← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 127

Sashe 5

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma inaga dole mu koma kan shawarata ta farko, na yakamata mu raba ɗaki, kinga ni ba waliyyi bane mutum ne kamar kowa, idan muna tare a guri ɗaya akwai matsala, ina gudun wani abu yazo ya faru, kinga na fara gazawa gurin riƙe Alƙawarin yarjejeniyar dake tsakaninmu"

"wallahi bazan kwana a É—akin nan nikaÉ—ai ba, duk inda zaka je sena bika"

"to idan na kuma kissing É—inki kika haÉ—emin rai se nayi abunda yafi haka, kina bani ciwon kai Widad, komai nayi laifi ne a gurinki, ki dinga sassauta min mana, a dinga jin tausayina"

Kwanciya tayi ta juya masa baya, shima kuwa ya kwanta a bayanta, banza tayi masa taƙi magana, ta lumshe ido da nufin tayi bacci, a kunnenta ya dinga raɗa mata  

"I love you My Queen, ina sonki Widad, and I mean it from the bottom of my heart, i love you"

Cike da ƙosawa Widad tace "Naji amma dan Allah ka ƙyaleni inyi bacci"

"to ba kice komai ba, kin haƙura kin dena fushin?"

"eh na haƙura jeka"

"kora ta fa kike Queen"

"Niba korarka nayi ba, bacci nake ji"

Yusuf yace "shikenan, Asuba tagari masoyiyya"

"kaika santa"

Yai murmushi ya koma kan shimfiÉ—arsa.

Ana ta shirye shirye za'a kai su Anwar kotu domin fara sauraren ƙararsu, akan tuhumarsu da'ake da haɗa baki gurin sace Daula, Anwar ya duƙufa sosai da Addu'oi babu dare babu rana.

Yana zaune da safe wani ɗan sanda yazo ya buɗeshi, aka tasa ƙeyarsa zuwa wani guri, wannan mutumin dai daya zo ya kuma gani, aka bawa Anwar kayansa da aka karɓa.

Mutumin ya miƙawa Anwar hannu suka gaisa yace "masha Allah, you are free now malam Anwar, muje in ajiyeka a gida"

Cikin mamaki Anwar ya kalle shi yace "i am free as how? An game bani da laifi kenan?"

"eh baka da laifi, muje"

Kamar soko haka Anwar yabi mutumin, kuma ya kasa tambayar sa waye shi, ya kai shi restaurant yaci Abinci sannan ya wuce ya kai shi har ƙofar gida.

Mutumin ya kalli Anwar yace "Anwar ina maka fatan Alkhairi, ina maka murnar fitowa da kayi da kuma tsallake tarkon azzalumai, seka kula Allah ya kiyaye gaba"

Anwar yace "sedai ni tunda kake zuwa gurina ban gane ka ba"

Mutumin yace "nasan baka sanni ba, kuma bazaka ganeni ba, sedai nima aikoni akayi ba'a bani umarnin sanar da kai wayeni ba, babu buƙatar hakan Daula yana tare da ubangida na, shiyasa aka ɗauke shi a Asibiti, yana gurinsa dan haka ka kwantar da hankalinka"

A firgice Anwar yace "dan Allah waye uban gidan naka? Daula bashi da lafiya, yana buƙatar kulawar likita"

"É—an samari kai dai ba Ruwanka, koma a wani hali yake ciki tunda dai kai ka fita, maza jeka zan tafi"

Jiki a sanyaye Anwar ya sauka, yana bin motar da kallo kamar wani soko, har motar ta bara layin.

Gate ɗin gjdansu ya nufa, ya ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin, Isa ne yazo ua buɗe ƙaramar ƙofar, yana ganin Anwar ya shiga mutstsuka ido ko gizo yake masa, Isa yace

"Kamar Yallaɓai Anwar nake gani"

Anwar yace  "eh nine Malam Isa"

Buɗe masa ƙofar yayi ya shigo, Isa yace "Yallaɓai an sakoka kenan?"

Anwar yace  "Alhamdilillah Isa an sakoni" nan ma'aikatan suka dinga murna suna taya shi farinciki.

Cikin gidan ya ƙarasa, yana shiga ya tarar babu kowa a falo, ɗakin mahaifiyarsa ya nufa, yasa hannu ya murɗa ƙofar ɗakin yayi Sallama, da sauri ta waigo dan mamar Muryar Anwar taji, aikuwa ba kama bane shi ɗinne, ai da hanzari ta miƙe, ta nufe shi da sauri 

"Anwar kaine? Garin yaya, ya akayi aka sake ka?"

Rungume ta yayi yace "Mummy ki bari in huta se in gaya miki, duk kin rame Mummy na"
Kuka ta saka tace "ba dole ba Anwar, baka nan na rasa me kemin daɗi, nasan zaman gurin nan sam ba daɗi yake maka ba, nayi zarya harna gaji anƙi a sakeka, ko Abinci bana iya ci, bana baccin kirki"

"shikenan, is over now, ai gani na dawo Alhamdilillah"

Suna nan zaune sega su Amal, dan ta manta ma bata sanar dasu dawowar Anwar ba, nan suka dinga murna suna farinciki da dawowar Anwar, aka shiga yi masa girki, yai wanka ya huta dan ko ina na jikinsa tsami yake masa saboda wahala.

Mummy tace "nikam ka gayamin, ya aka yi aka sako kame?"

Anwar yace  "wallahi Mummy ikon Allah kawai, ina zaune akace in fito, wani mutum ya ɗakkoni a motarsa yace bani da laifin komai, ya kawoni har gida ya tafi"

ÆŠan yatsine fuska tayi tace "meye haka sekace wata almara?"

"Wallahi Mummy dagaske nake miki, kiyi waya ki tambaya kiji"

"ikon Allah ko wane mutumi ne wannan oho? Ta be gaya maka waye shi ba?"

"nayi nayi ya gayamin, amma yaƙi sam, be gayamin ko waye shi ba"

Amal tace "Mummy koma dai waye, tunda Allah yasa an sako mana shi ai shikenan, mu dama fatanmu ka dawo gida"

Mummy tace  "Amma da mamaki, ina mamakin waye haka? Dan na san ba'a cikin waɗan cam tsinannun bane marasa imani"

Anwar yace "Mummy suwaye kenan kkke zagi haka?"

Da sauri ta wayence tace  "A'a karka damu, 'yan sanda nake nufi, ba irin zaryar da banyi ba amma suka ƙi bani belinka"

"Allah sarki, ai Abincin su suke karewa suma Mummy, bekamata ki tsine musu ba"

Mummy tace "hakane kam, na dena tsinemusu tunda nidai É—ana ya fito"

Yau Widad har takwas na safe bata tashi ba, tunda tayi sallar Asuba, Yusuf yaje kan shimfiɗarta ya riƙe hannunta a nasa yana ɗan matsawa yace  "My heart, ki tashi baccin ya isa haka, ki tashi kici Abinci"

Motsawa tayi a hankali tayi juyi tace "kaci Abincinka, ni bacci nake ji"

"A'a ni gaskiya bazan iya cin Abincin babu ke ba, ki tashi please"

Shiru tayi ta sake lumshe ido, "zanyi miki abunda bakya so yanzun nan fa"

Murmushi tayi tace "banyi brush ba dai" ta ƙarasa tana dariya, Yusuf yace "aini bana ƙyamar ki, kece kike ƙyamata komai naki ni so nake"

Widad tace "naji, É—akkomin brush É—in inje in wanke baki"

Ya duba inda take ajiyewa, ya É—akko ya bata, tana zaune akan katifar bata tashi ba, Yusuf yace "ya dai? Ko sena É—auke kine?"

Jinjina masa kai tayi alamar eh, aikuwa ya ƙaraso ya ɗauketa cak, dariya take tace "ajiyeni tun kan Baba Hari tamin ba'a ko ace na aikata wani babbam zunubi a koreni daga garin nan"

A tare suka kwashe da dariya, Yusuf yana kallonta cike da farinciki.

Tayi waje, taje tai brush ta dawo suka fara cin É—umamen tuwo.

Yusuf kallonta yake, da alama tana cikin nishaɗi, yanzu ne lokacin da ya dace ya gaya mata abunda yake son gaya mata, yai shiru yana saƙe saƙen yadda ze ɓullo da zancen yaji tace

"Me kake son gayamin ne da yake razanaka har yanzu ka kasa gayamin? Ka gayamin kawai ina saurarenka"

Littafin kuÉ—i, dan Allah a biya kafin a karanta badanniba dan girman Allah
A tuntuɓeni ta wannan lambar
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 50_51

NA KUƊI NE, BOOK 1 NE FREE, DAN ALLAH A BIYA KAFIN A KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH 🙏🙏🙏

gaba É—aya Yusuf ya É—an ruÉ—e yace "ba wani abu da nake son gayamiki ba fa, kece kike ganin kamar ina son in faÉ—i wani abu ne"

Murmushi tayi tace "Hmm Yoseef kenan, a ɗan zaman da nayi da kai daga lokacin da ka fara min aiki, na fuskanci halayenka da yawa, koba haka ba ina iya karantar abunda ke ran mutum ta hanyar fuskarsa, bana son ƙarya, karka ji wani abu, babu abunda zan maka, se abunda Allah yayi nufin ya faru da kai"

Yusuf yace "dama ina son in gaya miki yau nake son na cigaba da fitane, ina son in sai mana wasu abubuwan na buƙatunmu, wasu abubuwan duk sun ƙare"

Widad tace "Yaushe ka warke da har zaka fara zancen fita? Se kaje ka kuma haɗuwa da wata rashin lafiyar ko? toni babu ruwana, tunda dai ban takura maka nace seka saimin abunda baka dashi ba, ka ƙyaleni komai aka bani zanci, in wanda zan iya cine se inci, in bazan iya ciba kuma se in haƙura kawai"

Sosai ta bawa Yusuf tausayi jin abunda ta faɗa, Yusuf yace " duk da haka Yakamata ace nima ina taɓuka wani abun da kaina, in sauke haƙƙinki da yake kaina, in sai miki abubuwan da kike buƙata koba duka ba"

"Shikenan, amma nidai bance kayi abunda zaka cutu ba koka wahala ba, ka kula da lafiyarka"

Yusuf ya gama shirinsa tsaf ze fita, Saleh ya shigo gidan ya kalli Yusuf yace "Ahh Yusuf ina zuwa haka? '

" zani cin kasuwane Saleh " Yusuf ya bashi amsa

Saleh yace " Haba Yusuf, kasan fa baka da lafiya sosai "

Yusuf yace " shima zaman guri É—ayan babu daÉ—i Saleh "

Harice take a tsugune tana ta tattara ƙwan da kazarta tayi zata bayar akai kasuwa, Yusuf yace " Baba Hari, wannan ƙwan na siyarwa ne?"

Hari tace " Eh za'a akaimin kasuwane"

Yusuf yace "Masha Allah, inba damuwa a zuba na kaji biyar na zabi biyar, a kaiwa Queen idan na dawo insha Allah zan bada kuÉ—in"

Hari tace "meye kuma Kun?"

Yusuf yayi murmushi yace "A kaiwa Widad nake nufi"

"Awo sekace min Wudas, amma kun ai bazan gane ba idan kace haka"

Saleh yace "Hari baki abun magana, Queen yace ba kun ba, yana nufin sarauniya"

Kwaɓe baki tayi tace "Wace sarauniyar? Sarauniyar fitsararru ba"

Yusuf yace "Ayi haƙuri"

Hari tace "dan dai kaine, kuma ina jin kunyar ka, amma da ita zata siya bazan sayar mata da ƙwan nan ba"

Yusuf yayi dariya yace "ayi haƙuri, A temaka mana"

Saleh yace  "kedai kinji kunya, ki rasa da wadda zaki dinga faɗa se wannan Yarinyar"

Widad ta ƙaraso inda suke da kwanukan wanke wankenta a hannu tace
"Idanma baki siyar dan Allah ba, zan buɗe gurin ƙwan ne in kwashi san raina, ko in kama kajin naki in yanka in soye muci nida Yusuf tunda bashi da lafiya dama"

Dariya suka yi, Saleh ya dinga mamaki, dama Widad ta iya magana haka hadda tsokana?
Chapter 5 · 0% Book details