← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 127

Sashe 12

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf ya dinga wasa da gashin, yana ɗaga shi yana wasa dashi, can Widad tace 

"Yoseef wai dan Allah Aure dolene? Sannan meyasa ake Aure ne?"

LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

56_57

Dariya tambayar tata ta bashi yace 

"Habibty wannan wace irin tambaya ce haka kuma?"

"Kaima wannan wane irin sunane, ni dan Allah ka dinga faÉ—ar sunana"

"to naji Wudas"

"Allah ka ƙara gayamin kaima sena samo wani sunan na sama ka mara daɗi"

Dariya yayi yace  "ke baki san ina matuƙar jin nauyin faɗar sunan nan bane? Yanamin nauyi a bakina, bana iya faɗar sunanki fa"

Cikin Shagwaɓa tace "to meye abun wahala a Widad ɗin?"

"ƙaunar da nakewa me sunan ne yasa yake min nauyi"

"kaga ni duka ba wannan ba, ka bani amsar tambaya ta"

"meyasa kika tambayeni?"

Widad tace  "na tambaye ka kuma kana tambayata"

"to ai tambayar ta kice tazo a wata iri, nama rasa me zance miki"

A waje daka ke koyarwa in sun tambayeka wace amsa kake basu? "

" ƙureni zakiyi kenan? "

" ba wani ƙurewa ka bani amsa kawai "

Yusuf yaja ajiyar zuciya yace "Aure ba farilla bane, amma yana da fa'ida tunda Allah ya halatta yinsa, idan kika duba akwai tarin hadisan manzon Allah salallahu alaihi wassalam da suke magana akan Aure, sannan akwai ayoyi a cikin Al'qur'ani da suke magana akan Aure, akwai wani Hadisin Annabi salallahu alaihi wassalam yace  'kuyi aure ku hayayyafa domin inyi alfahari daku ranar Alƙiyama, kinga anan yana daga amfanin Aure samun zuriya, yin aure ka haifi' ya'ya nagari babban Alkhairi ne shima duba ga hadisin manzon Allah salallahu alaihi wassalam da yace 'idan bawa ya rasu dukkanin ayyukansa suna tsayawa banda abubuwa guda huɗu, wanda ya mutu yana me imani da Allah, da sadaƙatul jariya sadaka me gudana, kamar gina rijiya makarantar islamiyya da sauransu, ko wanda ya sanar da wani ilimi wanda ko bayan ya mutu ske amfani da shi, da kuma ɗa nagari, kinga anan yana daga cikin amfanin Aure kayi shi ka samu ɗa nagari ka mutu ya dinga maka addu'a, duk ayyukan bawa suna tsayawa idan ya mutu, amma in kayi Aure Allah ya baka ɗa nagari, yana maka addu'a, kinga babbar ribace wannan, ko yayi wani aiki da ladan ze dinga iskeka. Akwai hadisin manzon Allah salallahu alaihi wassalam da yake cewa 'ya ku taron samari, wanda ya samu iko a cikinku  to yayi Aure, idan kuma bashi da halin yin Aure to yayi Azumi, kinga Aure yana da amfani domin shi katanga ne daga aikata zina, yana sanya nutsuwa a zukatan wanda suka yi shi, akwai tarin hadisan manzon Allah salallahu alaihi da ayoyi da suka yi magana akan Aure, dan haka Aure yana da mahimmanci sosai your majesty"

Ajiyar zuciya Widad tayi tace  "idan mutum be Aure ba ya aikata laifi?"

"A'a, kamar yadda na gayamiki Aure ba farilla bane, dan haka babu laifi ga wanda beyi ba muddin ze kiyaye iyakokin ubangiji ya tsare kansa daga aikata dukkan wani nau'i na Zina, sedai darajar wanda yake da Aure da wanda bashi da shi ba ɗaya bane, mussman mace duk abunda tayi na aiki kona ibada a cikin gidan Aurenta tana da lada, hakama namiji duba da gaba ɗaya shikansa Auren ibada ne, akwai wanda sam Aure be halatta suyi shiba, misali wanda bashi da abunda ze iya riƙe Auren, ko yake da wata nakasa da baze iya sauke haƙƙin iyalinsa na Aure ba wanda ze zamana da cutarwa a ciki"

Se kuma yai shiru, be kuma cewa komai ba, Widad ta sake gyara kwanciyarta a jikinsa tace  "to amma a haka akewa mutum wani kallo dan mutum be Aure ba, yau anyi abunda ya ɓatamin rai, yau na fara ganin anawa mutum rashin mutunci akan ba shi da saurayi, baka ga Abunda aka yi wa Hindu ba, abun ya bani haushi sosai ya bani mamaki"

Yusuf yace "To ai cikar mutuncin mutum shine Aure Habibty, kece kike masa wani kallo na daban"

"to tunda dai Auren ba dole bane, ai bekamata a dinga takurawa mutum ba, yanzu by mistake idan tayi Auren wani abu daba a so ya faru still ita za'a É—orawa laifi, gaba É—aya yau wani iri ta wuni tayi kuka sosai"

"Kin damu da Hindu sosai Gimbiya"

Widad tace "Wallahi kuwa, ina sonta har raina tana da kirki"

Yusuf yace "Ashe kin san meye son, nine kawai bakya so"

"Nifa ban san irin son da kai kake faÉ—a ba, amma ina jin Hindu kamar 'yar uwata, inaji dama gidanmu É—aya ace ina da sister nima, nifa da zasu yadda idan zamu koma gida in tafi da ita"

Yusuf yace "Ai kina dasu, gasu Amal nan da Ramlah suma sisters ɗinki ne, amma kike musu wulaƙanci"

Widad tace  "Wallahi na tsanesu, tsana mafi tsanani da ban taɓa yiwa wata halitta ba, kuma ina nan idan na koma gida se sun bar mana gida, dan ba gidan ubansu bane"

"Subhanallah meyasa?"

"Bakomai" ta bashi amsa tare da gyara kwanciyar ta a jikinsa.

A hankali yace  "bazaki gayamin ba?"

Shiru tayi masa taƙi magana, tana jin yadda yake ta jera numfashi, kamar wani mara gaskiya, zuciyarsa na harbawa da sauri da sauri, ga ruwan sama da yake ƙara zuba kamar da bakin ƙwarya.

A ɗan shagwaɓe Widad tace "Yoseef am scared, kuma sanyi nake ji"

Yusuf yace "calm down, muna tare ba abunda ze faru insha Allah, keep praying"

Ta jinjina masa kai, a hankali Yusuf ya shiga kiran sunanta, tana jinsa amma taƙi amsawa, sema wata kasala da take saukar mata.

Tana jin abunda Yusuf yake yi, amma ta kasa ko motsi, duk yadda Yusuf yaso tattara nutsuwarsa ya guje faruwar wani abu a tsakaninsa da Widad abu ya gagara.

Ba dan ruwan saman da'ake ta kwararawa ba kamar da bakin ƙwarya, da babu abunda ze hana mutanen ƙauyen da kewaye sanin abunda ya faru a tsakaninsu, saboda yadda Widad ta dinga kuka da neman temako, rakin tsiya da kuma Shagwaɓa.

Tun tana kukan har tayi shiru, muryarta ta dena fita sosai.

Seda Yusuf ya dawo hayyacinsa dafe kansa cike da dana sani, da tuhumar kansa akan wani ganganci ne ya É—ebe shi ya aikata hakan?

Widad se ajiyar zuciya take, tana kuka ƙasa ƙasa, gaba ɗaya Yusuf ya bata tsoro kuma ya bata mamaki.
Gaba É—aya jikin Yusuf yayi sanyi ya kasa magana, ya rasa mema zece mata.

A hankali yaja rigarsa ya saka, ya miƙe ya ɗau bokiti da tukunya ya fita tsakar gida, a cikin wannan ruwan da ake ya tafi rumfar da'ake girki, ya dinga tona cikin murhun, ya tattara gawayi da ƙyar ya tashi garwashi, ya ɗora ruwa.

Haka ya zauna ya dinga fama, seda ruwan nan yayi zafi sosai ya haÉ—a mata, ya kai banÉ—aki ya ajiye.

Shi kansa jikinsa a matuƙar mace yake, ya koma ɗakin ya shiga ya tarar da ita a inda ya barta a kwance tana kuka, Ya durƙusa ya ɗagota ya samata hijjabi, a hankali yace  "tashi muje ga ruwan wanka can na kai miki"

Bata kula shi ba ta miƙe tsaye, ta dafa bango sedai tana zuwa bakin ƙofa ta tsaya, saboda tsoro ga tsigar jikinta dake tashi, saboda wani irin sanyi da take ji, gashi gaba ɗaya tsakar gidan ya jagwale.

Kawai ji tayi yayi sama da ita, ya kaita banÉ—aki ya ajiye mata fitila, ya koma can tsallaken wajen rumfa ya tsaya.

Ta daɗe sannan ta buɗe ƙofar banɗakin, Yusuf yaje ya ɗauke ta ya maida ita ɗaki, shi be tsaya wani dafa ruwa ba, saboda garwashin duk ya mutu, a haka ya ɗebi ruwan da sanyi da komai yaje yayi wanka.

Ya dawo ya tarar da ita ta kwanta, ta duƙunƙune a cikin hijjabi, yasa bargo ya rufeta, shima ya kwanta kowa yayi shiru yana saƙe saƙe a cikin ransa.

Mussman Yusuf wanda dana sani da haushin kansa suka baibayeshi.

Wani private hospital aka kai Nurat, nan da nan suka karɓeta a emergency,  likitoci suka shiga ƙoƙarin ceto ran Nurat, ta hanyar tsaida jinin dake ta zuba a goshinta.

Da ƙyar jinin nan ya tsaya, aka nan naɗe mata goshinta da bandeji, goshin ya kumbura suntum har gefen idonta saboda buguwar da tayi.

Mahaifiyar Nurat da mahaifinta suna reception, Mahaifiyar Nurat tana ta goge Hawaye, ta kasa zaune ta kasa tsaye.

Likita ne ya fito ya samesu a reception, suka yo kansa gaba É—aya suna jero masa tambayoyi.

"ku kwantar da hankalinku, raunine kawai ta samu, Allah ya rufa asiri be shafi idonta ba, amma idan ta farfaɗo akwai gwaje gwajen da zamuyi muga inda yuwuwar ayi mata hoton Ƙwaƙwalwa, dan naga jini yana fita daga hancinta, karmu je ko akwai internal injury "

Mahaifiyar Nurat tace " Na shiga uku, hoton Ƙwaƙwalwa kuma likita? Ba dai haukacewa tayi ba? "

Tsaki Alhaji Musa yayi yace " kaga dan Allah ƙyaleta, na fahimce ka idan ta farfaɗo ɗin in akwai buƙatar hakan se ayi hoton, ni dai fatana Allah ya bata lafiya"

"dole kace a rabu dani mana, tunda ka kusa kashemin 'ya, kuma yanzu kana wani nuna kamar ka damu da ita"

"A nan É—inma sekin nuna halinki ko?"

"ban sani ba, kuma wallahi duk abunda ya samu' yata kaine"

Likita yace  "haba dan Allah yallaɓai, da girmanku da komai, hakan be dace ba ai, akwai marasa lafiya a kwance, kamata yayi kuyi ta lafiyar 'yarku ba faɗa ba"

Haka sukayi shiru likita ya wuce.

Wayar Alhaji Musa ce ta shiga ringing, ya ɗanyi gefe ya ɗakko wayar yasa a kunnensa yace  "Hello ina ji"

"kana inane? Akwai magana fa"

"ina Asibiti, an kwantar da' yata"

"Subhanallah meye ya sameta?"
Chapter 12 · 0% Book details