← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 127

Sashe 35

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace "hakane, amma duk da haka yakamata ko gaisawa muyi, ina gaisheta amma ko kallo ban isheta ba"

Yusuf yace "Allah ya baka haƙuri, zata gyara insha Allah"

'hmmm Yusuf kenan, in dai wannan ce babu ranar gyarawa, baƙin da take magana kuma ba wasu bane, mata da miji ne, namijin shima ɗan megarine, matar ma kusan haka, ya tashi da' yan fitintunu ne baya ji, ga yawon tsiya se a shafe watanni uku huɗu, ba a ganshi ba, shine na ɗauke shi na kai shi makarantar horar da sojoji, to beyi karatun boko ba, dan haka kurtu ne yana barrack suna gadin gidan wani babban hafsin soja, shine yayi Aure ya tafi da matar, yanzuma ya samu hutun ƙarshen shekara ne, ga matar ta haihu shine muka haɗu a tasha sunzo gida, suyi hutunsu a nan amma banda haka babu wani abu, amma kai ɗan sanda ne ai, zaka iya bincikawa"

Yusuf yace "A'a babu buƙatar hakan, gara ta sanine ai, kasan bata da yadda"

"hakane amma ita nata yayi yawa ne"

"Hakane, amma ayi haƙuri dai, yanzu meye labari? Ya ake ciki a gida?"

Saleh ya ɗanyi shiru sannan yace  "Yusuf labari ba daɗi kama, sedai fatan ubangiji Allah ya shiga lamarin"

"Saleh, dan Allah kamin bayani gwari gwari mana, ban gane labari babu daÉ—i ba, aani abune ya samu Ummana? Ko mahaifin Widad? Ko kuma wata matsalarce ka gayamin mana"

Saleh yace "kwantar da hankalinka babu ɗaya, mahaifin Widad dai kamar yadda ka sani, har yanzun babu wanda yasan inda yake se Allah, ana ta bincike amma shiru, ko yana hannunsu, ko yana wani gurin Allah ne mafi sanin wannan, sannan mahaifiyarka tana lafiya, mun rabu da Suleiman akan zeje ya gaishe ta ma, sedai....... "  Se kuma yayi shiru.

" Se kuma me? Dan Allah ka gayamin kana É—agamin hankali fa"

"Yusuf jin meke faruwa bashi da wani amfani a gareka, abun da nake so da kai shine, kayi taka tsantsan gurin zuwa cin kasuwar nan da kake yi, sannan ka ƙara tsananta Addu'a, kuyi haƙuri kunci gaba da zama anan, dan sun saka a nemoku duk inda kuke"

Yusuf ya dafe kai yace  "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, yanzu meye abunyi? Zuwa yaushe ne zamanmu ze ƙare anan, kar mu takurawa mutan gidan, sannan kuma cigaban zamana da Widad a inuwar Aure shima matsala ne babba, babu wanda yasan batun Aure mukayi se kai"

Saleh yace  "batun takura, baku takura musu ba, dan munyi magana da megari, sannan Aurenku aini na san anyi, ina da sheda, kawai Allah yasa ku kawai Daula jika"

"Saleh, why are you not serious about this issue? Bafa abun wasa bane, wani irin kallo mahaifinta zemin, wani suna ze kirani dashi idan har muka koma gida da É—a?"

"Ahh kallon siriki ze maka mana, karka damu Daula ba baƙon zafi bane, idan har 'yarsa tana ƙaunarka, kaje ka tabattar da irin son da take maka tukuna, nidai fatana iya wuya, idan bani nazo nace kubar gurin nan ba, kuyi zamanku anan, ka koma maza karta fara zargin wani abu "

Har Yusuf ya shiga cikin gidan jikinsa a mace yake, gaba ɗaya ya easa meye yake masa daɗi, Saleh ya sake dagula masa lissafi, yanzu idan aka gano inda suke shida Widad meye sunansa? Idan ya kasance Widad ta samu juna biyu meye makomar yaron, sannan yayi mata adalci makuwa, idan har ya bari suka haɗa zuriya da ita, bayan bata san shi waye ba, ba tasan mecece tasa ƙaddarar ba balle yaji hukuncin da zata ɗauka akansa? Baya tunanin ɗorewar Alaƙa a tsakaninsu muddin taji waye shi, ba ita ba hatta mahaifinta baze farinciki ya zamo siriki a gareshi ba.

LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏

76_77

A haka Yusuf ya ƙarasa ɗakinsu, yana zuwa ya zauna yayi shiru ya zurafafa a cikin tunani.

"Meya gaya maka haka, wanda ya jefa ka cikin wannan dogon tunanin?" yaji muryar Widad.

"Bakomai" ya bata amsa

"Har yanzu fa ban canza daga Widad ɗin daka sani ba, bana son ƙarya bana son ɓoye ɓoye, ka gayamin tun kafin kaima in saka a Jerin wanda nake zargi"

Ya kalle ta yace  "zargin me kenan?"

"zargin zaku haɗa kai ku cutar dani, in ba haka ba, meye na ɓoyemin wasu abubuwan da dole nasan sun shafi rayuwata?"

Yusuf ya kalle ta yace  "har yanzu kina tunanin zan iya kasancewa cikin masu cutar dake?"

"Yoseef, zuciya bata da ƙashi ya kamata kamin uzuri, musamman a irin rayuwar da na tsinci kaina, amma ya kamata in dinga sanin al'amuran da suka shafeni"

"Ba wani abu bane, dama ya gayamin muƙara haƙuri da zama anan ne, saboda ana can ana nemanmu, maƙiyanki sun baza komar anemomu, tunda tuni labarin guduwarmu ya iskesu, sannan baƙon da suka zo tare, shima ɗan uwansane, soja ne sunzo hutune shida matarsa, shikenan "

Ba tayi magana ba, se riƙe gashin kanta da tayi, sekuma ta shiga jan numfashi tana zazzare ido, ta dunƙule hannunta, tana girgiza kai.

A Rikice Yusuf yace " Subhanallah, lafiyar ki kuwa Widad? Meyafaru? "

Girgiza kai take hawaye na zuba daga idonta tace " almost ten years, good ten years ana cutar dani, bani kaɗaiba har wanda ya raɓeni, yana ɗaya daga abunda ya nesanta ni daga mutane, bana son rayuwar wani ta shiga matsala saboda ni, amma ƙaddara ta haɗa rayuwarka da tawa kana ta faman wahala, an cutar dani an kassara lafiyata, an cigaba da bin diddigina ana son ganin bayana saboda abun duniya, kuma aka jefa ƙiyayyata a zukatan jama'a suka koma gefe suna zagin AƘIDATA, Insha Allah bazan mutu ba sena ga bayan maƙiyana, ko kuma mu yi mutuwar kasko nida su, i can't tolerate it anymore "

Tai maganar tana jifa da kayan gurin, sannan ta yunƙura zata miƙe, Yusuf ya riƙeta gama, fizge fizge ta dingayi tana kai masa duka tana nema ta ƙwace daga hannunsa, ya riƙeta sosai yana mata addu'a, surutai take sosai cikin ɗaga murya, idan Yusuf yasa hannu ya toshe mata baki, se taita kai masa duka, idan ya riƙe hannunta kuma seta hau surutai, yana gudun hankalin mutane ya dawo kansu, dan sam baya son wani yasan tana da larurar taɓin hankali, dan haka kawai ya haɗe bakinsa da nata.

Tun tana mimmiƙewa tana son ta ƙwace, harta gaji jikinta yayi sanyi, Numfashi take saukewa a hankali, hawaye na bin gefen idonta, seda yaga ta dena fizge fizgen sannan ya cire bakinsa daga nata, ta lumshe idonta kamar me bacci, Yusuf ya rungumeta yana cigaba da karanta mata duka Addu'ar da tazo bakinsa.

Widad ya kira sunanta, ɗaga masa hannu tayi alamar ya ƙyaleta, sun daɗe a haka sannan ta tashi zaune, Yusuf ya kalleta yace  "Sannu"

Jinjina masa kai kawai tayi ta sunkuyar da kai, ya riƙe hannayenta yace "dan Allah kidena saka damuwa a ranki, kinga hakan yana shafar lafiyarki"

"bazan iya dena damuwa ba, saboda an diga an gama kassara rayuwata, bana jin zan samu nutsuwa har se ranar da na gamsu, na É—au fansar abunda akayimin"

"Rayuwa ba zata tafi a haka ba, lafiyar ki abun dubawa ce, kalli yadda lokaci É—aya kika fita hayyacinki fa"

"Ai dama ba lafiyar ce dani ba, dan haka ba wani abu dan na ƙarasa a haka"

Kawai ta rufe bakinta da hannunta tana kuka, Yusuf ya shiga share mata hawayenta, yana cewa "ke lafiyayyiya ce, kuma ina miki fatan samun lafiya me É—orewa"

Tai murmushi me ciwo tace "wai in warke daga haukan? Ko ciwon zuciya?"

"Nifa ban yadda da wannan ciwon haukan ba"

Widad tace  "yakamata ka yadda, ka sawa ranka kana zaune da mahaukaciyane"

Yusuf ya ɗanyi shiru sannan yace "nifa akwai ranar da naga an saka miki wata ƙwaya a cikin tea, amma baki sha ba, shiyasa nake da question mark akan wannan ciwon naki"

Seda tayi shiru na wasu lokuta, sannan ta gyara zamanta tace  "Bayan an kashe Ammina, ɗaya daga cikin wannan mutanen, ya ɗakko wayarsa ya fara waya, yayi wayarsa ya gama sannan ya kalli sauran yace, ku cajemin gidan nan, akwai wata yarinya, ku kawomin ita nan, Widad na tsaye tana jinsu, bata ko motsa daga inda take ba, suka fito suka shiga bincike gidan nan, amma basu ga Widad ba, suka dawo sukace "mun caje ko ina a gidan nan bamu ga yarinyar nan ba"

Yace "ta yaya za kuce baku ganta ba, bayan tana cikin gidan nan?"

Suka haÉ—u har dashi suna dubawa, sun wuce ta inda Widad take yafi sau uku, amma Allah besa sun ganta ba.

Suka sauka ƙasa falo, babban ya sake kiran waya, ya sanar da wani cewar sun duba kaf basu ga Widad ba, kawai Widad ji tayi yace " An gama Oga.... "

Bata iya jin cikakken sunan daya faÉ—a ba, kamar taji dai dai kamar kuma ba daidai ba.

Babban yace  "kai mu tafi, Oga yace yasan yadda zeyi da ita, mu ɓace kafin a gane munzo"

Haka suka rankaya suka fita, cikin sanɗa Widad ta sakko daga kan benen, ta sakko falo taje ta leƙa taga, taga sunyi maganganu da Bala, sannan ya buɗe musu ƙofa suka fita.

Widad ta juya ta koma kan bene, ta koma É—akin da Amminta take cikin sauri, tana zuwa ta tarar da ita a yadda ta batta.

Widad ta shiga jijjigata tana kiran  "Ammi ki tashi mutanen sun tafi, baki ji ciwo bako?"

Ganin Ammin nata bata motasa ba yasa tace  "Ammina bacci kikayi ne? Ko kuma sanyi kike ji?"
Chapter 35 · 0% Book details