Sashe 15
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Bukar yace "yanzu magana ta farko dai shine, mu matsa lamba musan inda Daula yake, ɓatan Daula ma fa wani babban giɓine kuma hatsari a garemu, ga 'yarsa itama bamu san a inda take ba yanzu, ga wannan yaron da wannan maganar ta taso yanzu"
Alhaji Munir yace "Sannan wanda ya sa aka saki Yaron gurin Halima shima ba ƙaramar barazana bane a gare mu, dan bamu san waye ba, kuma banu san manufarsa ba"
Alhaji Musa yace "Aini nafi kowa shiga matsala, a hanzarta a nemo mafita gaskiya"
Alhaji Bukar yace "ku kwantar da hankinku, zan san abunyi insha Allah, nasan yadda zanyi da al'amarin"
Alhaji Munir yace "Yallaɓai meye mafitar to?"
Bukar yace "when I come out with the final decision I will let you know, Musa ka kwanta da hankalinka, ba abunda ze faru zanwa tufkar hanci"
Alhaji Musa yace "to shikenan tunda kace haka yallaɓai"
"Mummy karɓi wayarki, tana ta ringing kin barta a falo"
Hajiya Halima tasa hannu ta karɓi wayar tace "Salamu Alaikum"
"Wa'alaikum Salam, Halima yakike ya yara?"
Haɗe rai tayi tace "Kai harkuna da bakin da zaka wani kirani kana ya Yara? Bayan rashin mutuncin da kukayi min akan belin Anwar?"
Alhaji Haruna yace "ke, ki bar wannan maganar akwai matsala ne fa"
"Matsala ta ƙaremu ku acan tsakaninku banda ni, karka sake sani a cikin matsalarku tunda kowa kansa ya sani"
"Aikuwa kece a wannan matsalar, dan wallahi kina ruwa"
"Kamar yaya?" tai maganar cike da mamaki.
"Yaron nan Yusuf yake ko Yunusa, ashe jam'in sirrine, shine wanda yake binciken"
Mummy tace "kai ɗan tsaya mana, Wai Yusuf direban Widad?"
"Oho nima ban sani ba, wanda dai aka sacesu tare, ashe shine yaron da yake binciken nan, muna ganin munyi dabara ashe da kanmu muka burmawa kanmu wuƙa, yaron nan shine yake gudanar da binciken"
"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, na shiga uku Haruna dan Allah yaron nan dagaske É—an sanda ne?"
"ƙwarai kuwa, ɗan sanda ne ma farin kaya, kuma shike gudanar da binciken nan"
"Shikenan, wallahi idan ya dawo garin nan tabbas na kaɗe, an karɓi bayanin binciken kuwa?"
"ba'a karɓa ba dan ba'a samu ba, amma Alhaji Bukar yace mu saurare shi, ze faɗa mana abunda za'ayi"
Hajiya Halima tace "ni dai dan girman Allah ku gaggauta samo mafita, wallahi akwai matsala" tai maganar tare da ajiye wayar tana faɗin na shiga uku.
Amal tace "Mummy meyafaru ne?"
Ramlah ma shigowa tayi tana faÉ—in "Mummy lafiya kuwa?"
"Yara akwai damuwa fa, wai ashe munafukin yaron nan É—an sanda ne?"
Amal tace "wane yaron wai?"
"wannan shegen direban me siffar munafukai mana"
"Wai Yusuf?"
"Shi, wai ashe É—an sanda ne"
Ramlah tace "ta yaya ya zama ɗan sanda? Mummy ke waye ya gaya miki?"
"Yanzu mukayi waya da Haruna yake gayamin"
Ramlah tace "No wonder, sam wannan beyi kalar wanda za'ace yana cikin wahala ba, ko kuma rashin ilimi, ashe munafukine shiyasa na tsane shi, shege Azzalumi"
Amal tace "shiyasa wani lokacin nake hanaki yi masa wasu abubuwan Mummy, ki saki baki kiyi ta sakin maganganu anyhow, gashi abunda ya faru ai"
Ramlah tace  "dan Allah kiyiwa mutane shiru, yanzu mafita za'a nema ko surutan zaki cigaba dayi?"
Amal tace "ko anemi mafita ko kar anemi mafita aikin gama ai ya gama, sedai a kiyayi gaba"
Hajiya Halima tana jinsu tayi shiru, gaba É—aya ta shiga tunani yadda take sakin magana yadda taga dama, ashe kallonsu kawai yake"
Ramlah tace "Yanzu Mummy meye abunyi ne?"
Mummy tace "Nima ban sani ba, amma Bukar yace mu saurare shi, ze samo mafita"
"to Ubangiji Allah yasa mafitar me ɓullewa ce, amma nikaina abun ya tsoratani"
Ramlah tace "ki kwantar da hankalinki Mummy, Insha Allah bakomai, dan ni kaina a tsure nake, kin san na taɓa zuwa nace ya samomin Password ɗin Widad, Amma tunda Alhaji Bukar yace akwai mafita, to tabbas akwaita, ki kwantar da hankalinki"
Mummy ta jinjina kai, Anwar ne yai sallama a ɗakin, ya kalli fuskokinsu yace "Ya dai na ganku kunyi jugum jugum, akwai matsala ne?"
Ramlah tace "babu wata matsala"
"Ya zakice babu matsala bayan fuskokinku sun nuna hakan?"
A fusace Mummy tace 'Kai fita ka barmin ɗaki, uban bin ƙwaƙwƙwafi, ance maka bakomai amma ka dage "
" Allah ya baki haƙuri " daga nan yai waje abunsa.
Da Asuba tayi Yusuf ya dawo daga gurin karatu, lokacin gari yayi haske ya É—umama musu shinkafa sukaci da safe.
Ya miƙe ze fara shirin fita, ta kalle shi tace " naga kana shiri, ina zakane? "
" Yau ranar kasuwa fa, zanje nema"
Widad tace "ba inda zaka se ciwon nan ya warke"
"Meyasa?"
"Se kaje wani abun ya kuma faruwa? Ka bari ƙafar ta warke kana ɗingisawa da ƙyar kana maganar zaka fita"
Yusuf yace "Nifa lafiyata ƙalau, kawai dai..
" ba wani kawai, idan kace seka fita kana tafiya, nima zan É—auki hijjabina in tafi "
" ki tafi kije ina? "
" duk inda Allah yayi "
Yusuf yace " to shikenan, naji na fasa fita"
Widad tace "karma ka fasa ɗin"
Ta ɗau bokiti tayi waje, suka gaisa da Gwaggo, Gwaggo tace "Amarya ɗan miƙomin robar can me ruwan ɗorawa"
Widad ta tsaya tana waige waige, tace "tana ina robar take?"
Gwaggo tace "gata can a bayanki"
Widad tace "to ai ban san meye ɗuruwar ba"
Gwaggo tayi murmushi tace "ruwan ɗorawa nace, gata can a gefen randa"
Widad ta ɗakko robar, tace "Gwaggo meye ruwan ɗaurawa"?
"Kalar robar ce ruwan É—orawa"
Widad tace "Ok Yellow kenan zaki ce Gwaggo"
Gwaggo tace "Ahh mu nan haka muke cewa"
"Gwaggo dan Allah meye faskare?"
Hari tace "na shiga uku da wannan lamari, waike komai baki sani ba? Kwarankwatsa ko a birni an san waɗan nan abubuwan, amma kiyi ta rainawa mutane hankali"
Kamar basuji me tace ba, Gwaggo tace "Saran itace shine Faskare"
Widad tace "a dinga saran bishiya?"
"Eh a sassara bishiya, a farfasa yadda aza'a iyayin girki dashi"
Widad ta ɗanyi shiru, sannan ta jinjina kai, ta kuma cewa "Gwaggo wai meyasa naga ruwanku seya dinga yin kala, ni wanda Yoseef yake ɗebo mana yafi wannan kyau sosai"
Gwaggo tace "ban hana kiran sunansa kai tsaye ba"
Widad ta toshe baki tana dariya, tace "yi haƙuri na manta ne, wanda mijina yake ɗebowa"
Hari tace "hmmhmm wa yaga kwaÉ—o, ba kunya wai mijinta"
Widad tace "to da mijinmu ne nida ke?"
Hari tace "A'a ni Allah ya tsareni, mijinki ne ke kaɗai"
Gwaggo ta girgiza kai tace "Inda Yusufa yake ɗebo muku ruwane, ba giri ɗaya da namu ba, shi birtsatse yake zuwa ya ɗebo muku, kuma tafiyar da yake a ƙasa kafin yaje gurin ta ɓaci, da nisa sosai ita kaɗai ce burtsatse a garin nan"
"Gwaggo dan Allah meye burtsatsi?".
"Ruwan famfo, amma na tuƙa tuƙa"
"Nasan dai famfo, amma ban san meye tuƙa tuƙa ba"
Shikan sa Yusuf da yake ɗaki yana jiyosu, seda yace "Allah yasa kar Gwaggo ta gaji da wannan tambayoyin na Widad.
Allah yasa aka zuba mata ruwan É—umi ta tafi wankanta.
Bayan ta fito daga wankanne tana shiga É—aki, ta tarar Yusuf ya tattara kayansu na wanki ya É—aure a guri É—aya.
Ta kalle shi tace " wannan fa?"
"wanki zanje inyi mana"
"A ina?" ta tambayeshi
"Can wani gurine bakin ruwa, nake wankin, jira nake in ƙarasa yi miki girkin rana in tafi in wanko kayan"
Widad ta ajiye bokitin, ta ƙarasa tace "gaskiya zan bika"
"Ki bini ina?"
"Gurin wankin mana"
"No kiyi zamanki a gida inje in dawo, gurin ba kowa kuma bakin ruwane"
"gaskiya ban yadda ba, tunda muka zo garin nam ban taɓa fita ba, gaskiya ka tafi dani, nima base in koyi yadda akeyi ba im dinga yi mana"
"bana so Kisha wahala ne, ki bari inje inyi indai fitane, zam fita dake mu zaga gari"
A hasale tace "bana so tunda ba zaka dani ba shikenan"
Ya fuskanci haushi taji, dan haka ya ƙarasa inda take yace "Meyasa kike da saurin Fushi ne Masoyiyya, shikenan zamuje tare, kinsan bana son ɓacin ranki"
Tura baki tayi taƙi magana, ya juyota ta fuskance shi yace "smile mana habibty"
Tura baki ta sake yi tace "baza ai smiling ɗinba"
"In kina tura bakin nan i just feel like to kiss you"
Ɗago ido tayi da sauri cikin Shagwaɓa tace "kaga ka bari bana so"
"to yi min murmushi in ƙyaleki"
"to ai murmushin ne be zoba"
Yadda tayi maganar ne ta bashi dariya, yace "shikenan, ina bim bashi se anmin murmushin nan. To ko in ta yaki sa kayan?"
Da sauri tace "A'a bana so wallahi" tai maganar tsoro ƙarara a idonta.
Murmushi yayi, ya juya ya cigaba da haÉ—a kayan, seda ya kammala yayi musu girki, sannan yai waje.
Ta tsaya ta saka hijjabinta, da silifas ɗinta ɗan madina ta fito, Hindu taga Widad ta sha hijjabi, dan bata saba gani ba idan ba salla Widad zata yi ba sunyi hannun riga da hijnabi, Hindu tace "Amarya ina zuwa haka?"
"Fita zamuyi nida Yoseef, naga kamar Gwaggo wanka take inta fito ki gayamata"
Hindu tace "shikenan zan gaya mata insha Allah, sekun dawo yau zanyi wunin kaɗaici"
Widad tace "Allah sarki Hindu, nima zanyi kewarki, semun dawo"
"Shikenan Allah yasa karku daÉ—e"
Widad tayi hanyar fita, sedai tana zuwa ta tarar an zubawa Manyan ragunan megari harawa a hanyar fita wajen, gasu da manya manyan ƙaho a murɗe, sun kai su goma sha, suna ture ture suna cin Abinci.
Ƙura musu Ido Widad tayi, tana tunanin ta ina zata wuce.
Jin shiru Widad bata fito ba yasa Yusuf dawowa yaga ko lafiya.
Ya tarar da ita a tsaye tana kallon raguna, Yusuf yace "Madam ke nake jira fa, kim tsaya kallon raguna"
"Nifa tsoro nakeji"
"Tsoron mekuma?"
"kar inzo zan wuce su dakeni da wannan ƙahon nasu"
Yusuf ya girgiza kai yace "yanzu ragunan ne yasa kika tsaya kika kasa fitowa? Duk soyayyarki da dabbobin kuma yanzu tsoronsu kike ji?"
"To wai so kake, su dakeni da wannan ƙahon suji min ciwo, ko ance maka ni 'yar sanda ce?"
Yusuf yace "iyee au abun hadda baƙar magana, ai shikenan"