← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 127

Sashe 77

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"hmm Yaro man kaza, wato shi dai yaro yarone kam, ke a gwagwarmayar da nayi, babu kalar karuwar da ban gani ba, babu kalar barazana da kaidin matan da ban gani ba, nayi Aure Aure, nayi biye biye ba irin matan da ban gani ba, dan haka' yar ƙaramar barazanar ki bazata tsoratani ba, you better calm yourself down, ba'a kanki aka fara ba kuma ba'a kanki za'a ƙare ba, karki ƙarawa kanki ciwo akan ciwo, ki kwantar da hankalinki ki more ƙuruciyarki ki tara abun duniya"

Wani gululun baƙin ciki ne yazo ya tokare maƙogwaron Amal, wanda yasa ta jan numfashi da kyar, ta rasa me zata yiwa Alhaji Haruna wanda zesa taji ta rage azabar da zuciyarta ke mata, ga karaya data samu ga rauni a kanta, ga uwa uba fyaɗe da yayi mata, kuma yazo ya tsaya yana gayamata maganar banza, ta lumshe idonta wasu irin hawaye na takaici da baƙin ciki suna bin gefen idonta.

Tana jinsa ya buɗe ƙofar yai waje abunsa hankalinsa kwance wani nishaɗi yana ratsashi, dan ba abunda yake ji na damuwa ko tashin hankali a tare da shi dangane da abunda ya aikata.

Kusan mintuna ashirin da fitarsa, Ramlah tai sallama ta dawo ɗakin, ta janyo kujera ta zauna a gaban gadon Amal, Amal tace  "Ina Mummy ne?"

"Taje gida zata yi wanka ne, ta canza kaya"

Amal ta jinjina kai, tana sake jin wani irin zafi a hannuta da ƙasanta, ta ɗan rintse ido tana girgiza kai, an mata illar da bazai taɓa gyaruwa ba ta gyara kwanciyarta tana ajiyar zuciya
.

Ramlah ta kalleta tace  "Amal meye tsakanin ki da wannan mutumin ne, naga fa kamar akwai damuwa a tare da ke? Meyafaru ne"

Girgiza mata kai tayi tace "bakomai"

Ramlah tace "ki gayamin gaskiya, ko akwai taimakon da zan iyayi miki, naga kamar akwai wani ɓoyaayyen al'amari a tsakaninku ke da shi, naji yana yiwa Mummy wasu maganganu ne marasa kan gafo, wai ai shi ya gani yana so, wai idan zata bashi ke yana so, ni ina tunanin ma wannan hatsarin da akace kinyi, gaba ɗaya na kasa yadda abun kamar wani shirin film ko tatsuniya fa"

Amal taji kamar ta gayawa Ramlah gaskiya, se taga yin hakan tamkar tonawa kanta asiri ne, kuma idan harta nemi taimakon wani, to bata cika mace ba, yakamata ta nunawa Haruna tsantsar kaidi da makirci irin na 'ya mace.

Amal ta dake tace  "Idan ma yana nufin sona yake, gaskiya ni bazan auri tsoho kamarshi ba, amma in dai zan fizgi rabona a jikinsa ai shikenan, zan iya biye masa nima in tatsi arziki som raina, Amma dan Allah ki temakamin da ruwan zafi mana, zan gasa jikina, dan duk ciwo yake min"

Ramlah ta jinjina kai, taje samo mata ruwa me zafi ta rakata banɗaki, da ƙyar ta iya kintsa jikinta, saboda karayar hannunta, ga ciwo da kanta keyi, haka ta tsaya tai kuka me isarta a toilet sannan ta fito.

Saleh ya jigata sosai, Alhaji Bukar yaje yaga halin da Saleh yake ciki seda ya ɗan tsorata, dan kar Saleh ya mutu, dan muddin Saleh ya mutu shikenan, abubuwa sun lalace, dan haka yasa aka kira likitansa, ya duba shi yai masa allaurai ya samasa ruwa, da ƙyar Saleh ya farfaɗo koda ya farfaɗo ruwan leda ɗayane se garau garau na shinkafa da aka kawo masa, mutumin daya kwana uku babu abinci, amma ya faraka a bashi bushshsiyar shinkafa da wake, abunka da me jin yunwa ya kama Abincin nan ya dinga turawa, sedai ba'aje ko ina ba yaji kamar yana cin duwatsu ne, dan haka ya dinga aman abincin nan, Saleh ya galabaita sosy, dan kwanakin nan gaba ɗaya a ɗaure yake a igiya kamar rago, dan haka kowace gaɓa tasa ciwo take masa, ga shedar igiya ta fito raɗa raɗa a jikinsa duk fatarsa tayi jajawur, ga ciwon ƙirji saboda dukan da yake sha da katako kamar Ɓarawo.

Bukar ya kalli Saleh yace "wuya koda magani ba daɗi, ina fatan zuwa yanzu ka ɗanɗana kuɗarka kuma zaka bani haɗin kai, ka gayamin abunda na buƙata, ko kuma in sa a ninka maka wannan azabtarwar da ake maka.

Shiru Saleh yayi beyi magana ba, se suka numfashi dayake na wahala, yayi zuru zuri dashi kamar wanda yayi amai da gudawa, maganar duniya Amma Saleh yaƙi cewa uffan.

Me Adda yace "wai ba zakayi magana ba, semun ƙarasa sauke maka allon ƙirjinka?"

Bukar yace "saurara tukuna, wannan idan aka yi ƙwaƙwaran yunƙuri ze iya mutuwa, kuma idan ya mutu ze jamin gagarumar asarane a yanzu haka, dan haka ƙyaleshi tukuna, zuwa anjima idan be faɗa ba, a kamashi kusamin kansa a ƙasa, ƙafafunsa a sama a samo ruwan zafi ku saɓulemin fatarsa dashi, ku barshi anan gurin "

Saleh yabi Bukar da kallo, yana jinjina mugunta da zalunci irin na Bukar, haka Alhaji Bukar ya fice ya barshi a hannun su me Adda yayi tafiyarsa.

Akayiwa Amal aiki a hannunta, aiki yayi kyau an É—orata, mutane nata tururwar zuwa dubata a Asibiti, kullum a can Hajiya Halima take kwana, kwana uku da yin É—orin likita ya sallameta, yace su dinga zuwa duk bayan sati biyu ana dubawa harya gama warkewa gaba É—aya.

Aka basu magunguna da sauran abun buƙata suka tafi gida, ma'aikatan gidan su Nura su Murtalah duk suka shiga suka dubata, suna fitowa Nura yace  "Allah ya ƙara, Allah yasa karta warke da wuri hannunma ya ruɓe, jakar matar nan da yake 'yarta ce ta samu matsala, ji yadda ta dinga zarya a Asibiti, amma lokacin da megida yana kwance a Asibiti, sefa ta ga dama take zuwa, ɗantane kawai yaita wahalar jinya, shiba ubansa ba ba komai ba"

Isa yace "karkiya wa Amal wannan muguwar addu'ar, da dai waccan me ƙaton bakin ce Ramlah, ai gara Amal sau dubu da Ramla, dukda itama Amal ɗin ta iya rashin mutunci"

Murtalah dake gefe yace  "hakane kam, Allah sarki, Allah ne kaɗai yasan inda megida yake, kaga kaman ma sum rufe babinsa, basa neman inda yake Yusuf kawai suke nema"

Nura yace "Allah sarki, wallahi tsayinsa nakeji, koba komai ba ruwansa wallahi"

Isa yace "kai dai bari, aiko ni da nake jin haushinsa da addua nake masa yanzu, na dinga duba yadda wasu abubuwan suk dinga faruwa amma baya magana, nan ze zauna in ta gayamasa baƙaƙen magana amma ko kallo bam isheshi ba, ima dana sanin wasu abubuwan da nayi masa wallahi "

Nura yace " nima inayi, amma ka fini zaƙewa sosai, kaga nifa da ace wani ne wallahi ko dagaske sace yarinyar nan yayi, wallahi sena hana a kama shi, yasha wahalrta sosai wallahi, ta gara shi san ranta "

Isa yace " Ai wannan akwai sa'a, duk garawar da take masa basu rabu ba, ya dinga mata biyayya, nifa wallahi ban yadda shiya sace ta ba, makirci ne kawai "

Murtalah yace " makairci kamar yaya kenan? "

"Nan Hajiya ta kirani falonta tace min, duk yadda zanyi inyi in nemo mata inda adireshin gidansu Yusuf yake, nayi nayi ya gayamin yaƙi, in ba makirci na Meza tayi da adireshin sa, kuma kun san wani abu, babu ma'aikacin da ake ɗagawa ƙafa a gidan nan kamarsa saboda 'yar masu gida"

Murtalah yace "ƙwarai kuwa, dan ba ƙaramin ci musu mutunci take ba saboda shi, amma dagaske an saka nemo inda yake?"

Isa yace "wallahi dagaske nake, sedai sam kamar yasan an sani fafur yaƙi gayamin, shegen wayone dashi kamar dila"

Nura yace "ba É—an sanda bane, kai ka isa ka masa wayo nan da nan, ai kaima kasan baka isa ba"

Isa yace "kamar ya É—an sanda wai?"

"Au kai a labaran da aka sanar ba gani bane, to É—an sandan farin kaya ne, aikin bincike yake a gidan nan"

Isa yace "la'ilahaillalah illalah, dagaske? Yo aini ban sani ba"

Murtalah yace "to an barka a baya, baka san kanun Labaran ba kam, É—an sanda ne ai shiyasa hankalin mutan gidan ya sake tashi"

Isa yace  "tir ƙashi, amma wannan anyi munafuki, shine be taɓa gayamana ba, muka zauma dashi muyi ta sakin baki"

Nura yace "to mutan gidan ma basu sani ba, balle kai ance maka jami'in sirrine kawai seya zo ya fara gayamaka ai shi É—ansanda ne? Saboda be san aikinsa ba kobe san ciwon kansa ba? Kai dai Isa naga ranar sa zaka waye"

Haka suka cigaba da surutansu dai.

Ita kam Amal ta tsunduma a kogin tunanin me yakamata tayiwa Alhaji Haruna ta huce, da wani makami yakamata ta yaƙeshi ta ɗau fansar budurcinta daya rabata dashi? Sam ta kasa ko da cin Abinci, se uban tunani da koke koke, idan ta kulle kanta a ɗaki se tayi me isar ta, dan sam bata san me yakamata tayi masa bama, ta gama barazanar da zata yi masa amma bata san meye zata yi masan ba ta huce, gashi ta kasa gayawa kowa wannan labarin balle ta samu shawara, gani take zata tinawa kanta asiri ne a banza a wofi, tazo ta kasa samun mafita kuma, ta kalli hannunta dake nan naɗe da bandeji ga goshinta ma, ta lumshe idanunta tana jin zafi a zuciyarta.

Ramlah ta shigo ɗakin tace  "Amal kizo ga matan Alhaji Harun nan sunzo dubaki"

Kallon Ramlah tayi kamar bata gane me tace ba, Ramlah tace "ko bakiji bane?"

Amal tace "Ai abunne naji wani iri, sun sanni ne daza suzo dubani?

Ramlah tace "oho muku, sun san Mummy ai, idan ke basu sanki ba"

Amal tayi tsaki tace "ba inda zani"

Ramlah tace "meyasa?"

"haka kawai, bazan zo ba, ki koma ki san abunda zaki gaya musu"

Tai maganar tare da kwanciya, Ramlah ta ɗan taɓe baki ta juya ta fice.

Amal ta sake jinjina rashin kunya, da iskanci irin na Alhaji Haruna, saboda ya gawurta har matansa ya turo su dubata, to suce mata me? Ji tayi kamar taje ta tona masa Asiri a gurinsu, amma meye shedarta? Taja tsaki tai shiru tana ci gaba da tunani.

Kamar wadda aka mintsina ta miƙe da sauri, dan seda ta kusa fama hannunta, ta tako a hankali ta fito, a hanya suka haɗu da Mummy, dan Ramlah ta gaya mata saƙon Amal, Mummy tace  "da meyasa kikace bazaki fito ba?"
Chapter 77 · 0% Book details