← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 127

Sashe 126

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka cigaba da faɗansu da suka saba ita da Hari, Farm House aka sake gyarawa, aka canza furnitures wanda ya tattaka gidan da aka sauki su Hari, Hari se salati take da salallami  wai "Nidai Hindu, idan ana neman 'yar wanke wanke dan Allah zanyi"

Widad tace "Kina uwatta zaki zo wanke2"?

"eh wallahi zanyi"

Tun Widad na biyewa ƙauyancin Hari harta ƙyaleta, saboda abun nata bana ƙare bane.

Bayan sun rakata, sun mata addu'a Gwaggo tace "to Hindu, mu daga nan gobe in Allah ya kaimu zamu wuce gida, ki zauna lafiya da mijinki da kowa ma, nasan dai baki da matsala amma dai ayi haƙuri"

Hindu ta rirriƙe Gwaggo tana kuka, da ƙyar ta cikata suka tafi, suna tafiya tsoro ya cika Hindu, saboda ita girman gidan ma abun tsorone, gashi tana jiyo kukan dabbobi kaɗan kaɗan  a falon, tana cikin zare idone sega Daula ya shigo da abokansa.

Ta cukuikuye a cikin lifaya taƙi ɗago kanta balle ta kalli wanima, nan suka musu fatan Alkhairi sannan suka tafi.

Ayshercool
07063065680
12/22/21, 11:07 PM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

170

Bayan fitarsu Daula ya kalleta yace "taso mu tafi"

Ta ɗago a hankali ta kalleshi, sannan ta miƙe tana waige waige, ya miƙe yai gaba tana binsa a baya, wani gurin seta tsaya kallo, seta ɗago taga ya tsaya jiranta setai maza ta taho, ya dinga ratsawa da ita faluka, wai nan duk dan zaman mutum ɗaya akayi shi, suka zo ƙafar bene ya fara hawa tana binsa, sedai ta zame ta faɗi, saboda matattakalr benen kanta wata iri take ganinta, ga ƙananan fitilu a jiki, gata kamar ta glass ta tsaya kallo shine ta faɗi, a ɗan gigice ya waigo yna faɗin "subhanallah, garin yaya? Kodai ɗaukarki zanyi ne?"

Da sauri ta girgiza kai yace "sannu, miƙomin hannunki in riƙeki"

Ta miƙa masa hannu, ya riƙe hannunsa kamar bana namiji ba saboda laushi.

Haka suka ƙarasa saman bene, cikin katafaren falonsa, ji tayi sanyin data keji ya ƙaru, hartana nema ta fara rawar sanyi, yaje ya rage AC suka shiga bedroom, ai a jikin ƙofa ta tsaya tana kallon ikon Allah, lallai gaskiyar Saleh, da yace ko za'a saida duk kadarar da 'yan ƙauyensu suka mallaka baza su siyi ko da motar hawan Widad ba, balle wannan uban gidaje haka.

Ya bata gurin zama, ta zauna already kaji da kayan shaye2 suna ɗakin da plate da komai, amma juyin duniya Hindu taƙi ci, ba yadda beyi da ita ba, amma taƙi ci, se ƙyaleta yayi, sukayi alwala sukayi salla, bisa ga koyi ga sunnar ma'aiki salallahu alaihi wassalam, tare da yin addu'oi, ya miƙe yace mata ga gado cam taje ta kwanta, shi kansa gadon abun kallo ne, lallai Su Widad sun tara abun duniya.

Shima da ƙyar ta hau ta kwanta, ta dunƙule a guri ɗaya, ya ɗakko ƙaton bargo ya lulluɓa mata, ya cire babbar rigarsa taga ya sake tada salla, sannan hankalinta ya kwanta ta shiga baccin ta.

Wani irin laushine da katifar, ga bargon ma laushi se ƙamshine ke tashi a jikin bargon, cikin dare ta tashi a firgice saboda tsoro, Daula yace "lafiya kuwa?"

"tsoro nakeji"

Yai murmushi yace "aiba abunda ze sameki, ki rage yawan tsoro dan wataran ke kaÉ—ai zaki kwana a gidan nan, ki kwanta kiyi addu'a, ba abin da ze sameki"

Haka ta kwanta tana cigaba da rarraba ido.

Sedai a yau É—inne dai Hindu ta zama cikakkiyar matar aure, dukda tsoro da razanin data tsinci kanta a ciki.

Su Hari kuwa haka suka koma ƙauye, suna zuzuta haɗuwar gidajen da suka je, Abinci kam wannan duk azabar cin mugunta da suka yi seda suka barshi, akayi musu rakiya da sha tara ta arziki, yayin da ayyukan da ake musu sunyi nisa sosai, dan har an kai musu wutar lantarki ma.

Washegari Widad ta aika direba da Abinci ya kai gidansu, sedai ita amaryar ce taƙi sakin jiki sam, lokaci lokaci se Daula ya kalleta yayi murmushi, yarinya ce sosai sedai akwai kunya sosai.

Yace "ga Abinci Widad ta aiko, kizo kici ko in kirata in gayamata kinƙi cin komai"

"Aa' dan Allah karka gayamata"

"to zokici Abincin nan"

Ta sakko ta zauna, ya zuba abincin a plate, ya haɗa mata da tea ya bata, sedai kunyar ci take a gabansa, ta ɗan dinga cakala, ya karɓi plate ɗin, ya ɗebo a spoon ya kai bakin ta, kunya takeji sosai, ta sunkuyar da kai yace  "haka zamuyi dake? In gayamata kina gaddama ko?"

Ta girgiza kai, yace "in bakya so in gayamata, maza karɓi kici"

Abun har mamaki yake bata, babban mutum haka amma ya zauna yana lallaɓata, seda taci ta ƙoshi ya jata zuwa wani ɗaki ya nuna mata kayan lefenta.

Banda wanda aka shirya mata a drower.

Umman Yusuf, kwana uku da ɗaurin Aure ta tare a babban birnin tarayya, Widad taso zuwa sedai tana daf da shiga watan haihuwarta, dan haka akace ta haƙura.

Bulama kuma tuni aka shiga zaman kotu, aka dinga shari'a ana warware duk wata ƙulalliya da makirci daya aikata, laifukan nasa da yawa danshi ƙarshe se hukuncin rai da rai aka masa, sauran kuma daga me shekaru Ashirin da wani abu seme talatin, Hajiya Halima kuma shekaru Ashirin da takwas itama, Ramlah kuwa hauka ta dingayi tuburan saboda azabar shaye2, ƙarshe se gidan mahaukata aka maida ita.

Bulama kuma ya dinga larura, ciwo bayan na ƙanjamau ya din rashin lafiya, aka kai shi Asibitin gidan yari ashe cancer ce ta kama masa hanji zuwa duburarsa, ga kotu dukata ƙwace kadsrorinsa ta mayarwa da Daula, bashi da komai ba shi da kuɗin daza'a masa aiki, ƙarshe haka gurin bayan gidansa ya dinga tsutsa, ga wani irin wari yanayi, shima Fahad ya samu shekaru sha biyu a gidan yari, gashi ga ubansa Alhaji Musa kuwa shima rai da rai ne hukuncinsa, saboda hadda laifin kashe matarsa, ga sugar ya fito masa a ƙafa, shima ƙafa ta dinga ruɓewa kamar bata ɗan Adam ba.

A hankali Hindu take ɗan sakin jiki da Daula, babban abunda yake burgeshi da ita shine, tsananin biyayya kamar zata shige cikinsa, ko magana yake mata kanta a ƙasa, wanda rabonsa da samun farinciki tunda Huda ta rasu.

Satinta biyu yasa ta a makaranta, ya É—aukar mata me zuwa gida yai mata lesson, na ilimin addini dana zamani, kuma gata da saurin ganewa.

Yanzuma yana zaune ta ɗora kanta akan cinyar sa, yana nuna mata hotunan maman Widad daya ɗauka a wayarsa, Hindu ta zuba musu ido tace  "masha Allah, tana da kyau sosai gata kamarta ɗaya da Widad"

Sam bata nuna masa kishi ba, sema addu'a data dinga yi mata.

Daula ya bata wani littafin turanci, yace ta karanta yaji, aikuwa ta dinga karanta masa, gashi makarantar da yasa ta, malaman su turawa ne, tana yi yana tafa mata yana murmushi.

Jin sallamar su Widad a falon, yasa cikin hanzari ta tashi daga kan cinyar Daula, tana neman É—ankwali, wai kar Widad taga kamar ta raina shi.

Widad tai murmushi tace  "kekam Allah ya shiryeki, ni idan nice ba kunyarki zanji ba, mijin nakima da yake tsoho"
Hindu ta duƙunƙune fuska tana jin kunya.

Yusuf dai sedai ya kallesu yayi murmushi, sun daÉ—e a gidan se bayan goma sannan suka tafi gida.

A satin Saleh ya dawo, an masa aiki ya warke tsaf dashi, yayi murna da jin Daula ya Auri Hindu, shima an masa halacci sosai, sannan Daula ya canza masa aiki, aka maida shi Lagos.

Amal ma a nan Nigeria aka mata aiki, sedai taji sauƙi sosai anata ƙoƙari karta rasa hankalinta, likitan da yayi mata aiki ya nuna yana sonta ze Aure ta, Daula be ɓoye masa ba ya gaya masa komai game da Amal yace "Amma itama 'ya tace, idan kasan zaka aure ta ka wulaƙantata ka ƙyalemin' yata"

Yace "shi tsakani da Allah yake sonta"

Daula ya shige gaba ya karɓi kuɗin Aurenta, sedai ita tana Asibiti har yanzu.

Wataran da Safe, Hindu ta tashi daga bacci, sega kiran Widad, ta É—aga wayar tana cewa "Maman biyu kin haihune?"

Widad tace "kedai bari, ina nan ina ja, ima wannan dattijon yake? Zanyi magana da shi"

"Hindu tace " waye kuma dattijon? "

" Mijinki mana "

" gaskiya kidena ce masa dattijo "

Widad ta dinga dariya tace" lallai Hindu, Allah ya baki haƙuri yana ina? "

Hindu tace "bacci yake yi"

"idan ya tashi kice masa, zan tafi Asibiti na fara jin ciwo, yayi min addu'a zanje inji abunda zasu ce, zan iya haihuwa ko kuma aikin za'ayi"

Jikiua sanyaye Hindu tace "insha Allah zaki haihu lafiya, ki kwantar da hankalinki"

Widad tace 'to Allah yasa"

Hindu ta ajiye wayar tai shiru, Daula ya tashi zaune yana cewa matar dattijo ha dai.?

Kallonsa tai tayi murmushi tace "lafiya, Widad ce tace zata Asibiti a duba, idan zata iya haihuwa ko kuma aiki za' a mata"

Da sauri ya karɓi wayar, ya sake kira Yusuf ya ɗaga yace "Daddy mina Asibiti, daga zuwanmu suka riƙe ta sukace haihuwa zata yi"

Daddy yace 'wani Asibitin ne? Gani nan zuwa "

Ya gayamasa, aikuwa anan da nan suka shirya shida Hindu suka tafi Asibitin.

Ansha daru da Widad kafin ta haihu, Allah ya temake ta ta haihu da kanta, sedai Yusuf ya sha kira sosai da Daddy.

Aka fito aka miƙo musu, santalelen jariri me kama da Yusuf sak, Daula ya karɓi Jaririn yana faɗin masha Allah, Alhamdilillah.

Nan ya shiga bige bigen waya, yana sanar da haihuwar ta Widad, nan da nan aka cika Asibitin 'yan barka, se bayan awanni huÉ—u sannan aka sallameta, suka tafi gida.
Chapter 126 · 0% Book details