← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 127

Sashe 94

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Widad se kaffakaffa take da Cikinta, kar Bulama ya gane cikin nan yana nan be fita ba, dan ya fara ɗagawa sosai tana jin motsinsa, wasu lokutan yaji yana motsi sosai, wani lokacin kuma yayi dankam motsinma se kaɗan kaɗan, mussman idan bata da lafiya, duk lokacin da taji ya daɗe be motsa ba se tai taɓa cikin tana addu'a Allah yasa ba wani abunne ya sami abunda take ɗauke dashi ɗin ba.
Cuta kuwa kullum a cikinta take, gashi babu me gayamata yi kaza bar kaza, ita dai Sabuwa ta kan tirsasata ne taci Abinci, amma babu magani ga kwanciyar ƙasa da take, da shan abu me sanyi duk se tabi ta kukkumbura, babu hanyar zuwa Asibiti, ga Fahad dayake yawan kawo mata farmaki wasu lokutan, dan haka baccinma ba iya shi take cikin kwanciyar hankali ba, sedai tana yi tama farkawa, gani take da nannauyan bacci ya ɗauketa Fahad ze shigo yai mata wani abun.
Haka rayuwar Widad ke tafiya a wannan gurin da take, gashi dai yafi ɗakinta na ƙauye nesa ba kusa ba, amma ɗakinta na ƙauye ya fiye mata daɗi da kwanciyar hankali akan wannan ɗakin da take ciki haka a cike da wannan damuwar da tashin hanaklin.

Se wajen laa'sar sannan Ramlah ta dawo hayyacinta, daga wannan muguwar buguwar da tayi, taje tayi wanka ta canza kaya, ta nemi abunda zata saka a cikinta, ba tare da ta kula kowa ba, Hajiya Halima ce ta bita ɗakinta, ta sameta tana ƙoƙarin fara cin Abinci.
Ta ƙare mata kallo sannan tace  "Ramlah, wannan rayuwar ita kika zaɓawa kanki ko? Rayuwar shaye2, Ramlah kwalba huuɗ fa kika shanye a cikinmi, ke ko tsoron lafiyarki bakya yi, bakya tausayin halin da nake ciki ko? Ban san inda ɗan uwanku yake ba, ga wannan uban naku yana ta min barazana akan ze tonamin Asiri, amma a haka kike ƙara gayyato mana wata matsalar, meyasa haka Ramlah? "

" Dan Allah Mummy ki ƙyaleni injibds abunda ya dameni, ni Fahad ze kalla yace baze Aureni ba, bayan tuntuni yasan zaman jiran sa nakeyi, amma zemin haka"

"to yanzu dan yace naze aureki ba shine zaki kashe kanki? Shine zaki sha wannan maganin haka? Haba Ramlah shikaɗai me namiji ko shine autan maza, kina gani kuɗaɗen hannuna duka babu sun ƙare, shine yake kawo mana wanda suke siyan kadarorin nan fa a ɓoye, ki lallaɓashi ku rabu lafiya mu samu mu sake wawurarar abunda ya samu mu siyar, idan muka siyar seki ƙyaleshi, Allah ya baki wani ki aura"

"Mummy, ni gaba É—aya ma nakasa gane kan maganganun nan da kikeyi fa, kamar yaya babu kuÉ—i a hannunki, ina duk kuÉ—aÉ—en da kika saida filayen nan? Duk suna ina, kuma ga wannan kuÉ—aÉ—en da ake saka rai na gurin Bulama daze samo a hannunta suma basu samu ba, abun yazo da rainin hankali fa"

"wai bana gayamiki ubanku ke tamin barazana ba, kin sam maƙudan kuɗaɗen daya karɓa kuwa  hannu na?"

Ramlah tace "wai wannan jakin da yazo harya mareni kike nufi?"

"Eh, shu'aibu dai"

"to meyasa kike bashi?"

"Ramlah idan shu'aibu ya tinamin Asiri na kaÉ—e, dan na gama yawo, mutumin nan hatsabibin gaske ne, baku da wayo lokacin da muka rabu ai"

"Lallai Mummy, wallahi dana san hakane baza'a bashi ko kobo ba, sedai yaje ya tina karya fasa, yanzu shikenan mun tashi a tutar babu? Duk wannan baƙar wahalar da mukayi? Yana gefe kika dinga tura masa kuɗi, baze yuwu ba Wallahi"

"bazs yuwu ba kamar yaya? Ai tuni ya yuwu, bashi kuÉ—in nam sune rufin asirinmu, kuma karki kuskura kice zakiyi wani abu, kinji ma gayamiki sannan Ramlaj ki shiga hankalin ki, akan wannan mummunar É—abi'ar, babu inda zata kaiki shaye2 ba abunyi bame, kuma ba cinyewa bane "

'mhmm Mummy kenan, yadda raina yake a ɓace idan har ba caji nayiwa kaina ba bana jin daɗi, kawai ki ƙyaleni idan kuma kina buƙatar in dema shaye2 to tabbas Fahad ya aureni, idan bahaka ba bakiga komai ba har yanzu"

"Ramlah ni kike gayawa haka?"

"Ai gaskiya na gayamiki ba wani abu bz, idan harya Aureni shikenan an wuce gurin saɓanin haka kuma, komai ma zaki iya gani"
Ta ƙarasa magana, tare da fara cin Abimcinta, bata sake bi ta kan mahaifiyarta dake kallomta da mamaki ba.

Jiki a saɓule Hajiya Halima ta tashi ta fita ta bar ɗakin Ramlah, ranta sam babu daɗi, wai yanzu Ramlah ce a wannan mummunar hanyar.

Alhaji Musa sosai yake jin zuciyarsa tana ɗarsa masa wani abiua ransa, yana zargin Bulama kawai ƙoƙarin kifesu yake yi, yana can yana zare zaren, dan haka dole zeyi wani abu a akai, ta ƙarƙashin ƙasa ze bincika ya hani ko Bulama na karɓar wani abu basi sani ba.

Yauma akazo akace ana son ganin Yusuf, ya zata ma ko Ummace ko Suleiman wani ya kawo masa ziyara, sedai still wannan ɗan sandan ya gani, se wasu gandirobobi, aka saka Yusuf a wani tsukakkaken ɗaki, da gashi sesu a ciki, aka zaunar da Yusuf ɗan sandan ya kalleshi yace  "Hmm Nasan kayi mamaki, ganin yarinyar daka ceta ta juya maka baya taje kotu ta bada sheda akanka ko? Dama haka mata suke basu da tabbas, gashi tana can tana hutawa, ranar da za'a yanke maka hukunci, a satin za'a ɗaura mata Aure da Fahad Bukar Bulama.

A razane Yusuf ya kalleshi yace  "Bukar Bulama kuma?"

"Au kana mamakine? Ƙwarai Ɗan gidan Bukar Bulama, wato Fahad, yanzu haka ta aiko mune gurinka, akam cewar akwai ajiyar wani recording data baka, ka gaya mana inda recorder ɗin take, zamu je mu ɗauka '

Hankalin Yusuf sam baya kan ÆŠan sandan, sedai nanata Bukar Bulama day keyi a zuciyarsa, wato abu biyune ya haÉ—ar masa, ga mamakin Jin an Ambaci Bulama da Bukar, to kenam shine Bukar É—in da Widad take magana kokuwa? Idan shine ya akayi gake zaune a hannun sa? Idan ya cutar da ita fa? Sannan wani irin azababben kishi ya taso masa, dagaske Widad É—insa ce zata Auri Fahad?
'to idan bata aure shi ba me kake so tayi? Kaida rayuwarka zata ƙare a kurkuku, kuma taje har kotu ta bada sheda akan ka' wata zuciyar ta tunasar dashi, amma dukda wannan abun ya kasa jin tsanar Widad a ransa, shi wani irin tausayinta ne yake kama shi ma, kuma gefe guda zuciyarsa ma cigaba da begen sake kasancewa da ita.
"Kai Malam magana nake maka fa!"
ÆŠan sandam yai maganar cikin tsawa, Yusuf be razana ba ya kalleshi yace "ita Widad É—ince tace maka ta bani wani abu ajiya?"
"zan maka ƙaryane?"
Yusuf yace "to meze hana kayi ƙarya, tunda mutum ne kai ba mala'ika ba, kamar yadda tace muku ta bani ajiya, tazo da kanta ta Karɓa, ta gayamin lokacin data bani, sannan ta karɓa"
Ɗan sandan yai ƙasa da murya yace  "ka bani tunda wuri, ko kuma a ran mahaifiyarka"

Yusuf yace "Ran mahaifiyata yana hannun Allah, babu wanda ze iyayi mata abunda Allah be rubuta ze sameta ba, Magana É—ayace, ni bata bani komai ba, idan kuma ta bani ku kawota ta gayamin lokacin data bani ajiyar recording É—in"

Ɗan sandan nan ya jinjinawa azababben baƙin taurin kai irin na Yusuf, ya kalli gandirobobi yace  "ku tambayeshi"

Yusuf be motsa daga inda yake ba, suka dinga buga masa kulki kota ina, sedai yana ƙoƙarin karewa, babu wata gaɓa ta jikinsa da bata masa ciwo saboda azabar dukan da yake sha a kowane lokaci.
Suka farfasa masa jikinsa, banda targaÉ—e dake yatsunsa saboda duka.

'zaka bamu ko bazaka bamu ba"?

Yusuf yace "ni bata bani komai ba na gaya maka, karka ƙara tambaya ta"

Ya ɗaga hannu ze wanke Yusuf da mari, Amma jarumin ya riƙe hannunsa yace "karka kuskura ka mareni, kuyita dukana har lokacin da zaku ga na dena numfashi, tunda haka kuke so, amma karka kuskura ka sake ɗaga hannu kace zaka mareni"

Suka kum sashi gaba da duka, seda suka ga baya motsi, sannan hankalinsu ya kwanta, suka tafi suka barshi a gurin.

Widad na zaune kawai taji gabanta ya faɗi, hakan yasa kawai ta fashe da kuka, domin ta fuskanci kamar idan Yusuf yana cikin mawuyacin hali se taji wannan faɗuwar gaban, ai kuwa ta hau aikin kuka, tayi ta gaji ta haƙura, ta cigaba da yi masa addu'a, tans tuno irin haƙurin daya dingayi da ita, ga rarrashinta da yake yawan yi, da yadda ta koyi abubuwa da dama a sanadin zama dashi Yusuf mutum ne, wani irin shauƙin soyayarsa ne ke taso mata, ta rintse ido ko zata samu sassauci a zuciyarta, tana jin inama tana buɗe idonta ta ganata a kusa da Yusuf, lallai so ba ƙarya ne ba.
"Allah ya fitomin da kai Yoseef, ka dawo muyi rayuwa tare, mu rainin cikin nan tare da kai, nasan da muna tare zan samu kulawarka" tai maganar tana hawaye.

Can kuma tayi wani tunani a ranta, wani irin kallo Yusuf zeyi mata idan Allah yasa ya fito, bayan taje ta tsaya a gaban mutane ta tabattar da Yusuf saceta yayi.

Cikin kuka tace "wayyo Allah na, Yoseef kayi haƙuri ba laifina bane, nayi hakan ne dan in ceci rayuwarka, karsu kashemin kai, ban manta halaccinka a gareni ba Yoseef, ba yadda zanyi ne"

Sabuwace ta shigo da sauri tana faÉ—in "lafiya kike kuwa? Kinga ki dinga ramgwatawa kanki wannan kukan da kike yi haka, naji ance kina da ciwon zuciya gashi ba ganin likita ake kaiki ba, karki kashe kanki a banza mana"

"Ni ki ƙyaleni inyi kukana, baki san abunda yake damuna ba, ki rabu dani dan Allah ki ƙyaleni"

Sabuwa tace "A'a Allah ya baki haƙuri, na ƙyeki yi abunki som ranki"

Widad ta cigaba da gunjin kukanta.
"Allah ya isa tsakanina da kai Bulama, Insha Allah se gawar jaki tafi taka daraja, Azzalumi macuci"

Bulama yace  "yi addu'arki da kyau, ai ina kusa ba nisa nayi ba, duk abunda zaki faɗa ki faɗa"

"me Yoseef yayi maka? Meye laifin da yayi maka da kake azabtar dashi haka, kake neman cutar da rayuwar sa Kasashi a garari?"
Chapter 94 · 0% Book details