← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 127

Sashe 21

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya koma ya sameshi yace ya bashi jari, in Allah ya yarda ze alkinta, Amma Yusuf yace baze bashi suje su haÉ—u da sakarkarun abokansa su cinye ba se yayi hankali, haka yaita sintiri amma ya hana shi.

Da yaga hakan yaƙi seya koma ta gurin matar Yusuf wato Nadiya, watarana yaje ya sameta a falo, bayan sun gaisa yace  "Anty taimako nake nema fa"

Tace "temakon mefa?"

"Anty Yaya ya hanani Jari, nayi nayi amma yace se nayi hankali, dan Allah kisa baki, nasam yadda yake sonki da kince a bani ta zauna"

Nadiya tayi murmushi tace "ai kai lamarin naka ne se a hankali, se an baka kaje ku kewaye ku cinye kai da abokai, kamar baka da wayo"

"Nidai dan Allah kisa baki ya bani, Allah bazan ɓafnatar ba zan tattala"

Nadiya tace "shikenan, rashin sana'a ga matashi bata da daÉ—i, bari ya shigo gidan inga ya za'ayi"

Nasir yace "Yawwa Antyna ta kaina, Allah yasaka da alkhairi, ya kawo 'yan biyu sau biyu" (da yake tunda akayi auren bata samu rabo ba"

Tai murmushi ta ce "Ameen ya Allah Nasir, Allah yasa ya baka jarin nan, daga nan ka zama babbn done"

"Ameen Anty, bari in É—au carbi inta masa lazimi kafin ya dawo"

Tai dariya tace "idan ma be baka ba, ina sa ran a kawomin kuÉ—in gonata, se in baka"

Nasir yace  "zema bani insha Allah '

Suna cikin hirar ne sega Yusuf ya dawo, Yusuf yace  " Ashe kana nan, na biya ta can gidan in baka takalmin dana siyo maka amma baka nan"

Nasir yace "ai tun É—azi ina nan, gurinka nazo"

"Gurina kuma? To gani"

Nadiya tace  "ka zauna kaci Abinci tukuna, idan kaci se in gaya maka saƙon nasa"

Haka akayi, tare ma sukaci Abincin shida Nasir, bayan sun kammala Yusuf yace  "to Uwargida, ina jinki tunda naga kun haɗa kai, nasan wataƙila wani abu akeso na bayar ko inyi"

Dariya suka yi, Nadiya tace  "Yawwa ranka ya daɗe, kaga yanzu kamar Nasir ai bekamata ace seka sai masa takalmin sawa ba, kamata yayi ace duk wannan abubuwan shiyakewa kansa, dan haka yazo neman alfarma dan Allah a temaka masa da jari"

Yusuf yace "An hanashin baza'a bayar ba, in kuma bashi yake shida wancam yaron mara kunya su haɗu su cinye, gara ko meye yazo in sai masa, idan ya ƙara hankali se in bashi jarin"

Nasir yace  "dan Allah Yaya, Allah nayi hankali zan tattala"

Yusuf yace "Anƙi ɗin, ai tun rannan nace bazan sake baka ba"

Nadiya tace  "A dai yi haƙuri ranka ya daɗe, Insha Allah baze sake ba"

Yusuf yace "to naji, tunda haÉ—e mun kai zakuyi, naji zan bashi jari, amma rance zan bashi"

Nadiya tace "haba dai rance dan Allah"

"shikenan tunda bakwa so, ai bazan sake bashi kuÉ—i yaje yaci a banza ba, tunda besan zafinsu ba"

Nasir yace "Anty na yadda, Insha Allah zan dawo masa dasj, nidai a bani jarin"

Nadiya tace "dan Allah kace ya dawo maka da rabi, ya riƙe rabi mana"

Yusuf yace "Nifa in bakwaso kuÉ—ina sun huta, nasan abunda zanyi dasu"

Nadiya tace  "shikenan, munji mungode Yaushe za'a bamu?"

Yusuf yace "waini wace sana'ar ma zakiyi ne? Kuma nawa kake buƙata?"

Nasir yace "Yaya sarƙoƙi nake son in dinga siyarwa, zan kama shago a kasuwa sannan in zuba kayan, ance dubu ɗari biyar zasu isheni".

Zaro ido Yusuf yayi yace "dubu dari biyar? Kana da hankali kuwa?"

Nadiya tace "kana dasu fa, kafi ƙarfinsu dan Allah ka bashi"

"Gaskiya bazan bashi ba, zan dai bashi É—ari uku yaje ya nemi sauran, É—ari ukunma bashi"

Nadiya tace  "Nasir karka damu, idan aka kawomin kuɗina, kazo in baka sauran, inaji a jikina wannan sana'ar ds zaka fara itace silar arzikinka, ka zama hamshaƙin Attajiri, wanda ze tara Daula ta ban mamaki"

Nasir ya washe baki yace  "Allah yasa Antyna ta kaina, da duk sati sena kaiki Makka, shi kuwa yaya se shekara shekara zan dinga kai shi"

Yusuf yace "kar Allah yasa ka kainin, bana insha Allah zan tafi ai, kuma kema ban yadda ki bashi kuÉ—i kyauta ba, rance zaki bashi kuma tare zamu je da kaina a kama shagon"

Har zata yi magana, ya dakatar da ita, ya hanta magana, Nasir yaita godiya sannan ya tafi.

Bayan tafiyar sa Yusuf yace  "Nadiya, ina jin daɗin yadda kike nunawa ɗan uwana ƙauna kamar ɗan uwanki, ni kaina ina tunanin wace sana'a zan sama mishi, saboda nasan bayan raina babu wanda ze iya ɗawainiya dashi kamar yadda nakeyi, ba ƙinsa nake da nace rance na bashi ba, hakan ne zesa ya maida ya tattala abunda aka bashi "

Nadiya tace   " Shikenan tunda haka kace, Amma kana min kyautatawar dako nawa nakwa 'yan uwanka alheri dashi ban faɗi ba, amma tunda kace haka shikenan "

Bayan kwana bakwai, aka tattara kuɗi akaje aka kamawa Nasir shago, aka zuba kayan sarƙoƙi kala kala, Nasir ya maida kai sosai a tafi da shagon nan, duk yadda Bulama yaso a kassara shagon Nasir yaƙi, sedai wataran Bulama yazo ya taya shi zama koya yayi masa shara, shi kuma ya biya shi, amma a hakan Bulama yana taɓa ƙuruciyar ɓera wato sata.

Allah yasawa kasuwancin nasa albarka, nan da nan kasuwanci ya kankama, idan kuɗi suna nema su yanke masa idan ya zaga gurin Matar yayansa seta ƙara masa kuɗi, a hankali ya dinga sabawa da mutane, idan yaji labarin wani kasuwancin seya ɗibi kuɗi ya jarraba, shine ya buga nan ya buga can.

Wataran aci riba, wata ran a faɗi, Yusuf yana yi yana monitoring ɗin ƙanin nasa, idan ya tambayeshi yaushe zan dawo maka da kuɗin se yace 'ba yanzu ba, idan lokacin karɓa yayi zan karɓa'

Haka ya dinga faɗi tashi, da Nadiya ta ganshi seta fara tsokanarsa da seka gina Daula me ban mammaki babban don, a haka abokansa da maƙota suka fara kiransa da Daula kawai.

Ana nan wani hamshaƙin attajiri a kusa da gidan Yusuf, yaje ya auro wata balarabiya 'yar maroco, akayi shagali sosai' yan uwanta na can maroco suka zo Nigeria, akayi shagalin biki sosai.

Bayan wani lokaci balarabiyar nan ta haihu, aka kawo mata wata Yarinya a cikin danginta, ta zauna tare da ita saboda ta dinga tayata raino, kafin jaririn yayi ƙwari.

Nasir ya kan shiga gidan mutumin, da yake akwai babban ɗan mutumin me suna Ahmad a gidan, suna gaisawa sosai da Nasir, shi ya bashi shawarar fara sana'ar kayan sarƙoƙi na mata, dan haka Nasir yana shiga gidan sosai, dan ya saba da ita Amaryar wannan mutumin Islam wato balarabiyar maroco.

Duk lokacin da Nasir ya shiga gidan sukan haÉ—u da wannan balarabiyar Yarinyar me suna Huda 'yar uwar Islam , yana É—an jin larabci dan haka sukan gaisa, kokuma suyi magana da turanci.

Huda bata da saurin sabo, amma ta saba da Nasir, ko fita ba tayi amma Saboda Nasir har gidan Yusuf take shiga nemansa idan taga bata ganshi ba, saboda Nasir yana da barkwanci, gashi ya iya hira dan haka yakan É—ebe mata kewa sosai.

A hankali mutuncinsu ya rikiɗe zuwa Soyayya, sun shaƙu da juna sosai, da farko lokacin da tazo Nigeria cewa tayi ba zata fi sati biyu ba zata koma ƙasarsu, Islam na ta fama da ita ta zauna amma fafur taƙi, amma saboda Nasir se gashi ta shafe watanni uku ba tare da ta koma maroco ba.

Ya zamana Nasir ya dena karɓar Abinci a gidan yayansa Yusuf, saboda Huda zata ajiye masa idan an dafa a gidansu, idan yaje ta kawo masa su zauna yana ci suna hira.

Kasancewar Nasir mutumin kirki ne daga shi har yayansa, yasa duk mutanen unguwa sun sanshi, kuma shi wannan Attajiri mijin islam yasan Nasir sosai, kuma yasan yana zuwa gidansa, shi ya fara tsokanarsa yana cewa 

"Nifa Malam Nasiru ban gane wannan mutuncin haka tsakaninka da Huda ba, ko kaima marocon zaka ne?"

Tun suna ɓoye ɓoye harta bayyana ga mutane, Nasir da Huda soyayya sukeyi, wasu lokutan idan aka aiketa shiyake rakata, saboda wani abun bata sanshi da hausa ba, kyautar sarƙoƙi kuwa da yake bata babu adadi.

Wataran haka zata shiga gidan Yayan Nasir, gurin Nadiya ta wuni a gurinta suna hira, a haka har take sedai sam Allah be haɗa jinin Huda da Bulama ba, da tana ɓoyewa, harta kasa ɓoyewar take gayawa Nasir ita bata san ganinsa da wannan Bulaman.

Nasir yace  "Hudallahi Bulama abokina ne, kuma ɗan uwanane ban san me yasa bakwa shiri ba"

Huda tace "Nifa ba hanaku hulÉ—a nayi ba, amma idan zakazo gidan nan ka dena zuwa dashi, yaita faman kallona, ni kuma bana so"

Nasir yace  "ki kwantar da hankalinki, ba abunda ze miki, dan dai kallo ai ba cinye ki zeba"

Haka yaita rarraashinta, suka cigaba da soyayya ita da Nasir.

Watarana Yayarta ta kirata tace  "Huda, gida fa sun matsa akan lallai ki koma, kinga kin daɗe sosai a nan"

Maimakon Huda tayi magana, se tayi shiru idonta ya cika da ƙwalla, Islam tace  "kuka kuma? Me yasa ki kuka?"

Huda tace  "ni bana son in koma gida"

Islam tace  "meyasa, keda da ƙyar aka lallaɓoki kika yadda kika zauna"

Huda ta share hawayenta tace  "bana son in koma saboda...  Sekuma tayi shiru

Islam tace " Saboda Nasir ko? "

Huda ta jinjina mata kai, Islam tace " Amma Huda kin san bazasu yadda su aura miki shiba? Kin san irin tashin da mukayi a gidanmu, nima dan Alhaji yana da kuɗi ne suka yadda suka Auramin shi, amma kinga Nasir bashi da kuɗin daze iya biya ya Aureki, kuma a can ga Habibullah sun masa Alƙawarin bashi Aurenki"

Cikin kuka Huda tace  "ni bana son Habib, Nasir nake so, dan Allah Ukty kisa baki, wallahi ina son Nasir sosai"

Islam tace  "kidena kuka ukty, Insha Allah zan tayaki da Addu'a amma nasan ko zaki Auri Nasir zaki sha wuya"
Chapter 21 · 0% Book details