← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 127

Sashe 117

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tace "to naji, ka siyomin abu me daÉ—i, ina jin kwaÉ—ayi"

"To shikenan, zanje ƙauye in Hari tayi girki ta zubo in kawo miki"

A tare sukayi dariya, yace "shikenan sena zo"

Ya maida wayarsa ya ajiye, Suleiman yace "Yusuf zaka karya maganar Ummanka kaje inda Widad take kenan?"

Yusuf yace "yallaɓi, yakamata ka fahimceni Widad fa ita kaɗai take zaune a gidan nan, babu kowa kuma ina tare da Aurenta, duk haƙƙoƙinta suna kaina, Umma taƙi bani dama in mata bayani, bayan haka Widad tana buƙatar kulawa, duk ta kumbura saboda ciwon zuciya da hawan jini, kuma.. Kuma tana ɗauke da tsohon ciki fa" Yusuf ya ƙarasa magaanar cike da jin kunya da kuma damuwa.

Suleiman yace "hakane, yakamata ace Umma ta fuskance ka, amma tanaa gudun abunda ze sake kawo barazana ga rayuwarka ne, amma kabi a hankali, zata fahimta Insha Allah"

Yusuf yace "Allah yasa, amma ni batun Auren nam da Umma ta bijiro dashi, dan Allah Yallaɓi kasa baki, idan har nace zan Auri Nurat Widad zata rabu dani, kuma ina matuƙar son mata ta"

"Shikenan nagane halinda kake ciki, amma Nurat ma abun tausayi ce"

Yusuf yace "Nasani, badan kishi irin na Widad ba da zan iya auren Nurat, saboda tana sona sannan bata da wani aibu, sema nine nake da aibun da za'a gujeni saboda shi"

Suleiman yace " aibun me kenan?"

Yusuf yace "bakomai, manta kawai"

Suka cigaba da hirarsu, har zuwa gidan su Nurat.

Koda dukaje Khalil baya gida, megadi yaje ya sanar da zuwansu, aka musu iso.

Sedai Suleiman yace baze shiga ba sedai Yusuf yaje, haka kuwa akayi aka masa jagora har falon da aka saukesu wancan zuwa.

Yayar maman Nurat ce ta fara zuwa, Yusuf ya gaisheta cikin girmamawa, sannan ta koma ta turo masa Nurat.

Yusuf yana nan zaune yana sake kallon wayarsa, yana addu'a Allah yasa kar Widad tayi fushi, yaji ƙamshin turaren Nurat, ya ɗaga kai ya kalli Nurat, duk ta rame kallo ɗaya zaka mata kasan bata da lafiya, a hankali take tafiya tana ɗan lumshe ido irin na marasa lafiya, ta ƙaraso ta zauna a kan carfet.

Yusuf ya dawo kujerar da Nurat ke zaune a ƙasa, ya kalleta yace  "Light Dama baki da lafiya?"

Maimakon ta bashi amsa se cewa tayi  "ina wuni"

Yusuf yace  "lafiya ƙalau, ya jiki ɗazu Umma ke gayamin ban sani bane"

"Jiki da sauƙi Alhamdilillah" ta faɗa tana rausayar da kanta ƙasa.

"Amma kin daÉ—e kina rashin lafiyar nan, meke damunki haka?"

Girgiza masa kai tayi tace  "bakomai"

"ban yadda bakomai ba, ki gayamin meke faruwa ne?"

Kasa magana tayi, se hawaye da suka shiga zarya a fuskarta, ba tare da ta shirya zubarsu ba, dan tayi duk me yuwuwa ganin basu zuba ba, amma abun ya gagara.

Yusuf ya sakko daga kan kujerar, ya zauna a kan carfet É—in yana kallonta, a hankali yace "Nurat, dan Allah kiyi magana mana, meyafaru?"

Shiru tayi ta ɗauke kai daga kallon inda yake, dan data kalle shi sonshi ƙara shigarta yake, da kuma kishinsa.

"Nur ko nine nayi miki laifi?"

Ta ɗago idanunta ta kalleshi na wani ɗan lokaci, ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsunta, a hankali tace  "Nagode sosai kazo ka dubani, nagode ka gaida Umma"

Ta yunƙura ta miƙe zata tafi, cikin zafin nama Yusuf ya miƙe ya riƙo hannunta, ta juyo tana fuskantarsa, ta kalli inda ya riƙe hannunta ta kalli Fuskarsa taji tamkar ta rungumeshi tayi kuka, ita dai a rayuwarta maza dayawa sun nuna suna sonta, amma bata taɓa jin ƙauna da soyayyar wani a ranta kamar Yusuf ba, zata iya cewa akansa ta fara Soyayya.

Yusuf yace  "Nurat bana so in zama butulu, bana son zama ɗaya daga cikin masu butulci, ki gayamin me kike so? Meke saki kuka haka?"

Cikin sassanyar muryarta, me cike da karaya tace  "bazan samu abunda nake so ɗin ba ai, dan haka babu buƙatar cigaba da ɓata lokaci gurin faɗa"

Yusuf yace  "gayamin, ko mene ki faɗamin, me kike so?"

"Yusuf kai nake so, kaine Yusuf, ban taɓa so ba se akanka, ban san haka ake ji ba, sedai nasan bazan sameka ba, kamin nisa na har abada, nasan ko a mafarki Widad bazata yadda ka auri wata bayan ita ba, bayan haka ta fini komai, sannan ga abunda ke tsakaninta da mahaifina, ina ganin ƙiyayyata ƙarara a idonta, ga kuma bazan so ka dinga samun saɓani da mahaifiyarka saboda ni ba, dan haka ina muku fatan Alkhairi a rayuwar Aurenku me cike da alkhairi, Allah ya ƙara tsareku daga sharrin maƙiya, da mahassada nagode sosai Yusuf "

Gaba É—aya jikinsa yai sanyi, sosai ta bawa Yusuf tausayi, tabbas Nurat ta cancanci a tausaya mata, da tausayi halin da take ciki a yanzu, amma yasan ko wace kalar wiwi yake sha, baze haÉ—a Widad da wata ba, saboda yasan azabar kishi irin na Widad, Nurat ta zare hannunta daga nasa ta koma ciki da sauri.

Jiki ba ƙwari Yusuf ya fito daga falon, ya nufi waje, Suleiman ya kalleshi yace  "lafiya kuwa?"

Yusuf yace  "Yallaɓai akwai damuwa"

"meyafaru"?

"Nurat sona take dagaske fa"

Suleiman yace  "Au kaida baka san son naka take ba?"

Yusuf ya dafe kai yace  "Yallaɓai, dan Allah kamin alfarma ka kaini in ga Widad, dan Allah bazan daɗe ba insha Allah"

Sulaiman yace  "Shikenan, bakomai mije ina ne?"

Yusuf yai masa kwatance suka tafi, a bakin gate wani ɗan sanda ya taresu yace  "ya akayi?"

Yusuf yace  "a gayawa Widad Yusuf ne"

ÆŠan sandan yai murmushi yace "Ohhh ashe megidane, ai tun É—azu take jiranka"

Aka buÉ—e musu gate, Suleiman ya shiga da motar yana mamakin haÉ—uwa da tsaruwa gami da girman gidan.

Yai parking Yusuf ya fito daga motar, yace  "Yallaɓai zo mu shiga mana"

Suleiman yace  "Gurin budurwa ma ban bika ba se gurin matarka, a'a ina nan"

Yusuf kawai yai murmushi ya girgiza kai, ya shiga ya dinga duba falukan dake gidan, Kasancewar ya kirata bata ɗaga ba, can ya hangota a wani falo, tana zaune akan 3 seater, ta haɗe rai sosai, sanye take da dogon wando, da 'yar riga ƙarama, ta gyara gashin kanta ta saka ribbon saki ƙarshensa   a bayan ta, hakan ya bawa cikinta damar fitowa sosai, abun mamaki ta saka jambaki da kwalli a idonta, abun da Yusuf be taɓa gani ba, sedai ta haɗe rai.

Yusuf ya ƙaraso inda take yana murmushi yace  "farar mace alkyabbar mata, why are you sad? Ba gani nazo ba"

Ta É—aga kai ta kalle shi, ta mayar ta sunkuyar da kanta tana danna wayarta.

Yusuf ya ƙaraso ya zauna kusa da ita yace  "bazaki ɗago in ƙare miki kallo ba?"

Matsawa tayi daga kusa dashi, ya kalleta cike da mamaki yace  "lafiya kuwa?"

Ta ɗago tace  "Daga ina kake?"

Yusuf yace  "naje wani gurine shiyasa..

" Yoseef kasan bana son ƙarya fa, ina kaje? "

Maimakon yai mata magana, seya ƙura mata ido, ta saka idonta a nasa tace " Yoseef gurin Nurat kaje "

" waye ya gayamiki gurinta naje? "

" tunda ka cemin zaka wani guri, zuciyata ta kasa samun nutsuwa, naji a jikina gurinta zaka je, kuma kana shigowa naji kana ƙamshin turarenta, Yoseef wallahi gurinta kaje"

Yusuf yace  "lallai zuciyarki tana tare dani, dan ba tayi miki ƙarya ba, tabbas naje gurin Nurat bisa ga Umarnin Umma, naje na duba Nurat bata da lafiya, Widad, Nurat bata cancanci wulaƙanci ko banzatarwata ba, dukda abunda mahaifinta yayi, amma ta taka mshimmiyar rawa a gurin kuɓutata, kalli ta rasa mahaifiyarta, mahaifinta ya tafi prison, kuma a yau take gayamin tana sona, be cancanci in wulaƙatanta ba"

"Yanzu me kake so ka gayamin? Zaka Auri Nurat ne kokuwa?"

Tai maganar tana tsststare shi da ido, Yusuf yace  "ni bahaka nske nufi ba, itama tasan hakan bame yuwuwa bane, amma yakamata itama a dubata, a tausaya mata, ta rasa kowa Widad ko ban Aureta ba bata cancanci wulaƙanci ba, ta temakeni kuma kin.....

Cikin faɗa Widad ta dakatar da shi, ta hanyar cewa  " ni ka cikamin kunne da ta temakeka, ni wulaƙanta ka nayi? Ko kana zaton Nurat tana da abunda zata ja da Bukar Bulama ne? Kasan waye Bulama kuwa? Aiko mahaifinta da suke tare da Bulama, wallahi bashi da ƙarfin ja da shi, yana da arziki kuma goyon bayan manyan mutane a duniya ba ƙasa ba kawai, Yoseef Bukar yamin barazana ko inje kotu in bada sheda ko ya kashe Ummanka, ko kasan ba Nurat ce tai sanadin kuɓitarka ba Allah ne ya kuɓutar da kai, amma se da na bada kadarorina na miliyoyin nairori, aka siye mutanen Da Bulama ya siye, nasa aka ninka musu abunda ya basu, na ɗaukar maka babban lawyer wanda shine ya tsara komai? "
Chapter 117 · 0% Book details