Sashe 93
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
" Aurena da Fahad, ba abune me yuwuwa ba, ka gayamin shima ya gayamin, nagode nima ku jira matakin da zan iya É—auka "
Ta bar office ɗin Bulama, zuciyarta na ƙuna da raɗaɗin abunda sukayi mata, Amal na zaune a falo tana kallo, cikinta ss ciwo yake mata, ga wani irin ciwon baya da take fama dashi, gashi lokaci lokaci inda ta karye yana motsa mata.
Ramlah tana parking ta fito, ta buga ƙofar motar da ƙarfin gaske, tai ciki fuuuuu, kamar guguwa, Nura yace "Allah dai ya kwashe ma wannan baiwa Albarka, da ita da duk wanda suka je kotu suka bada shedar ƙarya akan Yusuf"
Murtalah yace "bari Nura, wallahi abun ya bani mamaki sosai, Amma nan aka zo aka taramu aka mana kashedi akan duk wanda yai wani yunƙuri, ze fallasa wani abu se an kasheshi, wayaga ta bakin magana, amma da tabbas nima sena bada sheda"
Isa yace "dan Allah Murtalah kaje ka bada shedar nan a saki Yusuf, wallahi zaluntarsa kawai ake yi"
Nura yace "Allah sarki duniya, kalli Isa wai kaine ke cewa ayi abunda za'a temaki Yusuf, abun da mamaki"
Isa yace "bari Nura, wallahi duk baƙin cikin mutum da iya ƙiyayyarsa, idan dai har mutum ya zauna da wannan bawan Allah, wallahi idan kaji za'a masa haka dole ka tausaya masa, kalli duk irin abunda muka dinga masa baya tanka mana, se azabar miskilancin tsiya a cikinsa kamar Uwarɗakinsa"
Nura yace "kai dai bari Isa"
Isa yace "kun san abunda ya É—auremin kai kuwa?"
Sukace A'a
"Wai ashe Sani me yankan farce shima ɗan sanda ne, shine fa ya haɗani da Yusuf yace ɗan uwansa ne, dana gayamasa ana neman direba, amma naji wannan lawyern yace wai Abbas be san zancen ba, Amma duniya babu gaskiya, tabbas yanzu nake ganin gimbiyar Daula bata da laifi na ƙin mutane, ka yadda da mutum ya cuce ka a banza, yanzu duk wanda suke jikin Daula suna morarsa sune suke zalintarsa, kalli matar gidan nan ko sau ɗaya ba taje kotun nan ba"
Murtalah yace "iko se Allah, wallahi Isa da zamu samu dama ko iya wannan shedun muka riƙa, aka shiga kotu dasu zasu temakawa Yusuf, amma wallahi ina jin tsoro, kuma wallahi dani akan matar gidan nan zan bada shedata"
Nura yace "kai ita ta dameka, a samu a Yusuf ya kuɓuta, wallahi dukda nima inajin haushinsa yadda ƙirƙiri ya samu fada fiye damu a gidan nan, musamman ni daya nemi ya ƙwacemin aiki na, Amma gaskiya Yusuf baze aikata haka ba, kalli fa ko magana ake, idan aka sakota ko aka zageta seya haɗe rai yana ɓata fuska yana kare ta, wallahi da yayi niyyar sace ta da tuni ya saceta, akwai dai yadda akayi "
Nan suka cigaba da tattaaunawa suna hirar a tsakaninsu.
Ramlah kuwa tana shiga falo, Amal ta kira sunanta, Ramlah ta waigo a fusace tace " lafiya kuwa? "
" Ashe kema kim bada sheda a kotu akan Yusuf "?
" Eh na bayar se yaya? "
" Yakamata kiyiwa kanki adalci Ramlah, a bar bawan Allah nan da wahalar da aka jefa shi a ciki, bakya ganin saboda Alhakinsa ne muma namu ɗan uwan yana nan kwana da kwanaki ba'a ganshi ba, ga mahaifiyarmu se fama take da marurar hawan jini saboda damuwane da ɓacin rai? "
'Ke dalla sauraramin, an bada shedad kiyi abunda zakiyi, da aga Anwar da kar a ganshi be dameni ba, abunda yake gabana shi zanyi, kuma karki ƙara yimin wannan maganar"
Ta nufi É—akinta, tana jin yadda zuciyarta take tafasa.
Tana zuwa ta jefar da Jakarta akan gado, ta buɗe wardrobe ɗinta ta ɗakko kwalaben syrup, kawai ta kafa kai ta kama tittilawa cikin ta, Hakan yai dai dai da buɗe ƙofar ɗakin da Hajiya Halima tayi, ta tarar Ramlah ya shanye kwalaben syrup ta faɗi a gurin, cikin fitar hayyaci.
"Na shiga uku, Ramlah me zan gani haka? Ramlah dama dagaske shaye2 kike? Me yasa zaki cuci kanki"
Sam Ramlah bata san me ake ba, tuni ta fara maye ta lula gajimare.
"Amal! Amal!" ta shiga ƙwalawa Amal kira.
Amal tazo tace "gani"
"Amal kinga, shaye2 Ramlah take yi, meke damunta haka zata faÉ—a wannan mummunar hanyar haka?"
Amal ta ɗan taɓe baki, tare da naɗe hannunta tace "Allah ya jiƙan Yaya Anwar, ba dan ya mutu ba, nan ya hukunta ta ya gayamiki ga abunda take yi, amma baki yadda ba, tuntuni take shaye shayenta, kuma wannan Fahad ɗinne ya koyamata, amma ba yau ta fara ba"
Hajiya Halima tace "Na shiga uku ni Halima, wannan wace irin masifa ce haka, Ramlah dama baki dena wannan halin ba, Kisha kwalba huÉ—u a cikin ki?"
Amal kam taɓe baki tayi tai nata guri ta barsu.
Kamar koda yaushe, yauma zaune suke suna tattaunawa, Bukar yai gyaran murya yace 'ga samu ga rashi, labaran kala biyune, masu daɗi da kuma akasin hakan, wannan yaron munyi magana da A dutse, ya tabbatar min a zama na gaba ze ƙarƙare shari'ar yaron nan, sedai wani hanzari ba gudu ba, ita wannan yarinyar da yake ita uwar Daula ce a jarabar taurin kai, taƙi bayar da abun nan, ba irin azabtarwar da banyi mata ba, amma taƙi ƙarshe ma se cewa tayi ai "Recording ɗin inda dukiyar take Daula yayi, ya bata itama bata san inda dukiyar take ba, kuma wai recoding ɗin yana hannun Wannan yaron Yusuf"
What! Cewar Alhaji Munir "to yanzu meye abunyi?"
Alhaji Musa yace "kawai aje kurkuku ta ƙarfin tsiya ace ya bayar"
Bukar yace "Mhmm, baku san azabar taurin kan mutanen nan ba, ya saka hannu kawai mugani a tabattar idan wannan signing ɗin nasa ne, me kama dana Daula, amma wallahi fafur yaƙi, shima an azabtar dashi kamar kamar me a gidan yarin nan amma yaƙi, na rasa abunyi"
Alhaji Haruna yace "a sake azabtar dashi mana, ya faÉ—i inda recording É—in yake, ko kuma aje a É—auke mahaifiyarsa, ai naga tana zuwa kotun"
Bukar yace "ai abun ya wuce tunaninku, idan mukayi wani yunƙuri zamu iya barin ɓarakar da za'a ganomu, komai a sannu ake samun sa, zan cigaba da bibiyar yadda za'ayi a samu"
Suka gama tattaaunawa suka watse, dama a office É—in Bukar sukayi meeting É—in.
Bayan fitowarsu Alhaji Haruna yacewa Alhaji Musa "Waini anya ba raina mana hankali Bujar keyi ba, yarinyar nan tana hannunsa fa, babu wanda yasan inda take, ta yaya za'ace ko yaya bata gaya masa wanj abun ba, nifa kamar mutumin nan raina mana hankali yake"
Alhaji Musa yace "kai dai bari kawai, kallonsa kawai nake yi, gaba É—aya kuÉ—aÉ—enmu sun tafi akan wannan harkar, amma Har yanzu babu wata riba"
"ba gara kaiba akaina, ni kamanta wannan yarinyar ta damfareni, rabin kuÉ—in account É—ina ta kwashe fa"
"kasa a sato maka ita, kaci ubanta ta mayar maka da kuɗinka, ni yanzu kallon Bukar kawai nake idan be wasa ba, zan ɓallo ruwa...
LITTAFIN KUÆŠI NE, IDAN KIN SIYA AMANANE, IDAN KIKA FITARMIN KINCI AMANA, KIMIN ADALCI KIYIWA KANKI
AYSHERCOOL
07063065680
11/29/21, 8:55 AM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
138_139
Alhaji Haruna yace "kamar yaya zaka ɓallo ruwa?"
"Eh zan ɓallo ruwa mana, muddin naga za'a cuceni, zan tads husuma ne, daga fara harƙallar nan zuwa yanzu zunzurutun kuɗi nawa muka kashe? Haka abun yayi yawa, mutumin nan ba imani ne dashi ba, ze iyayin komai dan haka gara mu saka ido yadda yakamata"
Alhaji Haruna yace "hakane kam, shikenan se anjima se yadda ta yuwu"
Daga nan suka watse.
Ramlah har gari ya waye, tana tangaɗi bata san me takeyi ba zabo maye, kwalba huɗu ta shanye babu sirki da komai, tayiwa kanta caji na sosai, yayin da Hajiya Halima ta dinga kuka, ganin yadda shaye2 ya ratsa Ramlah haka, ga ɓatan Anwar yana cin zuciyarta, gashi duk 'yan kuɗaɗen data tara Shu' aibu ya karɓesu, ta rasa inda zata saka kanta.
Amal kam bata tasu takeyi ba, gaba ɗaya bata jin daɗin jikinta, ta rasa takamaimai meke damunta, tana zaune tana danna wayarta taga wani business, wanda idan kayi investing kuɗinka, zasu nunnuku a lokaci kaɗan, nan da nan ta gyara zama tana sake duba yadda bayanin abun yake, ta shiga link ɗin group ɗin da aka bayar, taga yadda mutane keta comments wai sun sak kuɗinsu an riɓanya musu an basu.
Nan wani tunani yazo mata, dan wannan maƙudan kuɗin da suke account ɗinta bata san ya zata yi dasu ba, dan haka ta jarraba saka naira dubu hamsin, bayan awannin biyar aka turo mata dubu ɗari da biyu, abun ya bata mamaki, nan ta dinga murna akan ta samu sana'a daga kwance zata dinga samun kuɗi.