Sashe 10
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mayafin doguwar rigar jikinta ta ɗauka ta yafa, ta ruga da gudu tayi waje, aikuwa tana zuwa ta tarar da Anwar zaune a cikin mota, da sauri ta ƙarasa gaban motar, tana ganin Anwar ɗinne kuwa kawai ta tsaya tana murmushi a lokaci ɗaya hawayen tausayinsa da farinciki ya shiga bin fuskarta.
Ya rame sosai, se dogon hanci da manyan idanunsa da suka sake yin zuru zuru, ga duhu da yaya, koba a gaya maka ba akasan inda yaje babu komai se zunzurutun wahala.
Ya kalleta fuskarsa ɗauke da damuwa yace "ya da kuka kuma?"
"Yaya Anwar dole inyi kuka, baka ji ba baka gani ba daga abun alkhairi aka kama ka, kaje kasha wahala ba yadda banyi ba a ɓoye a samu a sakeka amma abu ya gagara, ƙarewa ma akace kotu za'a kaika na shiga damuwa sosai hankalina ya tashi, se gashi Allah yasa ka fito Alhamdilillah, ban taɓa zaton zaka fito ba"
Anwar yayi murmushi yace "hakane, amma yanzu dena kukan mana"
Murmushi tayi tace "ƙyaleni na farinciki ne, taso muje Mummy ma na ciki seku gaisa, amma dan Allah karka nuna muna wani abu tarene, kawai dai ka nuna ka biyo a gaisa ne please"
Anwar yace "karki damu, ba abunda zan nuna insha Allah"
Ya miƙe ya bita zuwa cikin gidan, a falo ya zauna yayin da Nurat ta shiga ɗakin mahaifiyarta  "Mummy kizo ga Anwar yazo ku gaisa"
Da ɗan mamaki ta kalli Nurat tace "Wane Anwar ɗin?"
"É—an gidan Hajiya Halima mana, yazo wucewa ne yace bari ya tsaya a gaisa ai an sako shi shekaranjiya"
Mummy tace "Allah sarki, yaron kirki ashe an sake shi, bari gani nan bari inzo mugaisa"
Ta sako mayafi ta fito, Anwar ya risina ya gaishe ta tace "Anwar ashe an sako ka? To Ubangiji Allah ya tsare gaba"
"Ameen ya Allah Mummy nagode sosai"
"bakomai Anwar, dan Allah ka gaisarmin da maman naka idan ka koma"
"zataji insha Allah Mummy, nagode sosai"
"Yawwa Allah ya tsare"
Suka amsa da Ameen, ita kuma ta koma É—akinta.
Nurat ta jashi suka koma harabar gidan, ta kalle shi tace "Yaya Anwar, ya akayi ka fito ne?"
Ya ɗanyi ajiyar zuciya yace "kowa tambayar da yake min kenan, wallahi ban sam waye ya fito dani ba, ban san mutumin ba, na tambaye shi waye shi, yace wai ba'a bashi damar ya sanar dani waye shi ba, amma kin san wani abu?"
Tace "A'a seka faɗa"
Anwar ya ɗan ƙara ƙasa da muryarsa yace "ya cemin Daddy yana gurinsu, shiyasa ma suka sa aka sakeni, amma ban san dalilin da yasa suka sa aka sakeni aka bar Doctor Sufyan ba"
Zaro ido tayi tace "yana gurinsu kuma? To suwaye su? Meyasa suka É—auke shi?"
"Nima be bani amsa ba Nurat, abun da ya cemin kawai kenan, wallahi gaba É—aya a cikin damuwa nake, babu Widad babu Daddynta, gashi ranar daza'a É—auketa kamar tasan abunda ze faru tacemin Anwar ga Amanar Daddy na nan ka kulamin dashi"
Cikin damuwa Nurat tace "kayi haƙuri Yaya Anwar, Allah ya gani kayi iya ƙoƙarinka, amma ƙaddara fa ta riga fata, babu yadda muka iya, sedai muyi ta musu Addu'a Allah yasa suna hannu nagari"
Anwar yace "Ameen, Amma abun da damuwa ace mace kamar Widad a hannun wanda ba'a san ko suwaye ba, akwai tashin hankali sosai Nurat, kin san ku mata kusa a cikin hatsari kuke, daɗina ɗaya tana tare da Yusuf, amma dukda haka abun ba daɗi, mussman shi ƙaddara ta faɗa masa beji ba be gani ba"
Nurat ta ɗanyi shiru tace "hakane kam, ni kaina ina tausayin Yusuf Anwar, amma dan Allah dagaske direban Widad ne?"
Anwar yace "meyasa kika tambaya?"
"bakomai kawai na tambaya ne"
Yace "eh direbanta ne, me kika gani?"
ÆŠan girgiza kai tayi tace "yana da kirki sosai, kuma da alama ta yadda dashi sosai, na zata É—an uwantane"
"Nima na gani, kuma yana ƙoƙari sosai akanta, yana mata biyayya ne sosai, kuma yana da haƙuri shiyasa suke shiri wasu lokutan"
Nurat tace "hakane kam, amma kuwa anje gidan su Yusuf ɗin, 'yan uwansa sun san halin da yake ciki?"
"Aini kinga ban daɗe da dawowa ba, wasu abubuwan duk ban san me ake ciki ba, ban san daga ina yake zuwa ba, sedai zan bincika inji ubangiji Allah ya bayyana mana su gaba ɗaya, amma ina cikin damuwa sosai Nurat, tun Widad na ƙarama nake sonta, ban taɓa furtawa ba, saboda sanin halinta, katsan bayan na dawo naji ance Fahad ɗan gidan Alhaji Bulama zata aura, naita ƙoƙarin in cireta daga raina, sedai ashe ita gaba ɗaya bata da babban maƙiyi a duniyar nan sama da Aure, tana yiwa Aure wani bahagon kallo ne, har a yanzu haka na kasa cireta daga raina, ina jin sonta a zuciyata, ko bacci bana iyayi yadda yakamata, gashi ban san inda take ba gashi na kasa riƙe amanar data barmin"
Wani irin tausayin Anwar ne ya kamata, a ranta tace 'ashe kaima kana cikin damuwar da nake ta soyayya'
A zahiri kuma tace "na tausaya maka Yaya Anwar, ka sawa ranka wannan É—in Jarrabawa ce, ubangiji Allah yasa mu cinye jarrabawar nan, kasha Lemom mana"
Girgiza mata kai yayi yace "A'a tafiya zanyi nagode sosai Nurat"
Æata rai tayi tace "gaskiya idan baka sha ba bazan ji daÉ—i ba, sekace na baka wani guba, ko kaima Widad É—inne?"
Murmushi yayi yace "wane ni in zama kamar Gimbiya"
Nan ya buÉ—e lenon ya tsiyayya yana sha suna cigaba da hira.
Mahaifin Nurat ne ya dawo suna tsaka da hira, ya shigo da motarsa gidan yayi parking, ya fito daga motar yazo ze raɓa su ya wuce, Anwar yace "barka da Rana Yallaɓai"
ÆŠan tsayawa yayi ya kalli Anwar yace "wa nake gani haka kamar Anwar?"
"eh nine ranka ya daÉ—e"
"Allah sarki, ashe ka fito?"
"Eh wallahi Na fito Alhamdilillah"
"to yayi kyau haka ake so ai, har yanzu kuma babu wani labari akan ɓatan Daula ko?"
"Babu har yanzu dai muna sauraren hukuma ne dai"
"Allah sarki, yanzu an fasa kaika kotun kenan?"
"Eh an wankeni, ance bani da laifi shine suka ƙyaleni"
Alhaji Musa yace "gaskiya ne, ai dama bekamata a tsare wanda bashi da laifi ba, hakan ba daidai bane, kuma lawyoyin naku ne suka fitar da kai?"
"A'a su hana su belina akayi, daga baya ma in sunzo hana su ganina ake, wani mutum ne yazo aka fitar dani"
"ikon Allah, shima lawyer ne kokuwa?"
Anwar yace "a'a ban san waye ba gaskiya, dan nima be gayamin ko shi waye ba"
Alhaji Musa yace "Allah sarki, to ubangiji Allah ya tsare"
"Ameen yallaɓai nagode"
Alhaji Musa ya shige cikin gida.
Duk a aikin gida da Widad ke koya bata taɓa attempting zuwa gaban murhu ba, saboda bata son hayaƙi sam, ko menene tana daga gefe.
Tana zaune a ƙarƙashin bishiya tana gyaran wake, Hindu tace "Amarya dan Allah ƙawayena ne suke so suma a dinga koya musu karatu, in basu dameki ba, in baza'a takura miki ba"
Widad ta É—anyi shiru sannan tace "shikenan tunda ta hanyar ki ne, aini ban isa ince a'a ba, su samo abun rubutu da littafi se mucigaba insha Allah"
Gwaggo tace "Amarya idan da takura fa karkiyi kara, kice musu a'a kawai su haƙura"
"A'a Mama babu takura, bana son mutane ne dai su fiye zuwa inda nake, amma ai bakomai shi ilimin 'ya mace ai abun sone, koba komai zasu amfani al' ummar da suke ciki, suzo zan koya musu Insha Allah"
Gwaggo tace "to Allah ya saka miki da Alkhairi, mu zuwanki garin nan alkhairi ne ai a wajenmu"
Widad tai murmushi tace "bakomai Mama, nima haÉ—uwata daku alkhairi ne ai".
Hindu tace "lallai su Indo zasuji daÉ—i, bari inyi sharar nan inje in gaya musu"
Hari tace "wudas dan Allah nima gasu abu na nan a haɗamin dasu dan Allah"
Hararta Widad tayi tace "baza'a koya musu ba ɗin, yaren yahudawan zan koya musu?"
Hari ta wangale baki tace "haba Wudas, dan Allah kiyi haƙuri ki koya musu"
"Anƙi a koya musun" Widad ta bata amsa tare da haɗe rai.
Hari bata kuma yin magana ba, tayi shiru ganin yadda Widad ta haɗe rai, Hanne ce ta fito tana wani yatsine fuska tana harare harare, Hindu ta kalle ta tace "Hanne ke zakiyi wanke wanke fa yau, kin bari ƙudaje se bin kwanukan suke"
Hanne ta galla mata harara tace "bazan ba, inda can ke kike sani inyi, banza uwar shisshigi da sa ido"
Hindu tace "ke kika sani, haka za'a miki auren kije kina ƙazanta, ki bar kwanuka ƙudaje nabi"
"Eh naji gara ni inada mashinshini ma, kefa ba uban wanda yake zuwa gjrinki, aba kamar mujiya aikin banza kawai"
Jikin Hindu ne yayi sanyi, tai shiru gwanin ban tausayi.
Hari se cewa tayi "ni kaina ina mamakin baƙin jini irin na Hindu, ba wanda yake zuwa inda take saboda tsabar girman kanta da baƙin jini"
Shiru Hindu tayi tana goge Hawaye, Gwaggo ce ta janyo Hanne ta dinga kifa mata mari a zuciye.
Widad tace "wai Auren nan dolene? Meye dan mutum bashi da saurayi? Saurayin banza dana wofi, Auren dole ne, itama wannan banzar mata hankali se kace ba sister É—inki ba, kuna uwa É—aya kina cin zarafinta"
Hansai tace "ba uwarsu ɗaya ba, Hindu ita kaɗai babarta ta haifa ta rasu, Gwaggo ce ta Riƙeta"
Widad tayi mamaki sosai, dan yadda Gwaggo ke son Hindu seka zata ita ta haife ta.
Widad ta ƙarasa inda Hindu ke tsugune tana kuka, Widad taje ta rugumo Hindu ta dinga rarrashinta tace "kiyi haƙuri kinji Hindu, Allah has a better plan for you kinji Hindu, kiyi haƙuri ki ƙyalesu, ai Aurem ba dole bane"
Gwaggo seda tayiwa Hanne tatas da zagi, ta tsitsstinka mata mari, tazo ta kama hannun Hindu tace "dan Allah kiyi haƙuri kinji Hinduna, muna nan insha Allah miji nagari zezo miki insha Allah"
Ita dai Hindu ba tace komai ba, se goge hawayenta da yake faman yi, tana jin zafin Gorin da akan mata na cewa bata da saurayi, Widad ma abun ba ƙaramin baƙantawa Widad rai yayi ba, dan bata son taga abunda ze taɓa mata Hindu, Allah ya haɗa jininsu sosai.