Sashe 101
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma tace " Haba Suleiman, kaifa ka cemin duk wanda yai yunƙurin taimakonsa barazana ake masa, taya ya za'a samu wanda zasu taimaka masa alhalin kowa yana kallon yadda akai shari'ar, kuma babu wani taimako da aka masa? Ni na karaya kawai, haka Allah ya ƙaddara masa rayuwarsa, ƙaddara babi babi, daga wannan se waccan " tai maganar tana kuka me taɓa zuciya.
Sulaiman yace" Umma, kece fa kike bani misali da Annabawan Allah, da irin jarabtar da Allah yayi masa, dan haka mu ɗauka jarrabawar sa ce a haka, kuma Allah yasa sanadin ɗaukakarsa ne yazo a haka, duk yadda Allah ya kai ga jarabtar bawansa, se kinga ta wani ɓangaren Allah ya masa wata ni'ima wadda ba kowa yayi wa ba, ki kwantar da hankinki Umma, shirye shirye sunyi nisa ta ƙarƙashin ƙasa, kuma insha Allah zamu bawa maƙiya kunya "
Umma ta gyÉ—a kai tace " to Allah yasa"
"Ameen ya Allah, ki cigaba da Addu'a Umma, ubangiji Allah ya bamu nasara"
"Addu'a ina nan ina yi, Allah yayi maka albarka da kai da iyalanka, ubangiji Allah ya jiƙan magabatanka ya rahamshesu, ubangiji Allah ya raya maka zuriyar ka akan tafarki madaidaici, yasa su zamo masu jin ƙai kamar kai, Matarka Allah yayi mata albarka ya sake haɗa kanku, tunda abun nan ya samu ɗana kake tsaye a kaina, kana bani gudunmuwa iyayinka, kaine dana ganka nake jin daɗi, nake jin daɗin yadda kake tausata nagode nagode "
Suleiman yace " bakomai umman Yusuf, karki damu duk yiwa kaine, ni ban rayu da mahaiyata ba, marayane ni tun ina yaro ƙarami, ina jinjina soyayyar uwa ga ɗanta, shiyasa nasan kina cikin damuwa rashin Yusuf da dole kina buƙatar a tausasa miki, ga Ɗanki mutum ne nagari kamili, wani abu da Yusuf ya taɓa yimin da bazan manta ba, lokacin mahaifina yana ciwon ajali sunje duba shi, baya iya cin Abinci sam, Yusuf ya kai masa dafaffen ƙwai da kayan marmari, naje siyo masa magani Yusuf ya zauna yana bashi ƙwan nan a baki, bayan ya gama bashi Baba yayi amai, ya ɓatawa Yusuf jiki, kayansa masu kyau a jikinsa suka ɓaci, amma be nuna damuwarsa ba ya ɗaga shi ya gyara masa jiki, kullum aka tashi daga gurin aiki se yaje ya duba mahaifina, har suyi hira, alhalin ni a lokacin ko kulani bayayi sosai, dukda ina shugabansa a gurin aiki, duk ranar da beje ba Baba ya dinga tambayar ina yaron nan me fararen idanuwa kuwa? Ranar da Baba ze bar duniya seda yayi masa addu'a sosai, bazan manta ba, naji daɗin yadda ya nuna damuwa akan mahaifina fiye da tunani, dukda wannan abun alkhairi da yayi min ba fiye shiga sabgata ba sedai in sha'anin aiki ya haɗamu, hakan ya tabattar min halinsa ne a haka, halin taimako da tausayi ga mutane, shiyasa bazan taɓa bari inga wani mummunan abu ya samu iyayen Yusuf ba"
Umma tai ajiyar zuciya tace "Kaga ni be taɓamin wannan hirar ba"
Suleiman yace  "Ai Umma wannan ɗan naki halinsa se shi, miskiline ajin farko sedai akwai tausayi da jin ƙai, ni dai fatana kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki"
(Wato shi alkhairi a rayuwa, idan har zaka aikata shi ko bayan ranka waninka ze mora, Kayi ƙoƙari kayi abunda mutane zasu dinga tunaka da alkhairin ka, ba da mugun aiki ba)
Nan Sulaiman yaita kwantarwa da Umman Yusuf hankali, shida matarsa.
Kamar yadda Bulama yai umarni, cikin dare su me Adda suka bazama gidansu Yusuf, inda suke kyautata zaton Umman Yusuf tana nan.
Amal har dare yayi tana fama da matsanancin ciwon mara kamar zata yi hauka, gashi ta kasa cin komai, se uban amai da take faman yi, ga jini se zuba yake yaƙi tsayawa ita kaɗai a ɗaki babu wanda yasan halin da take ciki sam.
Gaba ɗaya babu wanda hankalinsa ya kai kan cewar Nurat bata nan se bayan kwana ɗaya, tai ihun tayi bugun ƙofar babu wanda ya ji balle ya buɗe ta, gashi bata san halin da mahaifiyarta ke ciki ba, sakamakon taji ihutmnta amma bata da tabbas ɗin abunda ya faru da ita.
Khalil ne ya kalli Alhaji Musa yace "wai ina Nurat ne? Tunda mu kazo Asibitin nan ban ganta ba fa"
Cikin inda inda Alhaji Musa yace "Amm da yake itama bata da lafiyar ne, ban san ya nata jikin ba, bana son hankalin ta ya tashi ne, bari inje gidan in taho da ita"
Khalil yace "kace duk gidan ma basu da lafiya?"
"wallahi kuwa, Nurat É—ince ma ta fara sannan uwar"
"Amma an kaita Asibiti kuwa? Meke damun Nurat É—in"
. "A'a ba wani abu bane dama, dama nace zata koma karatu ne itakuma bata so, shiyasa take ta damun kanta dai, kusan damuwace ta saka take rashin lafiya"
  "Amma meyasa baka ƙyaleta ba, tunda bata so ba? Ka takura se taje kaga gashi ta shiga wani hali"
Maman Khalil tace "kai Khalil, wai nan a kotu muke ne? Jimin ja'irin yaro ka tasa mutum a gaba da tambayoyi".
Khalil yace "Allah ya bada haƙuri, muje semu taho nida Nurat ɗin kai seka huta kawai".
Alhaji Musa yace "No, bakomai ai ka bari zan kawota da kaina"
Maman Khalil tace "kuje tare mana, ai bakomai se su taho taho shida ita"
Khalil ya saka Alhaji Musa a gaba, da wani irin kallo wanda ya kasa tantance na menene.
Haka suka tafi kowa a motar Alhaji Musa, koda sukaje gidan Alhaji Musa yace "bari in kirata tana saman bene"
Khalil yace "shikenan babu laifi, bari in jira a nan" ya zauna a falo.
Alhaji Musa ya hau sama da sauri, danshi gaba ɗaya ya manta daya kulle Nurat a ɗaki, yana zuwa ya buɗe ya tarar da ita a baje a sume a ɗakin, a gigice ya ƙarasa yana kiran sunanta amma bata motsi, da sauri ya ɗakkota ya sakko daga benen, hannunsa riƙe da ita.
Khalil ya miƙe tsaye yace "lafiya kuwa?"
Alhaji Musa yace "a sume na tarar da ita"
Basu tsaya ba sukayi waje gurin mota, aka saka Nurat a ciki suka nufi Asibiti cikin gaggawa.
Itama a emergency ɗin aka karɓeta, aka rufu akanta don ceto rayuwarta itama, rufetan da yayi dama bata karya ba, ga kuka ga damuwa ga tashin hankalin da ta shiga jin ihun mahaifiyarta, hakan yasa ta shiga tashin hankali, garin kuka tai shaƙuwa numfashinta ya sarƙe ta faɗi, ga yunwa dan haka abun ya tarar mata, daya buɗe ɗakinma ya ɗakkota numfashinta iya ƙirjinta ne kawai, babu inda yake motsi a jikinta.
Alhaji Musa ya koma reception ya zauna ya dafe kai, yana tunanin wannan wace irin masifa ce haka kashi kashi? Ze kashe iyalansa ɗaya bayan ɗaya da kansa, da hannunsa duk a dalilin aikin banza, dalilin neman kare a Karofi, Bulama nata musu gafara sa amma babu ƙaho tsayin shekaru.
Bulama yana ta jiran yaji su me Adda sun bashi feedback akan aikin daya sa kasu, amma shiru ba suyi magana ba, ya kira layin me Adda babu adadi amma tun tana shiga ta dawo bata shiga, sema ace masa line busy, daga ƙarshema aka kashe wayar gaba ɗaya.
Alhaji Musa yana nan zaune, aka kira shi a waya aka sanar masa da an gano inda Anwar yake, yayiwa Bulama magana, akan me yakamata ayi? An kira wayarsa bata shiga se ace busy.
Kamar ya share ya basar, amma dai ya kira Bulama, Bulama ya É—aga yace "ya naji muryarka a hakane? Baka da lafiya ne?"
"A'a lafiyata ƙalau, amma ina Asibiti"
"me kake a Asibiti kuma?"
"Wallahi abubuwa sun damalmalemin gaba É—aya, bisa tsautsayi daga zan ture Maman Nurat daga bene in sakko, bisa tsautsayi ta faÉ—o kwananta biyu a Asibiti har yanzu bata hayyacinta, na rufe Nurat a É—aki saboda ta gano halin da ake ciki, ta gano da saka hannuna a abunda ke faruwa a gidan Daula, itama gata can a emergency bata san wake kanta ba, gaba É—aya na rasa abunyi ma"
Maimakon Bulama ya tausayawa Alhaji Musa halin da yake ciki, seya haushi da faɗa "wai kai wand irin mutum ne haka Musa? Ya za'ayi kabari yarinyar ka ta gano? Gaskiya baze yuwu ba sam, wancan karon dana maka magana ashe baka ɗau mataki ba? To dole kasan yadda zakayi tun wuri dole a ɗau matakin daya dace akanta, bazs yuwu ta tona mana Asiri ba"
Ran Alhaji Musa yai matuƙar ɓaci da jin Kalaman Bulama, bs tausaya masa halin dayake ciki ba, amma ya haushi da faɗa, dan haka a hasale yace "kaga ya isa naji, ance in gaya maka an gano inda Anwar yake, ɗan gidan Hajiya Halima"
Bulama yace 'to me kace musu? "
" me kuwa zance musu? Umarninka suke jira"
"Aina riga na gama bada umarni, a kasheshi kawai dan baze yuwu a ƙyaleshi ba"
Alhaji Musa yace "seka kirasu ka gaya musu, ni yanzu ina cikin wata matsalar ne"
Yana gama faɗin hakan ya katse kiran, tunani ya fara yi, Hajiya Halima tana da Alaƙa da Bulama 'ya' yanta kamar nasane, amma yace a kashe ɗanta dan kar Asirinsa ya tonu, dan haka babu shakka idan ya gama da Anwar kan Nurat ze dawo.
Ai nan da nan ya ɗau wayarsa ya kira Hajiya Halima, ta ɗaga wayar da ƙyar alamar tana jin jiki, tai sallama a hankali
Alhaji Musa yace "malama idan zaki ware muryar ki ki ware, an gano inda É—anki yake Anwar, amma Bulama yace A kasheshi dan karya tona masa Asiri....
AMANA! AMANA!! AMANACE!!!
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"