← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 127

Sashe 84

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Megari yace " Saleh ne ya kawomin su, yace garinsu faɗa akeyi, babu kwanciyar hankali an kashe iyayensu, shida ita 'yan uwane, amma ba ciki ɗaya ba, na wuce gaba aka ɗaura musu Aure saboda dai ai baka ƙi taimakon mutum ba, amma ni dai gaskiya ban yadda ace wai satota sukayi ba, dan lokacin da suka zo gidan nan, shi kamsa Yusuf ɗin kamar a galabaice yake bashi da lafiya, zaka ce daga gurin da ake yaƙi suke '

Sunusi yace "Amma abun da mamaki gaskiya"

Hindu tace  "kuma da kaje babu wanda ka gani a cikinsu, daga Amarya har mijin nata?"

Sunusi yace "ke, case É—infa babba ne, yafi gaban yadda kike tunani, kedai kiyi ta addu'a kawai"

Hindu tace "Allah sarki' yar uwata, gaskiya na tausaya mata, ashe 'yar gidan attajirai ce amma tazo tai rayuwa a wannan ƙauyen namu? Kuma taita binmu tana lallaɓamu mu koya mata abu, kuma da alama mijinta kawai ake nema, da akazo kamasu tambayarta suke yana ina"

Megari yace "koma dai yane, ubangiji Allah ya kuɓutar dasu"

Haka suka cigaba da tattaunawa suna salallami.

Aka buɗe ƙofar ɗakin da Widad ke ciki aka shigo, ko ba'a faɗa ba tasan waye ya shigo ɗakin, dan haka ko ɗaga kai batayi ta kalleshi ba, ta maida hankalinta ga wani gurin, ya ƙaraso ya zauna a gabanta yana ƙare mata kallo, still bata motsa ba balle ta ɗaga kanta ta kalleshi.

"koki kalli inda nake, ko karki kalla yin biyayya ga dukkanin umarnina ya zame miki dole a yanzu, tunda shine last option ɗinki, tunda kika riga kika gano waye Bukar, zan gwada miki aikinsa a aikace, ranar Litinin za'a kai wancan sakaram da kike iƙrarin mijinki ns kotu, kuma na ɗau dukkan wasu matakai dana san zasuyi amfani sena tura shi gidan yari ya ƙare rayuwarsa a can, babanki kuwa koma ina ya tafi ya tafi kenan, har Abada har gaba da Abada baze dawo ba, dama burina kenan in ɗaiɗai ta farincikin sa"

Widad dai bata motsa ba balle tayi magana, tai shiru ta cigaba da kallon waje É—aya.

Ya cigaba da cewa "ki temaki kanki tun baki makara ba, ki bani takaddun da ubanki ya ware, yace wai dukiyar akwai me ita, duk wanda yasa hannu akan takaddun nasane suna ina?"

"Idan ubaka ne ya tara masa seka sa in baka, bazan bayar ba nayu Alƙawarin me ita zan bawa, kuma na riga na miƙasu ga masu ita"

"Niki ke gayawa haka?"

"Na gaya maka É—in, tsakanin wuta da aljanna wacce kake da ita, balle ka sani? An faÉ—a maka É—in kayi abunda zakayi karka fasa"

"Ina binki sannu sannu ne, saboda har yanzu akwai ɓurɓushin imani a raina, mahaifinki yamin ranar dabe yiwa wani a rayuwa ba, sannan dukiyar ki ce dalilin tsayawar kasuwancina da ƙafafunsa shiyasa nake son in kamanta miki adalci, ina takaddun suke? Ki gayamin cikin ruwan sanyi tun ban saɓa miki ba, kokuma na gwada miki"

"Ban sani ba!" ta faÉ—a cikin shouting,

"Idan kana so ka kashe ni hankalinka ya kwanta, kuma zalunci indai nakane wanne ne ban gani ba, ai babu irin wanda baka gwadamin ba, ko zaka gutststura naman jikina, bazan baka ba"
ai kuwa ya kifa mata mari, abun da ba'a taɓa yi mata ba a rayuwar ta, dan seda bakinta ya fashe.

"Wallahi ko kina so, koba kya so sekin bani kuma ba kimin wannan raunin a banza ba se na É—au mataki a kanki"
"bazan bayarba, Amana ce kuma na danƙata a hannun masu ita suna rayuwarsu, me kake so inyi maka? Ko me zance maka?"

"ƙarya ki keyi, baki danƙata a hannun kowa ba, ki gayamin ina suke" yai maganar cikin tsawa.

Banza tayi masa, taƙi magana ta shiga goge jinin da bakinta yake yi, ai kuwa taji saukar tio a jikinta, tunda Widad take ba'a taɓa dukanta da abu me zafim wannan ba, bayan wanda aka mata da bakin bindiga, ta banƙare ta ƙwala ihu, take fatar jikinta ta tashi tai jawur kamar an ƙonata.
Tana zubar da hawaye tana girgiza kai, ji take kamar an saka mata wuta a bayanta, saboda azabar bala'i, ya sake zage ƙarfinsa ya shiga zuba mata, tun tana iya ihu harta kasa, se nishi da take yi yasa ƙafarsa da babu ciwon yai ball da ita, ai dukan da yayi mata be mata ciwo ba, kamar yadda yai ball da ita da ƙafarsa, ya ƙaraso inda take yana huci yace  

  "zaki gayamin ko bazaki faɗaba"

Ta ɗaga jajayen idanunta tana kallansa, ta shammaceshi ta kafa masa faratanta a inda aka masa ɗinkin nan a cinya, dayake naɗe ƙafar wandon yake, saboda karya sosai masa ciwon yaƙi warkewa.

Aikuwa haka ya buɗe baki ya ƙwala ihu shima, dan har jini gurin ya fara, ta janyo wuƙar nan da ta ji masa ciwo da ita akan taga, tace "wallahi idan baka fita daga gurin nan ba kashe ka zanyi, sena kashe ka wallahi '

Tuna yadda ya sha yanka da wuƙa ne wancan lokacin yasa shi fita da sauri yana faɗin  " dawowata ta biyu bazata miki daɗi ba, zaya kasance dawowa me muni a gare ki "

Ya fita hannun sa riƙe da cinyarsa, tana masa wani irin zugi, har yanzu Widad ba tayi laushi ba, halinta be canza ba na baƙar zuciya da taurin kai na jaraba, gashi dukda dukan databsha da rashin lafiyar da take ciki, be hana ta fama masa ciwon nan ba, dan gashi har ya fara tstatsafo da jini, ta fama masa yai ƙwafa ya fita yana tunanin yadda zewa Widad izaya irin wadda ba'a taɓa yi mata ba, wadda zata tirsasata yin abunda yake so.

Ita kuwa Widad zama tayi tana kuka, saboda azabar raɗaɗin da jikinta ke mata saboda dukan da ta sha da tio, jikinta duk yayi tsami, tai kuka tai kuka harta fara tari daga nan kuma se Amai, gashi ba komai a cikin nata, dan baka ta dinga yunƙuri amma babu abunda yake fita, se miyau ga ɗaci da maƙogwaronta yake, se kuma ta shiga aman jini, haka ta dinga kakarin aman nan gwanin ban tausayi, abun da bata saba ba ya sameta, taji ba abunda take so banda ta samu ƙanƙara ta matsa lemon tsami ta sha ba.

Tan nan ta kwanta akan tiles, tana jin yadda sanyin ke ratsata, jikinta kuma yana É—aukar zafi.

A hankali aka turo ƙofar ɗakin nata, ta tashi zumbur dan zatonta Bulama ne, wannan me aikince ta shigo cikin sanɗa, taga Widad a mawiyacin hali, dan tana jiyo kakarinta tun ɗazu.

Widad zata yi magana tai sauri ta girgiza mata kai, cikin ƙasa da murya tace  "karki ɗaga murya mana, kinga Alhaji Bukar yace kar a kuma baki Abinci se sau ɗaya a rana, ya gindaya mugayen sharuɗa akanki, ni kuma ina jin tausayinki zan ɗan temaka mikine, ga Abinci na kawo miki kici"

Widad tace "bana ci, ki bani ruwa me sanyi sosai, ki bani in sha"

"A'a, kici Abinci mana, cikinki bakomai ga jikinki ya É—au zafi sosai ki daure"

Ta tirsasa Widad yaci Abincin kaɗan, ta bata ruwan sanyi kamar yadda ta buƙata, sannan tai mata sallama ta fita.

Widad ta koma kan tiles É—in nan tayi kwanciyarta, fatar jikinta duk jini ya kwanta akan fatar ta, ta lumshe idonta ga sanyin A. C gana tiles haka tai kwanciyar ta abunta.

Umma jikinta sauƙi an sallameta daga Asibiti, sedai jikin nata ya kasa ƙwari, saboda tsabar damuwa da tashin hankali da take ciki, ta rame sosai tayi zuru zuru duk ta fita daga hayyacinta, bata iya cin Abinci sam sedai abunda ba'a rasa ba, kullum tana cikin Addu'a ne, dan da kanta taje ganin Yusuf amma aka hanata ganinsa, haka ta dawo gwiwa a saɓule.
Tana zaune ta idar da sallar la'asar, tana lazimi idonta duk yayi ja saboda rashin bacci, sallama taji anyi ta amsa sedai kafin ta bada izinin shigowa Suka shigo É—akin gaba É—aya, ta É—aga kai ta kallesu tace "Sannunku da zuwa Anty Asma'u"

"A'a riƙe sannu da zuwanki, zuwa mukayi muyi kallo sannan mu jajanta, yau dai kinga maganar da muke tayi tun shekarun baya, tsintacciyar mage bata mage, yau dai shege ya ɗakko miki magana, dama ina shege zeyi wani abun arziki, kina ta wahala kika saka ɗan uwanmu yaita wahala daku, ke juya shi kuma shege yau dak gashi ƙarshen Alawa ƙasa, ya zama gagarumin ɗan ta'adda ya sace 'ya yaje yai mata fyaɗe yana neman kuɗin fansa, Allah wadaran naka ya lalace "

Balaraba tace " Ameen dai Anty, alhakinmu ne ya kama su, da tasa ɗan uwanmu ya dinga wahala dasu, yana wulaƙantamu yau gashi kina kuka da idonki, kuka kam yanzu kika farashi, saura ke se sunzo sun haɗa ke dashi tukuna, tunda idan ya samo tare kuke ci"

Suka dinga zazzage mata rashin mutunci iri iri, ta inda suka shiha ba ta nan suke fita ba, Umma ba tace musu komai ba ta sunkuyar da kai kawai, ta cigaba da jan carbinta na tare da ta kulasu ba.

Suka yi suka gama san ransu, sannan suka tafi Umma ta girgiza kai kawai, tana share hawaye.

"Khalil ya ake cikine? Ka samu ganin Widad É—in kuwa?"

Khalil yace "Nurat, ban samu ganin Widad ba, bata gidan Alhaji Bulama ance wai bata da lafiya an kaita Asibiti, amma É—an nasa be gayamin ina take ba, wai shima be sani ba, nace masa zan kuma komawa inji abunda ake ciki"

Nurat tace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Yaya Khalil an kusa shiga kotu fa, Allah yasa dai a gano ta, na damu sosai dan Allah ka koma da wuri kaji"

"Shikenan insha Allah, karki damu zan koma inga yadda zamu yi dashi"

Alhaji Haruna ya kira layin Amal ba adadi amma taƙi shiga, ya rasa me yarinyar nan tayi masa ranar da tazo, ta barshi a yashe, yana ta tunanin ne kiran Alhaji Musa ya shigo wayarsa ji a sanyaye ya ɗaga.
Chapter 84 · 0% Book details