← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 127

Sashe 73

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nurat ta share hawayenta tace "Yaya Khalil, ka dena min ɓoye ɓoye, lokaci yayi da zaka temakeni, Khalil mahaifina azzalumi ne wallahi, jiya be kwana a gida ba, nasan saboda wannan dalilin ne, Wallahi idan ba'ayi wani abu a kai ba, rayuwar Yusuf zata shiga garari"

"Nasani Nurat, but am doing my best kinji, bari kinga yanzu zan shigo gidan naku kafin in wuce office"

Nurat tace "No karkazo, ka san shi da zargi, zefara zargin wani abune dan Allah karka zo ka bari kawai, mu dinga communicating ta waya ya isa, bana son ya gane komai"

Khalil yace "shikenan, naji ki kwantar da hankalinki, komai zezo da sauƙi zancigaba da bibiya inga yadda zata kaya"

"Shikenan brother nagode sosai, dan Allah ka ƙara ƙoƙari"

"karki damu sister, Insha Allah i will do my best for you"

Ta jinjina kai ta ajiye wayar, tana ci gaba da jujjuya kai tana tausayawa Yusuf.

Ma'aikatan gidan Alhaji Daula suka rikice jin kabarin abunda ya faru da Yusuf, sun kadu matuƙar gaske dukda wasun su suna jin haushinsa amma a zaman da suka yi dashi sun sanshi da sanyin hali, basa tunanin ze aikata wannan aiki haka.

Ɓangaren Suleiman makuwa ya kaɗu Matuƙa da jin wannan labarin, hankalinsa ya tashi sosai ya tafi headquarter da kansa dan ganin Yusuf, amma fafur aka hanashi ganinsa, dukda shima babban jami'ine amma a kace baze ganshi ba, ana kan gudanar da bincike akansu ne.

Yusuf kam yaci duka da kulki a hannun kuratan 'yan sanda, yama rasa dukan me suke masa? Me suke yai musu su ƙyaleshi, ya daku iya dakuwa ƙafafunsa da bayansa ya gaya masa saboda duka, yana nan gurin a duƙe wani ɗan sanda ya shigo aka ajiye ɗan sandan kujera ya zauna, ya sallami kowa daga gurin, ya ɗan ƙurawa Yusuf ido sannan yace   "Malam Yusuf"

Yusuf yai shiru be ɗagoba, yana nan zaune ya durƙusar da kansa.

"Ina so karka bamu wahala, kuma karka bawa kanka wahala, yana da kyau ka amsa laifinka tun a nan dan muyi gaggawar kaika kotu a yanke maka hukuncin daya dace, sannan abu na gaba shine, Widad ta baka bayanin inda dukiyar da mahaifinata ya ware take?"

Ɗago kai Yusuf yayi, ya kalli ɗan sandan, se yanzu ya ƙara tabattar da cewa wannan abun set up ne kawai, an shirya wulaƙant shi ne kawai.

Ya maida kansa ya sunkuyar, yaƙi magana.

Cikin shouting ɗan sandan yace" ba magana nake maka ba? Ta gaya maka ko kuwa, ka sauƙaƙawa kanka ka gayamin suna ina? "

Cikin dakiya da juriya irin na Yusuf, ya sake gyra zamansa ya ƙi kallon ɗan sandan, ai kuwa ɗan sandan nan ya harzuƙa, yasa aka kawo masa kulki, ya ding bugawa Yusuf, Yusuf ya dinga juyi a gurin saboda azabar wahala dayake sha, dan dukan kulkin nan ba ƙaramin shigarsa yake ba, amma sukayi sukayi, Yusuf yaƙi cewa uffan.

Widad kam aka hana 'yan jarida ganinta, aka gama bata magunguna da gwaje gwaje, Bulama ya É—auketa zuwa gidan sa, Widad sam bata iya ma magana yanzu, haka aka tafi da ita gidan Bulama.

Likitoci suka bada rahoton, wai ta samu raunuka a jikinta, kuma ta galabaita saboda rashin Abinci da azabtarwar da ta sha  hannun Yusuf da yayi garkuwa da ita.

Bulama ya tafi da ita gidansa, sedai banda sharar hawaye babu abunda take yi, ƙarshe ma maganar ta gagara, aka bata ɗaki, suna shiga ɗakin ta zube a ƙasa tana maida numfashi, saboda nauyin da taji ƙirjinta yayi mata, ta kalli Bulama tace  "meyasa ka kawoni nan?"

Yace "A'a, daughter nanma ai gidanku ne, meye na damuwa kuma?"

"Nan ba gidanmu bane, ina Daddy yake tunda nazo ban ganshi ba, yana ina?"

Hajiya Sarah ta kalli Bulama, shima ya kalleta yace "Amm daughter kin gane, ki kwantar da hankalinki kinji, Daddyn ki yana nan lafiya, kuma yana nan zuwa insha Allah, kedai ki kwantar da hankalinki kawai saboda lafiyarki"

Widad tace "ni babu abunda ya sameni, ka gayamin ina mahaifina yake? Ina Daddy na"

Hajiya Sarah tace  "Kaga, Ka gayamata gaskiya kawai, tunda har Allah yasa an gano ta bashi da wani amfani a cigaba da yi mata ɓoye ɓoye, dan haka kawai ka fito ka faɗa mata gaskiya"

Bulama yace "Sarah meyasa kike hakane? Kina ganin halin da take ciki amma kina wani zance daban meyasa kike hakane?"

Hajiya Sarah tace "dan meyasa ba zanyi haka ba, ka gayamata gaskiya mana da wuri, kasan halinta sarai ba baka sani ba, idan ta sani daga baya duk seta É—aga mana hankali gaba É—aya gidan nan, ni a yanzu hakama a tsorace nake, kafi kowa sanin halinta"

Bulama yace "koma meye halin nata ba haƙuri zakiyi ba, da  'yar kice haka zaki ce? Kiyi haƙuri mana muga yadda hali zeyi"

Sunata jayayya a tsakanin su, Widad ta zame jiki ta zauna a gurin, tai musu shiru ta lumshe idonta tana jin sautin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri sauri kamar zata tsaga ƙirjinta ta fito.

Bulama ya durƙuso gabanta yace  "ki kwantar da hanlinki kinji daughter, babu wata matsala Daddynki yana nan lafiya, zezo inda kike, amma sekin kwantar da hankalinki, kin san baki da cikakkiyar lafiya, mubi komai a sannu"

Idonta a lumshe bata buɗe ba tace  "Daddy"

Yace  "Na'am daughter"

"kasa a sakarmin Yusuf"

"saboda me? Meyasa zakice a sake shi, mutumin da yayi garkuwa dake, aka samoki da ƙyar a wani ƙungurmin ƙauye, sannan kice a sake shi, baki duba abunda yayi miki bane?"

"Yoseef beyi garkuwa dani ba sam, anyi garkuwa damune ni da shi, ba wahalar da beyi ba saboda in tsira da rayuwata, meyasa yanzu za'ace shine ya saceni? Anyi masa adalci kenan kasa a sake shi please, dan Allah a saki Yoseef bashi da laifin komai fa" ta ƙarasa maganar tana kuka.

Bulama yace "Ni yanzu ta yaya zan fara sakawa a sake shi? 'yan sanda sun fitar da rahoto akan abunda ya faru kawai ace nasa a sake shi, bafa a ko ina ake alfarma ba, yanzu gaba É—aya case na hannun hukuma, babu abunda zan iya ni"

"Shikenan tunda babu abunda zaka iya, ni zanyi ko zan ƙarar da dukiyar Daula sena fitar da Yoseef, saboda ni ba butulu bace ba, Yoseef yayi min halacci"

Ta miƙe ta kwanta a gurin, tana ta kera gwaron numfashi, wani na bin wani.

Suleiman gidan su Yusuf ya tafi, yana zuwa ya tarar da Umman Yusuf a kwance, an kewaye ta ana yayyafa mata ruwa, sam bata san inda kanta yake ba, ga Asmarta ta tashi tana jan numfashi da ƙyar, an sheƙa mata inhaler amma a banza.

Suleiman yace "Subhanallah, ya ba'a kaita Asibiti ba? Meye ya faru da ita haka?"

Wata maƙociyarsu tace  "wallahi yau da Asuba bayan ta idar da sallar Asuba, ya kunna radio taji ance an kama ɗanta Yusuf, shikenan muka jiyo kukanta, muna shigowa harta fara fita daga hayyacinta, numfashi yaƙi tsayawa a ƙirjinta.

Suleiman yace" da ba seku kaita Asibiti ba, koda kuwa na gwamnati ne ba, zata iya rasa ranta fa a haka, maza ku É—akkota ga mota can, a sata a ciki mu tafi Asibiti "

Haka kuwa akayi, aka sa Umman Yusuf a mota, da wasu maƙotanta suka Tafi Kaita Asibiti.

Suna zuwa aka karɓeta a emergency, aka shiga da ita, likitoci sukayi gwaje gwajen da zasuyi suka ga jininta ya hau fiye da kima, dama tana zuwa shan magani ana duba jinin, tun lokacin da Yusuf ya ɓata ta haɗu da hawan jini.

Yanzu jinin ya hau fiye da kima, ga Asma ta tashi saboda kukan da take yi, gaba ɗaya bata a hayyacinta, a nata ƙoƙarin ganin jinin ya sauka amma abu ya gagara, ƙarshe seda aka haɗa mata da oxygen, da allurai da drip, Suleiman duk ya biya charges ɗin.

Da Safe Amal bata tashi ba se wajen sha ɗaya na safe, ta tashi daga bacci ta tashi da wata irin yunwa, ta tashi ta shiga toilet tayi wanka, ta canza kayan jikinta daga na bacci, har zata fita tace "bari dai in kunna wayata, inga me wannan jakin kuma ya kuma turowa" ta zauna ta kunna wayarta, ta buɗe data messages nata shigowa, amma babu na Alhaji Haruna, ta taɓe baki ta tashi zata fita, sega kiran wayarsa ya shigo wayarta.

Ta koma ta zauna sannan ta É—aga, Alhaji Haruna yace
"yaushe zanzo in karɓi takaddar nan ne?"

"ba rana ba wata, muddin ba zaka cika sharuÉ—an dana sama ka ba"

"Waike ynzu 500k ne suka miki kaÉ—an? Haba ke kuwa dan Allah"

Amal tace  "kaga sauraramin, meye wani 500k,duk kuɗin da kake sata na haram kakeci, seni zaka rainawa hankali, wallahi bazan baka takaddar nan a 500k ba"

Aikuwa ya fusata yace  "ke wai wace irin yarinya ce, kwana bakwai fa kawai aka bani in kai takaddar nan, ya zakice bazaki bank ba haka akeyi?"

"Kai bari kaji in gaya maka wani abu, wallahi idan baka yi wasa ba sena sa takaddar nan ta zama hujja akanku gaba É—aya"

"har babar taki?"

"Eh har ita, duk zaka ja muku ne, bari in maka magana ta ƙarshe, wallahi bazan baka takaddar nan ba har se ka bani kuɗin da zaka fanshi budurcina da ka karɓa ta ƙarfi"

"Ke, ni kike gayawa haka? Wace irin magana ce wannan?"

"ai kace min ka ga kaidi iri iri na mata a bariki, to zan nuna maka nawa na dabanne, zan kawo ƙarshen bunsurancinka, wallahi ko inje in haɗa maka masifa da tashin hankali a gurin Alhaji Bukar ɗin, baka san kalar nawa kaidin ba zan gwada maka Akuya kawai"

Ai kasa magana yayi, se bin wayar yayi da kallo, lallai yarinyar nan bata da mutunci sam.

Ta ajiye wayar tace za kaga tsiya ganin idonka, tai tsaki ta saka wayar a caji ta fito falo, Dariyar Mummy taji da Ramlah, Ramlah tace  "dara taci gida, sunzo hannu Alhamdilillah, naji ance a ƙungurmin ƙauye aka gano su, koya akayi ta iya zaman wannan ƙauyen oho"

Mummy tace "su suka sani, ni dai tunda an kamo su na fara jin ƙamshin samun kuɗin nan"

Ramlah tace "Ance yana can hannun 'yan sanda ido ya raina fata, tun jiya ya fara cin ƙaniyarsa a hannunsu, ai gara yaji jiki, kafin a shiga kotu ya raina kansa"
Chapter 73 · 0% Book details