← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 127

Sashe 112

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khalil yace "karka damu Yusuf, dama haka Allah ya ƙaddara seya faru, ba kaine sila ba, Allah ya riga ya rubuta hakan dama, sedai kam tabbas tayi faɗi tashi a kanka sosai, tun daga ɓatanku har wannan lokacin"

Umma tace  "mungode, mungode Allah ya saka miki da alkhairi, Allah yayi miki Albarka ya jiƙan mahaifiyarki"

Nurat ta dinga jinjina kai, tana tuno Mummynta, ta kalli Yusuf tace  "Kasan kuwa an kashe Yaya Anwar?"

A razane Yusuf ya kalleta yace  "wane Anwar ɗin wai?"

Ta goge Hawaye tace  "Bayan ɓatanku, Daddyn Widad faɗuwa yayi, ya fara rashin lafiya babu kowa a gurinsa babu me zuwa gurinsa , Anwar ne kawai yake gurinsa, ya dinga jinyarsa tsawon lokaci, bayan wani lokaci aka sace Daddyn Widad a Asibiti, aka kama Anwar ya daɗe a tsare ya sha wahala sosai kafin ya kuɓuta, to kwanan nan dai Brother ya cemin ai Ya bar letter a gida, ya bar gidan gaba ɗaya ba'asan inda yake ba, ranar da aka gama shari'arka akace an kashe shi kuma ana zargin Bulama ne yasaka "
. Umma ta dafe kai tana faÉ—in innalillahi wa inna ialaihi raji'un, yayin da Nurat ta sake fashewa da kuka.

Khalil yace  "se haƙuri, da kuma mu taya su da Addu'a, Wannan me aikin gidan ne Murtalah, ya tsinto takaddar, ban san ya'akayi yai kyan kai ya kaiwa Barrister Hafiz ba, dan abun zamana yayi duk wanda yai wani yinƙuri na temakawa a gano gaskiyar lamarin, se an bishi da mummunar barazana, mutumin nan maƙurane gurin zalunci"

Umma tai shiru tana hawaye, tana jinjinawa zaluncin Bukar, musamman Da taji wai ashe Anwar É—ane a gurinsa.

Nurat ta kira Yayar mahaifiyarta suka gaisa da Umma, sun daÉ—e suna hira suna jajantawa juna, yayin da Suleiman da Khalil ke hira.

Nurat tai shiru a gefe, tana kuka Yusuf yai ƙasa da muryarsa cike da tausayinta yace  "Light am very sorry, kiyi haƙuri da ƙaddarar data same ki a sanadina dan Allah"

'Nifa ba kaine silar faruwar haka a gareni ba, dama Allah ya ƙaddaramin haka zata faru dani ne "

" Bazaki dinga kallona da abunda ya faru ba, koki zargi saboda ni haka ta sameki ba? "

Ta jinjina masa kai alamar eh, Yusuf yace " Nagode sosai, Allah ya jiƙan Mummy ".

Nurat tace " Ameen, naji ance an kaika Asibiti ya jiki kuma? "

Yusuf yace " jiki Alhamdilillah, mungode Allah "

" Allah ya kiyaye gaba, se nazo maka jaje "

Yusuf yace "A'a ni yakamata in sake dawowa in dubaki in sake miki ta'aziyya, Allah ya baki haƙurin jure rashin Mahaifiyarki"

Ta jinjina masa kai tana kuka, gaba ɗaya tausayinta ya kama shi sosai, ya cigaba da rarrashinta, Umma ta fito ta tarar dasu tace  "mu tafi ne ka taho kokuwa?"

Yusuf yace "A'a tare zamu tafi"

Ya miƙe Nurat ta rakosu har bakin mota, Yusuf yana ta sake bata haƙuri yana mata gaisuwa.

Suna tafe a motar, Yusuf yayi shiru yana tausayin Nurat, ga mutuwar Anwar data gigita shi, ga yana son ganin Widad.

Can yaji Umma tace  "gaskiya Yarinyar nan tana da nutsuwa da tarbiyya, na yaba da hankalinta gashi ta bani tausayi Yusuf, nikam ko zaka nemi Aurenta idan zasu baka?"

AMANA! AMANA! AMANACE!!! IDAN KIN FITAR ALLAH NA KALLONKI

AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

154_155

Gaban Yusuf yai mummunar faɗuwa jin abunda Umma tace, ya kalli Ummansa ta Mirror, amma yai shiru yaƙi cewa komai sema ɗauke kansa da yayi yana kallon waje.

Umma tace  "ya Kay shiru ba kace komai ba?"

Ƙin magana yayi, dan bayama son zancen, Umma tace  "Suleiman, dan Allah baka yaba da hankalin Nurat ba? Yarinyar tana da nutsuwa da kuma kirki sosai"

Suleiman yace "tabbas hakane Umma, ni kaina na yaba da nutsuwar ta, kuma da alama dai Yusuf akwai dalilin da yasa ta dage ta temake ka"

Umma tace  "jimin yaro da wulaƙanci, ana masa magana yayi shiru, kamar ba dashi ake ba"

Yusuf yace "Umma me zance ne? Nifa ina da Aure ya zanyi da Widad kuma?"

"Karka ƙaramin zancen wannan yarinyar, wadda bata san halcci ba bata san abun alkhairi ba, kai ko zuciya baka da ita, duk wannan abunda ya sameka sanadinka baze zame maka darasi ba Yusuf, irin wahalar da ka sha, ba kai kaɗai ba harni kaina da sauran mutane, amma kake ƙara nanata wai kana da Aure, toni ban san da wannan Auren ba, ba wani Aure da kake da shi, ni dai ga yarinyar da ta kwantamin"

Yusuf yace "Umma, Widad bazata bada sheda haka kurum ba, akwai wani dal.....

" Rufemin baki, bana son jin zancen yarinyar nan gaba É—aya, na gaya maka "

Yusuf yai shiru, ya maida idonsa wajen window, yana tunanin yaze da Umma akan Widad, gashi yana son ya haɗu da ita yana son su gana, amma Umma tana nema ta ɓata komai, kuma yaga alamar idan ya matsa, ze ɓata mata rai, shi kuma babban abunda baya so kenan, ɓacin ranta.

Haka Umma da Suleiman suka cigaba da hira har sukaje gida, ba tare da Yusuf ya tofa ta bakinsa ba, yai shiru dan bema san me suke cewa ba.

Suna zuwa gida Yusuf yaiwa Suleiman sallama ya shige gida abunsa, Umma kuma seda tayi sallama da Suleiman sannan ta shiga gida.

Widad kam sosai take jin mutuwar Anwar, ji take kamar mutuwar Anwar wani babban giɓine a gareta, dukda ba ɗan uwanta ne na jini ba, amma Anwar zuciyarsa ba irin ta mahaifiyarsa bace ba.
Tai kuka, tai kuka ƙarshe taje tai alwala ta tada salla mussman dan taiwa wanda ta rasa addu'a, ƙarshe ta ɗaga hannu zata yi Addu'a, ta kasa roƙar komai kawai ta fashe da kuka, "Allah ka yafemin laifukana, Allah na tuba ka yafeni, Ba Ammina, ba Daddyna, Ba Yaya Anwar, wanda nake sa ran zeji ƙaina maƙiya sun sa na masa abunda bazan sake kima a idonsa ba, ban san dangin mahaifina ba ban san na mahaifiyata ba, bani da wanda zan kalla a rayuwata inji sanyi, babu me raɓata babu wanda zan raɓa, Allah ka kawomin ɗauki "
Ta ƙarasa maganar tana rirriƙe gado da gefenta tana wani irin kuka me raunata zuciya, idanunta sukayi jawur ta fita hayyacin ta, ta rasa abunda yake mata daɗi, gashi har yanzu da tsoron mutane a ranta, tana jin tsoron raɓar wani, bata san meza'a kuma yi mata na cutarwa ba, ta fara tunanin ko ƙauye zata koma gurin Gwaggo?
Wata zuciya tace "suwaye a gareki? Suba danginki ba, wane karɓa zasuyi miki bayan suna zaune an tayar musu da hankali, hadda 'yan sanda ta yaya zasu sake karɓarki? Idanma zasu karɓekin kin san hanyar da za' abi aje a garin? '
Lumshe idinta tayi, hawaye na zuba daga idonta, tana jin yadda take sauke numfashi da ƙyar, alamun zuciyarta bata aiki yadda yakamata.
Ta takure a jikin bango, ta haɗa kai da gwiwarta, tana ci gaba da kuka, sanyin AC dake ratsata taji sanyin da take ji yayi mata yawa, nan da nan jikinta ya ɗau rawa, ta dinga rawar sanyi, kanta na wani irin sarawa amma ta kasa motsawa daga inda takey, ƙarshe ma ta haka ta kwanta a gurin, tana jin cikinta na motsawa, ta tuna Yusuf be san da cikin bama, ta shafa cikin a hankali tana tausayawa abunda ke cikin nata.

Amal ta ɗan farfaɗo, sedai befi tayi magana kaɗan a rana ba, bata magana sam seda ƙyar, gaba ɗaya ta ɗashe ta bushe saboda azabar bleeding da tayi, ga fargaba da tashin hankali da take ciki na kama Mummynsu, ga mutuwar Anwar da damfarar ta kuɗin nan da akayi, gashi har yanzu raɗaɗin fyaɗen da Alhaji Haruna ya mata yakasa barin Ƙwaƙwalwarta, dan haka abun ya mata yawa, ta samu depression, Ramlah ce ke kula da Ita take jinyarta, taga abun nata bana ƙare bane, ta ɗauketa ta kaita Asibiti.

Likita ya dubata, ya rubuta musu teses, ta kaita lap akayimata, suka kaiwa Likitan, ya karɓa ya duba ya kalli Amal yace  "ƙanwata, gayamin tsakaninki da Allah ƙanwata meyasameki kike bleeding haka?"

Amal ta kalli Likitan, ta sunkuyar da kai se hawaye, Ramlah tace  "doctor, ba lallai tayi maka magana ba, saboda tunda akayi mana rasuwa batavda sukuni, bata magana se kaɗan kaɗan, Fyaɗe akayi mata, harta samu ciki, shine taje ta zubar da cikin jini ya ɓalle mata yaƙi tsayawa"

Likitan yace "waye yayi mata fyaÉ—en?"

"Wani mutum ne" Ramlaj ta bashi amsa.

Yace "kuma an kai shi gaban hukuma da yayi mata fyaÉ—en?"

Ramlah tace  "doctor, bamu da wannan lokacin yanzu ma baka san da yadda na kawota ba, kawai ai mata abunda ya dace"

"Amma kun san illar dake tattare da ayiwa mace fyaɗe aja baki ayi shiru ba tare da ɗaukaf mataki ba, ba hujja bace a ɓoye irin wannan lamarin dan gudun jin kunyar mutane, ki tsaya ki ƙwaci haƙƙinki shine yakamata, yanzu yaushe abun ya faru? Kuma da ya faru an kaita Asibiti an mata gwaje gwaje ne? "

Ramlah tace " dan Allah ke dena wannan tambayoyin, kawai ka rubuta mata magani a wuce gurin "
Chapter 112 · 0% Book details