← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 127

Sashe 59

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To ko duk 'yan sanda zasu lalace, amma kai ka tsaya kai da fata akan gaskiya idan wasu basu yi nasara ba, wasu zasu samu sassauci a sanadin ka, dan haka' yan sanda ba 'yan rashawa bane kaji Masoyina"

Jidda tace "Abba, ko kunya ba kaji kake cewa É—an fari masoyinka ko? Allah yasa tsofaffi su jika, kasha zazzaga"

Bashir yace "sedai suyi su gaji, amma ina son masoyin nan nawa, inajinsa a zuciyata, idan na kalle shi ina samun farinciki da nutsuwa, nasan ko bayan raina akwai amfanin da zewa al'umma, É—an waliyin Allah me halin sufaye"

Jidda tace "ina ganin ikon Allah, kabari a faÉ—a mana kawai kasa shi a gaba kana ta koÉ—ashi, Taso muje in maka addu'a in kwantar da kai"

Bashir yace "ke yanzu me kike inba shagwaɓashi ba, baccin ma sekin kaishi, ƙyalemin yarona ya gama jin ɗumina tukuna"

"Ka maida shi ciki mana ƙarewar soyayya"

Sukayi dariya gaba É—aya.

Yusuf yace "Abbana É—an aljanna, ina sonka da kai da Umman Yusuf, Allah yasa ku a Aljanna"

"Ameen ya Allah, É—a É—aya tamkar da goma"

Suka cigaba da hirarsu cikin so da ƙaunar juna, can Yusuf yayi shiru yana tunani, Bashir yace "ɗan waliyin Allah, me kake tunani ne? Kowani abun akayi maka da kuka fita, gayamin ko waye inci ƙaniyarsa"

"Abba meyasa ka É—akkoni daga gidan marayu? .......

LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV

https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

100_101

Tsit sukayi gaba É—aya suka shiga kallon kallo ita da Bashir, Bashir yace

  "Yusuf, waye yace maka a gidan marayu kake? Wani mara hankalin me ya faɗi haka?"

Yusuf yace "Yaya Asma'au naji tana faÉ—a, Mamansu Amira, kuma rannan dana tambaya ance mana a makaranta wanda suke gidan marayu basu da iyaye, tsintarsu akayi an jefar dasu"

Bashir a fusace yace  "ƙarya take yi kaji ko, ba wani gidan marayu da aka ɗakkoka, ƙarya take nina haifeka"

Jidda tace  "Abba ya zakace masa ƙarya take, babba ce fa ba haka yakamata ka faɗa ba, tunda yarone bekamata kace masa babba kamar wannan tana ƙaryaba, ka gaya masa wani abun dai"

Bashir yace  "idan bance ƙarya take ba me zance? Ko so kike a sawa ɗana wani tunani na daban a zuciyarsa, nina haifi ɗana duk wadda ta kuma gayamaka haka kace Nine nan babanka, in ba haka su gayamaka gidan marayun dana ɗakko ka, kuma duk wanda ya kuma gayamaka haka kazo ka sameni ka gayamin, kaga yadda zan da mutum"

Ran Bashir ya ɓaci sosai ya dinga faɗa yana mita, dan ba ƙaramin jin haushi yayi ba, abun yana damunsa yadda ake aibata masa yaro, yaron da yake jin sonsa a cikin jikinsa

Bashir yace  "Ke yanzu a gabanki ake gayawa ɗana haka, amma ba kice komai ba, kuma ni baki gayamin ba balle in ɗau mataki, ɗana me haƙuri da hazaƙa amma a fara cusa masa tunani da ƙuruciyarsa, bazan lamunta ba Wallahi tabbas duk wanda ya kuma wannan gangancin zanyi maganinsa"

Ya tashi Fuuu ya É—au Yusuf, ya kai shi É—akinsa ya kwantar da shi, ya zauna yaita masa addu'a yana shafa kansa me É—auke da tarin suma me kyau, har bacci ya kwashi Yusuf, dukda zuciyarsa na cike da zullumi da tunani iri a kan maganganun da mutane ke gayamasa.

Haka Rayuwa ta cigaba da gudana, Yusuf yana cikin gata da jin daɗi dai dai ɗan talaka me rufin Asiri, Yusuf akwai tsanani biyayya da haƙuri, gashi tun yana yaro yana da ilimi sosai, gashi mahaddacin Al'qur'ani ne.

Bashir ɗan Sanda ne nagari, mutane sukance masa cinnaka ba ka san na gida ba, ko suce masa murmushin talaka, saboda gaskiya da riƙon Amanarsa, komarli kuɗinka da Arzikinka baze saurara maka ba idan baka da gaskiya, sannan umarni in dai na san zuciya ne, ba daga sama ba koda gurin uban waye baze karɓi umarnin san zuciya ba, aikinsa kawai yake bilhaƙƙi, ba son zuciya da cin Amanar ƙasa,shiyasa talakawa ke masa addu'a suke ƙaunarsa.

Shekarar Yusuf tara a duniya, Babansa Bashir akayi masa kiran gaggawa yayi tafiya Lagos a hanya 'yan fashi suka kashe shi, shi da uban gidansa.

Umman Yusuf da Yusuf sunji mutuwar nan, sun kaɗu dajin mutuwar nan, sunyi kuka, sunyi kuka dan sunsan sunyi rashin babban bangon jingina, Bashir mutum ne nagari, dukda ɗan takun saƙar dake tsakaninsa da maƙotansa akan Yusuf, amma sunji mutuwarsa, mutum ne me barkwanci da raha, ga kyauta da girmama mutane, mafi akasari in kaga anyi faɗa dashi to haƙƙin wani za'a take, shi be fiye daɗa akan kansa dan an masa wani abuba, sedai in an taɓa Yusuf ko Jidda, ko an danne haƙƙin wani, dan haka da talakawa masoyansa, da iyalansa da jama'ar unguwa sunji mutuwarsa sosai, hatta su kansu rundunar tsaron sun san sunyi rashin ma'aikaci.

Bayan an gama zaman makoki maƙota suka farayi da Jidda, wai saga yadda zata yi, ta miƙe ƙafa komai sedai miji yayi mata, hatta slifas na tsakar gida Bashir be yadda ta siya ba shiyake siyan komai, yanzu tunda ya mutu a ga yadda zata yi, gata ga yaron da ba'a san wace tayi cikin shege ta yar ba, sukaje suka ɗakko, yanzu ai taje ta maida ɗan da suka ɗakko ai.

Jidda bata da matemaki se Allah, rayuwa ta fara musu zafi, saboda bata da hanyar samun kuÉ—i, ta fara tunanin sana'ar da zata yi danta samu suci Abinci, kar É—anta yasha wahalar rayuwa.

Manyan 'yan sanda suka shiga yi mata romon baka, akan cewar zasu shiga su fita a samu haƙƙinsa ya fita, duk da jajircewar Bashir da wahalar da yayiwa Ƙasa, babu wanda ya kuma bi ta kan iyalansa, haka Umman Yusuf ta shiga faɗi tashin yadda zata yi domin ganin basu tagayyara ba, amma abun mamakin, komai ta kasa na siyarwa se maƙotanta suƙi siya, ko kuma su karɓe bashi su barta, sunaji suna gani haka ta cire Yusuf daga makarantar kuɗi ta maida shi ta gwamnati, dama ya gama primary secondary ze shiga, wasu lokutan har Abinci ma se tayi fama sannan suke iyaci, mutanen da Bashir ya dinga tallafawa babu wanda ya kuma bi takansu, dama ba'a batun danginsa tunda ba ƙaunarsu suke ba, haka Umman Yusuf ta samu Nanny a wata makaranta da ƙyar, ta kaɗa ta raya su ɗauketa aiki, tana da diploma amma suka ƙi, waisu masu degree suke ɗauka, sedai su bata Nanny, haka ta karɓi aikin Nanny take yi, tana zama ta zubda hawaye idan ta tuna Bashir, wata wahalar duk bata santa ba se daga baya, dama 'yan uwanta duk kusan matane, kuma uba ɗaya suke ba uwa ɗaya ba, kuma mahaifim nasu ya rasu, gashi dama suma duk fama suke da kansu, talakawa suke Aure, dama ita suke raɓa su samu wani abun, shima suna yi suna mata hassadar tana auren me rufin Asiri, tunda aka gama zaman makoki babu wanda ya sake ya waiwayarta.

A hakan ana wannan faman, amma Umman Yusuf bata yadda Yusuf ya fita da mummunar kama ba, ko yayi mummunar cima ba, ta yadda ta zauna da yunwa, Yusuf yaci.

Ga aikin Nanny ɗin nan babu wata riba, se zunzurutun wahala, ga wulaƙanci daga malamai, yaran da iyayen su dukda wannan ƙoƙarin da take yi ba'a gani.

Yusuf idan yaga tayi shiru se yace "Ummana kiyi haƙuri kinji, nima bana son wannan aikin da kikeyi, nima zan duba sana'ar da zan iya in dinga temaka miki, ki bar wannan aikin"

Umman Yusuf tace  "A'a ban yadda ba, yarone kai ƙarami kamata yayi ka maida hankali akan karatunka, idan kasan daɗin kuɗi bazaka maida hankali ba"

Fafur ta hana shi neman kuɗi, idan bashi da littafi yana son ya siya baze tambayeta ba, sedai ɗan ashirin ɗin motar da take bashi, da kuɗin break ɗinsa haka ze tafiyar ƙafa, dan ya rage ya siya, karya tambayeta yasan bata dashi, dubu goman da'ake bata na aikin bata zuwa ko ina.

Watarana Ummansa ta tashi babu lafiya, kusan sati biyu ba taje makaranta ba, gashi babu kuɗin magani, ko zuwa Asibiti tana ta fama da Asma, dan haka bata sani ba Yusuf yaje gidan Yayan Bashir, Ɗanlami yaje ya gaya masa amma yayi masa kaca kaca ya kore shi, yace baze taimaka musu ba, bayan zagi da cin mutunci da yayiwa Yusuf da gorin aishi ba ɗan ɗanuwansu bane, tun daga nan Yusuf ya ƙuduri aniyar kome ze samesu, baze ƙara neman taimako a gurin wani ba.

Haka Yusuf ya samu guri a hanya ya zauna yayi kuka, yayi kuka yai me isarsa sannan ya koma gida haka ya zuba ido, Jidda tasha jiki ta rame tayi wani iri, tana ɗanji sauƙi ta koma makaranta suka bata dubu huɗu, suka ce sun koreta, dukda sun san bata da lafiya, haka suka koma gida suka tsuguna, Umman Yusuf ta rasa inda zata saka ranta, ga larura ga babu ta musu katutu, kuɗin da aka bata dubu huɗun nan baze sai musu ishashsen Abinci ba, balle ta sai magani, maƙota babu me taimakonta dako ƙwayar hatsi, sedai in ta fito aita mata habaici ana yada mata magana.
Chapter 59 · 0% Book details