← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 127

Sashe 6

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hari tace tunda Yusuf ne ze sai ƙwan, ya biya kuɗin biyar, ta bashi biyar kyauta, amma bata yarda ya bawa Widad wanda ta bashi ba.

Widad tace "Hari dama kina ɗan dafa ƙwan nan kici, dase kinfi haka ƙiba da kyau, ke kullum cikin neman kuɗi kamar zakiyi ƙwace, kuma na rasa inda kike kai kuɗin"

Hararta Hari tayi taƙi ta kulata, aka ɗakko kwano za'a sakwa Widad ƙwai, Widad tace

"kuma idan kika samun ƙanana bana so, manya za'a bani dan nima ƙatuwa ce"

Haka Widad tasaka Hari a gaba, tana ta zolayarta ita kuwa Hari tunda Widad ta shaƙe Hanne take ɗan shakkarta.

Yusuf yace "Queen zan tafi"

Widad tace "ba zaka soyamin ƙwan ba zaka tafi?" tai maganar kamar wata ƙaramar yarinya tana sa hannu a gashin kanta.

Gwaggo ta sunkuyar da kai tana jin taɓara, Yusuf yace "ki bari in dawo"

Maimakon tayi magana se ta cuna baki tana kallonsa,

Yusuf yace "Shikenan Muje in soyamiki, amma nasan ba iya ci zaki yi yanzu ba, dan yanzu kika gama cin Abinci"

Gwaggo tace "Yusufa jeka abunka, za'a soya a bata kaji"

Widad ta cunkusa baki tace "Ni gaskiya Mama nasa nake so, naga kin fi son Yoseef dani, ni kowa baya sona"

Gwaggo tace "nina isa ince bana sonki, waceni niko nake sonkj, amma ina nema masa Alfarma, a ɗaga masa ƙafa tunda fita zeyi"

Widad tace "shikenan Allah ya temake ka, jeka seka dawo" tai maganar tare da kashe masa ido É—aya.

Hari tace  "A'uzubullahi wannan Yarinyar idan ka zauna a inda take seta karya maka alwala"

Dariya Yusuf yayi sukayi waje shida Saleh, Saleh yace "Salute to you Yusuf, babu wanda ya isa ya biyaka namijin ƙoƙarin nan da kake, kalli yarinyar da take rayuwa kamar wata halitta daban, me gudun jama'a da son rayuwar kaɗaici, amma ita ta sake a ƙauye haka take rayuwarta, cikin farin ciki fjye da wanda take a gidansu da yake da tarin arziki "

" Saleh, ai dama kuɗi dukiya ba sune kwanciyar hankali ba, farinciki zama cikin wanda suka damu da kai shine farinciki, mutanen wannan zamanin muke ganin in kana da kuɗi kana da komai, ka wuce baƙin ciki "

Saleh yace" tabbas hakane maganarka Yusuf, da fa tsakaninta da mutane kallon banza da hantara, amma yanzu kalli yadda ta sake da Gwaggo ta maida ta kamar wata kakarta"

Yusuf yace "sosai makuwa, akwai shaƙuwa a tsakaninsu, Gwaggo nada sauƙin kai, kuma tana janta a jiki, bata hantararta idan tayi mata wauta ko wani abu, shiyasa itama take sonta"

Saleh yace  "hakane, amma ya batun ciwon ta kuwa? Na taɓin hankali?"

Yusuf yace "ina doubting akan wannan ciwon da take dashi, ina da question mark akai, amma lokaci nake jira"

"Alhaji Musa, kaji wata maganar banza wai an saki Yaron nan Anwar"?

Alhaji Musa yace "haka nima labari ya isheni, ni kaina abun ya É—auremjn kai Munir, wane mara mutuncin ne haka, waye yayi wannan karambanin?"

Alhajj Munir yace "munyi waya da Bukar, yace ze bincika nima nasa a bincikamin amma har yanzu babu wani labari, an rasa waye yasa a sake shi, wai daga sama aka bada umarni"

Alhaji Musa yace "waye a saman ya bada umarni damu bamu sani ba? Ta yaya ana tuhumarsa da wannan babban laifin za'a sake shi, idan kuwa hakane to tabbas muna da abokan Adawa wanda suke mana zagon ƙasa akan lamarin nan"

Alhaji Haruna da tun É—azu bece uffan ba ya nisa yace "ni kaina gaba É—aya ya kulle, na rasa abunyi semun toshe nan se can ya buÉ—e, na rasa wane banzan ne yayi wannan aikin"

Alhaji Musa yace "tabbas akwai lauje cikin naÉ—i, yanzu abunda ze faru shine, zamu saurari Bukar muji me zece, lallai a binciki wanda yayi wannaan aika aikar, sannan a tabattar an kama yaron nan an maida shi"

"haka ma za'ayi, wannan shine abunda ya dace, akama shi harse an ga Daula"

Anwar yana zaune yana cin Abinci yace "Mumsy kin san wani abu kuwa?"

"A'a seka faÉ—a" ta bashi amsa

"wato bawa baya taɓa gane Allah subhanahu wata'ala yayi masa ni'ima, se yayinda wannan ni'imar ta gushe, kinga ko 'yancin kayi yawonka ɗin nan inda kaga dama, ba ƙaramar ni' ima bace, zama guri ɗaya bala'ine Mum, ga rashin gurin kwanciya me kyau, ba Abinci me kyau, wai danma nine fa wasu haka suke tagayyara a cikin gurin nan "

Hajiya Halima tace " Aini duk zance ya ƙare, tunda Allah ya fito min da kak, Se fatan Allah ya kiyaye gaba"

Anwar yace  "Ameen Mummy, ni yanzu fatana ubangiji Allah ya bayyana Daddy, yasa yana hannu nagari, dan na tsorata da abubuwan da suke faruwa"

Mummy tace "kai kam wannan dashi ya haife ka da an shiga uku, kai har yanzu baka shiga hankalinka ba, ba kaga masifar daka shiga saboda temako ba, still kai tunaninsa ka keyi"
. "Mummy ba zan taɓa iya dena tunaninsa ba, saboda gudunmuwarsa a rayuwar mu"

Wayar Anwar ce ta shiga ringing, ya ajiye spoon É—in da yake cin Abincin ya É—aga wayar yasa a kunnensa.

Lambar Bulama ce, bayan sun gaisa Bulama yace "Anwar ashe ka fito?"

Cike da ladabi Anwar yace "eh Daddy na fito"

"to Alhamdilillah, Allah ya kiyaye gaba inba damuwa ina son ganinka anan gida, zamuyi magana"

"to shikenan, Insha Allah idan nayi sallar la'asar zanzo"

Bulama yace "to babu laifi"

Anwar Ya ajiye wayar, Hajiya Halima tace "waye haka?"

"babansu Fahad ne, yace inaje yana son ganina"

"ba zaka ba" ta faÉ—a kanta tsaye.

"Mummy meyasa?"

"saboda haka naga dama, akanme zece kaje bayan ba irin sintirim da ba ba akan yasa baki a sake ka yaƙi"

Anwar yace "haba Mummy, kidinga yiwa mutane uzuri mana, a baya kinsha neman Alfarma yayi miki, dan wannan karon be miki ba be kamata ki manta baya ba, kiyi haƙuri i je i ji meze ce"

"shikenan tunda kace haka, amma ba dan haka ba Wallahi da bazaka ba"

"kiyi haƙuri, kar hakan yayi sanadiyyar lalacewar zumjncinku"

Da yamma Hindu tayi kwalliya itada su Hanne da ƙannensu zeuje biki, Widad na ganin Hindu tace "Masha Allah, you look so beautiful Hindatu, kina da kyau masha Allah"

Hindu tace "Rufani ki saya Amarya, ai daga kanku kyau ya ƙare, kina ganina baƙa kirin ina wani kyau yake?"

Widad tace  "waye yace miki baki da kyau? Ke nima fa ba wata kyakkyawa bace, dan dai ina da haske ne, amma baki ganki ba, kinyi kyau Allah ya baki miji nagari ɗan birni"

"hmm Amarya kenan, ni da ban taɓa zuwa birni ba, banyi boko ba ta ina ɗan birni ze ganni ya aura"

Widad tace "da ina da Yaya namiji zance ya aure ki Hindu, kina da kirki kaman Mama, wai ina zakune?"

"biki ne zamuje, a gangare"

Widad tace "laaa shine babu gayyata, ku jirani zan biku, dama ban taɓa fita waje ba"

Hindu tace "to ai Amarya baki da kaya irin Atamfa, duk kayanki ba irin namu bane, idan muka je seki zama abin kallo, kuma dama gaki ba kalarmu ba"

"se in saka hijjabi"

Gwaggo tace "A'a amarya bekamata ki fita ba, baki tambayi mijinki ba, se da yaddar sa sannan zaki fita"

"Mama baze ce komai bafa"

"dukda haka, kuda kukayi ilimi ma Amarya, ai kunfi mu sanin hukuncin hakan"

Hak Widad tana ji tana gani aka tafi biki aka barta a gidan.

Bata ji daÉ—in hanatan da Gwaggo tayi ba, sedai bata son yi mata musune.

Daf da la'asar Yusuf ya dawo, ya taho da kayan da Saleh ya bayar a siyo musu, seda Gwaggo ta kalli Widad sannan ta tashi, ta taya shi kai kayan É—aki.

Ya fito ya É—auki buta yana alwala, yace "Mama yau naga gidan shiru, ina mutan gidan ne?"

Gwaggo tace  "sun tafi biki, tace zata bisu nace karta je seta tambayeka, shine taƙi kulani"

Yusuf yayi dariya yace "babbar magana, faÉ—a tsakanin 'ya da uwa yau"

Widad tace "tunda nazo fa ban taɓa fita ba, kullum ina gida"

Yusuf yace  "idan kin fita Meza kiyi? Sarkin rigima"

"kaikuma kaji ka, Yoseef ka kiyayeni nice sarkin rigimar?"

Gwaggo tace "É—iyar albarka a dinga saya masa sunan mana, idan daga ke se shine seki faÉ—a, amma a gaban mutane mu nan abun kunyane mace ta dinga faÉ—an sunan mijinta kai tsaye"

Yusuf yace "yawwa gaya mata dai Gwaggo"

Cikin Shagwaɓa tace "to me zance masa?"

Gwaggo tace  "ki dai samo wani sunan mi dinga gaya masa, kafin Allah ya baku rabo, in kin haihu seki dinga cewa baban wane ko wance"

Haɗa ido sukayi da Yusuf, ga mamakinsa se yaga ta kwashe da dariya tace "taɓ sedai inya Auri Hanne ta haifa masa, amma ni babu wannan Kalamin, ai Yayana ne kai ko Yoseef?"

Tai maganar cikin sigar zolaya, tayi gaba ta bar tsakar gidan, Gwaggo ta zata kishine yake damunta, saboda tasan yadda basa shiri da Hanne, shi kuwa Yusuf, a wata cakwalkwalin cakwakiyar tunani ta kuma sashi, duk jikinsa yayi sanyi.

Bayan yayi sallar la'asar ya koma gida, ya tarar da Widad tana gyaran Akwati, ya kalleta yace "Queen waye yace miki zan Auri Hanne? Idan kuma Gwaggo ba taji daÉ—in abunda kika faÉ—a bafa?"

"Ai naga ita Hanne kaman she's having the same feelings on you, she also believes in love"

"Se kuma akace miki ni Aurenta zanyi?"

"to waye yasan muku? Ranar da zamu koma gida, idan ka sake ni base ka Aure ta ba, ka tafi da sabuwar Amaryarka ba"

Tsaki Yusuf yayi, saboda yaji haushi sosai, ya miƙe ya bar ɗakin, bin bayansa Widad tayi da kallo, ta taɓe baki ta cigaba da aiki ta.

Tunda ya fita be dawo gida ba se bayan sallar isha'i, sannan yaƙi kulata kwata kwata, dukda taji ba daɗin dena kulatan da yayi da yawan tsokanar ta da yake, yaji ba daɗi amma ta maze ta basar dashi itama, haka kowa ya kwanta be kula kowa ba.

Da Asuba ma da yayi salla, suka zauna zaman karatu seda gari ya fara haske sannan ya taho gidan, tun bayan da aka idar da sallar Asuba kafin a fara karatu, Saleh ya janyo Yusuf waje yace "Nifa zan koma, sammako zanyi in tafi tunda kaji sauƙi" .

Yusuf yace "da wuri haka Saleh?"
Chapter 6 · 0% Book details