Sashe 67
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta dinga bashi Abinci a baki, yana ci yana lumshe ido, dan dauriya kawai yake, har yanzu zuciyarsa babu daÉ—i, gaba É—aya a cunkushe ransa yake, amma ya daure yana murmushi dan kar ya É—aga mata hankali.
Ta ɗago ido taga ya ƙura mata ido yana kallonta, ta miƙa masa kofin kunun bakinsa, kawai taga idonsa ya cika da ƙwalla, tasan dauriya yake kawai, amma ransa babu daɗi.
Ta ajiye kofin tace "Yoseef menene kuma?"
Girgiza mata kai yayi, alamar bakomai, "da komai Yusuf menene ke kuma?"
Kawai ya lumshe idonsa ya bawa hawayen daya taru a idonsa damar gangarowa, É—aya bayan É—aya suna zarya a fuskarsa, yasa hannayensa biyu ya tallefe fuskarsa, hawaye na cigaba da bin fuskartasa.
Itama hawayen ne ya shiga zubo mata, tasa hannu ta janye masa hannayen daya rufe fuskarsa, ta janyo kansa jikinta, tana son rarrashinsa amma tama rasa me zata ce masa, aikuwa ya kwanta sosai a jikinsa, yana kuka hadda sheshsheƙa, kai kace wani ɗan yaye ne.
"Haba Yoseef, habe Yoseef is ok please, kana son wani ciwon ya kama min kaine? Idan ciwo ya shige ka ya zanyi, baka son kaga Lokacin da zamuyi building namu family ɗin, Allah yayi maka gata daya baka rai da lafiya Yusuf, Insha Allah zan share maka hawayen ka a rayuwa, bazan ƙara bari a maka gori ba, komai ya wuce ai, ya zama tarihi tunda ba shiri duk da kowanne mu ya fidda ran samun abokin rayuwa amma Allah ya haɗamu ya ƙaddara aurenmu, ba tare da mun shirya ba, tabbas ƙaddararmu tana kamanceceniya da juna, ni wallahi jinake dama ni na samu uwar riƙo kamar ummanka, Yoseef kana kallo ni ga gatan ga komai, amma inaji ina gani aka maidani mahaukaciyar ƙarfi da yaji, aka haɗani da larurar Ƙwaƙwalwa da zuciya, ga rashin kwanciyar hankali, ina so kamanta da wannan abun kamar be faru ba, kodai tunanin Salman kake ne? "
Duk da kuka yake, seda ya É—an murmusa sannan ya girgiza kai yace " inda ke babu macen da Yusuf ze tuna"
"to ina son ya zamana in dani, babu damuwar da yuzaraef ze tuna"
Yace "to Allah yasa hakan"
"Ameen ya Allah, Amma ai yanzu zaka yadda mu koma gidanmu ko?"
Yusuf ya girgiza kai, alamar a'a, Widad tace "saboda me?"
"Saboda ke nake so ba dukiyarki ba, ko abunda kika mallaka, dukiyarki ta kice mallakinki ce, dan haka zan sai mana gida daidai ƙarfina, in cigaba da aikina da sana'ata in riƙemu, ai zaki zauna dani da talaucina ko, duk abunda zan baki zaki karɓa ki zauna dani? "
Yai maganar yana kallonta, tai murmushi tace " na zauna da kai a ɗakin ƙasa, duk abunda ka banj na karɓa naci, kuma muke rayuwar mu a haka, ina ne zaka kaini bazan bika ba, amma gaskiya ni bana son aikin nan naka"
"Saboda me?" ya tambaye ta
Ta ɗanyi shiru sannan tace "Yoseef, DSP Bashir shine Abbanka da aka kashe saboda case ɗin Ammina fa"
Yusuf yace "na sani"
Kallonsa tayi tace "ya akayi ka sani"?
Yusuf yace "tun lokacin ina miki aiki, na nake bincike akan statement ɗin kashe mahaifina da akace 'yan fashi sunyi, inata tunanin abun, kina bani labarin ki Nagano musababbin kisan Abba, kuma na gane dalilin da yasa da najewa Umma da batun aiki a gidanku, take cemin bata so, dukda bamu taɓa hirar da ita ba"
Widad tace "Amma ya akayi baka gayamin ba?"
Yai murmushi yace "a gurinki na koya ai"
"Yoseef Kayi haƙuri kaji, ka dena koke koken nan hak, kana karyamin zuciyata sosai, ka dena kuka kaji ɗan gidan Umma"
Ya ɗan ja kumatunta yace "tom insha Allah zan dena"
"ka dena ko zaka dena"?
"Nima ban sani ba, amma ina fatan Allah ha haɗani da wani, wanda yake yana da alaƙa da iyayena, ko 'yan uwana komai talaucinsa ina son in samu in ga wani daga dangina, koa yake is not possible, tunda babu wanda ya sanni a dangin nawa, kuma nima ba wanda na sani "
Widad tace " bazaka dena kukan ba kenan? Ba gani ba, ba nace maka zamu haɗa namu family ɗin ba, mu haifi yara ga Daddy, ga Umma gamu da 'ya' yan da zamu haifa, ba Family ya haɗu ba kenan?"
Yusuf yace " bazaki gane ba Baby, anyway nagode sosai da kulawarki, banjin wani bayan Ummana ya taɓa min rarrashin daya shigeni kamar wanda kikamin, ban taɓa zama nayi makamancin hirar nan da wani ba, duk alaƙata dashi kuwa, ko Umma bama wannan hirara da ita, balle wani saboda kar in ɗaga mata hankali, taga hawayena dan kar taga kamar ta gaza da kula dani ne, dan nasan tabbas idan na saɓamata Allah baze barni ba, ta shayar dani ta bani duk wata kulawa ta uwa da ɗa, kece kawai nayi wannan hirar dake, shiyasa I express all how I feel in my heart, kuma naji daɗin gayamikin da nayi, naji na rage kaso mafi yawa na damuwata thank you sweet heart"
"Allah sarki mijina, kayi haƙuri kaji, tamu jarabatar kenan, amma ko abokinka Abbas baka taɓa yiwa zancen ba?"
Yusuf ya girgiza kai yace "A'a ban taɓa yi masa ba, amma me yasa kika tambaya?"
Widad tace "saboda na tsane shi, gaba É—aya siffar munafukai ce dashi haushi yake bani, shiyasa nasa aka rabaka dashi, aka maida shi nesa da gurin aikinka"
"Amma Widad meyasa? Abokinane fa ya bani gudunmuwa sosai fa a harkar aiki da sauran mu'amalar rayuwa"
Widad tace "Oho nidai na tsane shi, kuma wallahi idan ya kuma raɓarka sena ɗaureshi"
Cikin mamaki ya kalleta yace "but Baby why"
"Z" ta bashi amsa tare da ƙura masa ido, alamar bata son zancen.
"Yanzu za kamin Addu'ar in samu Babyn, kokuwa har yanzu baka son in haihu da kai"
Ya girgiza kai yace "Ai magana ta ƙare, tunda har kika amince dani dukda kinji labarina, Allah yabamu masu albarka Babyn Yoseef"
Washe baki tayi tana murmushi, ta rasa mema zata yi dan murna, kawai ta rungume Yusuf ta haɗe bakinsa da nata tana kissing ɗinsa, Yusuf ya rungumeta shima yana kissing ɗinta suna murmushi, daga nan kuma aka shiga wani bigire daban ..... (Nikuma na fece 🚶 🚶 🚶)
Bayan fitar shu'aibu Halima a fusace ta hau Ramlah da faÉ—a
"Ramlah kinyi haukane? Koba komai mutumin nan mahaifin kune? Kin san hatsarin dayake dashi kuwa? Ko dan kuna ƙanana na bar gidansa baku san irin halayensa ba, shu'aibu da kike ganinsa bashi da imani, bashi da tausayi tsohon ɗan dabane gawurtacce makuwa kuma matsafi, idan kika zaƙe wallahi ze iya kauda ke, dan akan rigimar gonar gado har ɗanuwansa uwa ɗaya uba ɗaya ya kashe, dan haka ki kiyayi wannan tsinannen bakin naki, wanda besan yakamata ba kina zaƙewa dayawa, tynda kika ga ina binsa sannu sannu, nasan hatsarin dayake da shine, idan kinƙi ji bakyaƙi gani ba, idan kin gadama ki gyara idan bahaka ba, matakin daze ɗauka baze mana daɗi ba dagani harku"
Ramlah tace "wallahi, wallahi ba ruwana da hatsabibincinsa, tunda ya haifeni ze gane ya haifi uwarsa a hatsabibanci, harni ze ɗaga ƙazamin hannunsa duk faso ya mara? Zan nuna masa ya haifi 'yar da zata kawo ƙarshen hatsabibancin da yayi a rayuwarsa, besan wacece niba ze gani"
"Ke rufemin baki, bana son cika baki kin san shi rashin jin da yayi"
Ramlah tace "shi ta shafa bani ba, but he must pay for what he did"
Tai gaba fuuu tana ci gaba da masifa.
Hajiya Halima ta girgiza kai tace "Amal ɗakko mayafinki, kizo ki rakani gurin Alhaji Haruna, zan kira shi a waya yanzu, idan yana nan muje mu sameshi ayi maganin wannan matsalolin"
Amal tace to, ta tafi É—akko mayafi a É—akin ta.
Gidan Alhaji Haruna sukaje, aka musu iso part É—insa, yana zaune yana kallon labarai a tashar Al Jazeera.
Suka samu guri suka zauna, tunda suka shigo yake bin Amal da kallo, kamar tsohon maye.
Hajiya Halima tace "gurinka nazo"
Yace "yaukuma da wacce kikazo? Danke kullum cikin rigima kike"
Hajiya Halima tace "nikam duk a bar wannan maganar, yaron wajena daya ɓata ba sace shi akayi ba, guduwa yayi daga gida, kuma baun takaicin shine, ya gano abubuwan da nake aikatawa, dan hara takadda ya bari"
Alhaji Haruna yace "Halima kina me haka ta faru? Garin yaya yasani, wannan yaron naki me kama da ustazai kin san ze iya tona mana asiri fa"
Halima tace "hmm wallahi ban san yadda akayi ya sani ba, shekara Goma ina ƙumbiya ƙumbiya muna wannan harƙallar tare, amma be sani ba, ban san wane munafikin ne ya gaya masa ba, kuma ma ba wannan ba ɗazu fa uban 'ya' yana yazo"
Yace "Wake nan?"
"Shu'aibu mana, koka manta bisa yarjejeniya da aka yi dashi ya sakeni, kuma tunda muka rabu, ba'a cika masa Alƙawarin ba, dan haka yazo yana barazanar karɓe yaransa, kuma wai sena tura masa wasu maƙudan kuɗaɗe koya tona mana Asiri"
Alhaji Haruna yace "toki tura masa kuÉ—in mana, ko kin fi son asirin naki ya tonu?"
Hajiya Halima tace "wace irin maganace wannan, kafa san hatsarin da mutumin nan yake dashi fa"
Alhaji Haruna yace "lallai akwai matsala gagaruma makuwa, amma yanzu abunda za'ayi ki saurareni, zamuyi magana dasu, yadda aka yanke zan miki magana"
Hajiya Halima tace "to shikenan, amma dan Allah kuyi maganar da wuri"
Yace "shikenan, karki damu wannan ma yarinyar kice ne? Naga harta fi yayarta kyau"
Hajiya Halima tace "eh itace 'yar auta ta ai, daga Ramlah se ita"
"Masha Allah, yaran naki masu kyau, sunfi kama da yayarta, Anwar ne ban san kamannin wa yayi ba"
Hajiya Halima tace "kamanin Ubansa yayi, wasu lokutan kuma dani yake kama"
Alhaji Haruna yace "A' a baya kama da shu'aibu sam, kamarsa daban shima"
Hajiya Halima tace "Amal jeki falo ki jirani kinji"
Amal ta miƙe tana haɗe rai, saboda kallon da Alhaji Haruna yake mata.
Tana fita Hajiya Halima tace "Anwar fa ubansa daban shima, dana rabu da mijina na fari akwai cikinsa ko wata ɗaya beba na auri shu'aibu, na haifeshi a gidansa amma ba shine ubansa ba"
Alhaji Haruna yace "ikon Allah, to waye nasa uban?"