← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 127

Sashe 78

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amal tace  "gaba ɗaya jikina ciwo yake, bana son hayaniya ne, sedai kuma naga babu daɗi, shiyasa nace kawai bari inzo mu gaisa"

Mummy tace "da dai yafi"

Suka fito gaba ɗaya falon, uwargidansace se Amaryarsa wadda take yarinya sosai, Amal ta ƙaraso suka gaisa, sukayi mata ya jiki, Amal ta amsa tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.

Da zasu tafi uwargidan tace  "ga mukullin mota yace a baki, gata can yace a baki tunda taki ta lalace, Allah ya ƙara sauƙi"

Amal tai murmushin takaici tace  "Amma fa nagode sosai, ai masa godiya ace masa naji daɗin motar nan fa, sannan ina nan tafe karɓar mukullin gida kuma"

Basu kawo komai ba, tunda ce musu yayi 'yace a gurinsa tunda sun san Hajiya Halima, Amal ta karɓi lambar wayarsu, tace sa dinga gaisawa.

Nurat tana zaune suna hira da Mummynta, ta gwada layin Anwar harta gaji amma shiru bata shiga, tun abun baya damunta har ya fara damunta, ta kalli mahaifiyarta tace "Mummy fita nake son yi fa"

"Kije ina?"

"Mummy duk inda ta kama, tunda aka samin doka yau kwana nawa ban fita ko ina ba, gashi ina buƙatar in ɗan fita ɗin in rage zafi, kullum ina cikin gida kamar wata mara gaskiya"

Mummy tace "nidai babu duwana, duk abunda kika jawa ka ki shikenan ba ruwana, kin san yadda kuka ƙareta dashi wancan karon dai"

"Mummy gidan Daula nake son zuwa, ina sin jin ko lafiya, layin Yaya Anwar baya shiga fa Sam"

"gidan Daula ko? Sekin dawo tunda baki da hankali"

"Mummy ba haka bane, ai gaida me gaishe ka ko baze amsa ba, amma tunda hakane, bari in jida zuwan bdk Khalil, idan yazo ya biya ya dubamin ko lafiya"

"Ke wani Khalil É—in, baki san ranar da yazo ya tarar dashi ba kirana yayi yana masifa ba, wai zaryar me Khalil yake masa a cikin gida ba? Wai in dakatar da shi da zuwa ba"

Nurat tace  "to Mummy ke kuma baki ce masa komai ba, sannan me Khalil yayi masa?"

"Oho kin san halinsa na rashin gaskiya ai, shi duk wani motsi seya zata bin diddiginsa ake, shiyasa kullum bashi da nutsuwa ai, shima dole zanyi masa waya, ya rage yawan sintir a gidan nan, ya bari se an kwana biyu yazo"

Nurat ta dafe kai tace  "Ohh my God, ba dai gudun tinon Asiri yake ba, Insha Allah ya gamu da shi kenan, in Allah ya yadda se asirinsa ya tonu"

"Ke rufemin baki, kar yazo ya tarar dske kina wannan maganaganun, ya zata wani abun muke shiryawa"

A fusace Nurat ta miƙe ta e  "to ya zata iɗn mana Mummy, na gajiya walilahi, am tired"

Ta juya ta bar falon ranta a ɓace, zuciyarta na wani irin tafasa tana tururi.

Yusuf na zaune yana zaune, Widad na kwance akan cin yarsa, yana ta wasa da gashin kanta, tana masa hira sedai gaba ɗaya hankalinsa baya kanta, ya tafi can duniyar tunani, ƙirjinsa nata bugawa haka kurum, yaka sa gank dalikin bugawar ƙirjin nasa, "Yoseef" ta kira sunansa, da sauri ya dawo hayyacinsa yace "Na'am"

"Me kake tunani ne?"

Yace mata 'bakomai "

Ta gyara kwanciyarta tace "Yuzarsef, kwana biyu Saleh bezo na, nifa hankalina yayi gida, gaba ɗaya na ɗan fara damuwa tunda yake zuwa be taɓa cemin komai akan mahaifina ba, zuciyata na son ganin mahaifina, ina yawan mafarkinsa ina son jin abunda ke faruwa gaskiya"

Seda gaban Yusuf ya faɗi, dan Saleh ha tabbatar masa babu wani sahihin kabadi har yanzu akan ɓatan mahaifinta, gashi ita bata sani bama, ya dake yace "tabbas nima ina ta fama da kokwanto a raina, ina son sanin meke faruwa a gida, gashi naga kwana biyu Saleh bezo ba"

Tace "hakane, dukda ni ba shiga sabgarsa nake ba, amma dole zan tambaye shi ya Daddyna yake, in dai lafiya ƙalau ne, baze jure tsawon wannan lokacin be gannj ba, dase yazo har nan kota halin yayane, amma tunda naji shiru something is going wrong somewhere, gidanmu nake son komawa "

" Insha Allah nothing is wrong anywhere, komai yana tafiya dai dai, am yakamata mu koma gida haka kam"

Tace "Allah yasa hakan"

Yace "Ameen, but Baby ta yaya zamu tabattarwa da al'umma Aurenmu, meye shedarmu?"

Widad tace  "Allah"

Yace "hakane Allah sheda ne, amma baze yuwu mu gayawa mutane haka ba, dole mu nuna shedar aure mukayi, tunda au can babu wansa yasan hakan"

Widad tace  "karka damu, Saleh ya sani, ga al'ummar garin nan da muka zauna tare dasu, suma sun isa sheda ai"

"Hakane, Allah yayi mana jagora"

Tace "Ameen"

Alhaji Musa yana zaune a ɗakinsa yana cin Abinci, ya ɗau waya ya kira Nurat yace yana son ganinta a ɗakinsa, Mamanta ta kalle shi tace  "lafiya kuwa? Ina fatan dai ba wani laifin tayi maka ba?"

"ina ruwanki ne? Nida 'yata bazan kirata ba, ki zuba ido kawai"

Tace "Ai gara in dingayi ina bin ba' asai, saboda naga kai abun naka se a hankali gaba É—aya"

Nurat tayi sallama ta shigo da dogon hijjabinta  a jikinta, yace "Bacci kike ne?"

Ta girgiza masa kai tace "A'a salla nayi"

Yace "madalla fatan a nayiwa Daddy addu'a"

Ta jinjina masa kai yace "yawwa 'yar gidan Daddy, dama ba wani abune yasa na kiraki ba, zan sanar dake jn the next couple of weeks zaki koma Karatu"

Nurat tace "A ina kenan?"

Yace "can inda kika baro mana abroad, na nema miki imperial College London, kije kiyi business administration É—in da kike so a can"

Girgiza masa kai tayi tace "Amma Daddy ai ba haka mukayi da kaiba, ka tambayeni nace maka ni a Nigeria nake son in cigaba, ka amincemin kuma yanzu kace ba haka ba"

Yace "look Nurat, ina nema miki sauƙi ne da kuma safe environment, inda zakije kiyi karatun ki cikin nutsuwa da kwanciyar hankali"

Tace "Nan ma akwai nutsuwa da kwanciyar hankali ai, ni dai kawai ka ƙyaleni a nan, bana son zuwa"

Aikuwa ya harzuƙa yace "ke, nine zance ga yadda za'ayi kice ke ba hakaba? Waye ya haifi wani tsakanin nida ke?"

Nurat tace  "kai ka haifeni, amma kaima ka cika Alƙawari mana Daddy, baka gudun yadda tarbiyyata zata kasance, ni ina can ku kuna nan ni gaskiya bazanje ba"

Ya kalli Maman Nurat dake gefe tana jinsu yace  "wato ke kike ziga yarinyar nan take rashin mutuncin da taga dama ko? Idan ba hakaba ya za'ayi ina magana tana magana?"

"Malam babu ruwana ni, 'yarka ce yau da gobe ai tafi ƙarfin wasa, ka fiye son kanka da yawa, shiyasa tun yarinyar nan na maka biyayya harta zo ta dena yi maka saboda son zuciyarka, kuma nima gaskiya ban yadda inyi nesa da ita ba, tunda mun baro ƙasar ma meye kuma ita za' a maida ita"

Alhaji Musa yace "lallai ba shakka, na ƙara tabattar da cewa ke kike ziga yarinyar nan, in faɗa ki faɗa tana gani ai dole itama ta fara, to bari kijin in gayamiki tafiya daram, seta tafi dole ta bar ƙasar nan taje inda na nema mata karatu"

Nurat ta fashe da kuka tace  "ni gaskiya bazani ba, kuma idan aka takura sena je, wallahi barin gidan nan zanyi, dama naga yanzu ba'a ƙauna ta, tunda har yunƙurin rabani da rayuwata akayi" tai maganar tana ficewa daga falon, tana ji yana ƙwala mata kira amma tai banza dashi tai tafiyarta ko waigowa ba tayi ba.

Yusuf yana kwance har wajen shaɗayan safe, idonsa a lumshe yayi rigingine yana jin yadda gabansa ke cigaba da faɗuwa akai akai, Widad ta shigo ɗakin ta fito daga wanka tace "Yoseef, wai ba zaka tashi bane haryanzu shaɗayan rana, seka sa Hari tazo tana gayamin magana ko? Ina jinta shekaranjiya wai na fiye jaraba goma na safiya ina rufe ƙofa saboda shegen sa ido irin nata"

Yusuf ya kwashe da dariya yace  "Ai gaskiya ta faɗa ba ƙarya ba, hakane abunda ta faɗa waike dole sekin samo Baby ba"

Widad ta buɗe baki tace  "lallai Yoseef sannu, hakama zakace ko? Kaifa kace in rufe ƙofa sanyi kake ji, shine zakamin sharri"?

"Ba wani sharri malama, ni bance ki rufe ƙofa ba"

Widad tace "Ikon Allah, ni nama rasa me zance maka"

"dole ki rasa mana, kuma yau bazan kwana akan katifarki ba, a ƙasa zan kwana"

"Kaje kaita kwanan mana ina ruwana?"

"A'a dai karkizo kina min kuka, wai kai Yoseef meye haka? Dan Allah kazo ka kwanta" yai maganar yana kwaikwayon muryarta.

Tace "Nikam na shigesu a gurinka, Allah ya shiryeka"

"to kice ba'ayi haka ba mana"

"Aini bazan sake magana ba, nayi shiru"

Yai murmushi ya maida idonsa ya lumshe, ta ɗan ƙura masa ido, ya ɗan faɗa sedai masha Allah Yusuf ba dai kyau ba.

Tai murmushi tace "Mutum da hanci kamar an zana cartoon"

Yace "Kyau yai miki yarinya, shiyasa kike min ba'a"

"Ba wani kyau a nan gurin, wannan zanƙalelen hancin kaman cartoon"

"Kyaji dashi dai, yabawa kika yi"

Tazo tasa hannu ta matse masa hanci, Yusuf yace "ko ki sakarmin hanci, ko kuma yanzu in ɓaro ɗan dake cikin ki"

Da sauri ta cika shi tace 'yi haƙuri "

Yai dariya yace " Yarinya baki da komai a wannan cikin naki "

Ta murguÉ—a masa baki tace "aini nasan akwai"

Tai maganar tana tura baki, yayin da ya bita da kallo yana jin sonta na ƙara ninkuwa a  zuciyarsa, idan ya tuna lokacin da take garashi da izza da rashin mutunci, ga gefe guda azabtuwa da soyayyarta daya dingayi ba tare da ta sani ba, idan akace masa akwai rana da zata zo su kasance a haka baze yadda ba, amma shine zaune da ita a ƙarƙashin inuwa ɗaya ta Aure, suke zaune ba tare da ya ɗaga masa hankali ba, wani farinciki ne ke ratsa zuciyarsa, tabbas da Widad ta rayu da masoya na gaskiya, mussman tare da mahaifiyar ta ba zata yi wannan izzar da jin kai ba, sedai rashin masoya, da kuma tsantstsar zalunci da butulci da aka gwada mata yasa tayi wa mutane gaba ɗaya kuɗin goro mussman talakawa.

Saleh gaba ɗaya ya sadaƙar, jira yake kawai suzo su fara gana masa azabar da Bukar yayi umarni, sedai basu yi masa komai ba sedai ɗaɗɗaureshi da suka kuma yi.
Chapter 78 · 0% Book details