← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 127

Sashe 75

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'bana son in wahalar da kai kafin ka mutu Saleh, ko dan irin wahalar da kayimin, amma gaddama da taurin kai zesa in maka uƙuba wadda zata yi ajalinka, Saleh kaine ka bawa Widad da direbanta mafaka, kasan inda suke kaine ka kuɓutar dasu, dan haka karka wahalar dani, ko ka wahalar da kanka kafin ka mutu, ka gayamin ina ka kaisu"?

"Ni bani na ɗauke su ba, ban san inda suke ba, dan haka karka ƙara tambaya ta na gaya maka"

Bukar yace  "Shikenan, tunda baka san rarrashi ba, bari a biyo maka ta inda ya dace, Me Addda ku gasamim shi tsawon kwana uku, muga iya juriyarsa a mtsayinsa na kurtun soja"

Daga nan Bukar ya tashi ya fita daga É—akin suka rufa masa baya.

Amal tana ta sauri taje ta kai takaddun nan, daga nan ta kai wadda aka bata ta kaiwa Alhaji Haruna, yamma ta fara yi sosai kuma bata son Mummy ta kama faɗan nata akan bataje aiken da tayi mata da wuri ba, dan haka a harabar gidan gurin shiga mota ta ƙarasa saka takaddun a jakarta, da wasiƙar gurin Anwar, da takaddar form ɗinta, ta buɗe mota ta shiga ta fice.

Unguwar da guest House É—in Alhaji Haruna take shiru babu mutane a unguwar, duk se kangwaye da sababbin gidaje, bata kawo komai a ranta ba tace bari taje ta fara kai masa tasa takaddar, daga nan kuma seta je gurin nata kai takaddar.

Tana zuwa megadi ya buɗe mata gate ta shiga, tace  "yana nan kuwa?"

Megadi yace "Eh yana ciki"

Ta fito daga motar ta shiga, ta murɗa ƙofar falon tare da yin sallama, sedai babu kowa a falon, ta nemi guri tayi zamanta a falon, shiru shiru babu wanda ya fito, ta tashi ta koma gurin megadi tace  "Anya kuwa yana nan? Naje nayi sallama amma shiru ba'a amsa ba"

Megadi yace "ai be fiye zama a falon ba, ki shiga yana ciki"

Tace "Cikin ina? Kaga ungo bari in baka takaddar ka ajiye masa"

Megadin yace "rufani ki saya, ai be yadda in karɓi kowane saƙo ba idan bashi yace ba, ki buɗe ƙofar dake cikin falon wasu falukan ne a ciki fa"

"kaga muje ka rakani da kanka, ni bazan shiga ni kaÉ—ai ba"

Yace "shikenan muje"

Ya rakata, yana gaba tana bin bayansa, suka dinga ratsa faluka, sukaje wata ƙofa yace "yawwa a nan yake ganin baƙi, ki shiga ki bashi"

"kazo dai mi shiga tare, danni bazan iya maida kaina waje ba, wannan gida duk lunguna kamar gidan matsafa"

Yace "A'a shiga dai ki fito, ina nan ina jiranki"

Tace "to shikenan"

Ta buɗe ɗakin ta shiga da sallama ashe bedroom ne, ya amsa mata yana zaune akan gado yana danna system, yana ganinta ya faɗaɗa murmushinsa yace  "Ashe kinzo, ai tun ɗazu nake jiranki" yai maganar yana binta da kallo.

Haɗe rai tayi tace  "eh nazo, ina falo ne ga takaddar tace akawo maka"

Alhaji Haruna yace  "ok kawomin nan"

Ta ƙaraso tana zumɓura baki, ta sa hannu a jakarta ta ɗakko takaddar, ta ƙarasa inda yake ta miƙa masa takaddar, sedai me se ya haɗa da hannunta, ya riƙe.

A fusace ta kalle shi tace  "meye haka kuma? Dalla malam sakeni"

Yace "haba Baby, gaki kamar wayayyiya amma kina wani kidahumanci, ki kwantar da hankalinki karki ji komai kinji"

"Dalla ka sakeni ko in maka ihu wallahi"

Yai murmushi yace "to idan kinyi ihu kina tunanin akwai wanda ze kawo miki É—auki ne? Ba wani abu fa rainane ya biya kawai, ki kwantar da hankalinki kici Arziki ki barshi"

Kici kicin ƙwacewa ta shiga yi amma ya riƙeta gama, yana wani lashe baki kamar kare yace "'yar uwarki ta fiki wayewa, ke kamar ba' yar birni ba"

Ya fara ƙoƙarin rabata da kayan jikinta, sosai Amal take ihu tana ƙwacewa, tana rirriƙe jikinta tana kururuwa, amma tsohon najadun nan ko a jikinsa, burinsa kawai ya cimma burinsa, Amal ta dunƙule hannu ta dinga kai masa naushi kota ko ina, wani naushi data kai masa a ido a gigice ya sake ta, yaja da baya, ta durƙusa tana ƙoƙarin mayar da kayanta, kuma taso mata yayi haiƙan yana kuma riƙeta, sosai kokawa ta ka came a tsakanin su, ya hankaɗata ƙasa ta faɗi akan hannunta, ta kurma wani uban ihu, saboda azababben zafin da taji ya ratsa hannunta, haka ta kuma yunƙurawa ta miƙe sedai ta kasa ɗaga hannun nata, ganin zata hana shi rawar gaban hantsi, be tausayawa halin da take ciki ba, ya shammaceta ya buga mata kwalba a goshi, ta kuma kurma ihu ta baje a gurin a sume.

Yusuf seda ya kwana biyu sannan ya iya cigaba da fita, sedai wata irin shaƙuwa da kusanci ne ke ƙara shiga tsakaninsa da Widad, wata irin kulawa take bashi ta musamman wadda bata masa a baya, ga Jamila dake ƙara sata a hanya yadda zata dinga kula da mijin ta, gefe guda kuma ta tara ɗalibai sosai, idan yamma tayi cika gidan megari ake yara da manya tana koyar dasu ilimin addini dana zamani.
Yau Widad ta haÉ—a kayanta dana Yusuf ta wanke su tsaf, gwanin ban sha'awa.

Yusuf ya dawo a gajiye, yana dawowa ya tarar da Widad harta dafa ruwan wanka ta ajiye masa.
Yusuf yayi murmushi yace "Waini wannan kulawar da ake bani fa, nifa abun yana mamaki, an maida ni wani É—an gata meye sirrin ne?"

Widad tai masa fari da ido tace  "tukuici kawai zaka bayar, if you really appreciate"

"to me akeso in bayar?"

Ba tace masa koma ba se murmushi da tayi, tana sake kashe masa ido, Yusuf yace "Ohh my God, wannan kallon da kikemin se in rasa ina zan sa kaina, gaba É—aya narkamin zuciyata yake Baby"

Widad tai dariya tace "shagwaɓaɓɓe kawai, ji yadda yake magana kamar wani Baby"

"Baby ne mana, tunda na auri Baby nima na zama baby ai"

"Naji, je kayi wanka kazo in baka Abinci a baki zaka ci?"

"zan mana, dayawa ma zanci sosai tunda Baby ce zata bani a baki"

Yai murmushi ya fice daga ɗakin, yaje yayo wanka ya dawo ɗakin, sedai ya tarar bata ɗakin tana tsakar gida, yana zuwa yaga babu kayansa, ya duba Akwatin Widad yaga kayansa a wanke, ya ɗadɗaga ya haska yagansu a wanke fes, mamkine ya kama shi, ya fito ya ƙwala mata kira, ta taso taje Yusuf yace
"My Wife, gani nayi kamar an wanke min kaya, ya haka?"

Widad tace "to meye yafaru? Ko laifi ne?"

"Amma waye ya wanke min? Nidai nasan baki iya wanki ba, ni nake mana to yaya akayi aka wanke su?"

"Shikenan kuma a haka zan zauna ban iya komai ba,? To in gaya maka na iya aiki sosai yanzu, nice nan na wanke mana su É—azu"

Yusuf yace "abun mamaki, yanzu ke kika wanke mana kayan nan duka? Ina mamaki fa"

"wallahi nina wanke mana, ko basu fita bane?"

"Ni na isa ince basu fita ba, sun fita fes, amma baki saba ba karki sake wankewa, zan wanke mana da kaina kinji matar Yusuf"

"A'a gaskiya, ni dai sena wanke"

Yace "bafa na son gaddama, kawai ka bari nagode Allah yayi albarka, amma ni zan dinga wanke mana kinji beautyna"

"A'a ai kai ba bawana bane, dan haka nima yakamata in dinga ƙoƙartawa, tunda ina iyawa ai bakomai kai ba murna zakayi ba ina koya ba"

Yusuf yace "naji amma ki bari mu dingayi tare, kinji Babyn Yusuf"

Tace "to naji"

"Yawwa Babyna I love you" yai maganar yana kissing din goshinta, bata bashi amsa ba se murmushi da tayi, tana lumshe ido, babban abunda yake bawa Yusuf mamaki da ita be wuce yadda idan har yace yana sonta, sedai tayi murmushi amma ita ta kasa gayamasa hakan, har yanzu yakasa gane haƙiƙanin abunda yake ranta, sedai yana ganin kishinsa da tausayinsa muraran a idonta, sedai tausayi da kishi suna cikin alama na soyayya.

Widad tace "zauna inzo in baka abincin, naga kwana biyu ba kaci kana ƙoshi, bana son mu koma gida a ganka a rame, bazanji daɗi ba, aga nayi ƙiba mijina kuma a rame ba'"

Yusuf yace "inyee kaga masu miji, kamar ba mutum ne yake cewa shi be yadda da Aure ba, baze aura ya zauna a ƙarƙashin wani ba, kawai se naji mutum yana cewa ina son Aurena Yoseef, Zan zauna da kai a yadda kake, ya akayi mutum ya canza ra'ayi ne haka da sauri?"

MurguÉ—a baki tayi tace 'bana son tsokana fa"

Yusuf yayi dariya yace "gayamin meyasa kike son Aurennaki ne? Gayamin mana"

Widad tace "nima ban san yadda akayi haka ba, a baya ina da dalilin da yasa nace bazan yi aure ba, amma yanzu na samu mijin marainiya, wanda yake lallaɓani ban yaɓa zaton akwai miji irinsa ba, ka bani farinciki mara misaltuwa, shiyasa nake jin kamar bazan iya bari kayi nesa dani ba, shiyasa nake son Aurena "

Yusuf yayi murmushi yace "Mutum ma ya faÉ—i gaskiya ma, se wani kauce kauce kike, zama ki faÉ—i gaskiya ne ai"

Widad ta buÉ—e baki tace "ba ruwana, Allah ya shiryeka, a haka kaman salihi amma mutum yaita sakin magana"

"Kyaji dashi dai, ni dai azo a bani Abincina inci yunwa nakeji"

Ta zauna tana bawa Yusuf Abincin sa a baki, suna hirarsu cikin nishaÉ—i da jin daÉ—i.

Amal kawai farakwa tayi ta ganta akan gadon Asibiti, taga kanta nannaɗe da bandeji, hannunta ma data faɗi akai haka, mamkine ya kamata ta juya ta ganta a ɗakin Asibiti a kwance, ga wani irin raɗaɗi da yake ratsata daga tsakanin ƙafafunta.

Shiru tayi taga Mummy ta shigo ɗakin hannunta da ledar magani, ta ƙaraso da sauri tana Autana sannu, ya jikin naki ne?"

Amal tace "Mummy meya sameni ne?"

Mummy tace "hatsari kika yi mana Baby, ina zaune a gida Alhaji Haruna yayi min waya yacemin bayan kin kai masa takaddar, kika samu hatsari a titin unguwarsu"

Wani uban ihu ta saki, da tuno abunda ya faru tsakaninta da Alhaji Haruna, ya mata fyaÉ—e kenan, kuma yake gayawa mahaifiyarta hatsari tayi.

Ta fashe da kuka, tana jujjuya kanta, wani irin baƙin ciki ne da takaici ya mamaye mata zuciya.
Chapter 75 · 0% Book details