← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 127

Sashe 26

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Huda tana zaune rungume da jaririyar nan tace  "Duk wanda yake ƙaunata, ya ƙaunaci jaririyar nan, duk wanda yaƙi jaririyar nan to tabbas ni yaƙi, a duniya yanzu banda Allah, se mijina da wannan 'yar, su kaɗai Allah ya mallakamin, inajin son' yar nan  a raina, kamar yadda nake son mahaifinta, Allah yasa ta zamo me jinƙi da tausayi kamar mahaifinta "

Nasir ya rungume Huda da jaririyarsu yace" tabbas nima duk me sona, to ya ƙaunaci Huda da jaririyar nan, Allah yasa mun ƙara yawa, ya azurtamu ta samun ƙaruwa, yanzu wani suna kike ganin zamu saka mata? Ko mu mayaf da Sunan Anty Islam '

Girgiza masa kai Huda tayi tace  "A' a idan ka mayar min da sunan Islam, bazan iya tsawatar mata ba, kamaninta ɗaya da Islam zan dinga ganin kamad itace, haka idan ka samun sunan Anty Nadiya, nan ma bazan iya tsawatar mata ba, saboda ina girmama Anty Nadiya, tambarin mutjwarsu baze taɓa barin zuciya ta ba, gara mu sa kamata wani sunan daban, mu sama ta Widad, wato soyayya da Abota, na zaɓi sunan ne saboda yana da kyakkyawar ma'ana, Ina sonta kuma itace babbar ƙawata"

Nasir yayi murmushi yace  "muna sonta dai'

Haka akayi gagarumin shagalin suna, a Nigeria, nan dangin mahaifin su Nasir suka dinga rige rigen zuwa, saboda Arziki ya samu, Bulama ya taya Nasir murnar haihuwar Widad sosai, duk da saɓanin da suka samu da Ahmad, seda yazo yayiwa Nasir barka, ya bawa Widad kyaututtuka, Bulama ne ya saiwa Widad Haikika, yayi Ƙaton Akwati da kayan jarirai, haka nan yaji yana ƙaunar yarinyar, sanadin abunda yayiwa Widad, yasa mafi yawa na ƙiyayyar da  Huda ke masa ta ragu, dan taji haushin rabuwar Nasir da Ahmad, abunka da abun masu Arziki da neman gurin zama, nan masu kuɗi suka dinga bajinta suna gwangwaje jaririyar nan da manyan kyautuka, dan kawai su birge Daula, ko ace wane ya bada kaza.

Kafin su koma Dubai, kusan kullum se Bulama da matarsa sunzo, dan ya ɗauki Widad, ko kuka take ya dinga rarrashinta kenan, Yana matuƙar son yarinyar.

Kwanansu Arba'in Nasir ya ɗauke Huda suka koma, Bulama ma albarkacin Nasir ya fara kama ƙasa, nan da nan ya shiga aure Auren mata, ya auri wannan ya saki, ya Auri waccan ya kora, tun Nasir yana masa faɗa harya ƙyaleshi.

Kadarorin da Aka tarawa Widad na suna, Daula ya haɗa ya siyar bisa shawarar Huda, suka haɗa kuɗi suka buɗe kamfanin sarrafa ƙarafa, manyan mutane har daga ƙasashen ƙetare suka zuba hannayen jarinsu cikin kasuwancin, nan fa Sunan Daula ya ƙara shahara, ya zama babban attajiri, me sana'a goma maganin me gasa.

Widad ta fara wayo a hankali tana girma, ta isa shiga makaranta se Daula ya koma England, saboda mafi akasari yanzu yafi ta'amalli dasu akan harkar kasuwancin motoci, aka saka Widad a makaranta, Huda kuma ta dage da koyar da ita na Addini, dukda akwai wani ustaz dayake koyar da yaran musulmai a ƙasar.

Sedai gaba ɗaya rayuwar Widad da girmanta, ya sha ban ban dana sauran yara, sun raba gari da duk wasu ɗabi'u na yara, duk inda yaro yake an sanshi da son kallon fina finan cartoon, kona dabbobi amma banda Widad, idan za tayi kallon film, daga wrestling, se film wanda ake yaƙe yaƙe ko harbe harben bindiga, kokuma fina finan horo na ban tsoro, kona harkar fashi, suke birgeta, sam bata kallon wani film ɗin Indiya ko soyayya da tausayi, basa gabanta, Huda taita fada tana mita, amma Nasir se yace ta ƙyaleta, nan gaba zata dena.

Huda taita mita tace  "yarinya kamar ba mutum ba, ke duk abunda mutane suke yi ko suke so, ke kunyi hannun riga dashi?"

Widad tana da miskilanci, bata magana seta ga dama, idan har kaji ta zage tana surutu, kodai da mahaifintane ko kuma Bulama ne ya kawo musu ziyara, bata wasa da 'yan uwanta yara, sedai taita gwada tsalle tsalle, da harbin bindiga da take gani a film, shine wasanta sosai abun yake damun Huda, Nasir yace tayi haƙuri irin tata ƙuruciyar kenan.

Widad tafi sakewa Da Babanta akan Amminta wato Huda, Huda tana da zafi sosai akan tarbiyyar Widad, yayinda Babanta duk abunda takeso shi yake so, amma duk da haka akwai soyayya da shaƙuwa a tsakanin Widad da Amminta, babban abunda yake haɗasu shine rashin son mutanen Widad da kuma wannan kallon da take yi.

Widad ko ƙawayen kirki bata da su, saboda rashin son maganar ta, sedai tana ji da magenta, tana nuna musu soyayya, sune abokan wasanta, dasu take hirarta.

Tun bayan haihuwar Widad me abun mamaki, Huda bata sake samun haihuwa ba, tana ta Addu'a tana fatan ubangiji Allah yasa ta kuma samun rabo.

A wannan lokacin shaharar Daula ta wuce iya Nigeria, da taimakon Allah Daula ya goyawa Musa baya da maƙudan kuɗaɗe, ya tsaya takara a wata jam'iyar siyayasa a wannan lokacin, a dalilin son da mutane suke wa Nasir Daula suka zaɓi Musa.

Tunda Musa yaci zaɓe nan ya ɓarke da bushasha, bashi da aiki se gantalin ƙasashen duniya, ya manta da al'ummar da suka zaɓeshi, da irin Alƙwarirukan daya ɗaukarwa mutane, Ya kai 'yarsa Nurat makaranta a ƙasar waje, inda Widad take karatu, Nurat tana matuƙar son Widad, Kasancewar Widad ce bahaushiya' yar uwatta a makarantar, duk sauran yaran turawa ne, tun Widad bata damuwa da Nurat harta fara kulata, a hankali suka fara sabawa suna shaƙuwa da juna.

Widad sam tun haihuwarta, rayuwarta tafi a ƙasar waje, idan sunzo Nigeria to hutu sukazo ko kuma ziyara, gashi Huda ba wani Hausa takeji ba, tama jin Husa amma ba sosai ba, dan haka wasu abubuwan duk Widad bata sansu ba.

Nasir ya haɗa kai da wasu 'yan china, suka buɗe wata katafariyar ma' aikatar harkar kwangila, na gine ginen tituna, da shigo da kayan gini, ya jawo matasa sosai cikin harkar, bayan wancan kamfanin ƙarafa da yake dasu, da sauran manyan kadarorinsa na mamaki, dan har rijiyar mai Daula ya mallaka, kullum Arziƙinsa gaba yake, baya baya, gashi ba wani babba ba a a wannan lokacin, amma ya tara Arziki da shahara.

Shekarun Widad bakwai a duniya, har Huda sun fidda ran samun wani ɗan, kawai ta tashi da matsanancin ciwon ciki, tayi zaton ɓacin cikine kawai, amma ta wuni a kwance, hakan yasa Daula ya ɗauketa zuwa Asibiti, a nan aka tabattar masa da tama ɗauke da juna biyu.

Daula ya rasa inda zesa kansa dan farinciki, sunyi murna sosai da samun wannan cikin, nan ya ƙara ririta Huda fiye da yadda yake yi a baya.

Da tayi motsi se yace "me unborn É—ina yake sone, har Widad ta fara kishi tace "Daddy, wai yanzu kafin son unborn É—in nan ne dani?"

"wane ni, ga gimbiyata ince nafison wani dake, ai you are my forever Queen, babu wanda ze rusamin fadarki, kiyi yadda kike so Gimbiyar Daula'

Ire iren wannan kirarin, da soyayyar da mahaifinta ke mata suke fasa mata kai, Widad bata taɓa kukan babu ba, bata san ta nemi abu ta rasa shi ba, haka ta taso cikin zunzurutun jin daɗi da dukiya ta ban mamaki.

Tun Widad tana ƙarama take bada kyauta, idan Daula ya ga dama, se yace "Ran Gimbiyata ya daɗe, ga wane me kike so a bashi?"

Duk abunda ta faÉ—a ta zauna, se an bawa mutum, Huda taita mita tama ya fiye sangarta Widad, shi kuma ya kance idan banyiwa Widad abunda takeso ba se yaushe? Idan na mutu bata mori dukiyar mahaifinta bafa?"

Ya sai kadarori da sunayen Widad, kadarorin daya siya da sunanta basu da adadi, Widad komai yi mata akeyi, suna da nanny.

A hankali Huda taga idan ta biyewa Daula, to Widad zata tashi a sangarce, dan haka take É—an koya mata waus abubuwan, kamar gyaran É—akin data kwanta, É—auke kwanon Abinci, da shara daidai wadda zata iya.

Katsam bayan tenure Musa ta farko, yana ƙoƙarin ya koma, labarin irin almundahanar da Musa yayi ta iske Daula, abun yayi masa ciwo, ya goyawa macuci baya ya jagoranci al'umma, amma ƙarshe ya zalunce su, Daula da kansa ya kai Musa EFCC yace su tuhume shi, a bincike shi ya fito da haƙƙin mutane.

Abun ya bawa mutane mamaki, ganin shiya kawo Musa Siyasa, amma da kansa ya kaishi gurin hukuma, sannan yace bashi bashi, kuma duk hukuncin daya dace ayi masa.

Gaba É—aya siyasar Musa, da mutuncinsa ya zube a idon mutane, dama farin jinin saboda Daula ne, mutane suka juya masa baya.

Ƙarshe da kyar ya sha a hannun EFCC, dan seda aka kaishi prison a ƙasƙance, aka ƙwace wasu daga kadarorin da ya mallaka, a wannan lokacin abubuwa basu taɓarɓare kamar yanzu ba, da ƙyara wasu daga 'yan siyasa suka dinga shiga suna fita, seda Musa yayi watanni shida a prison, sannan aka sako shi da kyar, shima se da aka ƙwace masa passport, dan gwamnatin lokacin ba tasu bace.

Wannan dalilin yasa Musa ƙulattar Daula, ya manta duk alkhairin da Daula yayi masa, ya manta yadda ya tsamoshi daga ƙangin talauci da shaye2, yayi aniyar rama abunda Daula yayi masa kota halin ƙaƙa, yayi Alƙawarin tozarta shi da wulaƙa ta shi, kamar yadda yayi masa, yayi alwashin ɗanɗanawa Daula baƙin ciki mafi muni a rayuwarsa, tunda ya ɓata masa suma ya lalata masa siyasarsa.....

LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: .LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

68_69

Cikin Huda ya ci gaba da girma, yayin da gefe ɗaya Daula ya fara tara maƙiya da mahassada, danshi duk abunda zeyi be yadda da cuta ko ha'inci ba, komai nasa tsakani da Allah yake yinsa, ga gefe guda mutanen daya ƙwacewa kasuwar wasu abubuwan, suma suka sako shi gaba suna jin haushinsa.
Chapter 26 · 0% Book details