← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 127

Sashe 116

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya juya ya shiga É—akinsa, yana zuwa ya ajiye kayan ya zauna ya dafe kansa yace "ua zanyi da umarnin Ummana, matar da ta dimga É—awainiya dani tun a zanin goyo harna zama mutum, bani da uwar data fita, sannan ya zanyi da matatat wadda a yanzu haka nauyin kula da ita a kaina yake, haba Umma ki fuskanceni mana"

Yai maganar yana sake dafe kansa dake sara masa.

Nurat kuwa har sukaje gida, bata ce komai ba, juyin duniya Khalil yai yai ta gaya masa abunda ke faruwa amma fafur taƙi, suna zuwa gida ta shige ɗakinta ta rufe ƙofa ta shiga aikin kuka, tana jin yadda soyayyar Yusuf ke ƙafa tsuma mata zuciya, tana shiga dukkan wani sashe na jikinta, amma tasan ssamun Yusuf idan ba wani iko na Allah ba, abune da baze taɓa yuwuwa ba, ya riga ya mata nisa tunda ya zama miji ga Widad, ko ba'a gayamata ba Tasan Widad bazata zauna da kishiya ba, kishiyarma ita wadda mahaifinta ke da Mummunan tabo a gurin Widad ɗin.
  Khalil duk ya shiga damuwa ganin Halin da Nurat ke ciki, a nan falo mahaifiyarsa ta fito ta sameshi tace  "Khalil har kun dawo ne? Ina Autar tawa take ne?"
Khalil yace "Ta shiga É—akinta"
Tace "yaya, da kuka fitan ta ɗam saki jikinta kuwa? Na fuskanci har yanzu Nurat tana cikin damuwa da alhini, bana son rashin walwalrata, gashi ni bani da 'ya mace balle ta samu' yar uwa, ni kuma ba son yawan hira take dani ba, na rasa ya zanyi, Abbanku ma ya faramin magana akan rashin walwalarta wai kowani abu nake mata? Nace masa ya za'ayi in takuramata tana 'yar ƙanwata? "

Khalil yai ajiyar zuciya yace " Mama akwai abunda yake damunta, kuma baze rasa nasaba da halin data tsinci kanta a ciki ba, dole se an bita  a hankali "

Mama tace " to shikenan, naga kai taku tazo É—aya sosai, dan Allah ka dinga kwantar mata da hankali, kana rarrashinta"

"to Mama Insha Allah, bari in shiga inyi alwala magariba tayi '

Ya tashi ya baf falon, uana jin inama ze iya É—aukewa Nurat damuwar da take ciki.

Widad kam tasha kuka data koma gida, taji ta tsani Nurat bata ƙaunarta sam, ta barwa ranta sedai ayi duk wadda za' ayi, amma bazata bari Yusuf ya auri Nurat ba.

Yusuf ya fita yai sallar magariba ya kai É—inkin kayansa, ya dawo yana daf da shiga gida wani yai masa sallama, ya tsaya ya amsa suka gaisa.

Mutumin yace "matarka ce ta aikoni, tace ga wannan in baka"

Yusuf ya karɓi ledar daya bashi, mutumin ya tafi, Yusuf ya shiga gida ya wuce ɗakinsa, yana zuwa ya buɗe ledar, sabuwar wayace kar a ciki da layi, tai rubutu a jikin kwalin wayar"

"switch on the phone, and call me Baby, Your wife"

Murmushi yayi cikin rawar jiki ya kunna wayar, ya duba yaga lamba ɗayace a ciki, maimakon ya kirata da wayar, seya kwafa a ƙaramar wayar dake hannunsa ya kirata.

Tana kwance akan gado, tayi rigingine wayar ta fara ringing, ai da sauri ta É—akko wayar ta É—aga.

"Hello My Queen"

"meyasa baka kirani da layin dana baka ba?"

"so kike Umma ta tambayeni ina na samo waya?"

"Shikenan, ya kake?"

Yace "lafiya ƙalau, ya ki kaje gida?"

Tai ajiyar zuciya sannan tace  "Alhamdilillah"

Yace  "Widad dan Allah kiyi haƙuri da abunda ya faru yau kin san"

"I understand, just forget sonake kawai muyi hira da kai, inji daÉ—i a raina, kaÉ—aici ya dameni ko Abinci bana iyaci Yoseef, ga bani da lafiya I need you Yoseef, i need your help"

Jiki a sanyaye Yusuf yace 'ki kwantar da hankalinki my wife, Insha Allah inaji a jikina komai ya kusa zuwa ƙarshe insha Allah, kiyi haƙuri karki cutarmin da kanki da Babyna, ki dinga cin Abinci please, karki mana illa "

" toni ya zanyi inci, babu me rarrashina ya bani a baki? Gashi bana samin irin Abincin da nake so, Yoseef dan Allah ka bawa Umma haƙuri ka dawo gare ni please "

" karki damu, Umma zata soki tana da sauƙin kai sosai, Insha Allah zam sam abunyi, amma dan Allah kici Abinci kinji Wudas ɗina "

" Wudas ko? " tai maganar a Shagwaɓe.

Yusuf yai dariya yace " ba haka Hari take ce miki ba? "

" to kai ita ne? Kasan meze faru kashe wayar, zanje inyi wanka video call nake son muyi in ganka "

Yace" shikenan, as you wish Babyna"

Yusuf ya rungume wayar nan.

Ko takan Abincin dare Yusuf bebi ba, Widad ta sake kiransa video call, ta saki dogon gashin nan nata, tana shafa mai.

Yusuf yace "Cikin nan ba ƙaramin kyau ya miki ba fa"

"Allah ne yayi cikin nan baze fita ba, amma allurar zubar da ciki Bulama yasa ayimin"

"cikin nawa aka so zubarwa?"

"Eh mana, sun kusa kasheni fa, akwai labari idan mun haÉ—u fa"

Yusuf yace "Allah sarki babyna, mun sha wuya sosai, ko da kikazo kotu kallo É—aya nai miki na gane ba'a kwanciyar hankali kike ba"

Widad tace  "bar wannan zancen kawai, kar ka ɓatamin rai ka rusa mana farinciki"

Yai murmushi yace  "to shikenan, kina min ƙwalele da gashin nan fa"

Tai murmushi tana masa gwalo ta waya, tace "ziro hannu ka taɓa mana"

"Inama in rufe idona in buÉ—e in ganni a kusa dake, in tayaki shafa man nan"

"Harka tunamin lokacin da muna ƙauye, gaskiya Yoseef kana da haƙuri kayi haƙuri dani sosai, shiyasa ka taka wani gagarumin matsayi a zuciyata my love"

Har tagama shirin kwanciya, ta kwanga video call suke, ba tare da sun sam dare yayi ba.

Ƙarfe biyu da rabi lokacin ne Umma take sallar dare, ta fita alwala ta dinga jin maganar Yusuf ƙasa ƙasa, ta leƙa tagarsa ta hangoshi akan gadonsa ya tasa screen ɗin waya a gaba yana murmushi.

"Ki kwantar da hankalinki, Insha Allah zuwa jibi zanzo in ganki masoyiyata"

"Allah ya kawo ka lafiya, zaman kaÉ—aici ya isheni Yoseef, babu kowa a kusa dani fa"

"Ai mace miki zanzo insha Allah, inzo in ganki inji labarin da kike son gayamin, inji yadda akayi kika samu wannan tabon haka a jikin ki, ki kwanta kiyi bacci dare yayi fa"

Tace  "ok come closer, hug me and kiss me, then we sleep together"

Yusuf yai murmushi yace  "nayi missing ɗinki Widad, yai kissing ɗin screen ɗin wayar yana lumshe ido, ƙarshe ya kashe wayar ya ajiye, ya rungume pillow sosai a jikinsa yana lumshe ido.

Umma ta jinjina kai ga wuce banÉ—aki domin yin alwala.

Da safe Yusuf ya tashi yana ta nishaÉ—i kamar bashi ba, Umma tana kallonsa amma ba tace masa komai ba.

Ranar da yayiwa Widad alƙawarin ze je yana ta kallon agogo, yana zaune Umma ta sashi a gaba yaci Abinci, ya gama ci wayarsa ta fara ringing, sedai ba suna amma yaƙi ɗagawa, Umma tana kallonsa.

Can yace  "Umma bari inje ɗaki zan kwanta bacci"

Umma tace  "ɗakko pillow ka kwanta a nan"

Ba haka yaso ba, amma haka nan ya haƙura, ya ɗakko pillow ya kwanta a ɗakin Umman.

Aikuwa babu daÉ—ewa bacci ya É—aukeshi, saboda dama dare yake rabawa yana soyayya.

Umma ta É—akko mafici tana masa fifita, Kasancewar an É—auke wuta gashi ya fara gumi.

Sedai tun ba'aje ko'ina ba Yusuf ya fara surutan bacci.

"My Wife, kiyi murmushi mana yarinya fushi baya miki kyau fa"

Umma ta juya tana kallonsa, iya saninta dashi tun yana yaro ƙarami, baya surutan bacci, amma yau da ranar Allah yana bacci yana surutu akan wata.

Bata gama mamakin ba ya cigaba

"Baby ki dena kuka, bana so fa, kinga baki da lafiya, kuma Gwaggo yau zata kawo mana kunun tsamiya, ai zaki sha ko?"

Suleiman ne yai sallama a gidan, Umma ta amsa masa, ya shigo ya zauna yana faɗin  "Lallai ɗan gata, yana bacci Umma na masa fifita, tashi c

Yai maganar yana taɓa Yusuf, Umma tace " ze tashi kuwa, yana mafarkin soyayya "

Suleiman yace " Soyayya kuma? "

" Eh mana, se surutai yake shikaÉ—ai"

Suleiman ya daddaki Yusuf, Yusuf ya buɗe ido a hankali, ya tashi zaune yace  "Yallaɓai dama kaine?"

"Eh nine, ka tashi ka shirya mutafi"

Yusuf yace "mutafi ina?"

Umma tace  "gidansu Nurat zaka je, Munyi waya da Khalil bata da lafiya!!!"

Wayat Yusuf ta shiga ringing, ya kalli wayar lambar Widad ce, tana can tana jiransa

AMANA! AMANA! AMANACE!!!
DUK WANDA YACI AMANA, AMANA ZATA CISHI

AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

158_159

Yusuf yace "Amma Umma, da wani guri nake son zuwa"

"zaka bijirewa umarnina ne?"

Yusuf ya girgiza kai, Umma tace "to tashi maza, jeka kintsa kazo ku tafi"

Jikin Yusuf babu daÉ—i, ransa sam ba daÉ—i yaje yai wanka ya shirya ya fito.

Umma tace "Suleiman, dan Allah ga Shi nan, ka tabattar yaje dan Allah ga kuÉ—i ku sai mata ko kayan marmari ne, aje a duba ta, gaida mai gaisheka ko baze amsa ba"

Yusuf dai bece komai ba yai waje, wayarsa na cigaba da ringing.

Suleiman ya fito ya shiga motar suka tafi, Umma ta maida Suleiman kamar É—anta Yaya a gurin Yusuf, dan shima tana masa hidima shida iyalinsa, tunda yaita faÉ—i tashi akan case É—in Yusuf.

Yusuf be kula Suleiman ba, gaba ɗaya ransa a ɓace yake, ya ɗakko wayarsa ya kira Widad, tana ɗagwa ta fara mita "Haba Yoseef, inata kiran wayarka kaƙi ɗagawa, na shirya ina ta jiranka fa"
Tai maganar cikin Shagwaɓa.

Yusuf yace "Am sorry, wata fitace ta gaggawa ta kama ni, amma idan na kammala zanzo insha Allah, ki kwantar da hankalin ki kinji my Wife"
Chapter 116 · 0% Book details