← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 127

Sashe 29

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf yace "kawai se aga mun shiga banɗaki tare? No banda wannan, sannan da kunya aga na taƙarƙare ina tayaki wankin kai a tsakar gida, ki bari seda daddare, muje toilet mu wanke gashin, yadda ba wanda ze ganmu"

Hararar Yusuf tayi tace  "ni yanzu nake so, idan aka wanke kafin dare ya sha iska, in aka wanke daddarw na kwanta ai wari zeyi tunda babu shampoo"

Yusuf yace "ni ya zanyi, kawai aga mun shiga banÉ—aki tare? Da kunya fa"

"Au wai nan kunya kake ji, amma ai baka jin kunyata tunda..

" tunda me? "

" ban sani ba"
Murmushi yayi yace "Allah ya barni da abar sona, ina sonki Habibty na, kura kike ga tsoro ga ban tsoro"

Suleiman ne tafe yana driving a motarsa, yana sauraren radio yana jiran ƙarfe huɗu ta cika ya saurari labaran yamma, kanin labaran ne suka ɗauki hankalinsa, hakan yasa shi maida hankali don jin cikakkun labaran.

Labarin farko da aka sanarne ya ɗau hankalinsa, ya kaɗashi matuƙa ya tayar masa da hankali, be gama tsinkewa da lamarin ba, seda ya ƙarasa traffic ta tsaida hannun da yake, wani yaro yazo ya tsaya a window motarsa yana masa tallan jarida, shafin farko ya kalla yaji gabansa yayi mummunar faɗuwa.

LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

MASU FITARMIN DA LITTAFI KUMA, IN DAI DAI KUKE KUN SANI IDAN AKASIN HAKANE MA KUN SANI
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

70_71

Da rawar jiki Suleiman ya sayi jaridar nan yayi parking a gefen titi, hoton Yusuf ne a bangon jaridar an rubuta wanted, ya buɗe cikin jaridar ya shiga duba shafin da labarin yake, wai 'yan sanda sun fitar da sakamakon binciken da suka yi akan ɓatan 'yar gidan Daula, bincike ya tabattar musu da direban Widad Nasir Daula wanda aka sani da Yusuf, shine ya sace Widad yayi garkuwa da ita, ba sace su akayi tare ba, dan haka jam'ian tsaro suna nan suna binciken inda suke, sannan duk wanda ya gano inda suke ya faɗa akwai kyauta me tsoka.

Gaba ɗaya jikin Sulaiman yayi sanyi, akanme za'a fitar da wannan sakamakon binciken? Meye dalili? Cikin hanzari ya juya sitiyarin motarsa zuwa wani gurin, tuƙin kawai yake amma hankalinsa sam baya kan abunda yake yi, Allah ne ya kaishi inda yake son zuwa.

Harabar headquarter 'yan sanda yaje yayi parking ɗin motarsa, ya fita da sauri daga cikin motar, yana shiga harabar gurin ƙananan' yan sanda sunata sara masa, cikin gaggawa ya nufi wani office, ya buɗe ya shiga suka gaisa da ma mallakin Office ɗin, Suleiman ya zauna ya miƙa masa jaridar hannunsa sannan yace  "SP waye ya fitar da sakamakon wannan binciken haka? Har aka sanar da 'yan jarida?"

SP yace "kamar yaya kenan? Sakamakon binciken da akayi kenan, kuma aka bada umarni mu sanar"

Suleiman yace  "haba SP, wannan yaron fa jami' inmu ne, ta yaya kake tunanin ze iya aikata wannan mummunan aikin haka, sam ba haka abun ya faru ba, ta yaya za'ace Yusuf ne yayi garkuwa da 'yar gidan Daula? Ta yaya?"

"Kaga karka zo ka É—agamin hankali mana, nima umarni aka bani inyi wannan Sanarwar kuma nayi, meye nawa a ciki?"

"An gabatar maka da sakamakon binciken da akayi kafin kayi wannan Sanarwar, wannan fa tamkar ɓatawa hukumar' yan sanda sunane, ta yaya wasu tsirarin mutane zasu sa ku saɓa dokar aikinmu saboda biyan buƙatarsu?"

SP ya kalli Suleiman yace  "ya akayi kasan wasu tsirarin mutane ne suka sa ayi hakan?"

Nan da nan Suleiman ya dawo hayyacinsa ya daidaita nutsuwarsa yace  "to koma dai a cikinmu ne mukayi hakan ai munsan mun saɓa dokar aiki, yaron nan abokin aikinmu ne, jajirtaccen ma'aikaci ne mara ƙyuya, ga gaskiya a harkar aikinsa, ya dace ayi masa haka, zan iya rantse maka ko a wasa Yusuf baze aikata haka ba"

SP yace "wannan kuma kai ta shafa bani ba, kai kake zaune dashi kasan halinsa, ni babu ruwana sakamakon da aka gabatarmin shi zan bayyanawa al'umma, dan haka in baka da abunyi zaka iya bani guri, ina da baƙi"

Cike da baƙin ciki da ɓacin rai, Suleiman ya baro office ɗin nan, gaba ɗaya tausayin Yusuf da mamaki suka cika zuciyarsa, tabbas idan akayiwa Yusuf haka an zalunce shi, kuma an zubar da kimar aikin ɗan sanda a idon duniya.

Saleh ne yayi jifa da jaridar hannunsa yace  "Impossible, Alhaji Musa anya kanaso mu gama da duniya lafiya kuwa? Ta yaya za'ace anyi masa wannan ƙazafin haka? Abun yayi yawa, yakamata mudinga yi muna jin tsoron Allah"

Alhaji Musa yace  "kai dakata! Meyasa ba zamu nemawa kanmu mafita ba? Ina ruwanmu da koma wani hali ze shiga, ai ba ƙarya akayi masa ba, in ba hakaba meyasa da suka gudu basu dawo ba, waye yasan inda suke? Dan haka shiya saceta yayi garkuwa da ita, kuma ya koma yayi garkuwa da mahaifinta, ai mafita muke nemawa kanmu, ɗan sanda nefa, yanzu idan ya dawo asirinmu ne ze tonu, dan haka gara da mukayi masa haka, idan kuma baka cikinmu ne zaka iya ƙarawa gaba"

Saleh yayi shiru cike da takaici da baƙin ciki, ya rasa mema yakamata yayi, idan aka yi haka an cutar da rayuwar Yusuf ba kaɗan ba, rasa abunyi yayi kawai ya juya ya fice a matuƙar fusace.

Hari tana ta fifitar Wuta, ta kuma kallon ƙofar ɗakinsu Widad tace  "taɓ amma wannan abu yayi yawa haka, ai kome suke yaci ace sun fito haka, sha biyun rana fa wane irin abune haka?"

Banza Gwaggo tayi da ita, yayin da Hansai tace  "ke kuma sa idonki yayi yawa, ina ruwanki da koma me suke yi ina ruwanki? Kedai bakya rasa abun faɗa shiyasa duk tabi ta raina ki"

"to naga abun magana bazan magana ba? Ai abun da damu ace garin Allah ya waye, har wannan lokaci suna ƙule a ɗaka, idan wani abun ya samesu fa"

Widad ce ta fito hannunta ɗauke da bokiti, ta ƙaraso inda Gwaggo take ta gaisheta, tace  "A temakamin da ruwa, ina so da ɗan yawa zan wanke gashina ne"

Gwaggo ta karɓi bokitin, taje rumfar da suke girki ta Ɗebo mata ruwan, Yusuf a kunyace ya fito suka gaisa da mutanen gidan, yaje ya Ɗebo ruwa a rijiya ya sirka ya kai banɗaki.

Widad ta ɗakko abun wanka, tazo ta shige banɗaki, Yusuf ya rasa yadda zeyi ya bita toilet ɗin nan saboda kunya, leƙowa tayi tace  "Yoseef ka shigo mana, kose ruwan yayi sanyi?"

Hari ta tsaya tana kallon ikon Allah, haka Yusuf ya shiga banɗakin nan, ta cire hijjabin jikinta daga ita se towel, ta cire ribbon ɗinta, ta zauna akan kujera, Nan Yusuf ya shiga tayata wanke gashin nan me matuƙar tsawo da yawa.

Hansai kam burgeta sukayi, yayin da Hari ta taɓe baki tace  "ni tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin baɗalar da nake gani a gurin bayin Allah nan ba"

Hansai tace "taɓ wallahi nikam birgeni sukeyi, yanzu kai anan ka isa miji ya wani ta yaka wanke kai, yadda yake ɗawainiya da ita ba ƙaramin birgeni yake ba"

Hari tace "mhmm, ai ko sharar É—aki baki isa miji anan ya tayaki ba, balle wani wanke kai, ai maza suna birni, mu nan se godiyar Allah kawai"

Hansai tace  "me kike nufi to?"

"Ni ba abunda nake nufi, karki ƙullamin sharri"

Haka suka cigaba da maganganunsu.

Yusuf dai bega wani datti da kan Widad yayi ba, ta dai damune kawai ta wanke kan nata, tunda ta saba wanke shi akai akai.

Seda ta gama ya bata guri tayi wanka, duk ya jiƙa kayansa da ruwa, Widad tayi wankanta ta kammala sannan ta fito, Towel ɗin nan kawai ta ɗauro ta fito, gashin nan ya baje a bayanta se ɗigar da ruwa yake.

Ai gaba ɗaya sukabi Widad da kallo, tubarkallah Allah yayi mata kyau da halitta me ɗaukar hankali, ta kama ƙasan gashinta tana yarfewa, ga towel ɗin iyakacinsa gwiwarta, fatarta se sheƙi take.

Hanne tabi Widad da kallo, tana tunanin me zata yi mata ta huce wannan baƙincikin, Widad kamar da gayya take juya jikinta har ta shiga ɗakinsu.

Hindu ta lura da irin kallon da Hanne ke yiwa Widad, dan haka tace  "Masha Allah, Allah me halitta duk mutumin da yake da mace kamar Amarya, wallahi babu me kama da bayan tukunyar daze kalla balle yayi sha" War Aurenta, kamar ita tayi kanta masha Allah "

Hanne ta kalli Hindu, taja tsaki tayi tafiyar ta abunta.

Yusuf ya kalli Widad yace  " Masoyiyya ba dai a haka kika fito ba? "

" A haka na fito menene? Ai dai naga ba maza"

"Anya kin san irin kyawun halittar da Allah yayi miki, koda ba maza baki abun gudu ne, dan Allah karki kuma fita a haka"

"Kaga nifa na fara jin yunwa"

Yusuf yace "maganar tawa ce bata da amfani ko? Shine kike sharewa"

Shiru tayi masa ta nemi guri tayi zamanta.

Hindu tayi sallama ƙofar ɗakinsu, ta kawo musu Abinci, Yusuf ne yaje ya karɓo ya dawo ya zauna, Widad bata da niyyar saka kaya, a haka take zaune abunta, Yusuf kam se ƙureta yake da ido, gaba ɗaya ya rasa sukuni har suka kammala cin Abincin idonsa a kanta.

Bayan sun gama yace "yau kuma baza'a sa kaya bane?"

"zan saka ban shafa mai bane"

Yace "Kawo in shafa miki"

Ɗakko zaitun tayi ta miƙa masa, ta koma ta zauna tana cin jiƙaƙiyar aya da Hindu ta koya mata ci.

Yana shafa mata man yanajin fatarta kamar ze ji mata rauni idan beyi a hankali ba, Yusuf yace  "me kike cine haka?"
Chapter 29 · 0% Book details