← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 127

Sashe 107

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf yace "banyi garkuwa da itaba, Alhaji Nasir ya nemi da inje gidan gonarsa in kwana, zan kai Widad Abuja dan ganin wani likitan Ƙwaƙwalwa, cikin dare aka turo masa saƙo a wayarsa, ina kwance ina bacci yazo tasoni nida Widad, ya nunamin saƙon yace maza maza in ɗau Widad mu bar gidan, na tsaya ina tambayarsa ina zamuje, yace maza maza in bar gidan da Widad, saboda saƙon da aka tura masa ana barazana ne ga kodai ya bada abunda akeso, ko kuma a hallaka 'yarsa, nace masa mu kira' yan sanda amma yace aa', in kula da Widad, na ɗauketa muka fita ba tare da nasan inda zamuba, munyi tafiya me nisa ga dare, kawai aka zagaye motarmu, da Widad kawai suka so su ɗauka, ta riƙeni tana kuka na hana su tafi da ita, shune suka haɗa dani, kwananmu biyar a hannunsu, Saleh ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan gonar Alhaji Nasir, yaje ya kuɓutar damu, an harbi Widad a hannu ya kaimu Asibiti, aka cire mata bullet, sannan ya bamu mafaka a wannan ƙauyen, ya cemin idan har muka dawo za'a hallaka Widad dani kaina, dan haka mu zauna zuwa lokacin da komai ze lafa, amma bani na sace ta ba"

Barrister Saminu ya mike yace  "meyasa baku shigar da ƙara ga hukumar 'yan sanda ba? Ka cigaba da zama da ita a inda babu wanda yasani tsawon lokaci?"

Yusuf zeyi magana Barrister Khalil yace  "zan gabatarwa da kotu, wata shedar wadda take nuna wanda ake zargi bashi da laifi a zaman kotu na gaba"

Nan kotu ta hargitse da Hayaniya, kowa yana tofa albarkacin bakinsa, Alƙali ya buga gudumarsa, akayi shiru, yai rubuce rubuce sannan yace

Duba da yadda lawyoyi suka gabatar da shedu da hujjoji, wannan kotu me albarka zata ɗage cigaban wannan sharia'r zuwa nan da sati biyu masu zuwa, dan yin zama na ƙarshe da yanke hukuncin daya dace akan wannan shari'a, sannan kotu tana umarni da hukumar 'yan sanda su binciki Alhaji Bulama da tawagarsa"

Kotu ta É—au hargowa da sowa, 'yan sanda suka tafi da Yusuf gidan yari, Umma ta kalli Suleiman tace " Suleiman ya haka? Naga za' a maida shi"

Suleiman yace "ki kwantar da hankalinki, kin san shari'a komai a hankali a binsa ki kwantar da hankalinki"

Suleiman yaita kwantar mata da hankali, yana bata baki.

Hajiya Halima ganin ba'a kama da ita ba, yasa ta silale tai gida, zuciyarta cike da fargaba da kuma tsoro, tana tunanin meye mafitarta ta ƙarshe? Tasan tunda Bulama yaje hannu itama tata ta ƙare, sedai tana zuwa gidan ta tarar da gate ɗin gidan hanhai a buɗe, ga motar 'yansanda, ga mutane sun cika gidan, kamar ta juya ta gudu, amma ta fasa ta ƙarasa, tana zuwa me zata gani, an rufe mutum da zani alamar ya mutu, Ramlah se uban kuka take, ga Amal a sume a gefe ana ta mata fifita, jiki na rawa ta ƙarasa gaban gawar, tasa hannu ta yaye zanin, Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!!!
Gawar Anwar ce É—anta, gawar se zubar da jini take, idonsa a rufe kamar me bacci, kamar kace tashi ya tashi a nutsensa yake, amma ya mutu.

Ta ɗora hannu a ka tana kurma ihu  "Wayyo Allah na shiga uku ni Halima, Bulama ka cuceni ka tarwatsa rayuwata, Allah ya isa tsakanina da kai Bulama, Bulama seda kasa aka kashemin Anwar? Nayi dana sanin saninka, da farko ka rabani da gidan uban Anwar, na Auri Shu'aibu shima ka kashemin Auren, ka haɗa kai da Shu'aibu kuka kashe matarsa ya sakeni dan Daula ya aureni, duk biyayyar da na maka, amma ka kashemin ɗana Me ƙaunata da gayamin gaskiya, wayyo Allah Anwar ɗina, wayyo Anwar ka tashi dan Allah, na shiga uku "

Tana wannan ihun, tana maganganun nan ana mata video, ita dai Ramlah kasa cewa komai tayi, se bin mahaifiyarsu da ido, ga Amal wadda babu tabaccin tana da rai itama, dan abun yazo mata akan gaɓa, dama ta gama galabaita babu jini a jikinta, kuma ga wannan mutuwar ta Anwar, ƙarseh wannan kururwar da Hajiya Halima keyi, se rufeta akayi a ɗaki akayiwa Anwar sutura.

Khalil kuwa yana ta rawar jiki yaje ya bawa Nurat labarin yadda shari'a ta kaya, akwai alamun nasara akan shari'ar Yusuf sedai yana zuwa gida ya tarar da fuskaokinsu wani iri, Nurat a zube a ƙasa ana ta fama numfashinta ya tsaya.

Khalil yace "lafiya kuwa?"

"Allah yayiwa mahaifiyar Nurat rasuwa, yanzun nan an tafi ɗakko gawarta daga Asibiti"  Anty Saddiƙa tai maganar tana kuka.

Khalil yace "la'ilahaillalah Muhammadu rasulillah salallahu alaihi wassalam, Antyna ta rasu kenan?wallahi Musane ya kasheta, shine ya kasheta"

Yai maganar yana zubar da hawaye.

Haka itama akayi mata sutura aka sallaceta, aka kaita makwancinta na gaskiya, Nurat kam tasha kuka kamar ranta ze fita, gaba É—aya ta birkice an kasa gane kanta ma gaba É—aya, se da aka samo likita yai mata alluarar bacci dan ta samu relief.

Amal kuwa har aka kai Anwar bata dawo hayyacinta ba, gawar Anwar ya tara mutane sosai kasancewarsa mutum ne na mutane, ga sauƙin kai da girmama jama'a.

Fahad ya kaɗu da jin labarin an kama mahaifinsa, da kuma harƙallar da suka ƙulla da shi da Hajiya Halima, suka dinga siyar da dukiyarsa ba bisa ƙa'ida ba, ga mutuwar Anwar data dake shi, ya kaɗu matuƙa da jin Anwar ya mutu, ya lallaɓa komtsan sa ya ɗau mota ya gudu.

Haka Bulama ya kasance a hannun 'yan sanda shima, Aka kama Alhaji Musa, shi laifuka biyuma aka kama shi dasu, ga laifin hankaÉ—o matarsa daga bene, gana wanda suka aikata da Bulama.

Tunda Amal ta farka ta farka ba a daidai ba, tunda ta buɗe idonta bata magana kwata kwata, sedai taita bin mutane da kallo, kamar bata sansu ba, Hajiya Halima kuwa kamar wadda ta shekara a daji, tai wujiga wujiga ko tayi shiru idan aka jima se surutai, taita tonawa kansu Asiri ita da su Bulama, itama ƙarshe ana cikin makoki 'yan sanda suka zo suka yi gaba da ita.

Nurat tana cikin tashin hankali, na rashin mahaifiyarta, ga kama mahaifinta anyi da wannan manya manyan laifuka haka, dukda tarin abunda yai mata na laifuka, amma ya haifeta, gaba ɗaya ta rame tai wani iri, ga labarin mutuwar Anwar ya risketa, mutuwar ta girgiza ta ƙwarai, ba zata manta halacci da kara irin na Anwar ba, Anwar mutum ne nagari me haƙuri da nagarta gaske.

Bulama a hannun Hukumar 'yasanda ɓangaren SWAT aka danƙasu, domin tuhumarsu, dama kuwa masu fushi da fushin wani, dan haka ba'a ragawa su Bulama ba sam, kamar yadda suke sawa a azabtar da wasu, haka suma suka shiga hannu aka dinga azabtar dasu.

Ana wannan halin, a haka sati biyu ta cika, aka koma kotu ranar da aka koma kotu kallo É—aya zakayiwa Khalil kasan yana cikin alhini sosai.
Kamar kullum an cika kotun nan maƙil, haka aka shigo dasu Bulama, wujiga wujiga.

Khalil ya fito gaban kotu, ya gabatar da shedarsa da suke dashi akan Bulama.

Babban abunda ya bawa Yusuf mamaki, be wuce yadda yaga Sunusi ya shigo ba, ya buÉ—e baki yana kallon Sunusi.

Sunusi yazo ya tsaya, Khalil ya masa umarni ya gabatar da kansa, Sunusi ya gabatar da kansa sannan yace  "tabbas wanda ake zargi bashi da laifi, Saleh ɗan uwanane, kuma akwai Bala Yayansa, Saleh ya haɗa kai da Alhaji Bulama da niyyar ya ɗau fansa akan Alhaji Daula na sakawa da 'yarsa tayi aka tsare ɗanuwansa, dan tana zargin da hannunsa a kashe mahaifinta, sedai Bulama ya gaza cika Alƙawarin da yaiwa Saleh ma ze saka a saki ɗan uwansa, su ɗau fansa akan Daula, ganin haka yasa ya koma taimakon' yar gidan Daula, ya kuɓitar dasu daga hannun masu garkuwar, sannan ya kaisu ƙauyenmu gurin mahaaifina, saboda muddin suka dawo za'a kashe yarinyar, kuma shima Saleh ze shiga matsala, lokacin da sukaje ƙauyen bata yadda da kowa se Yusuf, ga jikinta duk rauni se anyi jinyarta, shi kuma yace ita ba muharramarsa bace, babu yadda zeyi jinyarta wannan dalilin ne yasa Saleh ya shige gaba aka ɗaura musu Aure bisa amincewarta, shedar da aka saka ya bayar a kotu shedar ƙarya ce, tursasashi akayi kuma aka masa rauni a cikinsa saboda duka, akace za'a kasheshi in be bada shedar ba, shine aka kawo shi kotu ya faɗi wannan shedar, sannan lokacin da suke ƙauye ya gayamin idan har aka kama Yusuf za'a kasheshi dashi da Widad baki ɗaya, tunda Daula ma ba'asan inda yake ba, nace masa ya gayawa 'yan sanda, amma yace a"a akwai haɗaka me ƙarfin gaske tsakanin Alhaji Bulama da Hukumomin tsaro, dan haka yana da ɗaurin gindi, idan ya faɗa tamkar ya sake jefasu a garari ne"

Nan kotu ta ɗau salallami, Barrister Khalil yace " Alhaji Bukar Bulama, kaine mutum na farko da Alhaji Nasir ya kira bayan an sace 'yarsa, ya akayi wanda suke turo masa saƙo suka san inda suka tafi idan ba kai ka gaya musu ba? "

Bulama yace " ni.. Ni bani bane ba, ya za' ayi in saka a sace yarinyar da takemin kallon uba? "

Khalil yace " Akwai sheda, ina son kotu ta bani dama, in gabatar da sheda ta ta ƙarshe wanda zata tabattar da Alhaji Bulama shike da alhakin dukkan wannan abubuwan da suke faruwa, yasa akayi garkuwa da 'yar Amininsa, kuma yake bibiyar yadda ze mallake dukiyar Aminin nasa"

Aka bashi dama, wa Bulama ze gani? Su me Adda aka jero a layi, akaje aka tsaidasu, nan da nan Bulama ya sadaƙar yasan ƙarshensa yazo.

Aka tsaida me Adda, Khalil yace  "gayawa kotu sunanka"

"Sunana Hashimu, amma ana cemin me Adda"

"meka sani game da garkuwar da akayi da 'yar Nasir Daula?"
Chapter 107 · 0% Book details