Sashe 125
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amal kuwa a ranar Daula yasa aka É—auketa aka kaita Asibiti, dan a dubata a ga idan aikin ze yuwu a nan Nigeria.
Haka Widad tana ji tana gani, da yamma su Yusuf suka tafi Lagos, ta koma gidan Umma tai zamanta, kwana ɗaya da tafiyarsu Lagos, Daula yai hira a kafafen watsa labarai a can Lagos, ya sake bayyana kansa, ya bayyana dukiya ta Yusuf ce, da irin wahala da azabtarwar da Bulama yayi masa, ƙarshe yai jan hankali da nasiha me ratsa jiki, akan mutane su lura da suwaye masoyansu na gaskiya.
Umma da Widad basu san anyi hirar ba, se gani sukai mutane na zuwa gidan, wai sunzo yiwa Umma murna,ashe Yusuf É—an Daula ne, babu kunya ciki hardasu Yaya É—anllami masu yi masa gori, Sunga Arziki ya sameshi, Widad ta dinga mamaki wato a rayuwa idan kaga ana nan nan da kai, wata damace Allah ya baka, ko kuma kuÉ—ine da kai.
Garin su Hindu kuwa, tuni aka kai kayan aiki dan cika alƙawarin da Daddy ya ɗauka, da yake akwai kuɗi, nan da nan aka fara aiki, kuma yace a ɗau leburori a garin dan su samu wani abu suma, gefe guda sunata shiri suma murna akan Hindu zata Auri Daula, yayin da ita Hindu gaba ɗaya yake mata kwarjini, take tunanin taya zatai zaman aure dashi, mutumin daya girmeta nesa ba kusa ba, yama haifeta? "
Nurat kam ta riga ta haƙura da batun Yusuf, tayi murna sosai jin labarin ashe yana da alƙa da Widad, itama in akabi nasaba ɗan uwantane.
Ta samu Khalil a falo tace masa" brother, kaga wani iko na Allah ko? Duk wannan wahalar ashe dai É—an uwan Widad ne Yusuf, kuma akan dukiyarsa aketa wannan abun "
Khalil yace " hakane kam, Allah babu yadda be iya ba, Sakamakon haƙuri da juriya ga abunda Allah yayi masa, haƙuri me tadda rabo, kema Allah ya baki miji nagari wanda yake sonki"
Nurat tace "Aima ya bani"
"A ina yake? Baki gayamin ba"
"Sunanshi Barrister Ibrahim Khalil gora"
Da sauri ya kalleta yace "Are you serious?"
Ta jinjina masa kai tana murmushi, "yanzu kin yarda kima sona zaki aureni Nur?"
Ta jinjina masa kai alamar eh, murmushi ya shiga yi yana faÉ—in Alhamdilillah, Alhaji na dawowa zan sanar masa "
" Haba brother, meye na gaggawa kuma? "
" kar inje wani yayi min ba daidai ba, gara in hanzarta inyi wuf dake"
Nurat ta rufe fuskarta tana murmushi.
Wasa wasa, seda Yusuf sukayi Sati biyu sannan suka dawo Kano, kuma da suka dawo ɗinma seda Daula yaje har gidansu Nurat domin yi mata ta'aziyyar mahaifiyarta, abunda bata taɓa zaton Daula zeyi ba, tana ganinsa ta tsaya tana mamaki.
Daula yace "Nurat, ƙaraso mana"
Ta ƙarasa ta zibe ƙasa tana gaishe shi"
Ua amsa tare da faɗin "ya ƙarin haƙuri kuma?"
"Alhamdilillah Daddy"
"ubangiji Allah ya jiƙan ummanki, yai mata rahama"
Nurat tace "Ameen"
Nanma Yusuf ya sake yi mata gaisuwa, Daula yace "Nurat, idan akabi nasaba ina da alaƙa ta jini da mahaifinki, dan haka ki ɗaukeni Uba, duk abunda ya taso miki kike buƙatarsa, ki nemeni ko menene insha Allah, zanyi iya ƙoƙarina imga na miki, am your father now, kinji Nurat"
Nurat tace "to Daddy nagode sosai"
Seda Daula ya tsaya suka gaisa da mariƙin nata, sannan suka tafi.
Yallaɓai Suleiman kansa, seda ya samu tagomashin katafaren gida, da kuma kuɗi masu yawa a gurin Yusuf, saboda irin jajircewa da taimakon da yayi masa.
Kwanansu Uku da dawowa suka tare shida Widad a sabon gidansu, ya samu rakiyar abokan aikinsa gidan, Kasancewar bashi da wasu abokan kirki, Widad kamar tayi tsalle dan murna da farinciki.
Bayan kowa ya watse, gajiya duk ta damu Yusuf, saboda hada hada da mutane, dan har walima akayi na tariyar a event center, Daddy ya gayyato manyan abokansa, Yusuf duk ya gaji dan be saba da hada hadar mutane haka ba, ya shiga yai wanka, lokacin tuni Widad ta shiga ɗaya ɗakim tayi nata wankan, dan itama a gajiue take sosai, ta fito cikin riga da wando na bacci masu jikin bargo pink, ta kashe fitilar ɗakin ta bar dump side lamp, ta ƙaraso inda Yusuf ke zaune yana taje sumar kansa, Yusuf yace "malama ce miki akayi na gama kika kashemin fitila?"
Tace "kai ba mace na amma se ƙaƙale, da mace ne Allah kaɗai yasan me zakayi"
"Shi namiji baze gyara ba kenan, se kincemin ƙazami?"
Widad tace "kuma mayukana zaka dimga shafawa, na bleaching ne dai ba ruwana in ka zama fari"
Yusuf yai dariya yace "dan dai bleaching ai ba damuwa ranki ya daɗe, ince mata tace takemin"
Sukayi dariya tare, ta ƙaraso ta rumgumeshi ta bayansa, tana numfashi a hankali, kwararar hawayenta yaji a Ƙirjinsa da sauri yace "lafiya kuwa Widad?"
Kasa magana tayi, ta cigaba da kukan, ya janyota gabansa yana sake tambayarta, amma sema ƙara saugin kukan da tayi, yace "haba Babyna, mena yi miki kuma? Kodai shagwaɓarce?"
Still bata amsa masa ba, dan haka ya jata zuwa kan katafaren gadon su, ƙato ya zaunar da ita sannan ya zauna yace "gayamin, menene? Ko laifi nayi miki"
Rumgumeshi tayi tana kuka take faÉ—in "thank you very much Yoseef, thank you very much for your love, caring the sacrifice and all you have done for me, you change my life Yoseef, i love you"
"I love you too my wife, you also done a lot of things for me, bani da bakin godiya se dai zuciyata taki ce mata ta"
Haka suka cigaba da gayawa jinansu kalamai masu daÉ—i, masu cike da nuna kewar juna, daga nan kuma suka wula wani gurin.
🚶 🚶 🚶 🚶
Ji suke tankar lokacin suka yi aure, dan a wannan lokacin suke cin nasu amarcin a nutse, ba inda Yusuf yake fita, kullum yana gida tare da Widad, yana bata kulawa ta musamman.
Alhaji Ahmad ma ya nemi Auren Umman Yusuf, akasaka lokacin daidai lokacin bikin Daula, ayi biki gaba É—aya
Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, tun saura sati biyu biki, Widad taje ƙauye ta ɗakko Hindu daga ƙauye zuwa kano domin shirin biki sosai, motar da aka kawo Hindu Tint glass ne da ita, dan haka bata samu damar ƙarewa garin kallo ba, seda suka shiga gidan Widad, data fito daga motar cak ta tsaya tana ƙarewa harabar gidan kawai kallo.
Widad ce ta fito tana murmushi ta ƙaraso tana faɗin "oyoyo amaryar mu, sannu da zuwa Anty Hindu"
Hindu ta sunkuyar da kai cikin jin kunya.
Widad taja Hindu zuwa cikin gidan, yayin da Hindu ta kasa magana saboda tsantsar mamaki, ace a duniya akwai irin wannan gidan lallai jin daÉ—i yana birni, suna shiga falon Widad taji wani irin sanyi ya ratsata wanda babu shi a waje, tun Hindu na mamaki harta zubawa sarautar Allah ido, dan abun ya shallake hankalinta.
Widad ta dinga koyamata yadda ake amfani da wasu abubuwan, ta dinga kaita gurin gyaran jiki kafin lokacin biki.
Hindu tayi shar da ita, tayi kyau sosai sedai tana jin kunyar Widad sosai, saura kwana huÉ—u biki sannan Widad ta kira Daddynta a waya tace masa yazo ga amaryarsa a gidan ta.
Ba musu kuwa sega Daddyn a gidan, Hindu na jinjina rashin girman kai na mutumin nan, yana da matukar sauƙin kai da sanyin hali, dukda kuɗin da yake dashi, da kuma shekarunsa.
Yana zaune a falo, Hindu suka fito ita da Widad tayi kyau sosai, Widad tana ja da kyar saboda nauyin cikinta, Widad tace "Daddy ga amaryarka nan, bari in kawo muku abin sha" ta juya ta koma ciki.
Ƙafar Hindu na rawa ta ƙarasa gaban Dula, ta tsuguna tace "ina wuni"
Daddy yace "lafiya ƙalau Hindatu, ya baƙunta? Ina fatan dai Widad bata takuramiki?"
Hindu ta girgiza kai alamar a'a, yace "to in dai tana matsa miki, ki gayamin nida ita ne" yai maganar yana murmushi ƙarshe shikaɗai yai taɗin ya gama bata iya cewa komai, saboda kunya da kwarjinin sa.
Lokacin biki Aka aika da motoci ƙauyen su Hindu, aka kwaso su zuwa birni dan bikin 'yarsu, a tsohon gidansu Widad aka sauke su, sedai Hari tafi kowa rikicewa da ganin gidan nan, tun daga gate motocin dake harabar gidan suka rikita ta, suka shiga katafaren falon gidan, Hari ta rasa a ina zata zauna, tace "ohh ni Hari, yanzu wannan ko' a aljanna ka samu wannan ai ka more"
Hansai tace "ke Hari, ance talaka a gidan aljanna shine gidansa kamar girman duniya, kike cewa ki samu kamar wannan"
"Ke bari Hansai, ke kina tunanin kin aikata abin da da zaki samu wannan ne? Ai ni indai irin wannan ne yaseen ya isheni, kai jama'a kun lura da wani abun mamaki kuwa? Waje lafiya ƙalau amma ɗakin nan hunturu Aradu, sanyi ake sosai a cikin ɗaki ikon Allah"
Widad tasa aka dinga sauke musu Abinci, Abinci kala kala Gwaggo tace "Amarya wai ina 'yar tawa ne?"
Widad tace "wace' yar bayan nikuma?"
Gwaggo tai murmushi, Widad tace "zasu taho tare da Daddy, da kuma Umma"
Gida ya É—au harama, aka kawo Hindu, suka dinga zuba guÉ—a, gaba É—aya Hindu ta canza a sati biyun nan, tayi kyau sosai kamar ba ita ba.
Aka dinga ɗorawa ana sauke musu Abinci, aka ɗakko masu aiki da an ɓata guri su gyara, Da Yamma aka ɗauki Hindu aka tafi reception, na Daddy da abokansa da kuma Ahmad, dama umma cewa tayi ba zata ba.
Hanne kam ji take kamar tayi kuka, tafi Hindu kyau da haske amma zata auri wannan haɗaɗɗen mutum a birni, amma ita zata auri ɗan ƙauye, tunda suka zo Widad ko kallon inda Hanne take ba tayi balle tayi mata magana.
Washegari juma'a, aka ɗaura Auren Umma, da kuma na Hindu da Daula, anyi shagali sosai a gidan nan, dukda ba wani gagarumin taro suka yi ba, amma anci an sha sosai kowa yasan anyi biki, akaita yiwa Hindu Nasiha, akam haƙuri da tsoron Allah, Widad tace Gwaggo, da Hari suzo a raka Hindu gidan ta "
Hari tace" au wai dama nan ba'a gidanta muke ba? "
" Gidan Amaryar za'a sauke ku? Sannu Hajiya Hari me taɓargaza"