← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 127

Sashe 49

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hindu ta tsiri yin Faten tsaki, Widad tace suyi a kan risho ɗinta, suka gyara yakuwa tare da kabewa, anan Jamila ta sake lura shikansa aikin Widad bata iya ba, danma ba tun farkon zuwanta taga kwaɓar da Widad take ba.

Akayi fate aka gama, suka zuba suka fara sha, Widad da ƙyar tai spoon biyu tace

"ni gaskiya wannan abun ba daÉ—i, tayar min da zuciya ma yake, ga tsami ga gishiri ni na kasa gane ma meye taste É—in Abincin"

Jamila ta dinga tsokanar Widad, wai kodai cikine kuma baya son faten, ita dai Widad har yanzu bata sake da Jamila ba, amma taji daÉ—in bayanan da tayi mata.

Kuma babban abunda yake burgeta da Jamila, kullum jaririyarta tsaf da ita, kuma idan taje É—auka bata hanata, tana bata ta É—auka.

Jamila tace "kun shirya kuwa?"

Widad ta tura baki tace "baya ƙi kulani ba, me zance masa?"

Jamila tace "kinga abunda nake gayamiki ko? Allah yasa ba budurwa yayi ba wadda zata dinga tarairayarsa ba"

Zare ido Widad tayi ta harari Jamila tace "shi ya isa ma?"

"Au haka kika ce?"

"Eh haka nace"

Jamila tayi murmushi tace "ai shikenan, cikin hira ta cigaba da ganar da Widad wasu al'amuran, dukda wani lokacin in anyi gabas se tayi yamma.

Da yamma taga su Gwaggo suna ta shirye shirye, Widad tace" Mama ina zuku ne kuke ta shiri haka? "

Gwaggo tace  " bikine zamu wani ƙauye a gabanmu, Yayar Baffa ce zata yi Auren 'ya"

"Mama zan biku nima dan Allah"

"Ahh haka kurum, da mijinki da komai a' a ba ruwana"

Widad ta marairaice tace  "dan Allah Mama"

Gwaggo tace "to ki tambayi Yusuf tukuna, danmu kwana uku zamuyi"

"to ai bazece komai ba, dan Allah nidai zan biku zanje nima in haÉ—a kayana"

"Amarya, babu yadda za'ayi muyi tafiya dake, ba tare da kin nemi izininsa ba, idan ya bari bakomai semu tafi'

Widad tace  " bari yazo in tambayeshi to "

Wani wahalallaen bacci ne Nurat take yinsa bayan sallar Azahar, wayarta dake ƙasan pillow ta fara vibrating, a ɗan razane ta farka, tasa hannu a ƙasan pillowa ta ɗakko wayar, ta amsa sannan ta saka a kunnenta   "Hello Brother"

"Nurat, kina gida ne zan shigo yanzu?"

Ta miƙe zaune da sauri tace "No karka zo dan Allah, Daddy yana gida yanzu ze iya fara zargin wani abu, kuma kasan ya hanani fita, amma me ake ciki?"

Khalil yace  "Aikin da kika bani na fara, amma ko kin san cewa Yusuf ɗin nan ɗan sanda ne?"

"Kamar yaya? Wai dama dagaske ne shi ɗan sanda ne? Naji a labarai na zata ƙaryane ai"

Khalil yace "to gaske ne, É—an sanda ne na farin kaya, yayi basaja yaje a matsayin direba, kuma yayi garkuwa da yarinyar"

"Kahlil saboda wanke Yusuf yasa na sakoka a cikin wannan lamarin, dan Allah karka ƙara danganta Yusuf da wannan mugun aikin, baze taɓa aikata haka ba na tabatta"

Khalil yace "shikenan naji, karkiyi kuka, ai ina kan yin bincike ne, ban tabattar ba, abun da ake ciki zan miki magana, amma banda kuka kinji ƙanwata"

Nurat ta gyaÉ—a kai kamar yana ganinta.

Widad da wuri ta sallami ɗalibanta yau, dan wasa wasa da yammar nan cika tsakar gidan Megari akeyi, an samo musu alli da allo na rubutu, sannan kowa da littafinsa da abun rubutu, babban abunda yake burge Widad be wuce yadda suke girmamata ba, suna girmama malami a ƙauyen nan, kuma a hankali tana jansu a jiki yanzu, musamman 'yan ƙananan yaran nan, da sunzo kwanukanta ɗakinta har tsakar gidan duk se subi su gyara, saboda tsabar girmamawa.

Widad nata ɗokin Yusuf ya dawo ta tambaye shi, dan harta manta sunyi faɗa, seda ya dawo taga ba fuska, Yusuf be taɓa mata kwarjinin da yayi mata yau ba, sam ta kasa masa magana sedai kallonsa kawai da take yi.

Koda yayi alwala ya fita sallar magariba, se bayan isha'i sosai sannan ya dawo, ya É—au Abincinsa ya fara ci, ta zuba masa ido amma ta kasa magana, can dai taita maza tace

"Yoseef dama, su Mama ne zasu je biki, shine tace in tambayeka idan zaka barni in bisu, inje inga yadda akeyi"

Banza Yusuf yayi mata, kamar beji me tace ba, "Yoseef magana fa nake maka"

"Kiyi abunda kika ga dama kawai" ya bata amsa.

Jin maganar tayi wani banbarakwai ba tsari, wai tayi abunda taga dama.

"Ka barni inje kenan?"

"Meye na tambayata kuma ne? Nace kiyi abunda kika ga dama, ai damani baki É—aukeni miji ba, na kan manta in wuce gona da iri wasu lokutan, waini game mata, na kan manta ashe nifa direba ne, iyakaci in miki aiki ki biyani, dan haka idan harni mininki ne, to ban yadda kije ba, sedai nasan ba lallai ki yadda da hukunci na, saboda ban kai a kirani mijinki ba, ban isa komai a gurin kiba, dan haka kiyi abunda kike so, zama ko zuwa ya rage naki"

Yana gama maganar ya tashi ya bar mata É—akin, wani malolon takaicine ya tokare mata zuciya, dama Wai Yusuf ya iya fushi haka?

Har washegari be kumabi takanta ba, tana ji tana gani su Gwaggo suka shirya yaransu da manyansu suka tafi aka barsu a gida, Jamila na ɓangaren ta nata bisu ba, se abokiyar kishin Widad wato Hanne bata bisu tace bata da lafiya ita bazata ba dan haka tana gida itama.

Da daddare Yusuf ya idar da sallar isha'i yana lazimi, Widad a hankali tace 
"Yoseef" ta kira sunansa kusan sau uku, amma yayi shiru, can tace

"Yuzarsef"

Da sauri ya ɗaga ido ya kalleta jin sunan data faɗa, dukda be amsa ba amma taga damuwarsa ta ƙaru, ya kifa goshinsa akan gwiwar ƙafafuwansa daya ɗage.

Sanye da zumbulelen hijjabinta tazo, tasa hannu ta É—ago fuskarsa tace "wani laifin na kuma yi maka dan na kiraka da Yuzarsef?"

Girgiza mata kai yayi, alamar a'a yana ƙoƙarin maida kansa.

Ta sa hannu biyu ta tallafi fuskarsa tace "Yoseef, me nayi maka ne? Dan Allah kayi haƙuri"

Yusuf yace "aini baki min komai ba, sedai yau ina son in san saki nawa kike so in miki?"

Gabanta ne yayi mummunar faɗuwa, tace  "kamar yaya? "

Yace  "kamar yadda na tambayeki, saki nawa kike so?"

"Yaushe nace maka haka?"

Yace "kin manta abunda kika gayamin ne? Ina son in koyawa kaina rayuwa ko babu ke ne, kusan koyaushe kina maganar in sakeki, duk ƙoƙarina bakya gani, bakya tausayamin ya zanyi? Gara idan muka rabu inda wani ɗakin duk rashin kyansa a bani, in lallaɓa in fara koyawa kaina zama ko babu ke"

Aikuwa ta fashe da kuka tace "nifa ban san nayi ba, ban san meyasa nake jin haushi idan naga wata ta raɓeka ba, tun jiya nake maka magana, amma kana shareni, se kulaka nake amma kaƙi ko kallona, na tambayeka abu ka hanani, kuma banyi ba, amma ka kama min faɗa, you want turn on me ko, shikenan"

Ta juya zata tashi ya Riƙeta, yace "babu wani dalili da zesa in juya miki baya, sedai nine kin kasamin adalci, bakya iyayi min adalci a wasu lokutan, kiyi ta bani wahala saboda kinga ina sonki ko?"

Share hawaye tayi, ba tare da tace komai ba, Yusuf yace "yanzu me kikeson ayi?"

"Ka dinga kulani, ka dena É—auremin fuska"

"shikenan za'ayi yadda kike so, amma da bakinki nake son ki faÉ—i saki nawa kike so?"

Shiru tayi batayi magana ba, sema sunkuyar da kanta da tayi tana kallon wani gurin daban.

"Widad magana fa nake miki"

Ɗison hawayen ta ya gani yana ɗigowa a ƙasa, taƙi ɗaga kanta kuma taƙi magana.

Yace "shikenan, tashi kije ki kwanta"

Ta miƙe sum sum ta tafi katifarta ta kwanta, tai shiru tana tunani, wai yanzu dagaske Yusuf yake sakinta zeyi, se taji gabanta ya faɗi, 'to meye dan ya sakeki, dama ai akan haka kuke' wani sashe na zuciyarta ya gayamata.

'Amma dukda haka nayi sabo dashi, sabo me ƙarfin gaske, yanzu idan ya rabu dani ya zanyi? Zan koma irin rayuwar kaɗaici na ta baya kenan?'

Kawai ta sake fashewa da kuka, yana jinta amma yai shiru kamar be san tana yiba, se can dare bayan ya idar da sallar dare, yayi addu'oin da zeyi sannan ya tao a hankali ya hau kan katifar ya rungume ta a jikinsa, lokacin har riga tayi bacci, wannan fushin da yayi da ita na kwana biyu shikansa yaji a jikinsa, dan ba ƙaramin kewarta yayi ba, a jininsa yake jin soyayyar Widad na ratsashi, shi dai yana matuƙar sonta.

Kamar yadda Suleiman ya buƙata, Abbas yaje office ɗinsa, seda ya ɗan jira ya sallami baƙi sannan ya ganshi.

Bayan sun gaisa ne Suleiman yace "Abbas ashe ka shigo garin nan babu Labari, sekace wanda akayi zaman gaba aika leƙo a gaisa '

Abbas ya ɗan sosa kai yace " Ai Yallaɓai abubuwan ne dama duk se a hankali, kuma ni ɗanje ziyare ziyare ne, shiyasa amma dama can nayi niyyar in ɓullo a gaisa ai, da amana bazan watsar daku ba"

Suleiman yai murmushi yace "shikenan, ya aikin ya hanya?"

"Alhamdilillah, aiki can ai har yafi nan daÉ—i"

Suleiman yace "madalla ai haka ake so, nace ka kuwa ji abunda ya faru da Yusuf?"

Abbas yace "naji yallaɓai, abun ya bani mamaki, mutum a fuska mumini amma zuciyarsa ba Allah, saboda son zuciya kawai daga aiki seka yi garkuwa da 'yar mutane, gaskiya bewa kansa adalci ba, Yusuf ya bada mamaki"

Suleiman yai ƙuri da ido yana sauraren Abbas, se da ya gama sannan yayi ajiyar zuciya yace "to ai koma menene Allah baya bacci, kuma muna bayan ɗan uwanmu, Insha Allah, sannan bama saka ran Yusuf ze aikata abunda ake tuhhmarsa dashi sam, yanzu ni babban abunda yaaa na kiraka shine, kaga kaine babban Abokinsa, mahaifiyarsa tana cikin damuwa ƙwarai, naje gurinta take cemin taji ance kaje amma ba kaje ka mata jajen abunda ya samu Yusuf ba, dan Allah ka daure ka zagaya kayi mata jaje ko ka ɗebe mata kewar ɗanta"

Abbas yace "shikenan, dan dai wannan insha Allah daga nan ma zanje, Allah sarki insha Allah zan biya in gaisheta"

Suleiman yace "ba laifi hakan yayi kyau"
Chapter 49 · 0% Book details