigarta matsala"

"ka dena faɗar haka Yusuf, ai duk mumini dole ze yadda da ƙaddara me kyau ko mara kyau"

Yusuf yace "hakane, shigo mana"

Khalil yace  "zan shigo, bari inje in ga abokina a nan ƙasan layin ku"

Yusuf yace "to shikenan" ya koma cikin gidan.

Nurat tana zaune a guri É—aya, tai shiru Yusuf ya shigo ta É—aga kai ta kalle shi tana wannan murmushin nata daya zama nature É—inta.

Yusuf mabya mayar mata da murmushin, yaje ya É—akko mata ruwa a fridge da lemo ya kawo mata, yace " Sannu da zuwa light, ga ruwa Kisha umma tana daf da shigowa"

Shiru tai tana sunkuyar da kai yace  "ikon Allah, kunyata kuma kike ji? Ko kuma ba kya shan irin wannan?"

Ta girgiza kai tace  "ni kowanne ina sha"

"Na gidanmu ne bazaki sha ba kenan"

Ta girgiza masa kai tana murmushi yace  "idan Umma ta dawo kuwa sekin sha, Umma ba'a zuwa gidanta a ƙi karɓar abunda ta bawa mutum"

Ita dai sedai murmushin, amma ta kasa cewa komai.

Can Yusuf yace  "light, wai nikam dan Allah ya akayi kika san da abunda na ajiye a wayarki?"

Cikin sanyin muryarta tace "ai ka taɓa cemin kayi ajiya a wayata, amma baka gayamin meye ba, lokacin da aka kama ka sena gayawa brother, harda ajiyar da kace kayi a wayar, shine yace in bashi wayar, ya dinga bincike a kai, daga nan ya kaiwa wani Abokinsa, ban san yadda akayi suka gano ba "

Yusuf yace " Aini bani da bakin da zan miki godiya Nurat, Allah jiƙan Mummy, Allah yasaka da alkhairi "

Tace " Ameen "

Can kuma tace " dan Allah dagaske kana da Aure? "

Yusuf yai murmushi yace " Waye ya gayamiki? "

" Kai ka taɓa gayamin, da na kiraka a waya, ka cemin kana tare da matarka "

Yusuf yace " A lokacin tsokanar ki nakeyi, bani da Aure amma a yanzu ina da Aure, Widad mata tace "

Ƙirjin Nurat ya buga da wani irin ƙarfi, take annurin fuskarta ya ɗauke gaba ɗaya.

Yusuf yace " ya dai? Ko kina sona ne, kamar kishi fa nake gani a fuskarki"

Ta ɗago manyan idanunta farare ƙal, ta sauke akan Yusuf, take taji ta karaya gaba ɗaya ƙwalla na neman cika mata ido.

"Yoseef!!!"

Yaji an kira sunansa, kuma babu me ambatar sunansa a haka idan ba gimbiyar Daula ba.

AMANA! AMANA! AMANACE!!!
LITTAFIN KUÆŠI NE.
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

156_157

Yusuf da Nurat duk suka ɗaga kai suna kallon inda Widad ke tsaye a bakin ƙofa, seda ƙirjin Yusuf ya buga da ƙarfi ganinta a tsaye, fuskarta babu Annuri sam, dan kwata kwata be taɓa zatan ganinta ba a wannan lokacin, ba Yusuf kawai ba hatta Nurat seda hanjin cikinta ya kaɗa, ta shiga fargaba saboda yadda Widad ɗin tai kicin kicin da rai.

Yusuf ya tattaro dukkan jarumtarsa, ya dake ya kauda fargabar dake zuciyarsa ya kalli Nurat yace  "Light, gaskiya ki sha ko ruwane kafin umma ta dawo, bazanji daɗi kizo gidanmu ki tafi baki ci komai ba"

Fargaba ce lulluɓe a fuskar Nurat, jikinta se tsuma yake kamar taga zakanya.

Yusuf ya ɗakko ruwan roba, ya buɗe ya zuba a cup ya miƙawa Nurat, amma Nurat ta kasa karɓa se kallon Widad kawai da take yi, Widad ɗin dake tsaye tana huci.

Nurat tace  "Amm.. Am naga kamar gurinka tazo bari in baku guri"

Yusuf yace "yi zaman ki kawai, idan wani abunne ya kawota ta faÉ—a a nan ina jinta"

Widad ta kalli Yusuf, taiwa Nurat wani mugun kallo, ai ba shiri Nurat ta miƙe, a ɗarare ta raɓa ta jikin Widad ta fice daga ɗakin, tana fargabar kar Widad ɗin tayi mata wani abun

Yusuf ya yunƙura daga kan kujerar da yake, ze bar mata ɗakin amma ta sha gabansa ta kalle shi tace  "Yoseef, Anya kamin adalci kuwa? Na cancanci haka daga gareka? Bani da kowa se Allah, ba uwa, ba uwa, ba dangi ba kowa kasan bani da kowa se Allah, se kuma kai da nake sa rai, amma kamin haka? Yoseef tunda Allah yasa ka kuɓuta baka nemi inda nake ba, ina ta faman wahala da rayuwata babu me temakona se Allah, bani da wani jigo da zan jingina dashi inji farinciki, kawai se inzo in ganka da wata, bayan kasan zuciyata bazata iya jure hakan ba"  tai maganar idonta taf ƙwalla.

Yusuf yace "ni bance ba kimin adalci ba seke zaki gayamin haka? Duk tarin wahalar dana sha saboda ke, amma kika kalli duniya kika bada shedar ƙarya a kaina Widad, baki tausayawa halin dana shiga ba, seni zakiwa kallon ban kyauta miki ba?"

"Yoseef, a tunanina ko kowa be fahimceni ba kai zaka fahimceni, na gaya maka komai, kasan komai game dani fiye da kowa, na baka dukkanin yarda wanda har hakan yasa na gaya maka waceceni, da abunda ya faru da rayuwata, kasan bazan taɓa yin haka dan in tozarta ka ba, dukda na ɓoye maka waye Bukar, ba nayi hakan ne dan komai ba se dan tseratar da rayuwarka, da kuɓutar da kai daga sharrinsu, na ɓoye maka Bukar shine Bulama saboda na bar hakan a zuciyata har ranar da zan kama shi red handed, sedai ƙaddara ta riga fata, amma shikenan tunda baka buƙata ta yanzu a rayuwarka, zan rungumi ƙaddara da irin rayuwar da Allah ya ƙaddara zanyi, amma kafin nan "

Ta saka hannu ta cire dogin hijjabin jikinta, wanda ya kasance har ƙasa, ta cire doguwar rigar abayar dake jikinta, ya rage daga ita se gajeran wando, da kuma half vest.

Tozalin da Yusuf yayi da cikin dake jikin Widad ne yasa shi ya É—an rikice, tabbas idonsa ba gizo yake masa ba, cikine a jikin Widad gashi nan yayi girma sosai ya fito.

Ta ƙaraso gabansa ta kama hannunsa, ta ɗora a kan cikin nata tace  "dan Allah Yoseef, koka watsar dani karka watsar da ɗanka, yau idan na mutu bashi da kowa se kai, dan Allah karka bari yayi irin rayuwar dani ko kai mukayi, Yoseef ka tausayamin ko dan ɗanka da nake ɗauke dashi.

Yusuf ya kalli Widad ya kalli cikin jikinta yace  "You are pregnant Widad"
Chapter 114 · 0% Book details