← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 127

Sashe 42

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dama Hajiya Halima tayi tayi su koma wancan gidan, dan yafi haɗuwa da girma amma Widad tace baza"a koma ba, ƙarshe ma tasa aka zuba mata kiwon dabbobi a ciki, wani ɓangaren gida sosai, wani ɓangaren gidan gona.

Hajiya Halima tace "Yanzu kai Alhaji saboda ka rasa abunda zakayi da kuÉ—i, seka sai wannan dokunan? Suna fa da tsada, kuma me zata yi da wasu dokuna tana mace"

Daula yace "Ai babu itace damuwa, amma tunda akwai za'a sai mata, ian son abunda takeso, kin san ba wata lafiya ce sa ita ba, shiyasa nake son yi mata abunda takeso, kodan ta samu farinciki, na rasa me zanyi wanda ze dinga É—ebe mata kewa, yasa ta sake da kowa"

Widad data kawo kai zata shigo falon Daddy taji wannan maganar da suka yi, da yadda Halima take kushe a sai mata abunda takeso, Widad ta maze ta shiga falon ta kalli Daula tace 

"Weldone Dad"

"Weldone my Queen, how are you?"

"Fine Daddy"

Yace "Masha Allah, Alhamdilillah, ya akayi ne, ko zuwa zanyi?"

Widad tace "No but Daddy, i see over twelve cars in the parking space, what are they used for?"

Daula yayi murmushi yace "na gidane, wanda muke hawa, ni nawa biyune kawai sauran na mamanki ne da Yayyaenki, tunda kinzo kema se ki sai wanda kike so"

Widad ta haɗe rai cikin hura hanci tace "Niba uwata bace, bani da uwa dan haka bata haifeni ba, , and na saka a kwashe motocin a kaimin su farmhouse a ajiye, na barwa kowa mota ɗaya yayi amfani da ita ta isa, kai kuma an bar maka naka my king" ta ƙarasa maganar tana murmushi.

Daula yace "to babu laifi, godiya muke gimbiyar Daula, yadda kikace ai haka za'ayi"

Tayi wa Hajiya Halima wani kallon tsana na baki isa ba sannan ta fice, tana fita Halima zata fara complain, amma Daula ya dakatar da ita yace "itama dukiyarta ce, duk yadda tayi daidai ne"

Halima taji kamar ta samo abu ta kashe Widad dan baƙin ciki, tun daga Nan fa suka dinga takun saƙa da Widad da matar babanta, bata ganin mutuncinsu sam, sannan bata yadda da kowa ba, sakamakon duk wanda suke cutar da Mahaifinta Yaran talakawane daya janyo a jikinsa sukayi Arziki sanadinsa, wanda ya yarda dasu sune suke cutar dashi.

A wannan zuwan ma, seda akai kaiwa Widad Mummunan Hari, akaso a sace ta amma Allah ya kuɓutar da ita, daga nan ta tattara komatsanta ta koma England ta cigaba da zuwa makaranta.

Daula ya bubuɗe guraren kasuwanci da kuɗinta, ciki hadda manyan gidajen gona, shagunan kasuwa da sauransu, dan haka Widad ma ta kasance 'yace me arziki a ƙashin kanta.

Gaba É—aya a rayuwarta batayi zaman shekara shida a Nigeria ba, shiyasa abubuwa da dama ita bata sansu ba, ko in anyi take mamaki.

Wannan hali da ta tsinci kanta a ciki a rayuwarta yasa, ta yanke ƙauna da samun mutanen kirki, wanda ze zauna da kai a halin akwai ko babu, kuma ta yadda cewa duk talaka ze iyayin komai akan kuɗi, ta yadda idan har ka amince da mutum ya shiga jikinka, shine na farko daze fara cutar ka, ta lura mutane da yawa suna nuna mata kulawa ita da mahaifinta ne saboda wannan dukiyar da suke da ita, da babu wannan dukiyar da ba zasu dinga mutuntasu haka ba, dan haka itakuma take taka duk wanda taso.

Tun data bar Nigeria a wannan lokacin bata kuma dawowa ba, seda ta cika shekaru goma sha takwas, bayan shekara huɗu kenan, lokacin ta zama cikakkiyar budurwa, yanayin tsarin rayuwarta duk na turawa ne, dukda hali na rashin sakewa da mutane da take dashi, amma tana zuwa gurin shaƙatawa da buɗe ido.

Bayan gama high school ɗinta tace a Nigeria zata zo tayi karatun Jami'a, saboda kawai ta ƙallafa ran seta ta gano suwaye kuma suke da sa hannu akan kisan mahaifiyarta, suke cigaba da bibiyarta da mahaifinta akan dukiyar nan? Kuma tana son nunawa Hajiya Halima iyakarta saboda zaƙewar da take tayi yawa, da yadda take juya Daula yadda take so.

A wannan dawowartata ne aka kawo mata kusan direbobi uku, amma da sun fara aiki se taga kamar an haɗa baki dasu zasu cutar da ita, dan laifi ƙalilan seta kori mutum, bata ragayya bata sassauci bata afuwa ga ƙarya ko yaudara.

Dukda wannan tsawon shekaru, Magungunan nan basu dena aiki a jikin Widad ba, sakamakon ƙarfinsu ne da pressure da suke bawa jikinta yasa ta kamu da ciwon zuciya, ko kuma haka nan jikinta ya rikice ta fara wannan tsoron.

Widad ta ɗanyi shiru sannan tace  "Nasan akwai abubuwa da nayi da kake buƙatar sanin dalilina na yinsu, akwai ranar da mukaje Hotel nace maka ni karuwa ce, naje wannan Hotel ɗinne, dan ganewa idona wani abu kuma na gani, wasu mutane ne da nake zargi da sa hannunsu, na gansu tare da matar Daddy, da alama sunyi meeting ne, kuma nasan akan Daddy ne, munje Club tare ranar harka hanani shiga, naje ne domin in kama Fahad red handed ta yadda maganar Aure tsakanina da shi zata rushe, haka nan tun zuwanka naji wani sashi na zuciyata nason Amincewa da kai, dukda wani ɓangaren yana gargaɗina, nace bari in jarrabaka tukuna, duk inda zanje nake tafiya da kai, sannan na maka umarnin cewa ban yadda kayi magana da kowa ba duk inda zamuje, saboda ina tsoron a haɗa baki da kai, watarana kana zaune a gidanmu inda ka saba zama, ina kan varrendar na saman bene, kawai na hango Amal taje inda kake, ka taso kuka taho tare, na fito falo inga meze faru, za kayo hanyar part ɗina, se tace maka ai bana nan ina part ɗinsu, ka bita zuwa ɓangaren su, ni kuma na bi bayanku, nasan zakayi mamaki daka fito ka ganni a tsaye a gurin amma ban ce maka komai ba, haka kurum na fara sakewa da kai bayan na gano waye kai, ganin bibiyata da ake ya fara yawa yasa na ƙara jarrabaka, na baka ATM ɗina, ka tafi dashi tsawon sati biyu, a gaban mutanen gidanmu, wanda nasan dole su bibiyeka a kai, amma ga mamakina bayan sati biyu, se gashi ka dawomin da shi, ba tare da ko ƙwandala ta ɓata ba, kuma yana daga abunda ya ƙara nesantani da mutane shine, duk wanda ya raɓeni shima cikin matsala yake shiga, an dinga bibiyarsa kenan dan a samu wannan takaddun, shiyasa nake sake yin baya baya da kowa, sedai kai ka riga ka shigo rayuwata gaba ɗaya, ban iya kareka da shiga hatsarin da nake ciki ba, seda aka ritsa da kai, sannan ƙiyayyata ga Aure kuma ya samo asaline ga yadda naga Bulama ya maida Aure da saki tamkar shan ruwa, nakan bibiyi shafukan sada zumunta na kanga irin complains akan Aure, kuma ga mahaifina yayi Aure, Amma matarsa sam baya gabanta abunda yake hannunsa shi takeso, se nake ganin muddin nayi Aure tamkar na shiga matsala ne, kuma komai ze iya faruwa dank, kuma a yadda nake jina bazan zauna ƙarƙashin wani yayi amfani da ikonsa a kaina ya wulaƙantani ba, shine abunda ya faru har zuwa ɗaukemu sa akayi tare, Yoseef wannan shine ƙarshen labarina dana mahaifina, kaga laifina akan AƘIDATA? Ban cancanci in guji mutane ba? Ko kuma rayuwar kaɗaici zata zama laifi idan har nayi hakan ne dan kaucewa tarayya da azzalumai masu biyu? Mutane dayawa basu san meyafaru dani ba, abu ɗaya kullum suke kallo shine AƘIDATA "

Shiru Yusuf yayi, yasa hannayensa biyu ya dafe kansa, Widad tasa hannu ta janye nasa, tace " Kana jina kuwa?"

Wata irin ajiyar zuciya yaja, wadda seda Widad ta ɗan razana, ta ɗau fitila ta haskashi, sedai taga Hawaye a Fuskar Yusuf, jijiyon kansa duk sun ɗaga ya ƙara wani kwarjini, ga ja da idanunsa sukayi, saboda labarin Widad ya kaɗashi matuƙar gaske, gaba ɗayanta abun tausayi ce, taga jalala da iftila'i me ban tausayi, a kashe maka mahaifiya a haukata maka tunani, sannan a cigaba da bibiyar rayuwarka da barazana da tsoratarwa iri iri.

"Shiyasa na dinga ja maka rai fa akan baka labarin nan, kalli yadda ka É—aga hankalinka hadda kuka, dan Allah kabari Yoseef, ni yanzu na fara mantawa da wasu abubuwan saboda sadaukarwarka a gareni, baka yi sallar isha'i bama, gashi yauma munyi dare, kayi salla kaci Abincinka seka kwanta "

Bece mata komai ba ya miƙe, sosai yake jin tausayin Widad, gaba ɗaya labarin nan ya tsaye masa a ransa, Widad ta koma kan shimfiɗarta, sannan ta fara zubda nata hawayen dan bata son ta sake ɗaga masa hankali, tana kallonsa sau biyu yana sake sallame salla, yayi ya idar nan ma ya daɗe sosai akan sallayar sannan ya tashi, be ko kula Abincin ba, shimfiɗar ma beyi ba a ƙasa yaje ya kwanta a rigingine.

Nanfa Ƙwaƙwalwarsa ta shiga kaiwa tana komowa akan abubuwa da dama, da irin binciken da yayi, lokaci lokaci idan ya tuna labarin Widad se yaja tsaki, dan ya rasa a inda yakamata ya ajiye wannan tsagwaron zalunci haka.

Ƙarshe ma tashi yayi zaune ya sake dafe kansa, sedai Duk abun nan Widad tana kallonsa, tana tunanin yanzu akwai wanda zeji labarin abunda ya sameta ya tausaya mata haka, harya shiga wannan irin damuwar? Dukda tarin wulaƙanci da isa data dinga nuna masa, amma ya dake ya shanye har yake jin tausayinta haka, bayan ɗawainiyar da yayi da ita, da ƙoƙarin kareta daya dingayi, lokacin da akazo sace ta ba dashi sukayi niyyar ɗauka ba, ya dage ba zasu tafi da ita ba, shine suka haɗa dashi, ga wahala da azaba da ya sha gurin kuɓutarsu, gashi har yanzu a kan shan wahala yake, a rayuwar da tayi idan akace mata akwai mutum me irin zuciyar Yusuf a zamanin nan to tabbas za tace ƙaryane, ita kam me zata yiwa Yoseef, ta saka masa tasan ko duk abunda ta mallaka zata bashi bata isa ta biya shi ba.

A hankali ta tashi ta tafi inda yake zaune ya rafka tagumi, ta janye hannun tace  "wai bazaka kwanta bane? Kuma ina shimfiɗar kake zaune a ƙasa haka?"

"Bana jin bacci" ya bata amsa

"ko Abinci ma fa baka ciba, ga yunwa ga rashin bacci? Gaskiya ban yadda ba"
Chapter 42 · 0% Book details